Miyar kuka, miya ce da ta jima ana amfani da ita a ƙasar Hausa. Kusan ita ce fitaciyyar miyar da Hausawa suka fi amfani da ita a ƙasar Hausa. Kuka bishiya ce da ke fitar da ganyen kuka. Wannan bishiya na ɗaya daga cikin bishiyoyin da ake samu a muhallin Bahaushe da kuma dazuzzukansa. Ganyen ta ba shi da faɗi sosai kuma bai da tsawo sosai.
Akan yi miya da ɗanyen ganyen, ko kuma busasshe. Sai dai an fi yin
miya da busasshen ganyen na kuka. Akan kira miyar kukar da aka yi ta da ɗanyen ganyen
da suna swaɓe.
Idan kuwa busasshiyar
kuka ce, to daka ta ake yi
ta zama gari. Yayin da aka ɗanɗana, to za a ji bauri. Sai dai idan
aka kaɗa ta cikin miya, baurin ɓacewa yake yi.
Mahaɗin
Miyar Kuka
Akwai abubuwan da ake buƙata idan za a gudanar da miyar kuka waɗanda suka
haɗa da:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Kayan yaji
iv. Kuka
v. Nama
vi. Ruwa
vii. Tafarnuwa
viii.
Tarugu
ix. Tattasai
Yadda
Ake Miyar Kuka
Yayin samar da miyar kuka, za a fara daka kayan yaji da tafarnuwa tare da daddawa
a aje a gefe. Sannan a daka tattasai da tarugu da albasa. Ba a faye sanya tumatur ba a cikin
miyan kuka, domin zai sanya mata tsami, sannan za ta iya baƙi. Wasu suna tafasa nama da albasa su
kuma soya shi. Sai
dai idan ana son miyar
ta yi ɗanɗano
sosai, an fi son a wanke nama a cire masa dati sosai, ba tare da an
soya shi ba. A maimakon haka, za a soya shi ne tare da kayan miya.
Bayan an shirya tsaf, sai a hura wuta a ɗora tukunya. Akan iya amfani da manja ko man gyaɗa. Daga nan za a sanya kayan miya, a soya har sai sun soyu sarai. Bayan
kayan miya sun soyu, sai kuma a sanya ruwa a bi bayansa da kayan ɗanɗano.
Yayin da sanwa ta tafasa, za a tsame
naman da ke ciki tsaf, a aje a gefe (kada a manta ba da nama kaɗai ake miyan kuka ba). Akan yi ta da kifi, ko ma a yi ta haka lami ba
tare da kifin ko nama ba),
sai kuma a kaɗa kuka. Za a kaɗa kukar ne ta hanyar barbaɗa ta a hankali tare da juya miyar da balugari ko
ludayi. Bayan an kammala sanya kukar, za a burga miyar ta burgu ƙwarai. Daga nan za a rufe miyar zuwa
mintuna kaɗan, waɗanda
ba su wuce shida ko makamancin haka ba. Da zarar an kammala wannan, to miyar kuka ta samu.
Tsokaci
Hausawa sun tafi kan cewa, miyar kuka na da amfani ƙwarai ga jikin ɗan Adam. Bayan haka, miyar kuka na da sauƙin sarrafawa da kuma sauƙin kashe kuɗi. Wannan ya sa akasari Hausawa suka fi yawaita yin ta birni da ƙauye, saɓanin sauran miyoyi. Duk da haka, ba kowa ke shan miyar kuka ba, musamman mutanen da ke zaune a birane, inda aka fi amfani da nau’o’in abinci na zamani.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.