Tafasa, tsiro ce da ake sarrafa ganyenta domin yin amfani da shi wajen yin miya.Ta fuskar kamanni, tafasa ɗanyen haki ce mai ɗauke da ƙananan ganye waɗanda da kaɗan suka ɗara na zogale. Ta fuskar tsawo kuwa,tsiron tafasa bai wuce na alayyafu tsawo ba. A duk lokacin da aka dafa ganyen tafasa, launinsa yakan sauya daga kore zuwa baƙi.
Mahaɗin Miyar Tafasa
Daga cikin abubbuwan
da ake tanada, idan za a haɗa miyar tafasa su ne:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Gyaɗa
v. Kayan yaji
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Tafasa
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Tumatur
Yadda Ake Miyar Tafasa
Akan yi miyar tafasa ne tamkar yadda ake samar da miyar zogale. Za a daka gyaɗa[1] a saka tare da ganyen tafasar wanda ita ma za a wanke ta sosai tare da gishiri. Da zarar ta dafu, to miyar tafasa ta samu kenan. Akan ci wannan miyar da kusan dukkanin nau’o’in tuwo.
[1] Akan
yi amfani da ɗanyar gyaɗa ko soyayyiya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.