Ticker

6/recent/ticker-posts

Fassarar Mafarki Da Ire-Irensa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamu alaikum, inna son sanin fassarar mafarki da kashe-kashensa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam warahmatullah.

Wato ƴar uwa sha'anin mafarki abu ne babba wanda sai wanda suke da ilimin kawai, amman ga abin da na ɗan binciko cikinn ƙaramin ilimi da fahimta da Allah ya hore min.

Mafarki na gaskiya yankine na Annabta, kamar yadda akwai ruwayoyi da yawa daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Mafarkin ƙwarai yanki arba'in da shida ne na Annabci. (Al-imamul Bukhari 6472; da Muslim, 4201). (Al-Bukhari, 3; da Muslim, 231). Kuma wanda ya fi faɗin gaskiya shi ne ya fiku gaskiyar mafarki. Waɗanda su kafi mafarki na gaskiya su ne waɗanda suka fi,gaskiya a magana.” (Muslim, 4200).

“Idan zamani (tashin kiyama) ya kusanto, da wuya mafi yawan mafarkai basu zama na ƙarya ba. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: Hakan ze kasance ne saboda Annabci, saboda haka masu imani za a basu wasu abubuwa a yana yin mafarki wanda ze kusanto su ga labarai masu kyau ko taimakonsu akan su yi haƙuri da imaninsu. (Al-Bukhari, 6499; da Malam Muslim, 4200) Iri ɗaya za a iya cewa mu'ujizar da ta bayyana bayan lokacin Sahabbai. Wannan be faru ba a lokacinsu saboda ba sa buƙatar su, saboda ƙarfin imaninsu, amma mutanen da suka zo bayansu musamman a yanzu suna buƙatarsu saboda imaninsu yana da rauni.

MAFARKI KALA UKU (3) NE:

1. RAHMANI (Wanda suke zuwa daga Allah),

2. NAFSAANI (psychological, wato wanda suke daga mutum ne.)

3. SHAYTAANI (waɗanda suke zuwa daga gurin sheɗan).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Mafarki kala uku ne: mafarki daga Allah, mafarki da yake haddasa wuya da wanda yake daga sheɗan, da kuma mafarki wanda yake zuwa daga abin da mutum ya tuna bayan ya tashi, kuma ya ga (faruwarsa) lokacin da ya yi bacci.” (Al- imamul Bukhari, 6499; da Muslim, 4200)

Mafarkin Annabawa wahayi ne wanda an yi musu kariya daga sheɗan. Ummah sun yarda akan hakan. Annabi Ibrahim ya shirya cika umarnin Allah na yanka ɗan sa Isma'il lokacin da ya ga hakan cikin mafarkinsa; Allah ya ƙara musu Aminci duka.

Mafarkin sauran mutane wanda ba Annabawa ba sai dai mu auna su akan hasken wahayi [Misali Ƙur'ani da Sunnah]. Idan mafarkin ya dace da Ƙur'ani da Sunnah, to hakan dama ya tabbata sai mu amsa; idan kuma ya saɓa to ba za mu amsa ba balle mu yi aiki da shi. Wannan fa al'amari ne mai tsanani, saboda da yawa ƙirkirarrun al'amura da malaman sufaye da sauransu ta nan suke amfani su ce sun yi mafarkin abu kaza.

Duk wanda yake son ya yi mafarki na gaskiya to ya kasance zancensa gaskiya ne ko da yaushe, ya ci halal, ya kiyaye haram, ya tsaya akan abin da shari'a ta umarce shi, da kaucewa abin da Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) suka haramta, da barci a yana yin tsarki da fuskantar alƙibla, da tuna Allah har sai ido ya rufe. Idan mutum ya yi wannan da abubuwa masu kyau to da wahala ne mafarkinsa be zama gaskiya ba.

Mafarki mafi zama gaskiya sune waɗanda ake ganinsu a lokacin suhur, saboda a wannan lokacin ne Allah yake saukowa ƙasa (sakkowa da ta dace da shi (SWA)) kuma ake saukar da rahama da gafara..... (Duba Madaarij al-Saalikeen, 1/50-52)

Al-Imamul Haafiz ibn Hajar ya ce: Gaba ɗaya mafarki ɗayan biyu ne (wato kala 2 ne):

1. MAFARKIN GASKIYA. Wannan sune mafarkin Annabawa da mutanen kirkir waɗanda suka bisu. Ze iya kasance da sauran mutane ma, amman hakan yana da ɗan wuya, kamar irin mafarkin kafirin sarki wanda Yusuf (AS) ya fassara masa shi. Mafarkan gaskiya sune wanda suka zamo gaskiya a rayuwa bayan an ga faruwarsu a mafarki.

2. HARHAƊA MAFARKIN ƘARYA, wanda suke gargaɗi akan wani abu. Wannan suma kala kala ne:

1. Wasan sheɗan don ya wahalar da mutum, kamar irin mutum ya ga an cire masa kai kuma yana tafiya kan yana binsa, ko mutum ya faɗa cikin hargitsi kuma be ga kowa ba da ze taimake shi, da sauransu.

2. Idan ya ga wasu mala'iku suna gayamasa ya yi wani abu da aka haramta, ko yin wasu abubuwa da a hankalce ba za su yiyu ba.

3. Ko mutum ya ga wani abu da ya faru da shi a rayuwarsa ta gaskiya, ko yana so yafaru, kuma sai ya ganshi a mafarki ya faru; ko ya ga wani abu da yake yawan faruwa da shi idan yana farke. Irin wannan mafarkan mafi yawa suna magana ne akan abin da ze zo gaba ko yake faruwa yanzu ko ya jima da faruwa. Duba: Fath al-Baari, 12/352-354.

Abu Sa’eed al-Khudri (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Idan ɗayanku ya yi mafarki wanda yake so, to daga Allah ne, sai ya godewa Allah ya bayar da bushara da sauran mutane. Idan kuma ya ga abin da baya so, mafarki wanda baya so, to wannan daga sheɗan ne, sai ya nemi tsarin Allah daga gare shi kuma kada ya faɗawa kowa, baze cutar daahi ba.” (Al-Bukhaari, 6584, da Muslim, 5862).

Abu Ƙutaadah ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Mafarki magaskaci (mai kyau) daga Allah ne, amma sururu mafarki (mara kyau) daga sheɗan ne. Idan ɗayanku ya ga abin da ba haka daga abin da ba shi so, to lallai abin sani daga sheɗan ne, to lallai ya yi tofi gefen hagunsa sau uku, kuma ya nemi tsarin Allah daga sheɗan, kuma ba ta cutar da shi da komai.” (Al-Bukhaari, 6594, da Muslim, 5862 suka ruwaito). “tofin” yana nufin yawu kaɗan, ko kuma iska ba tare da tofa yawun ba.

An karɓo daga Jabir (Allah ya ƙara masa yarda) cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Idan ɗayanku ya ga mafarkin da ba shi ya so ba, to ya yi tofi a gefen hagunsa sau uku, kuma ya nemi tsarin Allah daga sheɗan sau uku, kuma ya canza gurin kwanciyarsa daga inda yake kwance zuwa ɗayan bangaren.” (Imamu Muslim, ya ruwaito, 5864)

Ibn Hajar ya ce: a haɗa abubuwan da aka ce game da mafarkai masu kyau, zamu iya cewa:

1. Mutum ya yabi Allah dangane da mafarki mai kyau.

2. ya yi farin ciki da shi.

3. Ya gayawa mutane waɗanda yake so ba waɗanda baya so ba.

Idan kuma zamu haɗa abubuwan da aka ce dangane da mafarki mara kyau zamu iya faɗin abubuwa 4:

1. Ya nemi tsarin Allah daga sharrin mafarkin.

2. Ya nemi tsarin Allah daga sharrin sheɗan.

3. ya yi tofi sau uku a gefen hagunsa idan ya farka.

4. Kada ya bawa kowa labari.

5. A cikin Bukhari, Baab al-Ƙayd fi’l-Manaam, an ambaci abu na biyar daga Abu Hurairah, wanda shi ne yin salla. Yadda ruwayar take shi ne: duk wanda ya ga wani abu da ba ya so (a mafarki) kada ya faɗawa kowa, sai dai ya tashi ya yi salla. Wannan ruwayar Mausul ce Imam Muslim y a ruwaito ta a sahih dinsa.

6. Muslim ya ƙara da abu na shida, wanda shi ne canza asalin yadda kwanciyar take zuwa ɗayan ɓangaren.

A ƙarshe, abubuwa shida ne za ayi, huɗun da muka ambata da kuma yin salla raka'a 2 nafila, da canza bangaren kwanciya. Duba Fath al-Baari, 12/370.

A cewar hadisi da ruwayar Abu Razeen daga Al-Tirmidhi, kada ya gayawa kowa sai dai wanda yake kusa da shi sosai yake son sa sosai kuma yake kula da shi, ko wanda yake da hikimah sosai. A cewar wata ruwayar, kada ya faɗawa kowa sai wanda yake da hikimah ko yake ji da shi. A cewar wata ruwayar kuma, kada ya faɗawa kowa game da mafarkinsa sai dai wani malami ko wanda ze bashi shawara mai kyau tsakani da Allah.

Al-Ƙaadi Abu Bakr ibn al-‘Arabi ya ce: game da malami, ze fassara masa shi ta hanya mai kyau iya kokarinsa, kuma wanda ze bashi shawara ta gaskiya ze koya masa wani abu da zeyi masa amfani ko ya taimake shi. Wanda yake da hikima kuma shi ne wanda yasan yadda ze fassara masa kuma ya gayamasa iya abin da ze taimake shi, ko kuma ya yi shiru. Wanda yake ji da shi ko yake son sa, idan ya san wani abu mai kyau ze faɗa, idan kuma be sani ba ko yana kokonto to ze yi shiru. Duba Fath al-Baari, 12/369

Imamul Baghawi ya ce: Ka sani cewa fassarar mafarki yana shiga ɓangarori daban daban. Mafarki za a iya fassara shi da hasken Ƙur'ani ko hasken Sunnah, ko ta hanyar karin magana da mutane ke amfani da shi, ko ta hanyar sunaye. (Sharh al-Sunnah, 12/220)

Ya ba da misalai akan hakan, kamar: Fassara da hasken Ƙur'ani: igiya da ma'anar dace, sabida faɗin Allah:

وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا

“Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gaba ɗaya, kuma kada ku rarraba.....” [Aal ‘Imraan 3:103].

Fassarar a haskem sunnah: kamar hankaka wakiltar haramtaccen mutum (fasiƙi), saboda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ambace shi da hakan.

Fassara ta hanyar karin magana: kamar haƙa rami ma'ana makirci, saboda mutane suna cewa: Idan za ka haƙa rami to haƙa daidai kai

Game da littafin “Fassarar Mafarkai” cewa an danganashi ga Ibn Seereen, bincike masu yawa sun nuna cewa za a yi dangana shi gare shi gaba ɗaya.

ALLAH NE MAFI SANI.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments