Ticker

6/recent/ticker-posts

Miyar Wake

Da busasshen wake ake amfani yayin samar da miyar wake. Akan jiƙa waken da ruwa, a surfe shi, sannan a wanke a cire dusa da hancin waken (wani lokaci kuwa akan bar shi da hancin, wato ba tare da an surfe shi ba). Yayin samar da miyar wake, wake ne babban abin haɗi. Shi ake sanyawa daidai gwargwadon yadda miyar za ta yi kauri. Akasarin miyar wake kuwa na da kauri sosai.

Mahaɗin Miyar Wake

Kayan haɗin miyar waƙe sun ƙunshi:

i. Daddawa     

ii. Gishiri         

iii. Mai             

iv. Ruwa

v. Wake           

vi. Kayan miya (tumatur, attaruhu, albasa da makamantansu)

Yadda Ake Miyar Wake

Hanyar da ake bi domin samar da miyar wake daidai yake da na sauran miyoyin da aka yi bayani a baya. Sai dai a wannan karon, idan sanwa ta tafasa akan sanya wake ne. Wato wanda aka rigaya aka jiƙa sannan aka surfe.[1] Za a rufe tukunyar a bar waken har sai ya dahu ya yi laushi sosai. Daga nan za a yi amfani da maburkaki a burge shi har sai ya haɗe gaba ɗaya. Da zarar an kammala haka, to miyar wake ta samu kenan.

Tsokaci

Shan miyar wake na taimakawa sosai a jikin mutum duba da amfanin wake a jikin ɗan Adam. Wannan ya sa birni da ƙauye duk ake ta’ammuli da miyar wake. Sau da dama akan ba da shawarar a riƙa ba wa marar lafiya miyar wake, domin amfaninsa wurin gina jiki. Hasali ma dai, Bahaushe ya ɗauki wake a matsayin na’ibin nama. Wato inda ba nama, wake sai ya maye gurbinsa. Haka ma, miyar wake na matuƙar taimakawa ga mata masu juna biyu. Ko ba komai dai, an yi amanna kan cewa, wake na daga cikin nau’o’in abinci masu gina jiki sosai. Makaɗa Ali Makaho mai gurmi ya ɗan fito da wani abu kaɗan game da matsayin wake a miya, inda yake cewa:

 Jagora: ........................................

:Ba don wake a miya ba,

: Da ka-fi-zabuwa yai tsada.

(Ali Makaho,Waƙar Mandula).



[1]Ana kuma iya yin miyar ba tare da an surfa ba.

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation: Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments