Gabatarwa
Idan za a iya tunawa, babi na shida an gina shi ne sukutum kan miyar gargajiya da nau’o’inta tare kuma da yadda ake samar da su. Wannan babi kuwa ya shafi miya ce ta zamani da kuma yadda ake aiwatar da ita a zamanance. A wani hanzari ba gudu ba, wasu nau’o’in miyar na zamani an same su ne daga waɗanda ake da su na gargajiya sakamakon sauye-sauye ta fuskar kayan haɗi da matakan sarrafawa.
Daga cikin
nau’o’in miyoyin na zamani akwai waɗanda ba sa buƙatar bayani. Dalili kuwa shi ne, ba su da wani bambanci
ta fuskar sarrafawa (yadda suke a gargajiyance, haka ake samar da su a
zamanance). Waɗannan nau’o’in miya su ne:
A babi na shida ƙarƙashin 6.2 an kawo
bayani dangane da miyar soɓorodo a gargajiyance. Miyar ta gargajiya ba ta da wani bambanci na
a-zo-a-gani. Bambancin da ake samu kawai shi ne wanda ya shafi kayan haɗin da ake
amfani da su. A zamanance ana amfani da nau’o’in kayan ɗanɗano da na
ƙamshi daban-daban.
2. Miyar Kuka
A ƙarƙashin 6.4 da ke
babi na shida, an kawo bayani tiryan-tiryan game da yadda ake samar da miyar
kuka a gargajiyance. A zamanance ma duk abin guda
ne. Bambancin da ake samu bai wuce na kayan haɗin da ake
amfani da su ba. A yau, ana amfani da nau’o’in kayan ɗanɗano da na
ƙamshi da babu su a miyar kuka ta gargajiya.
Babu wani bambanci
na sosai tsakanin miyar wake ta gargajiya da ta zamani. An yi bayanin miyar
wake a babi na shida ƙarƙashin 6.6. Bambancin da ake samu ya shafi kayan haɗi ne
kawai.
An yi bayanin miyar ayoyo a ƙarƙashin 6.2 da ke babi na shida. Bambancin da ke tsakaninta
da na zamani bai wuce na nau’o’in kayan ɗanɗano da na
ƙamshi ba.
5. Miyar Yoɗo (Karkashi/Kalkashi)
An yi bayanin miyar yoɗo a ƙarƙashin 6.8 da ke babi na shida.
An kawo taƙaitaccen bayani
dangane da lalo da yadda ake miyarsa a ƙarƙashin 6.9 da ke babi na shida.
An tattauna bayanai kan yadda ake miyar gauta a ƙarƙashin 6.10 da ke
babi na shida.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.