Mutane da yawa sukan yi kuskure wajen auna Malaman Muslunci, ta yadda suke daukansu kawai duka Malamai ne, za a daidaita su a sahu daya na Malaman Muslunci, har a nuna babu banbanci a tsakaninsu. An dauka cewa; sabanin da yake tsakaninsu kawai sabani ne irin na tsakanin Mazhabobin Fiqhu, wato sabani a Mas'alolin Ijtihadi, wadanda za a iya sabani a cikinsu, kuma kowa ya rike fahimtarsa a zauna lafiya, ba tare da inkari ma sashe ba.
A'a, dole akwai banbanci matukar sun banbanta a
Manhaji. Don haka babu yadda za a yi ka hada tsakanin Malamin da yake kan bin
Alkur'ani da Sunna bisa Mazhabar Salaf Ahlus Sunnati wal Jama'a, da Malamin da
ya bi hanyar Ilmul Kalam da Falsafa, ya gabatar da hankalinsa a kan Alkur'ani
da Hadisi. Don Annabi (saw) bai zo mana da Ilmul Kalam ko Falsafa ba, duka daga
Turawan Girka aka dauko su, aka shigo da su cikin al'ummar Musulmi.
Misali, tsakanin Ibnu Taimiyya da Fakhruddeen
al-Raziy, ko Abu Hameed al-Gazzaliy, kar ka dauka kawai Malamai ne cikin
Malaman Muslunci shi kenan, don haka kawai sabani suka yi a mas'aloli, kuma ba
matsala ba ne idan an yi sabani a cikinsu. Ta yadda za a kalle su ne a matsayin
kowanensu kawai ya kware ne a abin da dayan bai kware a kansa ba, ta yadda za a
iya cewa; wane ya dace a mas'ala kaza, wancan kuma ya kuskure a cikinta, amma
kuma ya dace a wata mas'alar daban, kamar yadda lamarin yake a mas'alolin Ijtihadi,
na sabani tsakanin Malaman Fiqhu.
A'a Malam, sam ba haka lamarin yake ba. Yadda
lamarin yake asali sun yi sabani ne a Manhajin Daukar Addini. Shi Ibnu Taimiyya
yana kan Manhaji ne na Salaf; Sahabbai da Tabi'ai da mabiyansu da kyautatawa.
Su kuma Ghazzaliy da Raziy, hanyarsu hanya ce ta Ilmul Kalam wanda ya samo
asali daga Falsafar Girka, ta su Aristotle. Don haka sabaninsu ba a Mas'aloli
ne wadanda za a iya sabani a cikinsu ba, a'a, sabaninsu ya wuce nan, sabani ne
a Manhaji da hanyar daukar Addini da Masdarinsa, da kuma sabani a manyan Mas'aloli
na Tushen Addini.
Raziy da Ghazzaliy su guma-gumai ne na Bidi'ar
Ilmul Kalam, wadanda suka kauce hanyar Sunna, tafarkin da Annabi (saw) ya dora
Sahabbansa a kansa. Suke ganin cewa; hankalinsu zai iya cin karo da Alkur'ani
da Sunna, kuma har su gabatar da hankalin a kan Alkur'anin da Sunnar! Har ya
kai ga za su yi tawilin Ayoyi da Hadisan, su tankwara su, su canza su, su sanya
su su dace da yadda suke so a tunaninsu da hankalinsu. Saboda su a wajensu
Hankulansu dalili ne na yankan shakku, amma su kuma Alkur'ani da Hadisi dalilai
ne na zato, ba sa bayar da yakini wajen sanin Allah da Siffofinsa.
Wannar ita ce Bidi'a mai hatsarin da Malaman Ilmul
Kalam suka kirkira a cikin wannan Addini. A Fili karara Raziy da shi da Amidiy
suka furta cewa; Alkur'ani babu yakini a cikinsa sai zato kawai.
Wannan ya sa suke kore hakikanin Siffofin Allah
suka zo cikin Alkur'ani da Sunna. Suke watsi da Hadisi Ahaad, suka ce: kwata -
kwata ba a daukar Mas'ala ta Akida daga gare shi.
A Babin Kaddara kuma suka tafi bisa abin da
hakikaninsa shi ne Akidar Jabariyya, masu kore wa bawa iko da zabin aikata
aiyukansa, don haka suke danganta wa Allah hatta aiyukan bawa munanan da
aiyukan alfasha, su ce aikin Allah ne. Don haka idan Allah ya azabtar da bawa
to ya zalunce shi. Saboda hakikanin "Kasab" (الكسب) shi ne cewa; bawa yana da iko amma maras tasiri a kan aikinsa
(da akwai da babu shi duk daya).
To ta yaya za a daidaita sabani a irin wadannan
mas'aloli da sabani a mas'alolin Ijtihadi wadanda Malaman Fiqhu suke sabani a
cikinsu?
Ta yaya za a sanya sabanin a tushen Addini da
Manyan mas'alolinsa ya zama tamkar sabani a Furu'a da rassa na Addini?
Amma shi kuma Ibnu Taimiyya fa, Manhajinsa manhaji
ne na girmama Wahayi, da daukan Addini kai tsaye daga gare shi, da kuma sabunta
Addini ta hanyar farfado da Mazhabar Salaf, bayan Manyan Bidi'o'i na Sufanci da
Shi'anci da Ash'ariyyanci da Falsafa sun binne shi. Ya zo ya yaki wadannan
bidi'o'i da hujja da ilimi da bayani, ya tabbatar - bisa dalilai - cewa;
lafiyayyen hankali ba ya cin karo da Tabbataccen Nassi. Tare da bayyana rashin
alaka tsakanin Mazhabar Salaf da hanyar Malaman Ilmul Kalam, da rashin kusaci
tsakanin Falsafa da Shari'a, kamar yadda su Farabiy da Ibnu Sina suka yi
kokarin daidaita tsakaninsu. Ya zo ya tsaftace Addini daga shubuhohin Malaman
Ilmul Kalam da 'Yan Falsafa da Sufaye, wadanda suka gurbata Addinin mutane da
su. Ya tabbatar da cewa; babu sabani tsakanin hankali na Fidira da Wahayi da
Nassoshin Shari'a. Ya taimaki Sunna, ya tabbatar da hujjar Hadisan Annabi
(saw); duk wanda hankalinsa ya nuna masa gaskiyar Annabi (saw), to idan ya ki
gaskata shi a Hadisinsa to ya karyata hankalin nasa, kuma ya zama hankalin ba
shi da amfani.
Don haka idan za a auna Ibnu Taimiyya da Raziy ko
Gazzaliy kamata ya yi a auna su da Manhajin da kowannensu yake kai, ba da
mas'aloli ba.
Misali a kan haka a wannan zamani; kamar Dr.
Qardhawiy ne tsakaninsa da Malamai irin su Shaikh Ibnu Baaz, Ibnu Uthaimeen da
Albaniy, asali Manhajinsu ba iri daya ba ne, don haka ba za a kwatanta su a
mas'aloli ba.
Wannan Qardhawiy kenan da ake danganta shi ga
malumta, ina kuma irin su Sayyid Qutub, Hassanul Banna da makamantansu, wadanda
an yi ittifaqi cewa ba Malamai ba ne.
Haka a kasarmu tsakanin Shaikh Abubakar Gumi da
Shehin Bauchi, ba za a daidaita su ba, saboda Manhajinsu ba iri daya ba ne.
Ala ayyi halin, idan za a auna Malaman Muslunci ba
dadai ba ne ana auna su da daidaikun mas'aloli, a'a, za a auna su ne bisa
Manhajin kowanne daga cikinsu. Babu yadda za a yi a daidaita mai Bin Mahajin
Sunna, Manhajin da Annabi (saw) ya dora Sahabbansa a kai da kuma wanda yake kan
Manhajin da ya saba haka. Babu yadda za a yi a daidaita su a sahu daya, saboda
ba a kan hanya daya suke ba.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.