An ɗauko wannan jadawalin sunayen abincin Hausawa ne daga littafin Cimakar Hausawa. Wannan littafi yana ɗauke da nau’ukan Ababan ci da na sha waɗanda Hausawa ke ta’ammuli da su guda ɗari biyu da casa’in da uku (293).

           

Abinci

Rukuni

Kayan Haɗi

1.        

A wara Waken Suya/ Ƙwai da Ƙwai

Awara

Waken suya, Tarugu, Tattasai, Albasa, Man gyaɗa, Ruwan Tsami, Kabbeji, Karas, Ruwa.

2.        

Abarba Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

3.        

Aduwa

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

4.        

Aful

‘Ya ‘yan itattuwa

Kai tsaye za a sha shi.

5.        

Agwaluma Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

6.        

Alaleɓa

Ƙwalama 

Fulawa, Tarugu, Tattasai, Albasa, Magi, Mai, Gishiri, Ƙwai, Ruwa.

7.        

Alale Mai Ganye

Alale

Wake, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Ganye, Magi, Kayan yaji, Gishiri, Ruwa

8.        

Alale Mai Kayan Ciki

Alale

Wake, Tarugu, Tattasai, Albasa, Kayan ciki, Mai, Magi, Kayan yaji, Gishiri, Ruwa.

9.        

Alale Mai Ƙwai A Tsakiya

Alale

Wake, Ƙwai, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

10.    

Alale Mai Miya

Alale

Wake, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Albasa, Alayyafu, Mai, Kayan ciki, Magi, Kayan yaji, Gishiri, Ruwa.

11.    

Alalen Ƙwai Da Kifi

Alale

Wake, Ƙwai, Kifi, Albasa, Tarugu, Man gyaɗa, Magi, Gishiri, Curry, Kayan Ƙamshi, Ruwa.

12.    

Alalen Wake

Alale

Wake, Kabbeji, Hanta, Albasa, Tattasai, Tarugu, Kifi, Gishiri, Kayan Ƙamshi, Main gyaɗa, Ruwa.

13.    

Alewar Gyaɗa

Ƙwalama

Gyaɗa, Suga.

14.    

Alewar Madara

Ƙwalama 

Madara kwata, Suga, Kwakwa, Flaɓour, Ruwa 

15.    

Alewar Madara (Tuwon madara)

Ƙwalama

Madara Kwata, Suga, Ruwa.

16.    

Alkaki 

Alkaki

Alkama, Suga, Fulawa, Yeast ko Nono mai tsami, Ruwa.

17.    

AlƘubus

AlƘubus

Fulawa, Yeast, Bakin foda, Gishiri, Suga, Ruwa.

18.    

Amala

Tuwo 

Kwalfar Doya, Kanwa, Ruwa.

19.    

Aya Ɗanya 

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

20.    

Ayaba Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

21.    

Ayah Busassa

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci ta

22.    

Baba Dogo

Ƙwalama

 Gyaaɗa, Suga, Tsamiya.

23.    

Bado Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci shi

24.    

Burabusko

Dambu

Shinkafa, Attarugu, Albasa, Mai, Curry, Ruwa.

25.    

Burabusko Wasa-Wasa

Wasa-Wasa

Burabusko, Gishiri, Ruwa.

26.    

Ɓalbalo

Ƙwalama

Kwakwa, Suga, Lemon Tsami.

27.    

Ɓulla

Tuwo 

Gero, Dawa, Masara, Maiwa, Ruwa.

28.    

Cin-Cin

Cin-Cin

Fulawa, Ƙwai, Bakin foda, Bota, Madara ta gari, Yeast, Sikarai, Ruwa

29.    

Dabino 

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci shi

30.    

Dafa Duka

Dafa Duka

Shinkafa, Wake, Taliya, Makaroni, Doya, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Kabbeji, Karas, Albasa, Alayyafu, Kayan yaji, Mai, Nama Kaza ko Nama ko Kifi, Ruwa.

31.    

Dafa Dukan Dafaffen Ƙwai Da Tattasai Ɗanye

Dafa Duka

Ƙwai, Tumatur, Tattasai ɗanye, Tarugu, Albasa, Ganye, Magi, Kayan yaji, Mai, Ruwa.

32.    

Dafa Duka Dankalin Hausa Da Kabeji

Dafa Duka

Dankalin Hausa, Kabbeji, Nama, Magi, Albasa, Gishiri, Tattasai, Tarugu, Ɗanya hakin tattasai, Mai, Ruwa.

33.    

Dafa Dukan Dankalin Turawa Da Ƙwai

Dafa Duka

Dankalin Turawa, Ƙwai, Kayan ciki, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Magi, Curry, Gishiri, Kayan yaji, Ruwa.

34.    

Dafa Dukna Dankalin Turawa Da Taliya

Dafa Duka

Dankali, Taliya, Nama, Tarugu, Tumatur, Tattasai, Alayyafu, Albasa, Kayan yaji, Mai, Ruwa.

35.    

Dafa Dukan Indomie

Dafa Duka

Indomie, Zogale, Tattasai, Tarugu, Albasa, Magi, Ƙwai, Nama, Mai, Kayan yaji, Ruwa.

36.    

Dafa Dukan Kuskus Da Wake.

Dafa Duka

Kuskus, Wake, Nama, Tattasai, Tarugu, Magi, Gishiri, Albasa, Mai, Alayyafu, Ruwa.

37.    

Dafa Dukan Makaroni Da Kabbeji

Dafa Duka

Makaroni, Kabbeji, Karas, Kukumba, Tarugu, Tattasai, Tumatur, Albasa, Kayan yaji, Magi, Mai, Gishiri, Curry, Nama, Ruwa.

38.    

Dafa Dukan Shinkafa

Dafa Duka

Shankafa, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Gishiri, Magi, Kayan yaji, Ruwa.

39.    

Dafa Dukan Shinkafa Da Alayyafu ko Zogale

Dafa Duka

Shankafa, Alayyafu, Zogale, Ganda, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Kayan yaji, Magi, Gishiri, Ruwa.

40.    

Dafa Dukan Shinkafa Da Taliya.

Dafa Duka

Shankafa, Taliya, Tattasai, Tarugu, Tumatur, Albasa, Nama, Mai, Magi, Gishiri, Kayan yaji, Ruwa.

41.    

Dafa Dukan Shankafa Da Wake

Dafa Duka

Shankafa, Wake, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Albasa, Kayan yaji, Kaya ciki, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

42.    

Dafa Dukan Soyayyar Shinkafa

Dafa Duka

Shankafa, Nama, Hanta ko Ƙoda, Wake ɗanyen haki, Tattasai ɗanyen haki, Karas, Kabbeji, Albasa, Tarugu, Magi, Gishiri, Curry, Mai, Ruwa.

43.    

Dafa Dukan Wake Da Taliya

Dafa Duka

Wake, Taliya, Zogale, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Albasa, Kayan yaji, Magi, Gishiri, Ruwa.

44.    

 Wasa-Wasar Dambu

Wasa-Wasa

Ɓarzazjiyar Masara ko Shankafa, Ruwa

45.    

Dambun Acca

Dambu

Kifi, Tattasai, Tarugu, Albasa, Karas, Kabbeji, Mai, Magi, Curry, Kayan Ƙanshi, Ruwa.

46.    

Dambun Alkama

Dambu

Alkama, Tattasai, Tarugu, Albasa, Kabbeji, Karas, Magi, Kayan, Ƙamshi, Mai, Ruwa.

47.    

Dambun Dankali

Dambu

Dankali, Tattasai, Tarugu, Gishiri, Magi, Kori, Albasa, Ruwa.

48.    

Dambun Gero

Dambu 

Gero, Tonka, Rama ko Zogale, Albasa, Mai, Magi, Kanwa, Ƙuli-Ƙuli, Ruwa.

49.    

Dambun Kuskus

Dambu

Kuskus, Nama, Tattasai, Tarugu, Alayyafu, Albasa, Karas, Mai, Curry, Magi, Kayan Ƙamshi, Ruwa.

50.    

Dambun Masara

Dambu

Masara, Alayyafu, Magi, Gishiri, Mai, Ƙuli-Ƙuli, Tonka, Albasa, Gyaɗa, Ruwa.

51.    

Dambun Nama

Nama

Nama, Albasa, Tarugu, Magi, Gishiri, Kyan yaji, Ruwa.

52.    

Dambun Shinkafa

Dambu

Shinkafa, Zogale, Albasa, Tattasai, Tarrugu, Magi, Gishiri, Mai, Kayan yaji, Tafarnuwa, Kabbeji, Karas, Nama, ko Kayan Ciki, Ruwa.

53.    

Dambun Tsakin Masara

Dambu

Masara, Sure, Mai, Magi, Gishiri, Ƙuli-Ƙuli, Albasa, Tonka, Gyaɗa, Ruwa.

54.    

Dankali Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Gishiri, Ruwa.

55.    

DaƘuwa Aya

Ƙwalama

Suga, Gishiri.

56.    

 Wasa-Wasar Dawa

Dafa Duka

Dawa, Gishiri, Ruwa.

57.    

Diɓila 

Diɓila

Fulawa, Yeast, Suga, Mai, Ruwa.

58.    

Durumi

‘Ya’yan itatuwa

Kai tasye za a sha shi

59.    

Ɗan Furut

‘Ya’yan itattuwa

 

Kai tsaye ake cin sa.

60.    

Ɗan Madaro

Ƙwalama

Madara, Mai.

61.    

Ɗan malele ko A ci da mai ko Ɗan shanana.

Ɗan Malele

Garin Masara, Gishiri, Magi, Mai, Tonka, Albasa, Ruwa.

62.    

Ɗan ta Matsitsi

Ƙwalama

Garin Ƙwame, Suga, Garura.

63.    

Ɗan Wake

Ɗan wake

Wake, Rogo, Dawa, Kuka, Kanwa, Gishiri, Ƙwai, Kayan Lambu, Ruwa.

64.    

Ɗunya

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

65.    

Fanke

Fanke

Fulawa, Madara, Suga, Bakin foda, Ƙwai, Bota.

66.    

Farfesun Bindin Naman Sa

Nama

Bindi, Kayan yaji, Tafarnuwa, Tattasai, Tarugu, Albasa, Gyaɗa, Magi, Kori, Gishiri, Ruwa.

67.    

Farfesun Kan Rago ko Naman Sa ko Naman Akuya

Namaa

Kan Rago, Albasa, Tumatur, Kayan Ƙamshi, Tattasai, Tarugu, Magi, Kori, Gishiri, Mai

 Ruwa.

68.    

Farfesun Kayan Ciki

Nama

Kayan ciki, Tattasai, Tarugu, Albasa, Kayan yaji, Tafarnuwa, Zogale, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

69.    

Farfesun Kaza

Nama

Kaza, Mai, Tattasai, Tarugu, Tumatur, Albasa, Kayan yaji, Tafarnuwa, Magi, Kori, Gishiri, Ruwa, Alayyafu.

70.    

Farfesun Kifi

Nama

Kifi, Citta, Tarugu, Tattasai, Albasa, Kanunfar,

Tafarnuwa, BaƘin yaji, Magi, Kori, Thyme, Gishiri, Daddawa. Ruwa.

71.    

Farfesun Kifi da Kayan Lambu

Nama

Kifi, Kayan miya, Albasa, Koren tattasai, Mai, Citta, Tafarnuwa, Ruwa.

72.    

Farfesun Nama

Nama

Nama, Kayan yaji, Tafarnuwa, Tarugu, Albasa, Tattasai, Gishiri, Kanamfari, Curry, Main gyaɗa, Ruwa.

73.    

Farfesun Nama Da Ƙasan Rago

Nama

Nama da Ƙasan Rago, Dadddawa, Kayan yaji, Tattasai, Tarugu, Albasa, Tumatur, Curry, Thyme, Magi, Gishiri, Mai, Ruwa.

74.    

Faten Acca

Fate

Acca, Tarugu, Tattasai, Albasa, Magi, Gishiri, Ruwa.

75.    

Faten Alkama

Fate

 

76.    

Faten Dankalin Hausa

Fate

Dankali, Tarugu, Tattasai, Tumatur, Albasa, Zogale, Kifi, Mai, Magi, Curry, Gishiri, Kayan yaji, Tafarnuwa, Ruwa.

77.    

Faten Dankalin Turawa

Fate

Dankalin Turawa, Tarugu, Tattasai, Mai, Albasa mai lawashi, Magi, Gishiri, Kayan yaji, Ruwa.

78.    

Faten Doya

Fate

Doya, Kayan ciki, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Kayan yji, Zogale, Magi, Gishiri, Ruwa.

79.    

Faten Kabewa

Fate

Kabewa, Nama, Alayyafu, Kayan miya, Kayan Ƙamshi, Magi, Mai, Gishiri, Ruwa.

80.    

Faten Makani

Fate

Makani, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Kayan yaji, Magi, Gishiri, Ruwa.

81.    

Faten Makani Gwaza

Fate

Makani gwaza, Tattasai, Tarugu, Albasa, Mai, Kayan yaji, Magi, Gishiri, Ruwa.

82.    

Faten Shankafa Ɗanya

Fate

Shankafa, Tarugu, Ganyen Yakuwa/Sure, Daddawa, Magi, Gishiri, Curry, Man gyaɗa, Nama, Ruwa.

83.    

Faten Shinkafa

Fate

Shankafa, Yakuwa, Alayyafu, Lawashi, Wake, Kifi, shuwaka, Mai, Tarugu, Albasa, Magi, Gishiri, Kayan Ƙmshi, Ruwa.

84.    

Faten tsakin Masara

Fate

Masara, Gyaɗa, Yakuwa, Alayyafu, Tarugu, Tattasai, Albasa, Magi, Mai, Gishiri, Kayan Ƙamshi, Ruwa.

85.    

Faten Wake

Fate

Wake, Kifi, Anta, Alayyafu, Tarugu, Tattasai, Albasa, Gishiri, Magi, Kayan yaji, Ruwa.

86.    

Fitsarin Abiola

Ƙwalama

 Fanta, Jolijus

87.    

Funkasau 

Funkasau 

Fulawa, Alkama, Ruwa, Mai, Kanwako Yeast ko Nono, Albasa, Ruwa

88.    

Funkasau Na Fulawa

Funkasau

Fulawa, Garin waken suya, Yeast, Gishiri, Ruwa.

89.    

Fura Gero

Fura

Gero, Kayan yaji, Tonka, Nono, Suga, Zuma, Ruwa.

90.    

Fura Shankafa

Fura

Maiwa, Nono, Suga, Zuma, Ruwa.

91.    

Garin Ɗanbuɗiɗis

Ƙwalama

Ɗiyan Ƙwame, Madara, Bunbita, Suga, Waken suya.

92.    

Gasasshen Nama

Nama

Nama, Magi, Gishiri, Kayan yaji, Tafarnuwa, Mai

Ruwa.

93.    

Gasasshiyar Kaza

Nama

Kaza, Attarugu, Tafarnuwa, Magi, Gishiri, Kori, Mai, Ruwa.

94.    

Gasasshiyar Kaza BanƘararra

Nama

Kaza, Mai, Magi, Gishiri, Tonka, Tafarnuwa, Kayan yaji, Ruwa.

95.    

Gawasa

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

96.    

Gazari Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Gishiri, Ruwa.

97.    

Gigginya

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

98.    

Goriba

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci ta

99.    

Guguru 

Ƙwalama

Masara, Suga, Madara, flaɓour.

100.   

Gullisuwa

Ƙwalama

Madara kwata, Suga, Mai, Ruwa.

101.   

Gurasa 

Gurasa

Fulaawa, Bakin foda, Suga, Gishiri, Ruwa.

102.   

Gwandar Masar

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

103.   

Gwanda Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

104.   

Gwaza (makani) Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Gishiri, Ruwa.

105.   

Gyaɗa (kwaras-kwaras)

Ƙwalama

Gayaɗa, Gishiri.

106.   

Gyaɗa Ɗanya

‘Ya’yan itatuwa

Gishiri, Ruwa.

107.   

Hanjin Ligido

Ƙwalama

Suga, Ruwa, Lemon tsami ko tsamiya.

108.   

Hikimma

Hikimma

Fulawa, Suga, Bakin foda, Mai, Ruwa.

109.   

Huce 

Dambu 

Masara, ko Dawa, ko Gero.

110.   

Hwaru 

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za asha shi

111.   

Ice Cream

Ice- Cream

Ayaba, Madarar ruwa, Flaɓour, Suga, Ruwa.

112.   

Innibi

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci shi

113.   

Jinɓiri (ɗanye wake)

‘Ya’yan itatuwa

Gishiri, Ruwa.

114.   

Kabbeji Da Nama

Nama

Kabbeji, Nama, Karas, Dankali, Ƙwai, Mai, Magi, Albasa, Gishiri, Kori, Ruwa.

115.   

Kaffa

Tuwo 

Masara, Ruwa.

116.   

Kaiwa

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci ta

117.   

Kaiwa

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha shi

118.   

Kankana Ɗanya

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

119.   

Kantun Gana

Ƙwalama

Gyaɗa, Suga.

120.   

Karas Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci shi

121.   

Karashiya

Ƙwalama

Ƙwai da Ƙwai, Mai.

122.   

Kwaruru Ɗanya

‘Ya’yan itatuwa

Gishiri, Ruwa.

123.   

Kaɗe

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha shi

124.   

Killishi 

Nama

Nama, Mai, Ƙuli-Ƙuli, Kayan yaji, Tafarnuwa, Kanunfari, Magi, Tonka, Kori, Gishiri, Ruwa.

125.   

Kukumba

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

126.   

KununNono

Kunu

Nono, Gero, Madara, Suga, Zuma, Kayan Ƙamshi, Ruwa.

127.   

Kunun ‘Ya’yan Itace

Kunu

Shinkafa, Ayaba, Kankana, Abarba, Tuffa, Kwakwa, Ruwa.

128.   

Kunun Acca

Kunu

Acca, Tsamiya, Suga, Ruwa.

129.   

Kunun Aduwa

Kunu

Gerro, Aduwa, Kayan yaji, Ruwa.

130.   

Kunun Alkama

Kunu

Alkama, Suga, Masoro, Kanamfari, Citta, Nono

Madara, Zuma, Ruwa.

131.   

Kunun Aya

Kunu

Aya, Suga, Madara, Kwakwa, Dabino, Kanunfari, Ruwa.

132.   

Kunun Dankali

Kunu

Dankalin Hausa, Dawa, Kayan Ƙamshi, Ruwa.

133.   

Kunun Gero Na Tsaki

Kunu

 Gero, Kayanyaji, Tonka, Suga, Zuma, Ruwa.

134.   

Kunun Gyaɗa

Kunu

Gyaɗa, Madara, Shinkafa, Lemon tsami, SugaRuwa.

135.   

Kunun Kamu

Kunu

Gero, Suga, Madara, Citta, Kanunfari, Kimba, Tonka, Ruwa.

136.   

Kunun Kuskus

Kunu

Kuskkus, Madara, Suga, Tuffa, Ruwa.

137.   

Kunun Kwakwa

Kunu

Ƙwakwa, Ɗanya Shinkafa, Tuwo, Suga, Citta, Ruwa.

138.   

Kunun Maiwa

Kunu

Maiwa, Kayan yaji, Ruwa.

139.   

Kunun Sabara

Kunu

Gero, Kayan yaji, Sabara, Ruwa.

140.   

Kunun Sanga-Sanga

Kunu

Gero, Kayan yaji, Sanga-sanga, Ruwa.

141.   

Kunun Shinkafa

Kunu

Shinkafa, Mangyaɗa, Flaɓour, Inibi busashe, Suga, Ruwa.

142.   

Kunun Tsamiya

Kunu

Gero, Kayan yaji, Tsamiya, Ruwa

143.   

Kunun Yara

Kunu

Alkama, Dawaja, Masara, Waken suya, Gyaɗa, Zuma, Ruwa.

144.   

Kunun ZaƘi

Kunu

Gero, Gasara, Suga, Lemon tsami, Kayan Ƙamshi, Dankali, Kwakwa, Ruwa.

145.   

Kunun Zogale

Kunu

Gero, Kayan yaji, Zogale, Ruwa.

146.   

Kurna 

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha ta

147.   

 Wasa-Wasar Kuskus

Wasa-Wasa

Kuskkus, Gishiri, Ruwa.

148.   

Kwakumeti

Ƙwalama

 Kwakwa, Suga

149.   

Kwakwa Ɗanya

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a ci ta

150.   

Kwakwa DandaƘa

‘Ya’yan itatuwa

Sai an fasa za a ci ta

151.   

Kwankwalati (kakan daɗi)

Ƙwalama

Suga, Tsamiya

152.   

Kwastad 

Kunu

Waken suya, Dawa, Gyaɗa, Masara, Ƙwai. Suga

Ruwa.

153.   

Kwaɗon Dambu da Kabbeji

Kwaɗo

Kabbeji, Ƙuli, Tarugu, Albasa, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

154.   

Kwaɗon Garin Kwaki da Salat da Zogale da Tafasa da Rama

Kwaɗo

Garin Kwaki, Tarugu, Ƙuli, Latas, Mai, Tumatur, Gishiri, Magi, Ruwa.

155.   

Kwaɗon Kabbeji

Kwaɗo

Kabbeji, Tumatur, Kukumba, Albasa, Ƙuli, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

156.   

Kwaɗon Ƙanzo

Kwaɗo

Ƙamzo, Ƙuli, Kayan yaji, Tumatur, Tarugu, Albasa, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

157.   

Kwaɗon Rama

Kwaɗo

Rama, Ƙuli, Gyaɗa, Tarugu, Albasa, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

158.   

Kwaɗon Salat da Tumatur

Kwaɗo

Salat, Tumatur, Albasa, Ƙuli, Mai, Magi, Gishiri, Kayan yaji, Ruwa.

159.   

Kwaɗon Shinkafa da Alayyafu ko Zogale ko Tafasa ko Sanga-sanga

Kwaɗo

Shinkafa, Alayyafu, Zogale, Tafasa, Ƙuli, Gyaɗa, Mai, Tarugu, Tattasai, Albasa, Magi, Gishiri, Ruwa.

160.   

Kwaɗon Shinkafa da Latas (salat)

Kwaɗo

Shinkafa, Latas, Ƙuli, Tarugu, Tattasai, Albasa, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

161.   

Kwaɗon Sure ko Soɓorodo

Kwaɗo

Sure, Ƙuli, Tarugu, Albasa, Tonka, Magi, Gishiri, Mai, Ruwa.

162.   

Kwaɗon Tafasa

Kwaɗo

Tafasa, Ƙuli, Tarugu, Tumatur, Albasa, Magi, Kayan yaji, Gishiri, Ruwa.

163.   

Kwaɗon Tumatur

Kwaɗo

Tumatur, Tarugu, Albasa, Ƙuli, Mai, Magi, Gishiri, Ruwa.

164.   

Kwaɗon Tuwo da Alayyafu ko Zogale ko Tafasa ko Sanga-sanga ko Yaɗiya

Kwaɗo

Tuwo, Ƙuli, Tonka, Mai, Albasa, Kayan yaji, Ruwa.

165.   

Kwaɗon Tuwon Dawa ko Masara ko Shinkafa

Kwaɗo

Tuwo, Tonka, Ƙuli, Magi, Gishiri, Mai, Albasa, Ruwa.

166.   

Kwaɗon Ɓula

Kwaɗo

Ɓula, Gyaɗa, Ƙuli, Tarugu, Albasa, Magi, Mai, Gishiri, Kayan yaji, Ruwa.

167.   

Kwaɗon Zogale 

Kwaɗo

Zogale, Tumatur, Tattasai, Tarugu, Albasa, Ƙuli, Kayan yaji, Tafarnuwa, Magi, Gishiri, Mai, Ruwa.

168.   

Kyak (Cake)

Kyak

Fulawa, Suga, Bota, Madara, Bakin foda, Ruwa.

169.   

Kyak Na Ayaba

Kyak

Ayaba, Fulawa, Ƙwai, Butter, Madara, Suga, Gishiri, Bakin foda, Busasshen Dabino, Busasshen Inibi. Ruwa.

170.   

Lemon Magarya

Lemo 

Magarya, Kayan Ƙamshi, Lemon ZaƘi, Zuma Ko Suga, Ruwa.

171.   

Lemon Lemon ZaƘi

Lemo

Kukumba, Lemo zaƘi, Ɗanya citta, Kwakwa, Suga ko zuma, Ruwa.

172.   

Lemon Zaki Ɗanye

‘Ya’yan itatuwa

Kai tsaye za a sha shi

173.   

Lemon Abarba

Lemo

Abarba, Kayan Ƙamshi, Flavour, Ruwa.

174.   

Lemon Abarba da Citta

Lemo

Abarba, Citta, Kayan Ƙamshi, Suga ko Zuma, Ruwa.

175.   

Lemon Abarba da Kwakwa

Lemo

Abarba, Kwakwa, Madara, Suga, Kayan Ƙamshi, flaɓour, Ruwa.

176.   

Lemon Ayaba

Lemo

Ayaba , Kankana, Strawberry, Madara, Suga, Zuma Ruwa.

177.   

Lemon Gwaiba

Lemo

 Gwaiba, Suga, Madarar ruwa, Ruwa.

178.   

Lemon Gwaiba da Tuffa da Kwakwa da Abarba 

Lemo

Gwaiba, Abarba, Tuffa, Kwakwa, Suga ko zuma,

Flaɓour, Ruwa.

179.   

Lemon Gwanda

Lemo

Gwada, Kukumba, Karas, Ɗanya citta, Ruwa.

180.   

Lemon Gwanda da Ɗanya Citta

Lemo

Gwanda, Citta, Kayan Ƙamshi, Suga, Zuma, Ruwa.

181.   

Lemon Innibi

Lemo

Innibi, Kayan Ƙamshi, Na’a Na’a, Zuma, Ruwa.

182.   

Lemon Kankana

Lemo

Kankana, Kayan yaji, Suga, Zuma, Ruwa.

183.   

Lemon Karas

Lemo

Karas, Madara, Kayan Ƙamshi, Ruwa.

184.   

Lemon Kukumba