Aduwa wata bishiya ce da galiban ta fi tsirowa a burtali (lawani), tana da ƙayoyi a jikinta, kuma takan yi ‘ya’ya da suke nuna farkon lokacin sanyi(lokacin girbin dawa). Ana shan (tsotsar) ‘ya’yan nata idan sun nuna. Daga cikin kayan da ake haɗa miyar aduwa da su akwai:
i. Ganyen Aduwa
ii. Albasa
iii. Daddawa
iv. Gishiri
v. Kayan yaji
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Wake
Yadda Ake
Miyar Aduwa
Da farko, za a niƙa tattasai da tarugu da albasa, sannan a daka daddawa tare da kayan yaji. Daga nan, za a soya
kayan da aka niƙa in sun soyu, a saka su tare da dakakkiyar daddawar nan da aka
tanada. Sannan a surfe wake a wanke a saka a ciki a zuba gishiri a saka ruwa. Idan
miya ta tafasa za a ɗauko
ganyen aduwa a wanke sosai, ana saka gishiri a wurin wanke ganyen, sai a saka a ciki kamar alayyafu. Idan ta dafu za a saka maburkaki a kaɗa ta. Za a iya cin miyar da kowane nau’in tuwo.
Tsokaci
An fi samun wannan nau’in miya a ƙauyuka. Ba kasafai
ake yin miyar tafasa a birane ba. Wannan bai rasa nasaba da kasancewar tafasa
tsiro ce
da ke fitowa da zarar an yi ruwa ba tare da an shuka ba. Saboda haka, takan
yawaita sosai a cikin ƙauyuka a dalilin wadatar filaye da suke da shi idan aka
kwatanta su da
birane da kusan kowane wuri a gine yake.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.