Ticker

6/recent/ticker-posts

Manzanni Ashirin Da Biyar

MANZANNI 25

Farko da sunan Allah
Hakimu Jalla Jalalah
Shakur abin madallah
Kyautarshi dalla-dallah
Shine Wahabu Sarki Allah.

Ni Madaki sarauta
Nayi nufin na rubuta
Batu akan Magabata
Manzanni ‘yan gata
Kaji masoyan Sarki Allah.

Ya jama’a fa ku ganni
Kira nake fa kuji ni
Ko a cikin Kur’ani
Akwaishi fanni-fanni
Batu akan Manzannin Allah.

Adamu Baba Ubana
Batunka yau zan zana
Uba na kakannina
Uwa -Uban dangina,
Adamu kakan Manzon Allah.

Da na duba da na hanga
Da na juya da na waiga
A duniyarnan wagga
Babu uba ko Oga
Wajenka Adamu Manzon Allah.

Allah Shi Ya yiyo ka
Mala'iku a gareke
Sujud sukai wa kamarka
Aljanna kai da gwanarka
Tazam masaukin Manzon Allah.

Sai Idirisu fa nawa
Gareshi zan juyawa
Idi mutum dan mowa
Shi aka yo wa dagawa
Zuwaga Sarki Maliku Allah.

Alkaluma ya feke
ittatafa ya mike
Anan ya samo like
Idi, uba gun Zulke
Madaukaki kuma bawan Allah.

Taurarin da ka hanga
Iliminsu shi ya kaga
Lissafi yaka kirga
Harda fa dinkin riga
Duk da nufin Mahalicci Allah.

Saifa Nabiyyin Allah
Mai wa’azi abi Allah
Yay hakuri dan Allah
Nuhu abin madallah
Akan kira gun Sarki Allah.

Nayi nufin jan carbi
Akan uban duk arabi
Mai zuri’a daga Rabbi
Hamu da Yafizu dubi
‘Yayane gun Manzon Allah.

Zan daga sauti nawa
Na addu’a gun bawa
Ni bani son mantawa
Da Nuhu mai juyawa
Akan ruwan Dufanar Allah.

Hudu da Salihu nawa
Suma sunci yabawa
Manzannin Adawa
Samuda masu adawa
Kan addinin bautar Allah.

Mu dai munyi maraba
Da zuwan Hudu da Baba
Salihu mai son Rabba
Madaki mai abarba
Dauki shirin bin bayin Allah.

Na daga hannu Allah
Ka kara tsira Jallah
Akanshi Hudu Nasallah
Annabi Salihu jimlah
Madaukaka gun Sarki Allah.
 
Zanyi rubutun alli
Yabo ko dadai hali
Akan mutum mai kwalli
Ibrahimu Kalili
A wajen mai yin mulki Allah.

Ya bi umarnin Sarki
Maliku mai yin mulki
Anan ya samu mataki
Ibrahimu na kirki
Imamu gun duk bayin Allah.

Bani da ikon karta
Batun uban magabata
Dan kuwa yayi nagarta
Ka’aba shi ya ginata
Gami da layyar idin Allah.

Annabi Ludu alaika
Rahamar Allah kanka
Manzanci a hanunka
Ka fi uba sai kaka
Kokuma kakan Manzon Allah.

Matarshi ta ki yarda
Da abinda shi ya yarda
Sai Allah ko ya yarda
Da shi cikakken yarda
Ya bashi sakon tsoron Allah.

Mala’iku suka zo su
Wajenshi Ludu da kansu
Mabarnata ko dukansu
Nufinsu tozarta su
Sai aka kona kazamai, Allah!

Isma’ilu alaika
Sallallahu wa Baraka
Ruwanka babu da jaka
Ko mara niyyar Zakka
Kai kayi salla domin Allah. 

Allah yai maka gata
Ka’aba dakai gininta
Zamzam ma tushenta
Isma’ilu na Mutta
Sannan Da gun Manzon Allah.

Allahu ya yabaka
Hakuri babu kamarka
Safa da Marwa a kanka
Farauta tun daga kanka
Tazam sana’ar bayin Allah.

Alhaji dauki shirinka
Akan yabon Manzonka
Koko kace mar Kaka
Ishaku kam son barka
Mai ilimi gun bayin Allah.

Mala’ika Jibirilu
Dashi da Mika’ilu
Suka je gunshi Kalilu
Ibrahimu Rasulu
Akan busharar Manzon Allah.

Ishiyaku 'Da Alimu
Allah ma fa karimu
Yayi kiransa Alimu
Dan ya zo shi da ilmu
Akan umarnin Sarki Allah.

Zuwa ga danka Ubana
Madaki dan gurfana
Amma cikin lumana
Dan baya son barna
Yakubu Baban Manzon Allah.

Yayi nasiha babba
Tun daga Da har Baba
Da dukka mai yin gaba
Da Danshi Manzon Rabba
Yakubu tsoho mai son Allah.

Yayi Makantar kunci
Kuka ko harda na zuci
Domin yanada takaici
Batan diyanshi maceci
Yusufu Dan Manzannin Allah.

Yau ‘yan amshi gani
Da ni da Zulhusunaini
Yusufu mai kyan badani
Na Rabbi 'Dan Manzanni
Yusufu 'Da mai tsoron Allah.

Yusufu 'Dan Ya’akuba
Nayi maraba da tarba
Dan nayi murnar tsaraba
Ba kwai ba koko abarba
Sai dai tsoron Sarki Allah.

Ru’uya yai ta’awili
Awu ko yai ta da kaili
Mulkinshi babu falli
Sannan shifa Kalil
Yaki jinin mai sabon Allah.

Allah ka bani dama
In yabi Manzon fama
Manzo ne mara rama
Shu’aibu mai yin hikima
Wujen isar da wasikar Allah.

Yayi bayani sosai
Akan awun cin kosai
Mudun ma na gilasai
Dadin zance kuma sai
Shuaibu bawan sarki Allah.

Allah na roke ka
Da dukkanin sunanka
Ka kara tsirar gunka 
Kan Manzon da ka aika
Madyana birnin sabon Allah.

Adole yau zan zauna
In yabi Manzon guna
Kallamu Musa ubana
Haruna ko kakana
Kaji mazajen Sarki Allah.

Haaruna kai da Musa
Kunyi jihadin fansa
Allah yayi nufinsa 
Ayoyi tara an sa
Akansu arnan bautar Allah.

Fir’auna kayi dagawa
Hamana kayi adawa
Akanshi Musa nawa
Karuna kaiko wawa
Kaki ciyarwa domin Allah.

Allah ya daukaka ku
Aljannarsa ya baku
Haruna ne babbanku
A haife banda zuwanku
Isarda sakon Sarki Allah.

Tun banji kasala ba
Ya dace nayi duba
Ga makerina babba
Dawud nayi maraba
Sannu da himma Manzon  Allah.

Yayi umarnin sallah
Yay shari’a dan Allah
Alkali mai kamalah
Dawud mai yin sallah
Tsakan dare dan Sarki Allah.

Ai huduba a wajenshi
Aka samo ta zuwanshi
Zabbura a hanunshi
Azumi ko tun a kanshi
Tai falala inji Manzon Allah.

Santsi ya debeni
Na fadi gun mai bani
Shine dan husunaini
Mulkinshi babu raini
Sannu Sulaiman Manzon Allah.

Baiwarsace ta sani
Nayo rubutun karni
Yay mulkin shaidani
Mutum da tsuntsun tsauni
Da daukakar Mabuwayi Allah.

Iska ce motarshi
Aljan ko bawanshi
Sarauniya matarshi
Duk kwari sun sanshi
Kaji Sulaiman bawan Allah.

Allah bani basira
In yabi Manzon tsira
Ayuba mai kyan sura
Bai da nufin almara
Wajen biyayyar Sarki Allah.

Jarabawa daga Jalla
Ta riski bawan Alla
Shaidan ne mara salla
Ya shafi Manzon Allah
Ayuba dattijo gun Allah.

Allah yayi kiransa 
Sabiru koko da Hausa
Mahakurci wan kasa
Domin ya dau fansa
Rashin gazawa domin Allah.

Zilkiflu mai sona
Yabonka yau zan nuna
Halinka zan tattauna
Manzon Ubangijina
Maliku Sarkin bayin Allah.

Duk wani bawan Allah
A zamaninka na sallah
Sun buya dan mara sallah
Ta nan ka samu kamalah
Zilkiflu mai kaunar Allah.

"Zil" ma’aboci kenan
"Kiflu" ko reno kenan
Zuwa ga hausa fa kenan
Dan haka shine wannan
Mai renon Manzannin Allah.

Yunusa Manzon tsira
Ya zama dole na tsara
Yabon dab a almara
Domin ka sha madara
A rakumar gun tekun Allah.

Kayi fishi dan Allah
Kan jirgi kayi sallah
Kuri’a da nufin Allah
Ta nuna Manzon Allah
A cikin dubban bayin Allah.

Ni Madaki muhti
Zan yabi bakon huti
Tasbihinsa da kati
Anan ya samu mataki
Cikin gidan aljannar Allah.

Sai wa na Iliyasu
Mai wa’azi ga dukansu
Arna masu yawansu
Koko nace maka masu
Bautan gunki wai shi Allah.

A Ba’alabak suka zauna
Da shi da dangin bauna
Ba’a'ala mai kan waina
Dan sun rikeshi da kauna
A maimakon Mahalicci Allah.

Ni’imar Allah kanka
Shi ya kira sunanka
Ilyasu kakan kaka
Mudi zashi wajenka
Ka tsakura mai tsoron Allah.

Cikin dabara zan je
Na gaida mai kyan saje
Yasa’u ka fi mazaje
Kaifinka ya fi na lauje
Wajen isar da wasikar Allah.

Alyasa’u Manzo ne
Cikin dubu kwara ne
Cikar sani wahayi ne
Dan haka mai ilimi ne
Annabi ne gun Sarki Allah.

Tahiyyati hannunka
Kasidati dominka
Muhibbati kallonka
Yasa’u komai naka
Sannu Nabiyyul Lahi na Allah.

Zani kiran Zakariyya 
Annabi ne mara karya
Danginshi babu karya
Shi ne baban Yahaya
Sannan dattijo gun Allah.

Bautarshi babu wasa
Yarenshi sak da Hausa
Kuri’arshi yaci gasa
Maryam innar Isa
Duk a hanun Zakariyan Allah.

Allah yayi kiranshi
Da shi da duk zuri’arshi
Zakariyya da diyanshi
Tare da ma matarshi
Wajen ibadar Sarki Allah.

Yahaya ja ni wajenka
Na shafi dan girmarka
Annabci a hanunka
Tun a gadon innarka
Kaji masoyin Sarki Allah.

Sallal Lahu alaika
Da kai da ma babanka
Nifa ina kaunarka
Ka bani dammar binka
Cikin gidan aljannar Allah.

Isa mai Linjila
Kaunarka ce yau zalla
Tasa nayo ma kwalla
Begenka na malala
Kan Mahamud mai tsoron Allah.

Ya warkas da makafi
Kuturu har mara tafi
Kurma Da da mahaifi
Har gawa mara karfi
Tay magana da Ma’aikin Allah.

Dan Maryam Manzo ne
Wajen Nasara Amir ne
Gun Allah bawa ne
Isa marar baba ne
Tamkar Adamu Manzon Allah.

Bani tunanin gunka
Da dukkanin natsuwarka
Zan yabi Manzon Makka
Muhammadun na so ka
Sannu fiyayyen bayin Allah.

Duk acikin Manzanni
Kai ka zamo murjani
Kai aka ba Kur’ani
Sarkin Hurul aini
Muhammadun mai tsoron Allah.

Yay hijira da Sahabbai
Jikinsu babu takubbai
Sunje basu da kwabbai
In karya ne tambai
Masu nasiha domin Allah.

Ya ma’abocin sallah 
Bashiru bawan Allah
Ka ceci bayin Allah
A randa ba wani haulah
Sai a wajen Mahalicci Allah.

Sannu madubi babba
Ga dukka Da har baba
Wanda yace ba kai ba
Aradu ba tababa
Zai ga azabar Sarki Allah.

Ni na kara salati
Wajenka mai kyan zati
Kafin inyi wafati
Ni Madakin baiti
Na gode maka Sarki Allah.

Na yabi duk manzanni
Su suka zo Kur’ani
Sai ku rikesu ku barni
Ni a Misau aka yo ni
Birnin bautar Sarki Allah.

Wallahul Musta'an!!!
Mal. Mahmudul Kalaam

Mal. Mahmudul Kalaam 
17 October, 2014

Post a Comment

0 Comments