Miyar ayayo miya ce da ake yi da ganyen ayayo. Ayoyo nau’i ne na tsiro da akan shuka a gonaki ko bayan gida. Ganyensa na da yauƙi sosai, kamar karkashi ko lalo. Idan za a yi miyar, akan saka mata wake don miyar ta ƙara armashi da ɗanɗano. Sai dai mafi yawanci an fi amfani da ganyen ayayo a ƙauyuƙa ba a birne ba.
Mahaɗin Miyar Ayayo
Abubuwan da ake buƙata yayin miyar ayayo sun haɗa da:
i. Ayayo
ii. Daddawa
iii. Kayan miya
iv.
Gishiri
v. Kayan yaji
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Wake
Yadda Ake Miyar Ayayo
Miyar ayoyo tana da matuƙar kamanceceniya
da miyar kuɓewa musamman ta fuskar dafuwa. Ma’ana dai, yadda
ake miyar ɗanyar kuɓewa,
haka ake miyar ayoyo. Bayan sanwa ta tafasa, a maimakon a sanya kuɓewa, sai a sanya ganyen ayayo. Akan wanke ganyen da ɗan
gishiri, sannan a yanka kafin a zuba cikin sanwar. Wani lokaci kuma akan zuba ta cikin
sanwa ba tare da an yanka
ba, amma akan tabbatar da an an
wanke duk da rashin yankawar.
Ban da wannan bambanci, dukkanin bayanin miyar ayayo, daidai
yake da miyar kuɓewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.