Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari a Kan Bambance-Bambancen Da Ke Tsakanin Wakokin Gargajiya Da Na Zamani, Bincike Na Musamman Na Wakokin Sarauta Na Alhaji Musa Danƙwairo Da Na Gama-Gari Na Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) – 6 Babi Na Biyar Da Manazarta

ƘUNSHIYA

1. Shafukan Farko

2. Babi Na Ɗaya

3. Babi Na Biyu

4. Babi Na Uku

5. Babi Na Huɗu

6. Babi Na Biyar

Wannan kundin binciken an samar da shi ne domin samun shaidar takardar karatun digiri na farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Tsangayar Karatun Digiri, Kwalejin Ilmi Da Ke Gumel, Kulawar Jami'ar Bayero, Kano.

NAZARI A KAN BAMBANCE-BAMBANCEN DA KE TSAKANIN WAƘOƘIN GARGAJIYA DA NA ZAMANI, BINCIKE NA MUSAMMAN NA WAƘOƘIN SARAUTA NA ALHAJI MUSA ƊANƘWAIRO DA NA GAMA-GARI NA AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA)

NA

ISAH MUHAMMAD KAWU
Lambar Waya: 07047484384

BABI NA BIYAR
KAMMALAWA, SHAWARWARI, MANAZARTA

5.1 Jawabin Kammalawa

Babu shakka wannan bincike ya zo ƙarshe kuma a cikin wannan babi ne za mu gabatar da jawabinmu domin kammala wannan bincike. Wannan aiki, aiki ne da ya ke da taken Nazari A Kan Bambance-Bambancen Da Ke Tsakanin Waƙoƙin Gargajiya Na Sarauta Na Alhaji Musa Ɗanƙwairo Da Na Zamani Na Gama-gari Na Aminu Ladan Abubakar Kuma an kasa wannan kundin bisa ga tsari na babi-babi inda na zuba shi bisa ga babi biyar.

Baya ga babi na ɗaya da babi na biyu waɗanda suka kasu ga abin da ake gudanarwa a ciki bai shafi gundarin aikin ba, amma hakan ba a yi ƙasa a gwiwa ba an yi amfani wajen duba kundaye da bugaggun littattafai da muƙala masu alaƙa da wannan binciken don ɗabbaka shi yadda zan yi armashi.

A babi na uku an kawo bayanai masu gamsarwa game da dabarun koyar da bincike inda aka yi bayanai akan kowane mataki na daban-daban.

A babi na huɗu kuma nan ne aka tsindima aikin kacokan inda aka ba da bayanan masana akan ma'anar waƙar baka ta gargajiya da ta zamani tare da samuwar kowannansu a ƙasar Hausa da rabe-raben makaɗa da mawaƙan baka, sannan an duba taƙaitaccen tarihin Alh. Musa Ɗanƙwairo Maraɗun da Aminu Ladan Abubakar tare da gudummawa da ci gaban da suka bayar a ɓangaren adabi.

Haka kuma bincike ya kawo kamancin waƙar gargajiya da ta zamani da kuma bambancin da ke tsakaninsu, inda kuma kowace suna da bambanci ta hanyar amshi da kiɗa da aiwatarwa a dandali. Kuma suna da kamanci ta hanyar isar da saƙo da sauransu.

A babi na biyar kuma nan ne aka naɗe tabarmar wannan bincike da jawabi na kammalawa da kuma shawarwari sannan kuma aka zayyano madogara da ake samu dukkan bayanan wannan aikin binciken.

5.2. Shawarwari

A matsayina na mai nazarin harshen Hausa ina ba duk waɗanda za su yi nazari a wannan fanni shawara cewa, in dai su ka ci karo da kundin nan ko makamancin irinsa kuma in har binciken nasu yana da alaƙa da wannan, to su yi ƙoƙarin gudanar da bincike mai zurfi su kawai da wannan ɗabi'ar ta kwafi-kwafi na kundayen bincike don wannan al'adar a wasu lokutan ba ta taimaka wa masu nazari wajen fahimtar gudanar batun da su ke bincike akansa yadda ya kamata. Kamar yadda na zaɓo taken da wani bai taɓa yi irinsa ba na yi shige-shige sosai a ɗakunan karatu ba adadi da shiga yanar zigo-zigo da sauraron waƙoƙin baka na Hausa da duba kundaye da muƙalu ba don komai ba sai don samo na tattaro bayanan da suka gina min wannan kundin don ya zama abin karatu da nazarce-nazarce, to lallai su ma ya zama wajebi su dage don su samar da wani abu mai amfani ko ɗabbaka shi, ba wai su kwashe duka abubuwan da wasu manazartan suka yi ba.

Daga ƙarshe kuma ina ba da haƙuri ga duk waɗanda suka ci karo da wannan kundi da su yi min uzuri dangane da wannan aiki da na gudanar. Ina ba da shawara ga makaɗa da marubuta da su dage sosai su samar da wasu abubuwa da ɗalibai za su nazarta ko karanta a wannan fanni na adabi.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan waƙar baka ta Hausa. Gaskiya Corporation Limited.

Abubakar, A. (2015) Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company LTD.

Al-Munajjid, M.S. (2004). Muharramat: Forbidden matters same people take lightly. International Islamic Publishing House, Saudi Arebia.

Ammani, M. (2019). Nazarin Awon Baka da Aiwatar wa a Wa ƙ o ƙ in Nafiu Yakubu Baba. Kundin Digiri na Uku (PhD). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jamiar Bayero.

Bello, G. (1976). Yabo da Zuga da Zambo a Waƙoƙin Sarauta Harsunan Nijeriya, V ol . V I:21-34. CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jamiar Bayero.

Bunza, A.M. (2014). In ba ka san gari ba saurari daka: Muryar nazari cikin tafashen Gambo Elkods Printing Hausa.

C.N.H.N (2006:466). Ƙamusun Hausa Na Jami'ar Bayero. Zaria: University Press, Ltd.

Ɗangambo A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. Madabaƙar Kamfanin Triumph Gidan Sa'adu Zungur, Kano da kuma shafin Rumbin ilmi.

Ɗangambo, A. (2005). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Sabon Tsari. Zaria: Amana Publishers Ltd.

Gusau, S.M (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmarks Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2011). Bitar Littafin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar: Alan waƙa Na Muhammad Lawan Barita (2011). Takarda wadda Aka Gabatar A Taron Gabatar Da Littafin Da Aka yi a Musa Abdullahi Auditorium. Sabuwar Jami'ar Bayero, Kano 15/01/2011.

Gusau, S.M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya: Musa Abdullahi Auditorium, New Campus, Bayero University Kano.

Gusau, S.M. (2014).Makaɗan Hausa Jiya da yau. In Garkuwan Adabin Hausa: A Festschrift in Tribute to Albdulƙadir Ɗangambo. Zaria: ABU Zaria Press.

Gusau, S.M. (2016). Diwanin Waƙoƙin Baka. Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maraɗun (1900-1991), Sarkin Kiɗan Maraɗun Jahar Zamfara. Juzu'i Na Huɗu. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Gusau, S.M. (2016). Makaɗa da Mawaƙan Hausa (1-2). Kano: Century Research and Publishing.

Rubuce-rubuce da dama sun kawo bayanai game da zuwan Musulunci ƙasar Hausa. Ana iya duba Shehu and Sani, (2019) ko Sani da Jaja, (2019) domin samun ƙarin bayani.

Sa'id, B. (1981). "Bambancin Waƙar Baka da Rubutacciya" In Yahaya I.Y: A.& Manga, A. (Ed) Studies In Hausa Language, Literature and Culture: The Second Hausa International Conference. Kano: Centre for Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Sarɓi, S.A. (2007). Nazarin Waƙen Hausa.Kano: Samarib Publishers

Shehu, M. & Sani, A-U. (2019). Intra-Religious Conflicts within the Hausa Hausa-folk. In EAS Journal of Humanities and Cultural Studies, Volume-1, Issue-3. Pp

Umar, M.B. (1987). Dangantakar adabin baka da al’adun gargajiya. Kamfanin “Triumph” Gidan Sa’adu Zungur.

Yahaya, D.H. (1991) "Alhaji Musa Ɗanƙwairo Makaɗin Fada ko na Jama'a" ? Kundin BA, Kano: Bayero University Kano.

Zaria: Ahmadu Bello University Press. Muhammad, U. (2015). "Zumuntar Tsafe-tsafen Hausawa da akarkari" Kundin Digirin M.A. Sashen Nazarin Harsunan Nigeria, Jami'ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Waƙoƙin Hausa

Post a Comment

0 Comments