Gauta ɗaya ne daga cikin ’ya’yan tsiro da ake samu a ƙasar Hausa. Ƙanana ne masu siffar attaruhu. Sai dai a maimakon zafi da attaruhu ke da shi, gautaytana da ɗanɗano ne mai ɗaci-ɗaci. Baya ga haka, akwai nau’in gauta da ke da matsakaicin girma. Irin waɗannan ba su fiye ɗanɗanon ɗaci ba, sai dai ɗanɗano main zaƙi-zaƙi kaɗan.
Mahaɗin Miyar Gauta (Ɗwata)
Akwai abubbuwan da za a tanada, idan
za a haɗa miyar ɗwata.
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv.
Kayan yaji
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Tarugu
viii.
Tattasai
ix. Wake
x. Ɗwata
Yadda Ake Miyar Gauta (Ɗwata)
Ita ma miyar gauta idan za a yi ta, akan jajjaga tattasai da tarugu da albasa a daka kayan yaji da daddawa da tafarnuwa. Bayan haka, sai a surfe wake a kuma wanke sannan a aje gefe. Daga nan za a soya jajjage tare da mai. Idan ya soyu, sai a saka daddawa a zuba wake a ciki, sannan a ɗan ƙara soyawa kaɗan. Bayan sun soyu tsaf, sai a saka gishiri a zuba ruwa, wato dai a yi sanwa. Daga zarar sanwa ta tafasa, za a matso da gautan da aka riga aka yanka sannan aka wanke.[1] Yayin da miyar gauta ta dafu takan warwatse ne tamkar guro. Abin da ya rage shi ne saka maburkaki a kaɗa, sai kuma sauke tukunya. Kusan akan ci miyar gauta da kowane irin tuwo.
Tsokaci
Mutanen Burma suna daga
cikin masu yawaita amfani da wannan nau’in miya. Sannan yawanci mata sun fi maza shan
miyar gauta. Wannan bai rasa nasaba da tasirin da miyar take da shi wajen ƙara wa mai jego ruwan nono. A dalilin
haka ne ma ake nuna buƙatar
yin amfani da wannan miya ga mai jego, musamman ga yankunan da ake amfani da
miyar sosai. Yara ba su fiye
son wannan nau’in
miyar ba, wanda hakan na faruwa ne a dalilin ɗan
ɗaci-ɗaci
da kuma bauri-bauri da take tattare da shi. Daga cikin garuruwan Hausawa da suke amfani da ita sosai akwai, Kano da Zazzau da Niger
da Katsina da Zamfara da kuma Kabi da
sauransu.
[1] Wani lokaci akan sanya gautar ba
tare da an yanka ba. A irin waɗannan lokuta, da kansa gautan yake warwatsewa a cikin miyar.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.