𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. fatan Kuna lafiya ya kokari Allah yakaro basira. Malam tambayata shi ne na kasance tun da muka yi aure da mijina ba mu taɓa kusantar juna ba, ba mu taɓa saduwa ba, Kuma auren ya yi shekaru saboda jinnu sun hana ni in bashi hakkinsa Idan zai kusanceni sai na ji raina ya ɓaci, kuma wani irin tsoro da fargaba ke zuwa min Sai na yi Kamar na ɗauki wuka na yankashi yanzu Idan na mutu a Haka ina da laifi a wajen Allah kokuwa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa alaikis salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce "Idan namiji ya kira matarsa zuwa ga
shimfidarsa, sai ba ta je masa ba, kuma ya kwana yana fushi da ita, to Mala'iku
suna tsine mata har ta wayi gari".
To amma wannan
hadisin yana magana ne akan irin matayen da ke Ƙin biyan bukatar
mazajensu ba tare da wani uzuri wanda shari'a ta yarda da shi ba.
Amma ke naki tun da
larura ne, in sha Allahu ba kya cikin jerin irin wadancan matayen. Tun da abun
yana faruwa ne ba bisa son ranki ba.
Kuma a cikin wani
hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce "Hakika Allah ya
yafe wa al'ummata abin da sukayi cikin kuskure da mantuwa, da kuma abin da aka
tilastasu akansa".
To kinga wannan
kauracewar da kike yi wa mijinki kamar Aljanun ne suke tilasta miki. Don haka
shawarar da zan baki anan ita ce ku yi kokari ku nemi magani irin na sunnah, a
wuraren da suka dace.
Kafin nan kuma ki
kula da azkar na safe da yamma, da kuma yawaita karanta Alƙur'ani a kullum tare
da sauraron kasset na Ƙira'ah. Musamman Suratul Baƙarah. Sannan duk
lokacin da kukayi niyyar saduwa da juna ke da maigidanki, ku yi alwala tukunna.
ku yi nafilfili ku roki tsarin Allah da kariyarsa daga sharrin shaiɗanun.
In da hali ku nemi man zaitun mai kyau, ku tofa fatiha 41, ayatul kursiyyi ma 41. Ƙul Huwallahu da falaƙi da nasi kowacce kafa 11. Sai ku rika shan cokali guda kullum safe da dare sannan ku shafe jikinku da shi kafin ku kwanta.
ƘARIN BAYANI
AMSA: Wa alaikis salam wa
rahmatullahi wa barakatuh.
Lallai addinin Musulunci ya
bayyana muhimmancin mace ta amsa kiran mijinta a duk lokacin da ya buƙace
ta, domin hakan yana kare mutuncin ma’aurata
da kiyaye su daga faɗawa
cikin haram. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi gargaɗi mai tsanani ga matan da
ke ƙin
mazajensu ba tare da wani uzuri na shari’a
ba. To sai dai kuma, wannan hukunci yana kan wadda take yi ne da gangan ko don
taurin kai. Amma idan mace tana da larura ta rashin lafiya, ko ta aljanu, ko
wani tursasawa na dabi’a
wanda ba ta da iko a kansa, to Allah Mai rahama ne kuma ba ya dorawa rai abin
da ba za ta iya ba.
Idan har abin da kike fuskanta
tursasawa ne daga shaiɗanu
(aljanu) waɗanda ke
shiga tsakaninki da mijinki, to ke kina ƙarƙashin hukuncin wadda aka tursasa ne.
Allah Maɗaukakin Sarki
ya ce a cikin Alkur'ani:
لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا
"Allah ba Ya ɗora wa rai wani abu sai
yadda ikonta yake." (Suratul Baqarah: 286)
Wannan aya tana nuna cewa tunda
ba da son ranki kike ƙin mijin naki ba, kuma tsoron da kike ji ya fi ƙarfin
ikonki, to in sha Allahu ba kya cikin fushin Allah. Haka nan, Manzon Allah
(SAW) ya bayyana cewa Allah ya yafe wa wannan al'umma abubuwan da suka faru ba
da saninsu ba ko ta hanyar tursasawa:
إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ لِي عَنْ أُمَّتِي
الْخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ
"Lalle Allah Ya yafe wa
al'ummata kuskure, da mantuwa, da kuma abin da aka tursasa su a kansa."
(Hadisin Ibn Majah da Baihaqi)
Shawarar da zan ba ku ita ce,
kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Wannan nau'i ne na jinnu da ake kira
Sihrul Ta'atil (asirin da ke hana aure ko saduwa). Ya kamata ku nemi magani ta
hanyar Ruqyah ta Shari'ah. Sannan ku lazami karatun Suratul Baqarah a cikin
gida, domin Manzon Allah (SAW) ya ce shaiɗan
ba ya zama a gidan da ake karanta ta.
Haka nan, yana da kyau ku kiyaye
addu'ar neman tsari kafin saduwa, kamar yadda ya zo a hadisi:
بِسْمِ اللَّهِ، اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ،
وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا
"Da sunan Allah. Ya Allah!
Ka nishantar da mu da shaiɗan,
kuma Ka nishantar da shaiɗan
daga abin da Ka azurta mu (na zuria)." (Bukhari da Muslim)
Ina ba ki shawarar yin amfani da
Man Zaitun da aka karanta ayoyin waraka a ciki (kamar Fatiha, Ayatul Kursiyyi,
da Mu'awwidhatain) kina shafawa a jikinki. Allah Ya ba ku lafiya, Ya raba ku da
sharrin shaiɗanun
mutum da na aljan.
Wallahu A'alam.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.