Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

GAME DA MU


1.0 Matashiya
Tuni Hausa ta yi fintinkau ga sauran takwarorinta (Harsunan Nijeriya) ta fuskar yaÉ—uwa da kuma bunÆ™asa. Wannan É—aukaka da harshen ya samu bai tsaya ga farin jini da sauÆ™in koyon da yake da shi ba kawai, har ma da gata da ya samu daga nazarce-nazarce da rubuce-rubucen da Turawa suka gudanar cikinsa. Wani dalili na bunÆ™asar harshen shi ne yadda ake nazarin sa a jami’o’in cikin gida da na Æ™asashen waje daban-daban. A waÉ—annan É“angarori, sai dai a ce Allah son barka.

A É—ayan É“angare kuma, duniya juyi-juyi ce… Sauyin zamani, musamman abin da ya shafi intanet, ya É“ullo da wata barazana ga harshen. HaÆ™iÆ™a ya tabbata cewa, harshen da kaÉ—ai cigabansa zai É—ore a halin yanzu shi ne, wanda a Æ™alla, ake jin É—uriyarsa a intanet. Kash! A wannan fanni kuwa, tuni aka yi wa Hausa fintinkau. Lallai kuwa, bai dace masu kishin harshen su yi Æ™asa a guiwa ba wajen ganin harshen ya shiga jeriyar gudun ya-da-Æ™anin-wani wanda ake falfalawa a wannan fanni. Saboda haka ne aka Æ™uduri samar da kafar intanet da za ta riÆ™a tattara rubutun masana da manazarta harshen Hausa. Hakan zai samar da Æ™arin kutsen harshen cikin sassan duniya tare kuma da samar da wata kafa ta binciken al’amuran da suka shafi harshen cikin sauÆ™i.

2.0  Æ˜uduri
Ƙudurin wannan kafar intanet shi ne, tattara rubuce-rubucen masana da manazarta cikin harshen Hausa, domin yaɗa harshen da kuma sauƙaƙa wa masu neman bayanai game da lamurra daban-daban da suka shafi harshen.

3.0 Manufa
Wannan kafar intanet na da manufofi kamar haka:
  1. Sanya harshen Hausa cikin jerin harsunan duniya da ke taka rawar gani a kafar intanet.
  2. Samar da wani rumbu na rubuce-rubucen ilimi cikin harshen Hausa a kafar intanet.
4.0 Ayyuka
Ayyukan da wannan kafa za ta riƙa gudanarwa sun haɗa da:

  1. Tattara rubuce-rubucen masana da manazarta cikin harshen Hausa, shirya su tare da ɗora su a kafar intanet domin duniya ta riƙa gani da kuma amfani da su.
  2. Samar da bayanai kan harshe da al’ada da adabin Hausawa domin sanin marasa sani da Æ™ara sanin masu sani. 
  3. KarÉ“ar tambayoyi daga masu ziyarar kafar tare da Æ™oÆ™arin samar da amsoshinsu cikin lokaci. 
  4. Ɗora abubuwan nishaɗi cikin harshen Hausa waɗanda suka haɗa da labarai da wasa ƙwaƙwalwa da kacici-kacici da almara da makamantansu.
5.0 Kira
Ana maraba da rubutun Hausa na ilimi kowane iri domin sakawa a wannan kafa. Za a iya turo rubutun ta É—aya daga cikin hanyoyin nan:
  1. official@amsoshi.com   
  2. Contact
Sannan muna maraba da shawarwari ko gyara game da kura-kuranmu.

Mun gode.

Post a Comment

2 Comments

  1. Naji dadin ganin wannan rubutun Allah yasa manyan mu hausawa zasu suyi kokari wajen sa harshen ajerin manyan harshen duniya Allah ya daukaka yaren hausa da hausawa

    ReplyDelete
  2. Abdulrashid S.Pawa Gusau14 August 2021 at 20:02

    Masha Allah. A gaskiya wannan kafa mai suna Amsoshi tana da matukar muhimmanci ba wai ga dalibai masu nazarin harshen Hausa ba a'a hatta ga duk wani mai amfani da harshen Hausa a ko'ina yake a fadin duniya zai amfana da wannan kafa wadda ta tara ilimi a cikinta. Don haka muke godiya ga wanda ya assasa wannan kafa wato Abu-Ubaida Sani Allah ya kara mai hazaka da basira amin. Bayan haka muna mika godiyarmu maras adadi ga malamai masana harshen Hausa musamman malami uban malamai wato Farfesa Aliyu Muhammad Bunza Allah ya karamai lafiya da tsawon rai da kuma, daukaka amin.
    Daga karshe ina ma wannan kafa fatan alheri, ni ne dalibin harshen Hausa Abdulrashid S Pawa Gusau (B.A Hausa. FUG graduand 2019).

    ReplyDelete

Rubuta tsokaci.