Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Raka'atanil Fajr

TAMBAYA (171)

Assalamu alaikum warahmatullah, ALLAH ya kara lfy da nisan kwana masu albarka Amin. Malam ina tambaya akan raka'atul fajr, yaushe mutum yakama yayi sallan raka'atul fajr. Na gode

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Ana yin sallar Rakaatanil Fajr ne kafin sallar Asubah sannan Kuma ba laifi bane idan mutum ya makara yayita bayan sallar Asubah din saidai baason ka maida hakan dabi'ar ka

Anan zanyi amfani da damar da Allaah ya bani ta bincike na qara fito Mana da girman ladan da ake samu silar sallar Rakaatanil Fajr

Wai shin ko kasan da cewar idan Dangote ya manta baiyi Rakaatanil Fajr ba Kai Kuma kayita kafin sallar Asubah din, a wannan ranar ka fishi arziqi domin kuwa ya tabbata a cikin Sahihu Muslim (725) cewar Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace sallar Rakaatanil Fajr tafi duniya da Abinda ke cikinta

Kuma Dangote fa shine mutum na 158 a kudi a duk duniyarnan mai daukeda mutane kusan biliyan 8 da Miliyan 500, matsayinsa a Africa ne dai yake na 1 domin kuwa ya mallaki Sama da 13.4 billion dollars, kamar yanda mujallar Bloomberg Billionaires Index ta wallafa a August 2024

Kuma abin mamakin shine, ita Rakaatanil Fajr fa Nafilace saboda duk abinda yake nafila baikai Farilla girman lada ba. Allaahu Akbar

Nayi Mana Misali da Dangote ne don mugane girman ladan dake cikin wannan Nafila ta musamman. Bernard Arnault mamallakin company Mai suna LVMH da suke siyarda Kaya irinsu Louis Vuitton, Moët & Chandon da Kuma Hennessy, shine Wanda yafi kowa kudi a duniya, yanada sama da $180 billion dollars Kaga ya ninninka Dangotenmu kudi sau 13 kenan

Elon Musk Kuma shine na 2 a duniya (yanayin sauka da hawan farashin dollars Kuma Yana zama na 1 wasu Kuma sukace shine na 2), yanada zunzurutun kudi sama da $247 billion dollars, shine mamallakin company Tesla, SpaceX da suke Kai mutane duniyar wata, Neuralink da The Boring company Kuma shine Wanda ya site Twitter gaba dayanta. Shine yace ya zabi ya sgiga Jahannama da ace dai ya musulunta, Wal iyazubuillah

Sai Kuma Jeff Bezos (shine na 2 ko Kuma na 3), Mai company Amazon, yanada sama da $211 billion dollars, mamallakin The Washington Post, Blue Origin, Kuma founder na Bezoe Expedition

Mukesh Ambani, dan Indiya ne, a qalla yanada samada, $125 billion dollars, mamallakin Jio Platforms, shugaban Reliance Industry India

Kai Kuma Mai karanta wannan bayanan, bakada ko dollar 1,000🤣a aljihunka ko a yar Purse dinki (dollar dubu shine N1,700 sau 1,000 zai kama N1,700,000 kenan), amman Alhamdulillah tunda ke musulmace idan kika sallaci Rakaatanil Fajr to ka zarce wadannan Kafiran ta fannin arziqin duniya da na lahira kamar yanda hadisin ya tabbata a cikin Sahihu Muslim, domin kuwa har yanzu ko Astaghfirullah ba wanda ya taba firtawa a cikinsu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ar-Razzaqu Allaah Azzawajallah Mai azurta mushrikai a duniya Mai sakawa musulmai a Lahira

Jamaa wallahi kada muje muyi biyu babu, garin neman duniya mu rasa Aljannah. Mu dage da sallar Rakaatanil Fajr

Wallahu taala aalam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments