Kowace kungiya tana da Usul, wato manyan ginshikan da aka gina ta a kansu, haka kuma tana da alamomi da siffofi na mabiyanta (السمات).
Misali ginshikan Khawarijanci su ne:
- Kafirta Musulmai da abin da bai kai kafirci ba,
bisa shubuhar "Hakimiyya".
- Da kuma halasta jinanen Musulmai, da daukar
makami a kansu.
Kowane daya daga cikin wadannan guda biyu suna
tabbatar wa mutum Khawarijanci. Shi ya sa duk wanda yake da Akidar kafirta
Musulmai, bisa shubuhar "Hakimiyya", ko da bai taba kashe kowa ba,
kuma ko da yana zaune cikin gari tare da sauran al'umma, to shi Bakhawarije ne
zaunanne, wanda ya zauna bai yi hijira ya yi kaura ya bar garin da suke kira
garin kafirci ba. Sawa'un yana kira ga Akidar tasa ko a'a. Irin wadannan su ake
kira Khawarijawa zaunannu (الخوارج القعدة). Dole
sai ya zama suna dauke da Akidar Khawarijanci, na ginshikan nan guda biyu da
suka gabata.
Kuma Khawarijawa suna da Siffofi masu yawa (السمات), wasu lazimai ne da su, ba sa rabuwa da su, wasu kuma ba
lazimai ba ne. Daga cikin siffofinsu lazimai akwai rashin fahimtar Addini
(jahilci), da wautar tunani, da guluwwi a ibada, a Sallah da Azumi da karatun
Alkur'ani, kamar yadda Annabi (saw) ya yi bayaninsu.
Haka daga cikin Siffofinsu wadanda ba lazimai ba
akwai: askin malu, wato aske kai tal-tal. Kamar yadda Annabi (saw) ya ce:
«يخرج ناس من قبل المشرق، ويقرءون القرآن لا يجاوز تراقيهم، يمرقون
من الدين كما يمرق السهم من الرمية، ثم لا يعودون فيه حتى يعود السهم إلى فوقه»، قيل
ما سيماهم؟ قال: «سيماهم التحليق - أو قال -: التسبيد»
صحيح البخاري (9/ 162)
((Wasu mutane za su fito ta bangaren gabashi, suna
karanta Alkur'ani amma ba ya wuce makoshinsu (ya isa zukatansu), suna fita daga
Addini kamar yadda mashi yake fita daga abin da aka harba, sa'annan ba sa
dawowa gare shi, har sai mashin ya dawo samansa, (wurin da ake daure zare). Sai
aka ce: miye alamarsu?
Sai ya ce: "Alamarsu ita ce aske kai, ko cewa
ya yi: malu)).
Ka ga wannan Hadisi yana nuni ne ga sifar
Khawarijawan farko, don haka a yau ba za ka ce dole sai ka ga masu malu kafin
su zama Khawarijawa ba.
Don haka yana daga cikin Guluwwi jingina mutum ga
Khawarijanci don kawai an ga wata alama tasu a tare da shi. Shi ya sa hatta
Munafurci ma, mutum ba ya zama cikakken Munafuki har sai ya hada alamomin da
Annabi (saw) ya fada a cikin Hadisi:
«أربع من كن فيه كان منافقا خالصا، ومن كانت فيه خلة منهن كانت
فيه خلة من نفاق حتى يدعها: إذا حدث كذب، وإذا عاهد غدر، وإذا وعد أخلف، وإذا خاصم
فجر»
صحيح البخاري (1/ 16)، صحيح مسلم (1/ 78)
((Wasu siffofi hudu duk wanda suka kasance tare da
shi to ya kasance tataccen Munafuki, wanda yake da sifa daya daga cikinsu to ya
kasance yana da sifa ta munafurci har sai ya barta: idan ya yi magana ya yi
karya. Idan ya kulla yarjejeniya sai ya yi ha'inci. Idan ya yi alkawari ya
karya. Idan ya yi husuma sai ya yi fajirci)).
Wannan ya nuna ashe sashe na siffofin Sunayen
Shari'a masu hukunci ba sa sa mutum ya zama tataccen mai wannan sunan, kamar
sunan kafiri, munafuki, bakhawarije, dan bidi'a da sauransu.
Wannan ya sa don kawai mutum ya yi inkari wa
shugaba a kan Mimbari ko ya caccake shi, ya soke shi, alhali shugaban ba ya
wajen, kuma shi mutumin ba ya dauke da wadancan ginshikan guda biyu to bai zama
Bakhawarije ba, duk da kasancewar hakan alama ce ta Khawarijawa. Khawarijawa
aka sani da tara jama'a suna sukar shugaba, da sunan inkarin munkari, alhali
shugaban ba ya wajen.
Wannan ya sa duk masu kafa hujja da riwayoyi daga
Salaf a kan inkari wa shugaba a fili cikin hujjojin ba mu ga wanda wani cikin
Salaf ya hau kan mimbari yana inkari wa shugaba ba, ko ya tara mutane yana
inkari wa shugabanni. Shaikh Ibnu Uthaimeen ya ce:
((كلامنا على الإنكار على الحاكم مثل أن يقوم الإنسان -مثلا- في
المسجد ويقول: الدولة ظلمت الدولة فعلت، فيتكلم في نفس الحكام، وهناك فرق بين أن يكون
الأمير أو الحاكم الذي تريد أن تتكلم عليه بين يديك وبين أن يكون غائبا؛ لأن جميع الإنكارات
الواردة عن السلف إنكارات حاصلة بين يدي الأمير أو الحاكم)).
لقاء الباب المفتوح (62/ 13، بترقيم الشاملة آليا)
A nan sai Ibnu Uthaimeen ya nuna cewa; don Gomnati
ta yi wasu Munkarai, ba dadai ba ne mutum ya tashi cikin Masallaci yana inkari,
alhali shugaban ba ya wajen. Sai ya tabbatar da wata ka'ida kamar haka:
((Dukkan inkarori ga shugaba wadanda aka ruwaito
daga Salaf inkari ne da suka faru a gaban gomnan ko shugaban kasan)).
Don haka ba za ka hau mimbari a garinku kana
inkari wa shugaban kasa ko gomna, alhali ba sa wajen, sa'annan ka zo kana raya
cewa: -wai- ai Salaf sun yi inkari wa shugaba a fili. A'a, ba mu san haka daga
Salaf ba. Irin wannan inkarin aiki ne na Khawarijawa.
Abin nufi shi ne fadakarwa a kan wadannan
mas'aloli da suka rikice wa mutane, tsakanin masu guluwwi suna Khawarijantar da
Malamai Ahlus Sunna da wani aiki ba ginshikai na Khawarijancin ba, da kuma masu
kafa hujja da inkarin Salaf don halasta inkari wa shugaba a kan mimbari, alhali
shugaban ba ya wajen.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.