Shuwaka, tsiro ce da itacenta ba mai tsawo ne sosai ba. Kunnuwan shuwaka suna da faɗi sosai. Sannan kuma, ganyen na da ɗan ƙarfi, kuma ɗanɗanonsa yana da matuƙar ɗaci
Mahaɗan
Miyar Shuwaka
Abubuwan da ake tanada yayin samar da
miyar shuwaka su ne:
i. Daddawa
ii. Gishiri
iii. Kayan miya
iv. Kayan yaji
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Shuwaka
viii. Tafarnuwa
ix. Wake
Yadda Ake Miyar Shuwaka
Ita ma miyar shuwaka kamar yadda ake yin miyar zogale haka ake yinta. In da suka bambanta shi ne, a
maimakon a zuba zogale yayin da sanwa ta dafu, to akan zuba shuwaka ne. Kafin a
saka shuwaka, sai an wanke ta sosai tare da gishiri. Wannan ne zai rage ɗacin da take ɗauke da shi. Mutane da dama ba sa son
miyar ta yi ɗaci sosai. A dalilin haka, akan ɓata lokaci domin tabbatar da an murje ta domin rage ɗacin. Sannan
sai an yanka shuwaka ake sanyawa cikin sanwa.
Tsokaci
Shuwaka ma miya ce da ake son koyaushe mace ta riƙa yi wa maigidanta da yara. Saboda tana ba da lafiya ga maza da mata da yara baki ɗaya. Ma’ana dai tana da matuƙar amfani ga lafiyar jiki. Wannan miya sananniya ce a ƙauyuka da biranen ƙasar Hausa, musamman yanzu da cututtuka suke ƙara yawaita.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.