Adashen Kauna 2 ta Abu-Ubaida Sani

    Gabatarwa

    Tun farkon É“ullowana, Allah ya sa mini haske da Æ™yalÆ™yali da za a iya kwatanta shi da walwalin-waliyo, tamkar dai na sunduÆ™in Ƙolin-Ƙoliyo. Kasancewar haka ne ma, taurari da dama kan kai caffa farfajiyata, wani lokacin har cikin da’irar da nakan zagaye yayin murnar haihuwar giwa a dokar jeji. Sai dai, ban taÉ“a ko da mafarkin marabtar É—aya daga jikin taurarin a matsayin Zara ba. Ba ina nufin raina haskensu ba ne, a’a, kawai ina gudun yanka wa kare ciyawa ne, musamman da yake a lokacin na kasance a filin dagan da alÆ™alami shi ne babban makami. Ko ba komai za a mini uzuri kasancewar ba a tauna taura biyu a baki guda. Toh! Sanin kowa ne dai sai an kula kashi yake É—oyi, to da yake ban sanya a ka ba (wai in ji É“arawon tagiya), sai na zamana sayau.

    Adashen ƙauna, waƙa ce ta biyu (wanda ta farkon ita ce Asusun Ƙauna) da na ƙaga domin nuna cewa, Allah ne bai kawo lokaci mafi dacewa da in tsunduma kogin iyon zamantakewa ba domin linƙayar da kan kai ga bagiren aure. Sannan a maimakon yaudarar kaina da na wata, da ma cacar lokaci da aljihu, gwara in yi tanadin abubuwan da watakila sun salwanta har zuwa lokacin dafafutukan zai zama mai tushe da madogara. Na nuna cewa, lokaci na zuwa da zan shigo tsarin, kuma ma har watakila in taka rawa da baza mai ban mamaki.

    Ana bikin duniya ake na kiyama, saboda haka ne na yi amfani da wannan dama wurin isar da saÆ™wannin faÉ—akarwa da jan hankali zuwa ga ma’aurata da ma waÉ—anda ke kan hanya, dangane da kyautata zamantakewa. Tun da ma dai, taÉ“arÉ“arewar zamantakewar aure abu ne da ya daÉ—e yana ci mini tuwo a Æ™warya, wai Allah wadarai naka ya lalace (inji jakin gida da ya ga na dawa). A Æ™arshen waÆ™ar kuwa, na nuna kasancewana tilo a jiki da zuciya, tare da Æ™aguwar ganin na marabci abokiyar rayuwa, duk da kuwa a lokacin ban kawo tunanin kowa ba (har a zahiri ba a duniyar waÆ™a ba kawai). Sai kuma na kammala waÆ™ar da barkwanci inda nake zolayar wannan tauraruwa da a lokacin tsara waÆ™ar babu ita.

    Bayan na kammala wannan waƙa tare da ɗora ta a intanet, na faɗa wa abokaina da dama cewa; da yardar Ubangiji kashi na uku na wannan waƙa zai fito ne da sunan mataimakiyar. Fatana a kullum, Allah ya sa mu riƙa tuna akwai haƙƙoƙin zamantakewa da addini ya wajabta a kanmu. Allah ya sa mu ɗauki rayuwar aure bauta, ba kamar yadda sau da dama ake kallon sa a matsayin filin kokuwar nuna isa da gadara tare da sauƙe fushi da ɓacin rai ba.

    Sadaukarwa

    Waɗannan baituka sadaukarwa ne ga masu tunani nagari da karɓar shawarwari nagari da kuma aikata aiki nagari.

     
    Ya Mahaliccin talikai,
    Da ya sanya mutane ke buki.

    A yo aure a yi haihuwa,
    Yayinsu biyun fa ana buki.

    Ka ba ni basira Rabbana,
    Yau na karkata zancen buki.

    Kai daÉ—in tsira ga Nabiyina,
    Da wurinsa mu kai koyin buki.

    Duk da kafinsa ana buki,
    Ga shi muka É—au darasin buki.

    A baya kaÉ—an nai tsokaci,
    Kan maganar nan ta buki.

    Adashe ni na raÉ—a mata,
    Adashen ƙauna ko buki.

    Kashi na biyu na taho da shi,
    Ga batun nan dai zancen buki.

    Na faÉ—a miki yau zan jaddada,
    Ina tanadin ranar buki.

    Tanadi na kuÉ—i gefe guda,
    A gefen ko sai tsarkin jiki.

    Ba jiki kaÉ—ai ba da zuciya,
    In tsare har ranar buki.

    Tuni na kulle makullen zuciya,
    MabuÉ—i na hannunta miki.

    Akalata na nan ga ke,
    Ja ni mu je ranar buki.

    Asirkan nan da a kai mani,
    Igiyun duk an damƙa maki.

    Kin riƙi sitiyarin zuciya,
    Tuƙa ni a sannu har buki.

    Me kike shayi ya sahiba?
    Ai kin nasara an bar maki.

    Ba mai ƙwace ni a gu naki,
    Muna nan tare mu sha buki.

    Ta yiwu mui zance kaÉ—an,
    Ko tattauna batu na arziki.

    Ko mui yi hirar illimi,
    Da wata É—iya ta arziki.

    Amma ba mu batu na SO,
    Wannan na tara maki.

    Ba ƙauna ba marrari,
    Babu zumuÉ—i sai ga ke.

    Ba hirar SO kowace,
    Sai in hirar nan da ke.

    Ki sha kuruminki kina da ni,
    Sam ba ni wulaƙantar da ke.

    A zamanmu da ke za ai batu,
    Maraɗa sa yo kassaƙe.

    Na ƙi duk hirar dandali,
    Na tanada zan yo wa ke.

    Na ƙi wasa ko da zolaya,
    Da mace, duk na tara wa ke.

    Ko da te-te ina maki,
    In har nai aure da ke.

    Ko a-sha-ruwa ko kike biÉ—a,
    Na tsuntsaye a sha da ke.

    Ko da langa kike biÉ—a,
    Sai in É—ana lako duk wa ke.

    Kai! Ko dungure na kule,
    Na wuntsila don faranta wa ke.

    Idan aiki na gida kuwa,
    Ban bari ya wahalshe da ke.

    Ko in taya ki a zahiri,
    Wato aikin mu yi ni da ke.

    Koko in yi kwance in bar ki can,
    Amma in yi ta ziga ga ke.

    Ko ÆŠanmaraya yana faÉ—in,
    A wurin yaƙi bai yin sake.

    In soja suna can kan wuta,
    Shi ko zai nan gun fake,

    Amma zai ta kiÉ—i wa su,
    Da zuga alhali dai fake.

    Ban fita hira in daÉ—e waje,
    Alhali gida na bar ki ke.

    Ban fita waje don daÉ—i in ci,
    A gida kuwa lami shi da ke.

    Ba ni bin ra’ayina duka,
    Alhali na ƙi naki ke.

    Ba ni hana maki walwala,
    Alhali ni ko ina sake.

    A gare ki zan yi É—awainiya,
    A taƙaice za ni kula da ke.

    Lafiyarki za ni kula da ta,
    Cinki, shanki duk ba sake.

    Za mu rinƙa zaman hira da ke,
    Mui almara ni da ke.

    Za mu yo barkwanci da ke,
    Fara’a kullum ni da ke.

    Idan akwai wata damuwa,
    Za mu tattauna ta ni da ke.

    Idan na kuskure gaskiya,
    Zan saurari batunki ke.

    Idan kika kauce gaskiya,
    Ni ko zan nusantar da ke.

    Son kai ke sanya hayaniya,
    To mu guje masa ni da ke.

    Lalaci kasalar zuciya,
    Mu guje su kadda mu yo sake.

    Ziga na ƙawaye kar ki ji,
    Har ‘yan uwa masu É“atar da ke.

    Ki lura da halin duniya,
    Kar daÉ—i ya É“atar da ke.

    Haƙƙin aure ki bar sake,
    Sauƙina ya ruɗar da ke.

    SO da nake nuna wa ke,
    Kul ya sakankantar da ke.

    Kar ki ji ke sai lalama,
    Girman kai ya É“atar da ke.

    Kar ki ji kin zarce faÉ—a,
    Kin fi ƙarfin a nusar da ke.

    Kar ki ji kin wuce tambaya,
    Sannan abin a hana wa ke.

    Kar ki ji ke in kin ka so,
    Abu dole-a-dole a ba wa ke.

    Banda gadara tutiya,
    Na kin mallaki mai aurenki ke.

    Ban da kallon rayuwar-
    Wasu, me ya talo ma ke?

    Kar da ki zam almubazzara,
    Addini ya yi hani ga ke.

    Na hore ki da godiya,
    Ga nufin Allah duk ga ke.

    Matsala ta gida ta tsaya ga mu,
    Kadda waninmu ya ji ga ke.

    Addini ko ki sa gaba,
    Kar shagala ta gusar da ke.

    Idan kin kama wanan batu,
    Da ma saura da na tsallake.

    Rayuwarmu na daɗi ƙwarai,
    Wane mai santin rake.

    Za mu zaga wuri-wuri,
    Da ziyara duk ni da ke.

    Za ni kai ki gari-gari,
    Mu buÉ—e ido duk ni da ke.

    Za mu je bakin ruwa,
    Da wurin hutu mu shantake.

    Za mu kallon namun dawa,
    Halittun Allah sassake.

    Na daÉ—e kewarki farin gani,
    Zuciya na hasko da ke.

    Fara, baƙa wa yas sani?
    Allah ne zai ba ni ke.
     
    Watakila ana ta hari ga ke,
    Fatsansu kikan tsattsallake.

    Sai tawa fatsar zinariya,
    Zan saƙala in saƙalo da ke.

    Allah sada mu da lafiya,
    Da imani ni da ke.

    A nan ne zan ja in tsaya,
    Amma da batu da na tsallake.

    Sai a gaba in mun haÉ—u,
    Inda zancen nan zan cike.

    Af! Na tuna ya Gimbiya,
    Tambaya É—aya zan yo wa ke-

    Ya bayanin KISHIYA?
    Ma’ana abokiyar zama ga ke?

    4 comments:

    1. Just remembered my teacher at secondary school "Wannan mai kwar biyu che"

      ReplyDelete
    2. Abu-Ubaida Sani27 July 2018 at 18:45

      Abin dariya wai yara sun tsinci hak'ori 😂.

      ReplyDelete
    3. Tabbas wannan kanin namu Allah ya baka wata baiwa wacce bamu da irin ta a kaf fadin Misau. Muna maka addu'a Allah ya kara maka basira, ya kara maka kariya da kuma daukaka

      ReplyDelete
    4. Abu-Ubaida Sani7 August 2018 at 14:32

      Malam Kawuwa (Yaya), muna godiya sosai.

      ReplyDelete

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.