An yi bayanin miyar guro a ƙarƙashin 6.5 da ke babi na shida. Akan samu ‘yan bambance-bambance tsakanin miyar guro ta gargajiya da kuma ta zamani. A ƙasa an ɗauki samfurin samar da miyar guro guda an feɗe biri har wutsiya cikin taƙaitattun kalmomi. Kayan haɗin da aka yi amfani da su, su ne:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Guro
iv. Karas
v. Kayan Yaji
vi. Magi
vii. Mai
viii. Ruwa
ix. Tafarnuwa
x. Tarugu
xi. Tattasai
xii. Nama ko kaza ko kifi ko Ganda
Abu na farko da za a yi shi ne, a wanke guro sosai a yanka ta da wuƙa. Idan kuma za a yi irin ta zamani,
to akan goga ta ga magurji ko a niƙa
ta ga turmi ko a yi niƙan ga injin ɗin hannu na zamani (bilanda). Sannan
idan da nama za a yi, ana iya tafasa shi tare da albasa da magi da gishiri kaɗan, sannan a soya shi. In kuma ana buƙata,
za a iya soya shi tare da jajjage kamar yadda aka yi na miyar kuka. Idan kuma da naman kaza za a yi, za a wanke kazar sosai
a tafasa ta tare da kayan yaji da tafarnuwa da magi da gishiri ɗan kaɗan.
A gefe guda kuma, za a daka daddawa da
kayan yaji a aje gefe ɗaya, sannan sai a soya kayan miyar kamar yadda aka yi a miyar kuka. Daga nan za a ɗora sanwa, tamkar dai yadda aka
bayyana a nau’o’in miya da aka bayyana a baya.
Bayan sanwa ta dahu, za a kawo kuɓewa a sanya. Idan ana buƙatar sanya karas, to akan kankare shi sosai kafin a saka.
Idan miyar da kifi za a yi, to ba a sanya kifin har sai bayan an sanya kuɓewa. Sanya karas zamani ne ya zo da shi. Sai a ɗan saka kanwa kaɗan ba da yawa ba, kuma za a buɗe marfin tukunyar kaɗan. Buɗe
tukunyar zai hana miyar zubewa, domin da zarar kuɓewar
ta fara nuna, za ta riƙa
kumfa da cika tukunya. Sau da dama akan yi amfani da ludayi
domin motsa miyar gudun kada ta zuba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.