Miyar soɓorodo miya ce da ake yi da ganyen soɓorodo. Soɓorodo yana daga cikin ganyaye da Hausawa ke miya da su a ƙasar Hausa. Soɓorodo dai ana samunsa ne daga tsiron sure (yakuwa). Yana da launi fari ko ja. Sai dai an fi amfani da farin soɓorodo a wajen miya. Idan ya yi jawur, ya kai ƙarshen nuna kuwa, an fi amfani da shi a wajen haɗa soɓo na ruwa. Duk da haka, akwai masu miya da jan soɓorodo, sai dai yana da tsami sosai. Shi kuwa farin soboroɗo, shi ne wanda ba a bar shi ya nuna sosai ba. A maimakon haka, akan cire shi kafin ya buɗe ’ya’yansa su fito. Da irinsa ne aka fi yin miyar da ake kira ta soɓorodo.
Mahaɗin Miyar Soɓorodo
Abubuwan
da ake tanada idan za a haɗa miyar soɓorodo sun
haɗa da:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Kayan yaji
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Soɓorodo
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Wake
Yadda Ake Miyar Soɓorodo
Yayin da za a yi miyar soɓorodo,
za a wanke shi soɓorodon sosai sannan a tsane shi. A
gefe guda kuwa, za a yi jajjage ko markaɗen kayan miya. Sannan za a daka kayan yaji haɗi da daddawa a ajiye gefe guda.
Bayan an tanadi kayan haɗin miya, sai batun aza tukunya bisa wuta. Za a sanya mai tare da jajjage ko
markaɗen da aka yi, har sai sun soyu. Daga nan
za a sanya kayan yaji, tare da daddawa. Haka za a riƙa motsawa har sai sun haɗu sarai, sai kuma a zuba ruwa.
Bayan an sanya ruwa, sai kuma a sa
gishiri. A wannan gaɓa ne ake sanya kifi ko nama, idan har
an tanade su (kada a manta da, an riga an tafasa nama a gefe guda). Idan sanwa
ta ɗan jima da tafasa, sai a sanya sure wanda aka riga aka wanke. Za a bar wannan miya ta nuna sosai har na tsawon mintuna talatin ko
ma sama da haka. Da zarar an kammala wannan, to kuwa miyar soɓorodo ta samu. Akan yi amfani da wannan miyar domin cin
tuwon masara ko shinkafa ko ɓula.
Tsokaci
Ita ma miyar soɓorodo kamar miyar sure ce da mata masu ciki da marasa lafiya suke buƙatar su ci abinci da ita. Haka kuma,
za a iya la’akari da cewa, mata da yara sun fi son miyar soɓorodo, wato dai ba kamar yadda maza ba su damu da ita
sosai ba. Mutanen da ke zaune a ƙauyuka
sun fi shan miyar soɓoro. A garuruwan Katsina da Kabi da Zamfara da Sakkwato da Niger da sauran wasu garuruwan ƙasar Hausa duk akan samu wannan miyar
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.