Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari a Kan Bambance-Bambancen Da Ke Tsakanin Wakokin Gargajiya Da Na Zamani, Bincike Na Musamman Na Wakokin Sarauta Na Alhaji Musa Danƙwairo Da Na Gama-Gari Na Aminu Ladan Abubakar (ALAn Waka) - 1 Shafukan Farko

ƘUNSHIYA

1. Shafukan Farko

2. Babi Na Ɗaya

3. Babi Na Biyu

4. Babi Na Uku

5. Babi Na Huɗu

6. Babi Na Biyar

Wannan kundin binciken an samar da shi ne domin samun shaidar takardar karatun digiri na farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Tsangayar Karatun Digiri, Kwalejin Ilmi Da Ke Gumel, Kulawar Jami'ar Bayero, Kano.

NAZARI A KAN BAMBANCE-BAMBANCEN DA KE TSAKANIN WAƘOƘIN GARGAJIYA DA NA ZAMANI, BINCIKE NA MUSAMMAN NA WAƘOƘIN SARAUTA NA ALHAJI MUSA ƊANƘWAIRO DA NA GAMA-GARI NA AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA)

NA

ISAH MUHAMMAD KAWU
Lambar Waya: 07047484384

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan kundin binciken ga mahaifiya ta; Maryam Muhammad (Inta) da yaya ta Safiya Muhammad, waɗanda su ka bani gagarumar gudummawa maras adadi na ɗawainiyar karatuna ta fannoni iri-iri tun daga farkonsa har zuwa ƙarshe don ganin na kammala cikin aminci. Da fatan Allah ya saka musu da alkhairi ya ƙaro musu lafiya da wadata ya kuma sa su amfani wannan karatun nawa ya bani damar faranta musu har kullum.

GODIYA

Alhamdulillah. Dukkan yabo da godiya su ƙara tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai kowa, mai yadda ya so akan wanda ya so, ko ana so ko ba a so. Wanda shi ne ya fahimtar ɗan Adam dangogin ilmi ya kuma fifita shi a doron ƙasa ta hanyar ba shi hankali da tunani da dabaru daban-daban sannan ya ba shi damar amfani da su wajen gano abubuwa. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammadu, Sallallahu Alaihi wa sallama.

Bayan haka, ina matuƙar godiya ta musamman waɗanda ba za su iya musultuwa ba ga Malamin da yi jagorancin wajen duba wannan kundin binciken wato Dr. Musa Isah Abubakar bisa shawarwari da ƴan gyare-gyaren da ya yi don ganin wannan aikin ya ƙayatar da samun yabo da son barka ga ɗaliban ilmi da manazarta da sauran al'ummar Hausa baki ɗaya. Sannan ina miƙa godiya ta ga dukkan Malaman Sashen karatun Digiri na gida da na waje, tsangayar nazarin harsen Hausa bisa ɗawainiya da mu da kuma koyar damu ilmi da tarbiyya da su ka irin su; Malam Gambo Idris Abubakar, Habu Isa Garki, Sani Suleiman, Ibrahim A. Garba, Dr. Binta Usaini Umar, Dr. Haruna Alkasim Kiyawa, sai Malaman waje irin su; Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau da Farfesa Muktar Abdulƙadir Yusuf da su ke Jami'ar Bayero da kuma Dr. Hafsat Bagari da ke Kwalejin Tarayya da ke Kano. Allah ya saka musu alkhairinsa, Amin.

Gaisuwa ta ba za ta tsaya a nan ba sai na gaishe da malaman da suka koyar damu ilmi na bai ɗaya kamar su; Dr. Turaki Usman, Turaki Ɗahiru, Dr. Abubakar Aliyu, Malam Sagiru Birniwa, Dr. Ado Na'iya Idris, Malam Jamilu Ringim, Dr. Lawan Shu'aibu, Dr. Dauda Habu Galadi, Jamilu Sani, Baffa Dodo, Surajo Muhammad, Dr. Mus'ab Shu'aibu, Marigayi Dr. Alasan Yahya Nahuce, Dr. Ishaq Jibril Isah, Dr. Shamsu Ibrahim, Shitu Ahmed, Ɗahiru Inuwa da kuma Shugaban makaranta Dr. Nura Muhammad Ringim. Allah ya saka wa kowa da alkhairi ya ƙaro girma da ɗaukaka.

Sannan ina miƙa saƙon godiya ta ga Malaman da suka kulawa da a harkokin karatu da kuma tare da dukiyoyi da lafiyarmu irin su Shugaban Sashen karatun Digiri; Dr. Lawan Shu'aibu Gumel, Dr. Ado Na'iya Idris, (Dr) Bala Zakar, Mudassir Haruna, tare da sauran Malaman da su ka tsare mu a lokutan da mu ke gudanar da jarabawar ƙarshen zangunan karatu sannan da masu shige da fice irin su; Ayala da sauran laburori da masu gadi. Allah ya saka wa kowa da mafificin alkhairi, Amin.

Daga ƙarshe kuma ina miƙa saƙon godiya ta ƴan uwa da abokan arziki bisa addu'o'i da fatan alkhairi da su ka yi min ba dare da bara. Har ila yau, ina kuma sake miƙa saƙon godiya ta ga Baba Gambo Abubakar, Barista Garba Abubakar, Baba Isa Nakara bisa bani wani kaso da su ka yi a matsayin tallafinsu wajen biyan kuɗin makaranta a shekarar ƙarshen zangon karatuna. Da fatan Allah ya saka musu da alkhairi ya ƙara buɗi.

TSAKURE

Rubuce-rubucen nazari da aka yi game da waƙoƙin baka na gargajiya da na zamani musamman na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da shi da Aminu Ladan Abubakar (Alan waƙa) sun fi shurin masaƙi. A wannan kundin binciken an ba da ma'anar waƙa da samuwarta a ƙasar Hausa sannan an bibiyi taƙaitaccen tarihin Alhaji Musa Ɗanƙwairo da shi da Aminu Ladan Abubakar da gudummawa da kuma ci gaban da suka bayar dangane da raya adabi da kuma wasu muhimman abubuwa dake ƙunshe da su. Duk da haka, mafi yawan rubuce-rubucen sun karkata ne kan zaƙulo fasahohi da ke cikin waƙoƙin gargajiya da na zamani tare da nuna yadda suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa da yabo da zuga. Daga ƙarshe kuma an zayyano wasu daga cikin kyawawan halayen mawaƙa wanda ake so da kuma munana wanda ake ƙyama sannan an binciko bambanci da kamancin da ke tsakanin waƙoƙin gargajya da na zamani. Wannan kundin binciken na da fahimtar da al'umma cewa an bar wani babban giɓi wanda shi ne nazarin fanɗare wa dokokin addini cikin waƙoƙin baka na Hausa. Aikin nan na da manufar binciko muhallan da ɗiyan waƙoƙin baka na Hausa suka keta dokokin da Allah ya shimfiɗa wa bayinsa. An tattara bayanai ta hanyar sauraron waƙoƙin da tsamo misalan ɗiyan waƙoƙin da abin ya shafa, tare da ciro hukunce- hukuncen da suka yi bayani kansu daga Alƙurani da hadisan manzon Allah. Binciken ya fahimci cewa, akwai tarin misalan fanɗare wa addini a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Daga ƙarshe an ba da shawarwarin da suka haɗa da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da ire-iren waƙoƙin ba su yi tasiri wajen gurɓata tarbiya nagartacciya ba.

ABUBUWAN DAKE CIKI

SHAFIN FARKO - i

SHAFIN AMINCEWA - ii

SADAUKARWA - iii

SHAIDAWA - iv

GODIYA - v

TSAKURE - vii

BABI NA DAYA

GABATARWA

1.0 Gabatarwa - 1

1.1 Matsalolin Bincike - 1

1.2 Dalilin Bincike - 3

1.3 Manufar Bincike - 3

1.4 Muhimmancin Bincike - 4

1.5 Hasashen Bincike - 4

1.6 Tambayoyin Bincike - 4

1.7 Farfajiyar Bincike - 5

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 Gabatarwa - 6

2.1 Kundayen Bincike - 6

2.2 Bugaggun Littattafai - 11

2.3 Muƙalu - 18

2.4 Naɗewa - 20

BABI NA UKU

HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

3.0 Gabatarwa - 21

3.1 Dabarun Gudanar da Bincike - 21

3.2 Tsarin Bincike - 21

3.2.1 Bincike ta Hanyar yi wa Jama'a Tambayoyin Baka da Baka - 22

3.2.2 Raba Tambayoyi A Rubuce (Questionnaire) - 22

3.3 Jama'ar Bincike - 22

3.4 Samfurin Bincike - 22

3.5 Tambayoyin Bincike - 23

3.5.1 Tambayar Bincike Ta Baki Da Baki - 23

3.5.2 Tambayoyin Bincike Ta Baki Da Baki - 24

BABI NA HUDU

4.0 Gabatarwa - 31

4.1 Ma’anar Waƙa - 31

4.2 Rabe-raben Waƙa - 32

4.2.1 Waƙar Gargajiya Ko Ta Baka - 32

4.2.2 Samuwar Waƙoƙin Gargajiya - 34

4.2.3 Waƙoƙin Gargajiya - 35

4.2.4 Mawaƙan Gargajiya - 36

4.3 Taƙaitaccen Tarihin Musa Ɗanƙwairo Maraɗun - 38

4.3.1 Haihuwarsa - 38

4.3.2 Ƙuriciyarsa da Tasowarsa - 38

4.3.3 Fara Waƙar Musa Ɗanƙwairo - 39

4.3.4 Ɗanƙwairo ya Kama Cin Gashin Kansa na Waƙa - 40

4.3.5 Ire-iren Waƙoƙin da Musa Ɗanƙwairo ya yi - 40

4.3.6 Yadda Musa Ɗanƙwairo Yake Shirya Waƙoƙi - 40

4.3.7 Mataimakan Musa Ɗanƙwairo Na Waƙa (Ƴan karɓi) - 41

4.3.8 Yawace-Yawacen Musa Ɗanƙwairo a Waƙa - 42

4.3.9 Waƙoƙin Fadar da Musa Ɗanƙwairo Ya fi Sha'awa - 42

4.3.10 Dangantakar Musa Ɗanƙwairo da sauran Makaɗa - 43

4.3.11 Shaharar Musa Ɗanƙwairo a Waƙa - 43

4.3.12 Iyalan Musa Ɗanƙwairo - 43

4.3.13 Rasuwar Musa Ɗanƙwairo - 44

4.3.14 Zuriyar Musa Ɗanƙwairo - 44

4.4 Gudummawa Da Ci gaban Alhaji Musa Ɗanƙwairo da ya Bayar - 44

4.5 Waƙoƙin Zamani - 57

4.5.1 Samuwar Waƙoƙin Zamani - 59

4.5.2 Samuwar Waƙoƙin Baka na Situdiyo - 60

4.6 Taƙaitaccen Tarihin Aminu Ladan Abubakar - 61

4.6.1 Sunansa Na Yanka da Laƙabinsa - 61

4.6.2 Asalin Iyayen Aminudden Ladan Abubakar da Nasabarsa - 61

4.6.3 Shekarar Haihuwar Aminu Ladan Abubakar - 61

4.6.4 Ilmin Aminu Ladan Abubakar - 61

4.6.5 Sana'a Wajen Aminu Ladan Abubakar - 62

4.6.6 Rubutun Aminu Ladan Na Labarun Zube - 62

4.6.7 Aminu Ladan a Ɓangaren Rubutun Waƙoƙi - 63

4.6.8 Aminu Ladan a Kiɗa da Waƙa - 63

4.6.9 Kayan Kiɗan Aminu Ala - 63

4.6.10 Fara Waƙar Baka da Bunƙasar Aminu Ala - 64

4.6.11 Iyali da Ƴaƴan Aminu Ala - 64

4.7 Mawaƙan Zamani Waɗanda Suke Haɗawa Da Kiɗa - 73

4.8 Taƙaitawa - 161

4.9 Sakamakon Bincike - 162

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA, SHAWARWARI, MANAZARTA

5.1 Jawabin Kammalawa - 163

5.2 Shawarwari - 164

Manazarta/Madogara - 165

Waƙoƙin Hausa

Post a Comment

0 Comments