Asali 'Yan Bidi'a sun yarda Maulidi Bidi'a ne. Sun san babu dalili na Shari'a da ya yi nuni a kan bikin Maulidin. To ganin Ahlus Sunna sun matsa musu da inkari, saboda Annabi (saw) ya ce: "Duk wanda ya yi bidi'a an mayar masa", kuma ya ce: "Kowace Bidi'a bata ce,, kuma tana wuta", to sai suke neman abokan bata, abokan shiga wuta. Ma'ana su ba za su dena bidi'ar ba, amma ku ma Wahabiyawa kuna yin bidi'a, don kuna yin Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi.
Wannan shi ake kira "Ilzami" a ilimin
"Jadal da Munazara", amma sai dai hujja ce mai rauni a wajen
"Mu'aradha", sai dai a yi amfani da "Ilzami" don nuna bacin
ra'ayi ko bacin dalili, wannan kuma ba shi ne muhallin maganarmu da su ba.
Don haka abin tambaya shi ne; shin da gaske yin
Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi bidi'a ne, ko yana da asali a Shari'a?
Lallai ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari da
Muslim, daga Ibnu Abbas (ra) ya ce:
«كان رسول الله صلى الله عليه وسلم أجود الناس، وكان أجود ما
يكون في رمضان حين يلقاه جبريل، وكان يلقاه في كل ليلة من رمضان فيدارسه القرآن، فلرسول
الله صلى الله عليه وسلم أجود بالخير من الريح المرسلة»
صحيح البخاري (1/ 8)، صحيح مسلم (4/ 1803)
"Manzon Allah (saw) ya kasance mafi kyautan
mutane, kuma ya kasance mafi kyauta a cikin watan Ramadhan, lokacin da Mala'ika
Jibril (as) yake haduwa da shi, ya kasance yana haduwa da shi a cikin kowane
dare na watan Ramadhan, sai su yi DARASIN ALKUR'ANI TARE, lallai Manzon Allah
(saw) ya fi iska mai kadawa yawan kyauta da alheri".
Wannan Hadisi ya nuna cewa; Lallai Annabi (saw) da
Mala'ika Jibril (as) suna haduwa suna yin darasin Alkur'ani a kowane daren
Ramadhan har ya kare.
Shi ya sa Ibnu Battal ya ce:
"...ومدارسته له القرآن فى كل رمضان. وخص رمضان بذلك، لأن الله تعالى
أنزل فيه القرآن إلى السماء الدنيا، ولتتأسى بذلك أمته فى كل أشهر رمضان، فيكثروا فيه
من قراءة القرآن، فيجتمع لهم فضل الصيام والتلاوة والقراءة والقيام".
شرح صحيح البخارى لابن بطال (1/ 40)
Sai ya ce: suna yin Darasin Alkur'anin a kowane
dare na Ramadhan ne don a Ramadhan din aka sauke Alkur'anin, kuma DON
AL'UMMARSA SU YI KOYI DA SHI, su ma suna yin Darasin Alkur'anin a kowane watan
Ramadhan.
Malamai masu sharhin littatafan Hadisai sun
tabbatar da cewa; wannan Darasi na Alkur'ani a cikin Ramadhan MUSTAHABBI ne,
saboda wannan Hadisi. Kamar al-Nawawiy, al-Ainiy, inda ya ce:
"ومنها استحباب استكثار القراءة في رمضان ومنها استحباب مدارسة
القرآن وغيره من العلوم الشرعية".
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (1/ 77)
In kun lura shi har ma ya kara da sauran Ilmomin
Shari'a, duka dogaro da wannan Hadisi na Ibnu Abbas (ra).
Sannan akwai Hadisin Abu Huraira (ra) wanda Muslim
ya ruwaito, wanda ya fadi ladan masu haduwa a Masallaci suna Darasin Alkur'ani:
Annabi (saw) ya ce:
«وما اجتمع قوم في بيت من بيوت الله، يتلون كتاب الله، ويتدارسونه
بينهم، إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة وحفتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن
عنده،».
صحيح مسلم (4/ 2074)
"Babu wasu mutane da za su taru a daki daga
cikin dakunan Allah (Masallaci), suna karanta Littafin Allah, suna Darasinsa a
tsakaninsu, face nitsuwa ta sauka a kansu, rahma ta lullube su, Mala'iku sun
kewaye su, kuma Allah zai ambace su a wajen wadanda suke wajensa".
Malamai sun yi sharhin Hadisin inda suka bayyana
cewa; Hadisin yana nufin mutane su taru a Masallaci, sashensu yana koyar da
sashe, kamar yadda Alkali Iyadh ya fada, inda ya ce:
"قال القاضى: قد يكون هذا الاجتماع للتعلم بعضهم من بعض، بدليل
قوله: "ويتدارسونه بينهم"، ومثل هذا لم ينه عنه مالك ولا غيره".
إكمال المعلم بفوائد مسلم (8/ 195)
Shi kuma al-Dibiy shi ya fito da ma'anar DARASIN
ALKUR'ANIN A FILI, inda ya ce:
"و"يتدارسون" شامل لجميع ما يناط بالقرآن من التعليم
والتعلم، والتفسير، والاستكشاف عن دقائق معانيه."
شرح المشكاة للطيبي الكاشف عن حقائق السنن (2/ 665)، وانظر:
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح (1/ 287)
Ya ce: "Ma'anar suna Darasinsa" ya
kunshi dukkan abin da yake rataye da Alkur'ani na koyarwa da koyo da TAFSIRI,
da kuma binciko boyayyun ma'anoninsa".
Kuma wannan bai takaita ga Masallaci kadai ba,
kamar yadda Imam al-Nawawiy ya ce:
"ويلحق بالمسجد في تحصيل هذه الفضيلة الاجتماع فى مدرسة ورباط
ونحوهما إن شاء الله تعالى ويدل عليه الحديث الذي بعده فإنه مطلق يتناول جميع المواضع
ويكون التقييد في الحديث الأول خرج على الغالب لا سيما في ذلك الزمان فلا يكون له مفهوم
يعمل به".
شرح النووي على مسلم (17/ 22)
Saboda haka idan mun lura da wadannan Hadisai guda
biyu za mu ga cewa; MUSTAHABBI ne ana haduwa a Masallaci ko wani wajen daban, a
cikin watan Ramadhan ana yin Darasin Alkur'ani, har watan ya fita.
Kuma Malaman sun ce: Ma'anar Darasin Alkur'ani shi
ne a samu bangarori guda biyu suna karanta Alkur'ani, suna TAFSIRINSA, suna
bayanin ma'anoninsa, sauran mutane kuma suna sauraro suna koyon ilimi.
Da wannan muke cewa; Tafsirin Alkur'ani a watan
Ramadha yana cikin Addini, kuma Sunnar Annabi (saw) ne, kuma Mustahabbi ne.
Aikin lada ne mai girma. Don Allah zai saukar da Mala'iku su kewaye su, kuma
nitsuwa za ta sauka a kansu, rahama za ta lullube su.
Wannan shi yake nuna cewa; Tafsirin Alkur'ani a
watan Azumi SUNNA NE BA BIDI'A BA. Ba kamar Maulidi yake ba, wanda shi kam
bidi'a ne da bata mummuna.
Kun ga dai duka wadannan Malaman da na kawo maganganunsu
babu Bawahabiye ko daya.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.