Ganyen lalo shi ma dangi ne na karkashi da kuma ayoyo. Wato dai, yana da yauƙi sosai. A lokuta da dama, lalo ba ya buƙatar a shuka shi kafin ya fito. A maimakon haka, yakan fito ne da zarar an yi ruwa. Akan same shi a bakin rafi da cikin gonaki da kuma iyakokinsu. A wasu lokutan, lalo na fitowa har a cikin gidaje ko a kufayi. Bayanin miyar lalo na da makusanciyar kama da ta karkashi da kuma ayoyo, waɗanda tuni aka bayyana yadda ake gudanar da su a baya. Banbancin kawai shi ne, yayin da sanwa ta tafasa, sai a sanya ganyen lalon da aka yanka, a maimakon ganyen karkashi ko ayoyo.
Mahaɗin
Miyar Lalo
i. Daddawa
ii. Kayan miya
iii. Gishiri
iv. Lalo
v. Mai (idan an ga dama)
vi. Ruwa
vii. Wake
Tsokaci
Mutanen karkara sun fi ta’ammuli da miyar lalo, sama da mutanen da ke zaune a birane. A ƙauyukan akan sami tsiron lalo har a kusa da gidajen al’umma. Kamar dai yadda aka bayyana a sama, lalo ba ya buƙatar a shuka shi a mafi yawan lokuta.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.