Ticker

6/recent/ticker-posts

"Malam Bawa Magajin Doka" Inji Dakta Mamman Shata Katsina

An haifi Malam Abdullahi Attahiru da ake yi wa laƙabi da Malam Bawa a garin Shinkafi, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Shinkafi ta Jihar Zamfara a shekarar 1942.

Ya yi karatun Addinin Musulunci gwargwadon hali, haka zalika ya halarci Makarantar Elimentare ta garin Shinkafi wadda ake kira Magaji Dango a halin yanzu, a cikin shekarun 1950s, daga nan kuma ya shiga aikin Doka.

An naɗasa Magajin Doka na Shinkafi a lokacin mulkin Marigayi Mai girma Dagacin Shinkafi, Alhaji Ibrahimu wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 1950 zuwa rasuwarsa a shekarar 1990. Allah ya jaddada masa rahama, amin.

Malam Bawa Magajin Doka ya shahara sosai a cikin wannan aiki nasa saboda ƙoƙari da ƙwazo da gaskiya da riƙon amanarsa. Mutum ne mai basira da hikimar aiki ainun.

Bayan an mayar da aikin Doka zuwa aikin Ɗan Sanda sai aka canza masa aiki ya zuwa hukumar kula da Yan Sanda. Aikin da ya ci gaba da gudanarwa har zuwa lokacin da ya yi ritaya. Ya yi ritaya a daidai lokacin da ya ke aiki a "Yar Marina Police Station" dake cikin Birnin Sakkwato wadda tana cikin muhimman wurare na aikin Yan Sanda dake Sakkwato da kewaye a wancan lokaci.

Ya amsa kiran Mahaliccinsa, Allah SWT a watan Nuwambar shekarar 2012, a lokacin ya na da shekaru 70 daidai a duniya. Allah ya jiƙan sa da rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

Ya bar matan aure, da 'ya'ya guda 8. Maza 2, Mata 6 kuma suna nan raye a wurare daban daban na Nijeriya suna ci gaba da rayuwa. 

"Malam Bawa Magajin Doka" Inji Dakta Mamman Shata Katsina

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
08149388452,
08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Talata, 10/09/2024.

Post a Comment

0 Comments