Monday, 25 November 2019

Zan Ƙara Aure // 10: Kun Bar Jaki Kuna Dukar Taiki

07:53 0


Zai iya yi miki kyautar dubu 20 ya kwana 7 ba ko sisi. Mutumin da bai da tausayi ko na anani, in yaro ya faɗi a gabanki zai kece da kuka saboda tsabar jin abin a jikinsa. Zai iya gaya miki bai taɓa yanka kaza ba kuma bai iya kashe cinnaka bare ɓera. In ya gano ke 'yar ɗariƙa ce kullum za ki gan shi da zabgegen carbi ga hoton Shehi a wuyarsa. Bai da zance sai na zikiri. In ke 'yar Izala ce ya ɗingile wando ga geme.

Sunday, 24 November 2019

Ɓurɓushin Naƙasa a Adabin Hausa: Tsokaci Daga Karin Magana

10:45 0


Tsakure: Karin magana a matsayin nau’i na adabin baka na Hausa ɗamfare yake da tunani da tsarin rayuwar al’umma tattare da alƙiblarsu a kowane lamari na rayuwa. Shi ya sa ya zama tamkar rumbu ne na adana falsafa da al’adun al’umma. Da yake rayuwar kowace al’umma tana tattare da lafiya da cututtuka da kuma naƙasa, shi ya sa wannan maƙala ta dubi ɓurɓushin nakasa a karin maganar Hausa. An kalli nakasa da nau’o’inta, sa’annan aka nazarci kare-karen magana masu ɗauke da hoton nakasa a kowane nau’i. Sakamakon nazarin ya gano cewa, a zahirance, irin waɗannan karin magana suna fito da irin ƙalubalen da naƙasa ke zamo wa mai ɗauke da ita wajen gudanar da al’amuransu na rayuwar yau da kullum. Haka kuma karin maganar na fito da irin tunanin al’umma a kan ɗabi’u da halayyar mai ɗauke da kowane irin naƙasa. An ɗora nazarin ne bisa ma’ana ta zahiri a tsarin karin maganar da aka yi amfani da su.

Hankaka Mai da Ɗan Wani Naka: Waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau a Bakin Mawaƙan Ƙarni na 21

10:36 0


Tsakure: Mazaunin wannnan maƙala shi ne nazari kan yadda mawaƙan Ƙ21 suke baddala waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau zuwa waƙoƙin zamani na kiɗan fiyano, shi ya sa ma aka yi mata take da ‘Hankaka Mai Da Ɗan Wani Naka’. An kawo tarihin rayuwa da gwagwarmayar da Sa’in Makafin Zazzau ya yi da kuma shahararsa a fagen waƙa duk da kasancewarsa makaho mabaraci. Binciken ya kawo mawaƙan da suka bi salon waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau tun daga makafi almajiransa da kuma mawaƙan zamani da suka baddala waƙoƙin nasa suka gwama su da kiɗan fiyano. Maƙalar ta gwama tsakanin gwanjo da orijina inda aka fito da waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau waɗanda mawaƙan Ƙ21 irin su Adam A. Zango (Ba ni bayanin Zango) da Funkiest Malam (Ga Lemu) da Sadi Sidi Sharifai (Direba Makaho, Idi Wanzami, Bayanin Naira) da sauransu.

Tarurrukan Daidaita Ƙa’idojin Rubutun Hausa Cikin Tarihi Daga Bamako Zuwa Kaduna: Ina Aka Fito? Ina Ake? Ina Aka Dosa?

10:26 0


Tsakure: Ƙa’idojin rubutu dokoki ne ko ladubban da ya kamata mai rubutu ya kiyaye wajen rubutunsa. Shi ya sa harshen Hausa kamar sauran harsuna da suka bunƙasa yana da nasa ƙa’idojin da aka shimfiɗa domin rubuta shi tsawon lokaci, musamman a tsarin rubutun boko. An gudanar da tarurruka a mabambantan wurare bisa manufar daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa, tun daga shekarar 1966 zuwa 1980. Ire-iren waɗannan taruka su suka haifar da ƙa’idojin rubutun da ake amfani da su tun bayan yarjejeniyar da aka cim ma a taron Yamai na ƙasar Nijar a shekarar 1980. Tsawon shekaru talatin da tara (1980-2019) daga waccan yarjejeniyar, an sami gudummawar masana da manazarta da dama (Yahaya, 1988; Sa’id, 2004; Bunza, 2002 da sauransu) wajen ɗabbaƙa ƙa’idojin rubutun Hausa cikin littattafan da suka wallafa. Sai dai duk da wannan ƙoƙari, rubutun Hausa na fuskantar barazana da karan-tsaye daga masu tu’ammali da rubutun. Saboda haka wannan takarda ta waiwayi jiya ta fuskar tarurrukan daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa da aka gudanar tun daga Bamako a shekarar 1966 zuwa Yamai a shekarar 1980 da zummar jaddada irin waɗannan taruka a matsayin kafa ta daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa domin amfanin yau da gobe. Takardar ta haska fitilar samar da mafita ga barazanar da rubutun Hausa ke fuskanta sakamakon bijire wa tsayayyun ƙa’idojin rubutun Hausa da wasu ke yi a rubutunsu.

Zan Ƙara Aure // 09: Ka Yaudare Ta

10:21 0


Za ka sami wanda zai tausaya wa yarinya da irin halin da take ciki, kamar talauci ko canjin addini da sauransu, sai ya fara nemanta ba tare da ya yi shawara da uwayensa ko abokai ba, kawai sai ta kware masa sai ya ba da haƙuri ya yi tafiyarsa.

Zan Ƙara Aure // 08: Kafin Ka Fara Tunanin

10:15 0


Na taɓazama da 'yan ƙasar Ethiopia, ni ne ma wakilin angon, ɗan Nigeria ne, ya musluntar da ita ya aure ta. Soyayya ba kama hannun yaro. Kullum tana jikinsa. Ba ta yarda ta yi nesa da shi. Kai ko titi za a tsallaka ba za ta yarda ya tsallaka ya bar ta ba, sai dai su tafi tare.