Amru bn Salama al-Hamdaniy ya ce:
((Mun kasance muna zama a kofar gidan Abdullahi bn Mas'ud (ra) kafin Sallar Asubah, idan ya fito sai mu tafi Masallaci tare da shi. Sai Abu Musa al-Ash'ariy (ra) ya zo ya same mu, sai ya ce: "Shin Abu Abdirrahman ya fito?"
Sai muka ce: A'a, bai fito ba tukun.
Sai ya zauna tare da mu, har sai da ya fito. Yayin
da ya fito gaba dayanmu sai muka tashi muka tafi wajensa. Sai Abu Musa (ra) ya
ce masa:
"Ya Baban Abdirrahman, lallai dazu na ga wani
abu a Masallaci wanda ban san shi ba, amma - Alhamdu lillah - ban ga komai ba
sai alheri".
Sai ya ce: "Miye shi?".
Sai ya ce: "Idan muna raye wata rana za ka
gani". Sai ya ce:
"Na ga wasu mutane a Masallaci suna zaune sun
yi da'ira, suna jiran Sallah. A kowace da'ira akwai mutum daya a tsakiya, suna
rike da tsakuwa a hanayensu, sai ya ce musu: ku yi kabbara 100, sai su yi, sai
ya ce: Ku yi Hailala 100, sai su yi. Sai ya ce: Ku yi Tasbihi 100, sai su
yi".
Sai Ibnu Mas'ud ya ce: "To me ka ce
musu?".
Sai ya ce: "Ban ce musu komai ba, ina jiran
ra'ayinka da umurninka".
Sai ya ce: "Ba za ka umurce su su kirga
munanan aiyukansu ba? Na lamunce musu kyawawan aiyukansu ba za su bata
ba".
Sa'annan sai ya wuce muka tafi, har sai da ya je
da'ira daya daga cikin wadannan halkoki sai ya tsaya a kansu, sai ya ce:
"Menene wannan abin da na ga kuna yi?".
Sai suka ce: ya kai Baban Abdirrahman, tsakuwa ne
muke kirga kabbarori da Hailala da Tasbihi.
Sai ya ce: "Ku kirga munanan aiyukanku, na
lamunce muku babu wani abu na kyawawan aiyukanku da zai bata.
Kaiconku ya ku al'ummar Annabi, Na yi mamakin
saurin halakarku! Wadannan Sahabban Annabinku ne (saw) suna nan a cike, ga nan
tufafinsa ba su rube ba, ga nan kwaryayen da yake amfani da su ba a fasa ba. Na
rantse da wanda raina yake hanunsa, lallai imma kuna kan hanya wacce ta fi
hanyar Annabi (saw) shiriya, ko kuma ku masu bude kofar bata ne!".
Sai suka ce: Ya Baban Abdirrahman, Wallahi ba mu
nufi komai ba sai alheri!
Sai ya ce: "To mutum nawa suke nufin alheri
amma ba za su dace da shi ba?!".
Lallai Manzon Allah (saw) ya ba mu labari:
((Lallai wasu mutane suna karanta Alkur'ani amma
ba ya wuce makoshinsu)). Na rantse da Allah, ban sani ba la'alla mafi yawansu
daga cikinku suke)).
Sa'annan ya juya ya tafi.
Amru bn Salama ya ce: Mun ga da yawan wadancan
halkoki suna sukarmu da masu a ranar yakin Nahrawan, suna tare da
Khawarijawa)).
Duba:
سنن الدارمي (1/ 286 - 287)
A yau idan ka samu 'Yan Maulidi ka ce: Me kuke yi?
Sai su ce: Babu abin da muke yi a cikin Maulidi
face Karatun Alkur'ani, da Zikiri, da Salatin Annabi (saw), da Karanta
Tarihinsa, da rera wakokin yabon Manzon Allah (saw), don nuna soyayya ga Annabi
(saw) da murnan zagayowar ranar haifuwarsa.
Sai ka ba su amsa da maganar Ibnu Mas'ud (ra) inda
ya ce:
"Lallai imma kuna kan hanya wacce ta fi
hanyar Annabi (saw) shiriya ko kuma ku masu bude kofar bata ne!".
Idan suka ce: Wallahi mu ba mu nufi komai ba sai
alheri!
Sai ka fada musu maganar Ibnu Mas'ud (ra) ya ce:
"To mutum nawa suke nufin alheri amma ba za su dace da shi ba?!".
Bidi'a shu'uma ce, aikin Ibada, bisa kyakkyawar
niyya, amma saboda ba ta cikin Shari'ar da Annabi (saw) ya zo da ita sai ta
zama sharri a maimakon alheri.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.