Wannan nau’i ne na tuwo da ake samar da shi daga garin gero. Akan surfe gero a wanke sannan a daka. Garin geron shi ake tuƙawa a haɗa da kanwa ya zamo tuwon gero. A ƙauyuka an fi yin tuwon gero a maimakon birane. Haka kuma, mata da maza da yara da suke zaune a ƙauyuka sun fi yawaita cin tuwon gero fiye da sauran nau’o’in tuwo. Bugu da ƙari, har gobe a ƙauyuka ana tuƙa tuwon gero tare da ɗaiɗaikun gidaje a birane.
Mahaɗin
Tuwon Gero
i.
Gero
ii.
Kanwa
iii.
Ruwa
Yayin samar da tuwon gero, akan samu geron karan kansa a surfe a kuma bushe. Daga nan sai a wanke geron (wasu kuma ba su cire dusa). Za a a daka geron. Yayin da ya
daku, sai a tankaɗe shi. Bayan nan, sai a zuba ruwa a tukunya a aza bisa wuta saman murhu har sai ya tafasa.
Bayan ruwa ya tafasa, za a rage shi
cikin ƙwarya ko wata
roba. Sai kuma a ɗebi gari ko tsakin da ya yi saura da aka tankaɗe a yi talge da shi. Idan za a yi talge, za a jiƙa kanwa a cikin ruwa a tace ta saboda
tsakuwa. Sa’annan a kwaɓa gari ko tsakin tare da ruwan kanwar. Wasu kuma da sun rage ruwan zafi sai a kaɗa guntuwar kanwa cikin tukunyar. Amma
abin lura, a
jiƙa kanwar a tace ya fi, saboda tsabtace abincin. Za a zuba wannan talgen a cikin ruwan zafin da aka rage a cikin
tukunyar. Yayin da ake zubawa, za a riƙa
gaurayawa da muciya domin ya haɗe sosai ba tare da gudaji ba.
Akan rufe tukunya kimanin mintuna ashirin (20) bayan talge, ko
kuma adadin lokacin da aka tabbatar ya dafu. Bayan tabbatar da
dafuwar talgen, za a ɗauko
garin da aka aje, a riƙa
barbaɗawa ana kuma juyawa da muciya har sai
garin ya ƙare. Sai kuma a
fara tuƙa tuwon sosai. Bayan an kammala tuƙi, za a bar shi rufe har tsawon mintuna ashirin (20) ko wani lokaci makamancin haka. Kafin a rufe tukunya akan ɗan zuba ruwan zafi kaɗan. Idan an tabbatar da ya salale sai a sake tuƙawa da muciya.
Da zarar an kammala
tsaf, sai batun kwashewa. Akan yi amfani da mara wajen ɗebowa da zubawa cikin ƙwarya domin malmalawa. Daga nan sai batun sanyawa cikin
kwanuka ko robobi ko kuma kuloli, musamman yanzu da zamani ya
samar da su. An fi cin wannan nau’in tuwo da miyar yauƙi.
Tsokaci
Tuwon gero na ɗaya daga cikin nau’o’in abinci da ke
samar da ƙarfin jiki ga ɗan Adam. Za a iya hasashen cewa, yawan cin irin waɗannan nau’o’in
abinci da mutanen ƙauye ke yi, shi
ke ba su damar gudanar da ayyukan ƙarfi
sama da mutanen birni. Kusan za a iya cewa, yaran ƙauye sun fi yaran birni ƙarfi da kuzari. Wannan kuwa ba ya rasa
nasaba da bambancin abinci da akan samu daga birni zuwa ƙauye.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.