Ticker

6/recent/ticker-posts

Nau’ukan Kwalama (Makulashe) Na Zamanani Da Yadda Ake Sarrafa Su a Abincin Hausawa

Gabatarwa

A babi na goma sha shida an kawo bayanai dangane da nau’o’in abincin ƙwalama a gargajiyance. Misalan abincin ƙwalama da aka kawo a babin sun haɗa da, alewar gyaɗa da kantun gana da hanjin ligidi da sauransu. Wannan babi zai mayar da hankali kan nau’o’in abubuwan maƙulashe da ake samu a zamanance.

Alewar Madara

i. Filebo

ii. Kwakwa

iii. Madara kwata

iv. Suga

A ɗora suga a wuta a saka ruwa kaɗan a bar shi ya dafu. Idan ya dafu, za a ga ya yi danƙo-danƙo. Daga nan za a gurza kwakwa a saka madara ana yi ana tuƙawa da ludayin miya ko cokali. Za a bar ta da ruwa-ruwa. Bayan nan sai a samu tire a ɗora leda a samansa a shafa mai a jikin ledar, sannan a kwashe alewar madarar a zuba a cikin tiren. Za a bar ta ta sha iska lokaci kaɗan, kafin a fara yanka ta.

Gullisuwa

i. Madara

ii. Mai

iii. Suga

Za a haɗa madara da suga a kwaɓa da ruwan ɗumi. Idan za a kwaɓa, da tauri za a yi kwaɓin. Bayan nan a dinga ɗiba ana mulmulawa kamar ƙwallo amma ƙanana-ƙanana. Da zarar an kammala mulmulawar, sai a ɗora mai a tukunya. Bayan man ya yi zafi, sai a soya gullisuwa. Ana sanya wuta kaɗan-kaɗan a lokacin suyar.

Kwakumeti

        i.            Kwakwa 

      ii.            Suga

Za a zuba suga a cikin tukunya a ɗora bisa wuta ba tare da an saka ruwa ba. Sai a samu ludayi a yi ta juyawa har ya narke. Daga nan sai a gurza kwakwa a zuba a ciki a yi ta tuƙawa har ya haɗe gaɓa ɗaya. Idan ya dafu, za a ji yana ƙamshi sai a sauke a rinƙa mulmulawa.

Ɓalɓalo (Carbin Malam)

        i.            Kwakwa

      ii.            Lemon Tsami

    iii.            Suga

Za a zuba suga a cikin tukunya a dafa shi ya dafu. Daga nan sai a goge kwakwa a zuba a cikin sugan tare da lemon tsami. Idan ya dafu, sai a bar shi ya huce, daga nan sai a fara mulmulawa. Bayan nan za a samu farar leda doguwa a mulmula shi kamar ƙwallo a saka a ciki a ɗaure, haka za a yi ta yi har a gama.

Alewar Gyaɗa

a.       Gyaɗa 

b.      Suga

A daka gyaɗa sai ta yi gari, sai a zuba suga a tukunya a ɗora a wuta, ba sai an sa ruwa ba. Za a yi ta juyawa har sai ya koma ruwa. Daga nan sai a zuba gyaɗar a yi ta tuƙawa har sai ta yi ja. Bayan ta yi ja, za a samo faranti a shafa masa mai (man zai hana gyaɗar ta kama shi idan an zuba). Sai a zuba wannan gyaɗar da aka dafa cikin suga a kai. Bayan ta bushe, sai a riƙa ɓallawa ko yankawa daidai gwargwadon girman da ake buƙata.

A Ci Da Mai

a. Albasa         

b. Garin masara         

c. Mai              

d. Ruwa                      

e. Yaji

Za a ɗora tukunya da ruwa a bisan wuta, kuma za a bar ta har sai ta tafasa, sannan a yi talgen garin masara ko ƙullunta. Za a bar shi ya dafu sosai sannan a juye a saman tire. Daga nan sai a soya mai a malale samansa, sai kuma a ƙara albasa da yaji. Za a riƙa yayyankawa da wuƙa ko cokali.

Alallaɓa/Ƙwalan (Ƙwalan Na Taɓi)

i. Albasa                     

 ii. Fulawa                  

  iii. Gishiri

iv. Magi                       

v. Mai                          

vi. Ƙwai

vii. Ruwa                   

 viii. Tarugu                 

ix. Tattasai

Za a kwaɓa fulawa tare da tarugu da tattasai da albasa da magi da gishiri sannan a fasa ƙwai a ciki. Idan an kwaɓa, za a saka ɗan mai a saman marfin kwano wanda aka ɗora a saman wuta sai a riƙa soyawa sama-sama.

Ɗan Madaro

i. Madara 

ii. Mai 

Za a sanya mangyaɗa cikin tukunya a ɗora bisan wuta, sai a bar shi ya soyu ba tare da albasa ba. Daga nan sai a zuba madara a ciki sannan a yi ta juyawa. Za a tabbatar ba ta yi ƙololo/gudaji ba. Za a ci gaba da juya ta har sai ta koma ruwan ƙasa. Daga nan sai a samo tire a shafa masa mai, sannan a juye a cikinsa. Tun kafin ta sha iska, za a fara ɗiba kaɗan-kaɗan ana mulmulawa. Za a ajiye waɗannan mulmulallun a gefe guda. Da zarar an ƙare, an kammala ɗan madaro kenan.

 The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022

Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments