Ticker

6/recent/ticker-posts

Tubar Wanda Ya Yi Kudi Ta Hanyar Tsafi Da Ruwan Maniyyin Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam kuruciya da kuma son duniya ya rude ni DA NI da wani abokina. Mun dade muna fadi-tashin neman kuɗi bayan mun kammala karatun sakandire. Muna da nauye-nauye akanmu sannan muna da buri kala-kala arayuwa. Wannan ya sa abokina ya samo mana wani boka (ba zan fadi garin da yake ba) ya yi alkawarin zai yi mana wani aikin da zamu samu kuɗi. Amma sai mun je mun yi zina da wasu 'yan mata (ya gaya mana kalarsu). Maniyyin da ya fita daga jikinmu ta wannan zinar shi zamu kawo masa sannan ya yi mana kuɗin. Mun je mun yi kuma mun kai masa. Hakika abokin nawa yanzu haka yana da tireloli nasa na kansa. Ni kuma yanzu ina Abuja da kampanina, na zama ina harkar kwangila (contractor). An samu kuɗi ba laifi. Na dade da fara yin nadama ina tunanin cewa duk kuɗin nan da muka tara fa watakila na haram ne, kuma watakila duk ibadar da nake yi ba karbabbiya bace. Ina so in tuba amma ina jin tsoro saboda bokan ya ce mana wai akwai mummunan abin da zai faru idan muka tuba. Na dade ina wannan tunanin, to sai kuma naci karo da irin rubuce-rubucen da kuke yi a Zauren Fiƙhu dangane da kwanciyar Ƙabari da ranar hisabi da sauran abubuwa masu tsoratarwa. Shi ne na ga dacewar in turo da tambaya gareku tare da fatan samun mafita da kuma addu'a daga gareku da sauran bayin Allah nagartattu.

TUBAR WANDA YA YI KUƊI TA HANYAR TSAFI DA RUWAN MANIYYIN ZINA

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakika in banda Annabawa (alaihimus salam) dukkan 'yan Adam masu saɓo ne. Amma mafiya alkhairin masu saɓo sune masu tuba zuwa ga Allah (SWT).

wannan abin da kuka aikata, babban zunubi ne kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da kansa ya bayyanar da hakan Ƙarara a cikin hadisai da dama. Misali akwai hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya tambayi Sahabbai shin kuna so in ba ku labari game da mafiya girman laifukan nan guda uku?

Sai suka ce "Kwarai kuwa Ya Rasulallah"

Sai ya ce musu "Yin shirka ga Allah, da kuma bijire wa iyaye, da kuma shaidar zurr".

A cikin wani hadisin kuma ya lissafa manyan zunubai guda bakwai waɗanda ke saurin hallakar da mutum. Kuma ya ambaci SHIRKA ita ce ta farko. Kuma tabbas bisa ijma'in dukkan maluman Musulunci, babu wani laifi mafi girma kamar shirka wato tsafi.

Amma tabbas ba Ƙaramin alkhairi ba ne gareka da kayi niyyar tuba zuwa ga Ubangijinka domin Shi mai gafara ne mai jin kai ga bayinsa.

Allah Madaukakin Sarki ya fa'da a cikin Alƙur'ani:

إِنَّ اللَّهَ لَا يَغفِرُ أَن يُشرَكَ بِهِۦ وَيَغفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ وَمَن يُشرِك بِاللَّهِ فَقَدِ افتَرَىٰٓ إِثمًا عَظِيمًا

"Lalle ne Allah ba ya gafarta a yi shirka gami da shi, kuma amma Yana gafarta abin da yake bayan wannan ga wanda Ya so, kuma wanda ya yi shirka da Allah, to lalle ne ya kirkiri zunubi mai girma.” (Suratun Nisa’i: 48).

Amma ayar tana nufin wanda ya mutu yana yin shirka ne, ba tare da tuba ba. Amma duk wanda ya tuba, Allah zai karɓai tubansa. Komai girman zunubin da ya aikata. Inda ya yi cikakkiyar tuba irin wacce Allah yake so.

Kamar yadda Allah ɗin da kansa ya faɗa wa Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallam:

قُلۡ یَـٰعِبَادِیَ ٱلَّذِینَ أَسۡرَفُوا۟ عَلَىٰۤ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوا۟ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِیعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِیمُ

"Kace Yaku bayinsa waɗanda suka aikata ɓarna akan kansu!! Kada ku fidda tsammani daga samun rahamar Allah. Hakika Allah yana yafe zunubai baki dayansu. Domin Shi Shi ne mai gafara mai jin ƙai" (Surah Az-Zumar: 53)

Kuma Yace:

إِلَّا ٱلَّذِینَ تَابُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ ذَ ٰلِكَ وَأَصۡلَحُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ

"SAI DAI WAƊANDA SUKA TUBA BAYAN NAN (WATO BAYAN SUN AIKATA LAIFIN) KUMA SUKA KYAUTATA AIKI, TO HAKIKA ALLAH MAI GAFARA NE MAI JIN ƘAI GARESU". (Surah An-Nuur: 5)

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Allah yana murna da bawansa ya yin da ya tuba fiye da yadda dayanku yake murna ya yin da ya tsinci dabbarsa bayan ta bace masa alhali tana ɗauke da abincinsa da guzurinsa.

Kuma ya ce Allah yana yafe wa bawansa idan ya tuba. Mutukar dai bai kai gargara ba. (wato mutukar bai kai lokacin fitar ransa ba.).

Amma sharudan tuba sun hada da:

1. Yin nadama bisa abin da ya gabata.

2. Niyyar Ƙaurace wa wannan zunubin, har abada.

3. Fita daga zunubin, wato dena aikatashi nan take ba tare da ba ta lokaci ba.

4. Idan akwai hakkin wani ko wasu, to wajibi ne ka mayar musu da hakkokinsu ko kaje ka nemi yafewarsu.

Amma kamar a cikin yamayin da kake, abin da zai fi kwanciyar hankali gareka shi ne ka fita daga wannan dukiyar baki dayanta. Wato kayi kokari ka rabu da dukiyar, domin gaba dayanta haram ce, daga ita har ribar da kullum kake Ƙara samu a cikin dukiyar.

Sallolin da ka barsu abaya kuma, wajibi ne ka ramasu kamar yadda maluma da dama suka faɗa. Kuma babu abin da zai Cutar dakai don ka tuba. Allah zai kiyayeka mutukar ka tsaya bisa tafarkin gaskiya.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments