Ticker

6/recent/ticker-posts

Tuwon Tsaki

Tuwon tsaki, wani nau’in tuwo ne da ake yi da tsakin masara. Ma’ana sai an tankaɗe garin masara bayan an daka. Daga nan ne za a yi amfani da tsakin da ya rage a mayar da shi tuwo. Galibi tuwon tsaki abinci ne da mata suka fi ta’ammuli da shi. Baya ga wannan, tuwon tsaki shi ma ba kullum ake yin sa ba, sakamakon sai an yi tuwo kusan biyu ko uku a gida za a tara adadin tsakin da zai isa a tuƙa tuwon na tsaki. Wannan nau’i na tuwo,na daga cikin dabarun mata na yin abincin gaggawa saboda rashin wadataccen lokaci da kuma tattalin kwananniyar miyar da ta yi saura domin gudun ka da a zubar da ita a banza. Haka kuma, idan an rasa abinci a cikin gida, akan ɗauko tsakin da aka aje a tuƙa tuwon da shi a matsayin abincin gaggawa.

Mahaɗin Tuwon Tsaki

Yayin samar da tuwon tsaki. Akwai abubuwan da ake buƙata kamar haka.

i. Masara ko Dawa ko Gero

ii. Ruwa

Yadda Ake Tuwon Tsaki

Da farko za a fara tanadar tsaki. Ana iya yi da tsakin dawa ko gero ko na masara. Idan an samu tsakin ɗaya daga cikin waɗannan da aka ambata, za a tankaɗe don a rage masa garin da ke cikinsa. Daga nan sai a aza tukunya bisa wuta a zuba ruwa a cikinta, a bar ta nan har sai ruwan ya tafasa. Sannan za a ɗauko tsaki a wanke shi sosai a regaye. Kada a bari ya jiƙe ƙwarai don cire masa ƙasa da sauran dusar da ke ciki. Bayan nan, sai a rage ruwan zafi a ajiye gefe ɗaya. Sai kuma a riƙa ɗibar tsakinan ana barbaɗawa a hankali a cikin tukunya. Sannan za a saka muciya cikin tukunyar ana tuƙawa har sai ya yi kauri. Sa’anan sai a rufe tukunya a bar shi ya salale na tsawon wani lokaci. Idan ya ɗan jima, za a buɗe a sake tuƙawa. Da zarar an yi haka, haƙiƙa tuwon tsaki ya haɗu kenan. Galibi shi tuwon tsaki akan ci shi da kowace irin miya.

Tsokaci 

Yara ƙanana da kuma mata su ne suka fi cin tuwon tsaki. Maza (manya) ba su cika cin wannan nau’i na tuwo ba. Sannan ba a cika ɗaukar wannan nau’in tuwo da ƙima ba. Wasu na ganin kamar ba tuwo ne da za a ci a ƙoshi ba. Wannan na faruwa ne kasancewar sa tuwo mai ruwa-ruwa. Wannan ya sa ake ganin sa abinci ne na yara da mata. An fi samun irin wannan abinci a garuruwan Zariya da Kabi da Zamfara, ba a cika samun irin wannan abinci a garuruwan Kano da Katsina da sauran garuruwa ba. Yana da kyau a riƙa yin tuwon tsaki kasancewar zai taimaka ainun wajen sarrafa abinci da ake ragewa don yin amfani da shi, musamman ga ƙananan yara waɗanda za su iya dawowa daga makaranta ba a gama abinci da wuri ba, tuwan tsaki zai iya tallafarsu kafin a gama abinci. Baya ga haka kuma, tuwon zai taimaka wajen tattalin abincin da ake da shi a gida.

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation: Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments