Citation: Abdulrahman, Aliyu (2024) “Nazarin Nau’o’i da Salon Rubutattun Waƙoƙin Gazal na Larabci da Hausa” Algaita Journal of Current Reseach in Hausa Studies, Volume 17, No 1, May 2025. Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. ISSN: 2141-9434.
NAZARIN NAU’O’I DA SALON RUBUTATTUN WAƘOƘIN GAZAL NA LARABCI DA NA HAUSA
DAGA
Abdulrahman Aliyu
Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya
ksarauta@gmail.com
08036964354
Tsakure
‘Waƙoƙin Gazal’ sun samo asali
ne daga ‘waƙoƙin Larabci, inda suka kasance kamar shimfiɗa ne ga duk wanda zai
yi waƙar ƙasida, baitukan da ke ɗauke da waƙoƙin Gazal ba su wuce biyar zuwa
sha biyar ba. Suna ɗauke da bayanin irin
kewar da mawaƙi ke ji game da wata masoyiyarsa da ta yi masa nisa ko ya rasa
ta. Kamar yadda irin waɗannan waƙoƙin suke a Hausa ma an tusgo su ne daga cikin
waƙoƙin soyayya da kuma waƙoƙin da suka shafi kaɗaita Allah da Sufaye ke
aiwatarwa da fuskar yaba kyau ko zatin mace. wannan maƙala za ta yi duba ne kan
nau’o’i da salo tsakanin waƙoƙin Gazal na Larabawa da na Hausawa. Manufar
ƙasidar ita ce, yin kwatancin nau’oi da salon waƙoƙin Gazal na Larabci da na
Hausa ta fuskar gano yadda kowane ɓangare suke shirya nasu waƙoƙin tare da yin
duba ga waƙoƙin na Larabawa da na Hausa. An bi hanyoyi da yawa wajen ganin an
samu nasarar wannan binciken da suka haɗa da tattara waƙoƙin Gazal na Larabci
da fassara su zuwa Hausa, da ganawa da masana da yin tambayoyi ga wasu mutane
da ke da alaƙa da waɗannan waƙokin. Sannan an yi amfani da kafafen sadarwa na
zamani wajen samo bayanai da suka taimaka aka gina kwatancin ta yadda aka riƙa
musayar bayanai daga Larabci zuwa Hausa. Ganin yadda wannan nau’i na waƙa ya
samu karɓuwa a faɗin duniya, shi ya sa wannan nazarin ya yi amfani da Ra’in Kwatancin Adabi
(Comparative Literary Theory) wanda Hugo
Meltzl ya samar a shekarar 1877, wanda ra’i ne da ya samu goyan bayan masana
irin su H.M Posneet a wani fitaccen aikinsa mai suna “Comparative Literature
(1886. Wannan ra’i ana amfani da shi wajen kwatancen adabin al’ummomi, waɗanda ake
ganin suna da
wata dangantaka ko
kuma wasu kamanni
a wasu ɓangarori na
adabi ko al’adu
domin a tabbatar
da alaƙarsu. A ƙarshen wannan
maƙala an gano cewa akwai bambance-bambance tsakanin nau’in waƙoƙin Gazal na
Larabci da na Hausa, a ɓangaren salo kuma maƙalar ta gano cewa yawanci irin
salon da ake samu a waƙar Larabci ana samunsa a waƙar Hausa. Har ila yau, nazarin ya gano irin yadda Hausawa suka
ari wani reshe na Gazal suka samar da
nasu a Hausa.
1.0 Shimfiɗa
An yi tunanin yin wannan aikin ne ganin yadda da yawa Hausawa suke kallon kamar waƙoƙin
Gazal ba su da muhalli a Hausa. Wasu kuma suna
yi musu kallon fanɗararru ne. Wasu kuma suna kallon bayan waƙoƙin
Soyayya a Hausa babu wasu waƙoƙi na
Gazal. Shi ya sa aka yi wannan bincike domin a yi kwatancen siga da fasalin
waƙar Gazal tsakanin
Larabawa da Hausawa,
da kuma faɗakar da cewa akwai
waƙoƙin Gazal a Hausa masu zaman kansu.
Tushen kalmar ‘Gazal’
asalinta daga Larabci ne. A lugga, ‘Gazal’
na nufin “Tufafin da aka saƙa da auduga”. A ma’ana ta zahiri kuwa ‘Gazal’
na nufin mai da hankali
a kan hirar mata da nuna matsananciyar soyayya ko yawan raɗaɗin
rabuwa da mace a lokacin da ake tafiya cikin
tawaga. A fagen waƙa, kalmar tana nufin, wani nau’in waƙa da ke bayyana tsananin
raɗaɗin ciwon rashi ko rabuwa a ɓangare
guda, da kuma nuna matsanancin kyawo na masoyi ko masoyiya duk a lokaci
guda tare da yaba kyan hali
ko ɗabi’a. (Badr Ibn Ali: 2007)
A taƙaice dai ‘Gazal’ wani nau’in waƙa ne da mawaƙi yake bayyana tsananin
ƙaunarsa ga abin da yake wa waƙar ta hanyar yabo da siffanta kyawun jiki
da na hali da ɗabi’a. Wani lokaci ma har da yanayin mu’amular
soyayyarsu.
Siga a wannan aiki shi ne bayyan yadda waƙokin Gazal suke da kuma yadda
za a iya gane su da rarrabe su da waɗanda
ba na Gazal ba. Sai kuma fasali wanda shi ne yake fayyace irin saƙo ko kuma ƙunshiyar da waƙoƙin Gazal na
Larabci da na Hausa suka ƙunsa, domin suna da fasalinsu
wanɗanda da zaran
an sauka daga gare shi, to an fita maganar waƙoƙin Gazal.
Babbar manufar wannan maƙala ita ce gano sigogi da fasalolin waƙoƙin Gazal a
Larabci da na Hausa da kuma fito da kwatancin da ke akwai tsakanin
rubutattun waƙoƙin Gazal na Hausawa da na Larabawa.
An bi hanyoyi da dama wajen gudanar da wannan bincike. Hanyoyin da aka bi sun haɗa da fassara
matanoni waƙoƙin Gazal na Larabci zuwa Hausa, da ganawa da masana da kuma yin
tambayoyi ga waɗansu mutane da suke da dangantaka da waƙoƙin da aka yi amfani
da su.
Sannan an yi amfani da wallafaffun Litattafai da kundayen bincike wajen
samun bayanai da suka taimaka wajen
gudanar da wannan bincike. Haka kuma, an yi amfani da kafafen sadarwa
na zamani domin neman bayanai da suka taimaka wajen kammaluwar wannan aiki.
2.0 Ra’in Bincike
A wannan
maƙala an yi amfani da Ra’in Kwatancin Adabi,
(Comparative Literary Theory) Wannan Ra’i
na Kwatancin Adabi ya fara ɓulla
ne a yankin Hungarian a ƙarni
na 18 daga wani
masani mai suna Hugo Meltzl (1846-1908), wanda ya kasance shi ne edita kuma mamallakin mujallar “Journal Acta Comparationis Litterarum Universarum (1877)” an sami kuma wani masani mai suna H.M Posnett wanda ke zaune
a yankin Irish, wanda shi ne ya fara samar da littafin kwatancin Adabi mai suna‚ “Comparative Literature (1886)” Wannan tunani na H.M Posnett ya samo asali ne daga shawarar Johann Wolfgang von Goethe ƙwararren masanin adabin duniya.
Wasu daga
cikin waɗanda suka biyo bayan waɗannan masana wajen amfani da wannan ra’i akwai
Alexander Veselovsky (1838-1906) da Viktor Zhirmunsky (1891-1971). Wannan ra’i ya fara zama da
gindinsa a ƙarni na 19 daga rubuce-rubucen
Zhirmunsky Rachel Polonsky, da
littafinsa mai suna English Literature
and the Russian Aesthetic Renaissance. Wannan ra’i ya wanzu a yankin ƙasar Jamus a a ƙarshen
ƙarni na sha tara (19), bayan kammala yaƙin
duniyan na biyu ta hannun masana irin su
Peter Szondi (1929–1971) wanda ya rubuta
littafin kwatanci adabi na waƙoƙi da wasan kwaikwayo mai suna "General and Comparative Literary Studies" har zuwa lokacin da
Tübingen, Wuppertal. Ya rubuta littafinsa na kwatancin Adabin da Jamusanci mai
suna Der kleine Komparatist (2003).
A ƙasar
Hausa, wannan ra’i ya samu tagomashi sosai, inda aka samu ayyuka da suka yi
magana kan kwatancin adabi kamar haka: Sankalawa (2005) da aikin sa mai suna
“Kwatanta waƙoƙin Aliyu Namagi da Takwarorinsu na Sani Yusuf Ayagi” da aikin
Rabi’u (2018) “ Kwatancin Habarcen Nijeriya da Nijar: Tsokaci A Kan Tatsuniya”
da aikin Adamu (2019) ”Kawatanci Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Jumhuriya Ta Uku Da Na Jumhuriya Ta Huɗu A Nijeriya” da
aikin Salihi (2020) na “Kwatanta Littafin Kitsen Rogo Da Jatau Na Kyallu
Dangane Da Dabarun Jawo Hankali” da aikin Yahya (2021) mai taken “Kwatanta Jigo
Da Zubi Da Tsarin Waƙoƙin Bello Muhammad Aji Mai Karama Da Na Sani Abubakar
Hotoro” da sauransu da dama.
Wannan
ra’i na kwatancin Adabi yana da manufofi da suka haɗa da:
- Kwatanta wasu ayyukan adabi
da sauran ɓangarori na rayuwar Al’umma
- Kwatanta wasu ayyukan adabi masu alaƙa da juna, misali kwatanta
wata waƙa da wata makamanciyarta daga mabambanta
marubuta
- Kwatanta wasu ayyukan adabi da ke sajewa a cikin
al’adu domin fito da abubuwan da suke tattare da su na adabi da kuma na
al’adun.
- Nuna bambancin da ke akwai tsakanin wasu ayyukan
adabi masu kama da juna, domin a rarrabe su.
- Samar wa ayyukan adabi mazauni na kwatanci tsakanin wasu
mabanbanta ɓangarori na duniya da ake
ganin suna da alaƙa da juna. Da sauransu
2.1 Dangantakar Manufar Ra’in da Manufar
Aikin da Aka Aiwatar
Kamar yadda
aka gani daga cikin manufar wannan ra’i akwai kwatanta wasu ayyukan adabi masu
alaƙa da juna. Misali kwatanta wata waƙa da wata makamanciyarta daga
mabambantan marubuta ko al’umomi mabanbanta.
Ita ma wannan
maƙala daga cikin manufar ta akwai kwatanta nau’o’i da salon waƙoƙin Gazal na
Hausa da na Larabawa domin gano inda suke da alaƙa da kuma inda suka sha bamban
a tsakanin al’umomin guda biyu.
Haka kuma,
manufar wannan ra’i ita ce a samar wa
ayyukan adabi mazauni na kwatanci tsakanin wasu mabanbanta ɓangarori na duniya
da ake ganin suna da alaƙa da juna. Ita ma wannan maƙala zata duba mazaunin
waƙoƙin Gazal ta fuskar nau’o’insu da salonsu tsakanin Larabawa da Hausawa
domin ganin irin kamanci da bambanci da suke ɗauke da shi.
Kazalika manufofin wannan ra’i da na wannan maƙala sun
tafi daidai ta fuskar kwatancin waƙoƙin
Gazal na Larabawa da na Hausawa.
3.0 Kamanci
da Bambancin Nau’o’in Waƙoƙin Gazal na Larabci da na Hausa
A tsawon
zamani, tun daga ƙarni na 7 har zuwa na 13, waƙar Gazal ta Larabawa ta ci gaba
da samun bunƙasa, har ya kasance aka karkasa ta zuwa nau’o’i daban-daban,
waɗanda suka haɗa da:
1
Al-Ghazal Al-Sarhi (Umarite Ghazal/Ghazal Al-Majun)
2
Al-Ghazal Al-Afif
al-Badawi
3
Al-Ghazal
Al-‘Udhri
A Hausa ma
akwai nau’o’in waƙoƙin Gazal guda kamar haka:
- Waƙoƙin Gazal na Soyayya
- Waƙoƙin Gazal masu zaman kansu
- Waƙoƙin Gazal na cikin sauran waƙoƙi
- Gazaliyya
3.1 Al-Ghazal Al- Sarhi
ya samo asali ne daga lokacin jahiliyar Larabawa, lokacin da babu wayewa ko
kuma bayyanar ilimin addinin Musulunci ga Larabawan. Al’adar Larabawa ta kiwo ta na daga cikin dalilin samuwar wannan
kaso na Gazal.
A lokacin
Larabawa matasa maza da mata duk suna da al’adar yin kiwo. Wannan al’adar ce ta
sa aka samu waƙoƙin Gazal suka fara ɓulla daga waɗannan makiyayan na
Larabawa. A wannan kaso akwai ƙananan
rassa guda biyu da ake gina waƙar Gazal ɗin da su. Na farko shi ne ɓangaren waƙar Gazal ta cikin
ƙasida wadda ake samun baiti biyar zuwa sha biyar. Irin waɗannan waƙoƙi an same
su da yawa kuma suna ɗauke da fasali da ya bambanta su da sauran kason, na
farko waɗannan waƙoƙin na Gazal a waƙa
ɗaya za a iya yi wa mace fiye da ɗaya, kuma mafi yawan mabuɗin waƙar ana fara
wa ne da ambatar kufai ko sararin fili ko hanya ko wani rafi. Misali in aka ɗauki waƙoƙin Imru’al Qais za a ga cewa sun faɗo wannan kason na waƙar
Gazal ta gargajiya. A ƙarƙashin wannan kason, akwai ƙananan jigogi kamar haka:
1
Udhari (Qawa Zuci)
2. Hassi
(Bayyana ƙirar jikin mace)
- Tamhidi ( wasa mace da zugata ta siffar nuna wasu halayenta na kirki ko akasin haka). (Muqbil, Badr
ibn Ali:2007)
Waɗannan su ne fitattun jigogin waƙoƙin da ke ƙarƙashin wannan jigo na Ghazalul
Sarhi. Misalan
waɗannan waƙoƙin sun haɗa da waƙoƙin Imru’al Qais irin su;
i.
Kifa nafki min zikira habibi wa Irfani
ii.
Liman ɗalalu Afsartu fashajani
iii.
Kifa nafki min zikiri habibi wa munzali
iv.
Ayana Hindu la tankihi bwat’an da sauransu
Misali waƙar
Imru’al Qaisa mai suna Liman ɗalalu
Afsartu Fashajani ya samar da ita ne bisa irin wannan nau’i na Gazal
Al-Sarhi, ga misalin wasu baituka daga cikin waƙar.
لِمَنْ طَلَلٌ أبْصَرتُهُ فَشَجَاني
كخط زبور في عسيب يمانِ
دِيَارٌ لهِنْدٍ وَالرَّبَابِ وَفَرْتَني
ليالينا بالنعفِ من بدلان
ليالي يدعوني الهوى فأجيبهُ
وأعينُ من أهوى إليّ رواني
Fassarar mai bincike
Wannan kufan gida
na wanene? Da ya sa man baƙin ciki,
Gidan ya zama kamar rubutu ne a kan gindigirin[1]
dabinon Bayamane[2].
Waɗannan gidaje ne na Hindu da Rabab da Fartana,
Ka tuna dararen mu a kan wani tudu a Badalani.
Ka tuna dararenmu a lokaccin da soyayya ke fisga ta, sai
na amsa ma ta,
Idanun waɗanda na ke so ɗin suna duba ya zuwa gareni.
A Hausa ba a
samu wannan nau’i kai tsaye ba saboda bambancin al’adu da ke akwai tsakanin
al’umomin guda biyu, musamman abin da ya shafi al’adar kiwo wadda a nan ne aka
fi samun waɗannan waƙoƙin sai dai an samu wani nau’in waƙar Gazal mai ɗan
kamanceceniya da wannan nau’i, wato nau’i na na uku daga cikin nau’o’in waƙoƙin
Gazal na Hausa wanda ake samun waƙoƙin Gazal na cikin sauran waƙoƙi, inda
mawaƙi zai yi baituka biyar zuwa goma ga masoyiyarsa ko masoyinsa a farkon
waƙar sannan sai mawaƙi ya cigaba da waƙarsa. A mafi akasari irin wannan kason
an fi samunsa ga waƙoƙin da aka shirya na zambo ko habaici ga wani. Sannan a
waƙoƙin siyasa ma ana samun irin wannan kaso na waƙar Gazal. misaln irin
waɗannan waƙoƙin sun haɗa da;
i.
Wasiƙar So ta M.B Umar
ii.
Tsarabar Masoyi ta Bello Sa’id
iii.
Mun shaƙu mun gama Zautuwa ta Binyaminu Zakariyya
Hamisu da sauransu.
Irin wannan
misalin shi ne waƙar Binyaminu Zakari mai suna mun Shaƙu mun gama Zautuwa ga kadan daga cikin waƙar.
Har
Muntaha mun je ga Dal,
Maleji ma na ƙarar tuni.
Ni
nata ne
ita tawa ce,
Ruhinmu
dai ne ba hani.
Don
ni a kai ta ya Adamu,
Gun
Hauwa, ba ma
yin kini.
Hankalina ya tashi ƙoli ma,
Zan yi rashinta a zamani.
Ko da ganinta ta fi ni ma,
Ga shi har za ta cutar da
ni.
Zuciyata sai tafasa take ta yi,
Za mu rabu da mai zamani.
Wayyo Allah ni ya za ni yi?
Wata kil sai dai a sa likkafani.
Bambancin da
ke akwai a Hausa ba samun waƙar Gazal da ake yi wa fiye da mace ɗaya waƙa,
kamar yadda ake samu a nau’in waƙoƙin Gazal na
Al-Sarhi, wanda shi a Hausa na fi mayar da hanakali ne ga mace ɗaya.
3.2 Al-Ghazalul Afif al-Badawi, shi wannan ya yaɗu ne a ƙauyen Hijaz a wata
ƙabila da ake kira Bani Uzratu da Kuza’a a tsakanin matasan da suka kasa yin
hijira da tafiya jihadi, amma waƙoƙinsu na Gazal ba su yin ƙarya a ciki, kuma ba su zuwa da
kalmomin nuna batsa ƙarara, wanda bai kamata a siffanta mace Musulma da su ba.
Mafi yawan jigogin waƙoƙin wannan kaso ba su wuce:
·
Yabo
·
Gwarzantawa, da sauransu.
Misalan
waƙoƙin sun haɗa da irin waƙoƙin Umar
Bin Abi Rabi’ata waɗanda suka haɗa da:
i.
Amin ali nu’umi anta gadi fa mubakur
ii.
Hiya shamsu tasri da sauransu.
Misalin irin
wannan waƙa dake wannan nau’i akwai waƙar
Umar Bin Abi Rabi’ata mai suna Hiya
shamsu tasri, ga kaɗan dagab cikin baitocin waƙar;
أَمِن آلِ زَينَبَ جَدَّ البُكورُ
نَعَم فَلِأَيِّ هَواها تَصيرُ
أَلِلغَورِ أَم أَنجَدَت دارُها
وَكانَت قَديماً بِعَهدي تَغورُ
هِيَ الشَمسُ تَسري عَلى بَغلَةٍ
وَما خِلتُ شَمساً بِلَيلٍ تَسيرُ
وَما أَنسَ لا أَنسَ مِن قَولِها
غَداةَ مِنىً إِذ أُجِدَّ المَسيرُ
أَلَم تَرَ أَنَّكَ مُستَشرَفٌ
وَأَنَّ عَدُوَّكَ حَولي كَثيرُ
فَإِن جِئتَ فَأتِ عَلى بَغلَةٍ
فَلَيسَ يُؤاتي الخَفاءَ البَعير
Fassarar mai bincike
Shin daga iyalan gidan Zainab ake yin sammako?
Eh! To wace irin soyayya ce take zama irin haka?
Shin gidanta yana kwari ne ko a tudu?
Har ta kasance tuntuni tana gafala daga Alƙawari na.
Ita rana ce tana tafiya a cikin dare a saman alfadari,
Ban taɓa tsamanin cewa rana tana tafiyar dare ba.
Ban natsu da maganarta ba, kuma bana natsuwa da maganarta,
A safiyar Mina lokacin da nike ƙoƙarin tafiya.
Tace shin baka gani mutane sun sa maka ido,
Kuma maƙiyanka suna da yawa a gefena.
To in za ka zo ka zo bisa alfadara,
Domin in ka zo kan raƙumi ba zai iya ɓoyuwa gare su ba.
Akwai
kwatancin Wannan nau’i a waƙoƙin Gazal na Hausa wanda aka ba shi suna Nau’i
“Waƙoƙin Gazal ma su zaman kansu”, dukkanin waɗannan nau’o’i guda biyu ba a
saka ƙarya a cikin su. Shi wannan nau’i ya samo asali ne daga malaman sufaye da
suke shirya waƙar Gazal da sunan mace, amma a matsayin nuna kusanci da kuma
kaɗaita Allah tare da nuna irin ƙudirarsa, sai dai su waɗannan waƙoƙin duk da
sunan an yi mace su ne. Wannna nau’i kacokam an ɗauki nau’in Al-ghazalul
Afif al-Badawi ne wanda kai tsaye ke nuna rabuwa ne ya ke nunawa tsakanin
mace da namiji. Misali waƙoƙin Ibrahim Sodang da suka haɗa da:
i.
Ƙarshen Tafarkin hankalina
ii.
Ku kirani Majanuni
iii.
Zuciyata ko kin mace
iv.
Idan ni bana ganinki...
v.
Muna son juna amma to ba zamu faɗi ba da sauransu.
Misalin wata
waƙa a wannan nau’i ita ce waƙar Ibrahim Sodangi mai suna “Ku kirani Majnuni” a wasu baituka ya na cewa;
Ni da Allah muna son
ki,
Shi Ya riga yi son ki
gaban zamani.
Ni wallahi ina kewar
ki,
Idan ƙarya nake
Allahu Ka ƙone ni.
Ina hawaye cikin
tausanki,
In ba haka ba Rabbu
Ya azabce ni.
Wani so ne na ban
mamaki,
Ya zarcewa zuhuri
wane ya buɗuni.
Bambancin da
ke akwai a wannan shi ne ita waƙar Gazal mai zaman kanta ta Hausa galibi bata
cika wuce baiti sha biyar ba, saɓanin nau’in Al-ghazalul Afif al-Badawi wanda ana iya samun baituka fiye da hamsin,
kuma a nau’in na Gazal Al-Afif ana musayar zance ne tsakanin samari da
‘yanmatansu, wanda a Gazal mai zaman
kanta ba haka abin ya ke ba.
3.3 Al- Ghazal Al’udhari: wadda ke wakiltar soyayya ta gaskiya ita ce da Larabci
ake kira 'Udhrit’. Mawaƙa ne masu taƙawa
da masu tsoron Allah ne suke shirya waƙoƙin wannan nau’in. Yawancin lokaci
mawaƙan da ke shirya wannan fasalin su ne waɗanda ba su yi nasara ba a cikin
harkokinsu na soyayya, saboda yanayin
zamantakewa da al'ada ko kuma bambancin addini ko rashin hallacin auren wadda
yake so ɗin a ɓangaren addininsa.
Wannan rashin
da suka yi da kuma abin da suke ji shi ne suke bayyanawa a cikin waɗannan
waƙoƙi masu wannan fasali. Sannan kuma baki ɗaya irin waɗannan waƙoƙi babu
batsa a cikinsu ko kuma fayyace ni’ima ko sigar mace, tsananin kewa ce kawai a
cikinsu.
Wannan nau’i
ya samo sunansa ne daga ƙabilar Udhrah, wadda mutanenta ne suka samar da wannan
aji sakamakon shahara da suka yi da soyayyar gaskiya wadda ba a cika rabuwa ba
sai dai mutuwa. Daga cikin mawaƙan wannan ƙabilar da suka bayyanar da wannan
fasali a sarari akwai mawaƙi Jamil b. 'Abdallah b. Ma’mar, wanda aka fi sani da
Jamil Buthaynah (d.82\701), wanda ake ganin shi ne jagoran assasa wannan nau'in. Amma duk da haka, akwai
mawaƙa ‘udhri’ daga wasu ƙabilu, kamar Majnun Layla, wanda ɗan ƙabilar Banu ‘Amir ne. Wannan nau’in na Udhri ya kasance an yi amfani da shi
sosai a dukkan makarantar mawaƙan
Hamadar Larabawa ta tsakiya.
'Soyayyar
Udhri soyayya ce mai mutuƙar tsafta
wacce take kaiwa ga mutuwa. A
Udhri mutum na son mace ɗaya ne kawai, ya sadaukar da rayuwarsa da waƙoƙinsa
gare ta; sai da kyar ake haɗa baitukan da wasu nau'i, kamar yabo (madh}. An
siffanta masoyiya a cikin udhri a
matsayin mace ta gari, kuma mai son mawaƙinta a matsayin shahidin soyayya.
Wannan nau’in na Gazal an yi amfani da
shi lokacin da Manzon Allah (SAW) ya yi hijra daga Makka zuwa Madina sai aka
samu wasu daga cikin mawaƙan Larabawa suka riƙa amfani da wannan nau’i wajen
waƙe ‘yan matansu da suka yi hijira, wanda a lokacin wannan nau’i ya yi tashe
sosai. Misalan waƙoƙin wannan kaso sun haɗa da waƙoƙin Antarah Bin Shadda da na
Qais Ibn Muwallah. Daga cikin waƙoƙin akwai:
i.
A ya Shibaha Laila
ii.
Hal gadarar Shu’ara’i min mutaraddami
iii.
Khalilayya la wallahi la’amliku lazi da sauransu.
Misalin irin
waƙoƙin wannan nau’i sun haɗa da waƙar waƙar Qais bin Mulawwa ta ‘A ya Shibaha Laila’ wadda ita a
cikinta mawaƙin ya bayyana irin yadda aka yi tafiya da shi zuwa aikin hajji
domin ya roƙo Allah SWT ya cire masa sonta, amma sai ya ɓuge da ba ta labarin
yadda tafiyar ta zama ƙunci a wajensa saboda rashin ta kusa da shi, ga wasu
daga cikin baitocin waƙar;
أَيا شِبهَ لَيلى لا تُراعي فَإِنَّني
لَكِ اليَومَ مِن بَينِ الوُحوشِ صَديقُ
وَيا شِبهَ لَيلى أَقصِرِ الخِطوَ إِنَّني
بِقُربِكِ إِن ساعَفتِني لَخَليقُ
وَيا شِبهَ لَيلى رُدَّ قَلبي فَإِنَّهُ
لَهُ خَفَقانٌ دائِمٌ وَبُروقُ
وَيا شِبهَها أَذكَرتَ مَن لَيسَ ناسِياً
وَأَشعَلتَ نيراناً لَهُنَّ حَريقُ
وَيا شِبهَ لَيلى لَو تَلَبَّثتَ ساعَةً
لَعَلَّ فُؤادي مِن جَواهُ يُفيقُ
Fassarar
mai bincike
Mene ne abin da yai kama da Laila? Duk duniya babu
kamarta,
Ni a yau ko a
tsakanin namun daji ni zan kuɓutar da ke.
Ya kai abin da yai kama da Laila ka taƙaita takunka ina
kusa da kai,
Idan ka matso kusa da ni zan aboceka da kyawawar ɗabi’a.
Duk wani abu da ya dace da kama da Laila zan maida
hankalina gare shi,
Zan zama liƙe da
shi kowane lokaci kuma zan haskaka shi.
Ya kai mai kama da Lailai kai abu ne da ake tunawa kuma ba za a manta kai ba,
Zan tsayar da haske wanda zai haskaka ko’ina gareka.
Ya kai abin da kai kama da Laila, da ace za a cuɗanyaku a
waje guda,
Ita zuciyata za ta iya karkata ga wanda yake na Laila.
A Hausa an samu kwatancin irin
wannan nau’in da aka ba sunan ‘waƙoƙin
Gazal na cikin waƙoƙin soyayya’, wanda waƙoƙi ne da ake samu cikin waƙoƙin soyayya inda ake tsara
waƙoƙi masu ɗauke da sigogin waƙoƙin Gazal, a Hausa irin waɗannan waƙoƙin ana
masu kallon waƙoƙin soyayya kai tsaye sai dai sun bambanta da waƙoƙin soyayya
domin su za ka same su da fasali da siga na waƙar Gazal misali, zaka same su
ƙwar biyu ne aka tsara su kuma ba sa wuce baituka biyar zuwa goma a sha biyar,
sannan suna ɗauke da fasalin nuna kewa ko raɗaɗin rasa masoyiyar. Wannan kaso
ya na da kamanci da nau’in Gazal na Larabci wato Gazal Al’udhari, domin shi ma
a wannan na Hausa yana tafiya ne bisa ƙananan jigogin da suka haɗa da, Kewa da
Ƙawa Zuci da kuma zuga mace amma kuma ta fuskar nuna raɗaɗin rasa ta ko kuma
yin nisa da ita. Misalan iin waɗannan waƙoƙin un haɗa da wasu da aka samu a
cikin littafin Dausayin Soyayya. Daga cikin su akwai;
i.
Tsarabar Masoyi ta Bello Sa’id
ii.
Bege ta B.A Salim da sauransu
A waƙar
Tsarabar Masoyi ta Bello Sa’id a wasu baituka ga abin da yace;
Ya masu ribbantar zukatan ‘yan Adam,
Na zo ina kamun ƙafa wajjanki,
Kin ribace min tawa duk na barka ce,
Na kawo kokena ina roƙon ki,
Na faɗa kogi kamfacece na nutse,
Ba wanda ke tsamo ni in baicinki,
Wallahi kin harban da kibiyan nan ta so,
Ba magani na tabbata sai naki.
Ke ce farar tauraruwa mai haskake,
Sassa da annuri, taho Gamzaki.
Kusan
waɗannan nau’i guda biyau a iya cewa suna tafiya ne bisa abubuwa iri ɗaya, ke
nan Hausawa ne suka ari wannan kaso na Gazal Al’Udhari suka samar da kasaon
nasu Gazal ɗin da suka tsarma su a cikin waƙoƙin Soyayya.
Waɗannan
nau’uka guda uku na Gazal a Larabci da kuma Hausa su ne suka taru suka samar da
ire-iren waƙoƙin Gazal da ake amfani da su, kuma duk wata waƙar gazal wajibi ne
ta faɗo cikin wannan kaso.
4.0 Bambancin Nau’o’in Waƙoƙin Gazal na Larabci da na Hausa
A nan kuma maƙalar ta fito da bambancin da aka samu ne a tsakanin nau’in
waƙoƙin Gazal Larabci da Hausa, a Larabci an samu Nau’i uku yayin da a Hausa
aka samu Huɗu duk da waƙoƙin Gazal na Larabci da na Hausa suna da matuƙar
kamanci da juna, amma hakan bai hana aka samu wasu abubuwa ba da suka bambanta
su, wanda ake samun su a Hausa ba bu su a Larabci.
4.1 Gazaliyya (waƙar Gazal ta Hausa)
A Hausa akwai nau’in waƙar Gazal
wanda Yahya (2014) ya kira da suna Gazaliya, wanda ya bayyana cewa ita ce waƙar
da aka tsara gaba ɗayanta tana bayyana tsananin so ga masoyi, wani lokaci har
da bayani kan raɗaɗin rabuwa ko yin nisa da masoyi. Wannan waƙar namiji ne ke
shirya wa namiji dan’uwansa ita ko mace ta shiyra mace ‘yaruwarta. wanda ya
kasance uban gida ko malam ko shugaba ko ma aboki, a bayyana irin kyautatawa da
karamcin da aka samu a lokacin da ake rayuwa tare da wannan da ya yi wa waƙar,
wanda a halin da ake waƙar ba sa tare ko dai an masa nisa ko kuma an rasu. Irin
wannan fasalin babu shi a waƙoƙin Gazal na Larabci, sai da a Hausa. Misali
waƙar Gudale ta yabon Alhaji Giɗaɗo Ibrahim Yabo, wadda Haliru Wurno ya rubuta
ga wasu daga cikin baitocin waƙar:
Na
yi kiran Allah shi ishe ni,
Al’amarin
ga da yad dame ni.
Na
yi salatu ga Hairil halƙi,
Ahmada
ya zo man da Mubini.
Na
yi salatu dubu da salama,
Alaihi
wa alihi ahlid dini.
Na
ga rashin abkin kayana,
Don
haka tsoro ya ribce ni.
Na
ga dare da subahin haske,
Ga
kuma rana ta dushe ni.
Na
yi farat na sheƙa
inwa,
Na
ga kwamarci ya kore ni.
Na
ga ruwan gulbi na zallo,
Na
zo na shiga sun toye ni.
Na
tuma na koma can ganga,
Ba
wani mai jinya ya fake ni.
In za a lura za a ga cewa tun a baitin farko wannan waƙar
ta saɓa da fasalin waƙokin Gazal na Larabawa inda aka fara buɗe waƙar da
ambaton Allah, wanda ba a samun haka a waƙoƙin Gazal na Larabawa.
5.0 Kamanceceniyar Waƙoƙin
Gazal na Larabci da na Hausa ta Fuskar Salo
A nan an yi ƙoƙarin fayyace irin salon da mawaƙan gazal
na Larabci da na Hausa suke amfani da su domin isar da saƙonsu ga masu karatu
ko sauraren waƙoƙin. Kamar dai yadda aka riga aka sani, Salo hanya ce da ake gane dabaru
ko hikimar da marubuci ya bi domin isar da saƙo. Kamar yadda Dangambo
(2007) ya bayyana, “salo wani yanayi ne na zaɓen yadda mai rubutu
zai yi amfani da kalmomi ko lafazi domin ya isar da zance wanda kan bambanta
shi da wani marubuci wanda ba shi ba”. Salo yakan ƙara armashi a rubutu saboda
akan bi hanyoyi na musamman kamar amfani da karin magana ko kwatanci ko sarƙa
kalmomin wani harshe wanda ba harshen da ake amfani da shi wurin rubutun ba da
sauransu. Salo yana ƙara bayyanar da hikimar marubuci wajen bin hanyoyin ƙara
wa rubutunsa daraja.
5.1 Salon
Waƙoƙin Gazal na gabaɗaya
Ga nazarin waƙoƙin gazal na Larabawa da na Hausa, kai
tsaye za a ce salon rubutunsu mai armashi ne, saboda yana da sauƙin ganewa, ba
salon kwan- gaba kwan- baya ba, domin ana shirya zaren tunanin waƙoƙin
daki–daki yadda mai karatu zai fahimci
saƙon nan da nan. Ban da sauƙin gane
waƙoƙin, akwai kuma armashi a salonsu na gaba ɗaya, domin ana amfani da salon
ƙawata magana wajen rubutu.
5.2 Amfani da Sauran Hanyoyin Salo
Wajen kawo salon gaba ɗaya, an ambaci cewa waƙoƙin gazal
ana amfani da salo mai armashi, wanda ke jawo hankalin mutane ga saƙon da yake
son isarwa. A wannan ɓangare an fitar da
mafi yawan waɗannan hanyoyi daki–daki gwargwadon abin da zai sa a gane manufa,
saboda fitar da hanyoyin da mawaƙan gazal ke amfani da su gaba ɗaya zai yi
matuƙar wuya. Don haka abin da za a sa gaba a nan shi ne, kawo gwargwadon
bayanai da misalai game da hanyoyin dabarun salo daban – dabam waɗanda aka yi
amfani da su a waƙoƙin.
5.2.1 Salon
Kwatantawa
A salon kwatantawa
kamar yadda kalmar kwatantawa ta bayyana, ana kwatanta ko auna abubuwa biyu ko
fiye, domin a fitar ko a gane dangantakar da ke tsakaninsu. Kwatantawa ta kasu
kashi uku akwai kamantawa da siffantawa da kuma jinsintarwa.
5.2.1.1 Kamantawa
Wannan hanya tana
kamanta abu biyu ko fiye ta hanyar amfani da wasu kalmomin awo irin su ‘kamar’
ko ‘tamkar’ ko ‘awa’ ko ‘ya’ ko ‘daidai da’ ko ‘wane’ ko ‘ ya zarce’ ko ‘ɗara’
ko ‘wuce’ ko ‘fi’ ko ‘gota’ ko ‘tsere’
ko ‘gaza’ ko ‘ƙasa’ da sauransu. Dabarar kamantawa ta kasu kashi uku, kamancen
daidaito da kamance fifiko da kamancen kasawa.
5.2.1.1.Kamancen
Daidaito
A nan mawaƙi zai kamanta wasu abubuwa biyu ko fiye, yana
nuna ɗayan daidai yake da wani, ko waɗansu abubuwa daidai suke da waɗansu.
Wannan kamanci na iya zama don aibantarwa ko don rage darajar abin da ake yin kwatanci a kansa.
Misali na wanan kwatance ya fito a waƙar Antarah Bin Shaddad mai suna, Hal
gadarar shu’ara’u mi mutaradammi, in da yake cewa:
وَكَأَنَّمَا نَظَرَتْ بِعَيْنَيْ شَادِنٍ
رَشَأٍ مِنَ الْغِزْلانِ لَيْسَ بِتَوْأَمِ
Fassarar mai bincike
Idonta in ta kalleka kamar
tana kallonka ne da idanin ɗan Barewa,
Ƙaƙƙarfa, wanda ba tagwaye ba shi kaɗai aka haifa.
A waɗannan baitocin ana
daidaita sifa ta masoyiyarsa da wasu sifofi mafi kyau da shahara, an daidaita
siffar idonta da idanun ɗan barewar da aka haifa shi kaɗai, wanda idanuwansa
sun kasance dara-dara ne masu matuƙar sheƙi da haske.
A cikin waƙar Binyaminu Zakari
Hamisu mai suna, ‘Nan yini
nan kwana..’ a wasu baituka yana cewa;
Ga kwalliyarta
kamar Ɗawisu in ta taho,
Tamkar Agwagwa a ƙasaita saman Ɓauna.
*****
A waɗannan baituka da ke sama,
za a ga cewa a baiti na farko mawaƙin ya daidaita kwalliyar masoyayarsa da kyau
irin na Ɗawisu. Ko shakka babu irin wannan kwatancen ana samun sa sosai a
waƙoƙin gazal na larabawa da na Hausa.
5.2.1.2
Kamancen
Fifiko
A wannan salon ana kawo kalmomin mizani da ake kwatanta
abubuwa daidai ko kwatanta wani abu da wanda ya fi shi ko da wanda ya kasa shi.
Don haka a wannan kamance na fifiko akwai kalmomin da ake amfani da su wajen
nuna fifikon wani abu ko wasu abubuwa a kan wani ko wasu. Kalmomin mizanin sun
hada da ‘zarce’ ko ‘wuce’ ko ‘ɗara’ ko ‘fi’ ko ‘gota’ da sauransu.
A waƙoƙin gazal wannan salo yana bayyana sosai sakamakon
cewa mafi yawan waƙoƙin akwai bayanin fifita masoyiya shi ya sa ake samun
wannan salon sosai a waƙoƙin na gazal a Larabci da Hausa. Misalai a waƙar Waƙar Imri’al Qais mai
suna “Liman ɗalalun afsartuhu fa shajani” ga abinda ya ce a wani baiti;
لهَا مِزْهَرٌ يَعْلُو الخَمِيسَ بِصَوْتهِ
أجَشُّ إذَا مَا حَرّكَتْهُ اليَدَانِ
Fassara mai bincike
Tana da Molo, yana
gagarar hargowa ta runduna mai sassa biyar,
in aka kaɗa shi mai yawan ƙara ne idan hannu ya ƙaɗa shi.
A wannan baiti Imru’al Qais ya yi amfani da salon kamance na fifiko ne inda
ya daga darajar wannan malo na mawaƙiyarsa fiye da hargowar tarin runduna wadda
ke da sassa biyar. Ya nuna cewa duk irin hargowar mutanen da ke cikin wannan
runduna, to amom molon mawaƙiyarsa ya fi shi tashi
A Hausa ma mawaƙan gazal sun yi amfani da irin wannan
salon a cikin waƙokinsu misali waƙar Ibrahim Sodangi mai suna ‘Abar bauta
Majanuni’ ga abinda ya ce a wasu baituka;
Ai ko Ka'abar
Rahmani,
Inuwar zatinki ta fi
sa shauƙi ya shige ni.
Haka taƙarar Ƙur'ani,
Karanta rubutunki ya
fi ratsa min uznaini.
A waɗannan baituka Ibrahim ya yi amfani da salon kamance
na fifiko domin fito da wasu muhimman abubuwa da yake so a cikin waƙarsa, in da
tsananin jazaba ta kwasheshi har yake nuna cewa shi a wajensa inwar zatain
masoyiyarsa ta fita shauƙin son ya ziyarta
Ka’aba.
5.2.2 Siffantawa
Siffantawa kwatanci ne na kai tsaye tsakanin wani abu ko
wasu, domin a nan za a ɗau wani abu a ce
shi ne wani kai tsaye ba tare da an yi amfani da kalmomin mizani da ake amfani
da su a wajen kamantawa ba. Akwai salon siffantawa da dama a waƙoƙin gazal, sai
dai za a kawo misalai ne kawai domin tabbatar da wannan magana. Misali a waƙar Umar bin Abi Rabi’a
mai suna ‘Layyata Hindu, a wasu baituka yana cewa;
أَكَما يَنعَتُني تُبصِرنَني
عَمرَكُنَّ اللَهَ أَم لا يَقتَصِد
فَتَضاحَكنَ
وَقَد قُلنَ لَها
حَسَنٌ في كُلِّ عَينٍ مَن تَوَد
Fassarar mai bincike
“Shin kamar yadda yake siffanta ni wurin kyau,
ko yana wuce gona da iri?” Allah ya
tsawaita rayuwarku.
Sai suka yi dariya suka ce mata,
“Ai so makaho ne”.
A wadannan baituka mawaƙin ya yi amfani da salon
sifantawa ne kai tsaye inda ya ambaci wuce gona da iri a matsayin kwatancen
kyau mafi ƙololuwa, sai kuma aka ƙara bayyana so a matsayin makaho wato wanda
bai gani, a taƙaice an siffanata so da makaho, kennan duk yadda shi Umar ke
siffantata ma ta wuce haka a wajensa, saboda duk abinda za a faɗi masa game da
ita ba zai saurara ba idonsa ya riga da ya rufe kan sonta da kuma bayyaa
kyawunta a idon mutane wanda har hakan ya sanya ta a kokwanto.
A waƙoƙin gazal na Hausa ma an samu irin wannan salon na
siffantawa misali a waƙar Bello Sa’id mai suna, ‘Tsarabar Masoyi’ a wani
baiti ga abinda yace;
Na shekara har uku cur ba hankali,
Duk na ɗimauce na kaɗe dominki.
Kullum ina fama da ƙunar zuciya,
Ko na yi barci sai na gano kurwarki.
Ko da cikin sallar farilla ne ni ke,
Sai zuciyata ta raya wajjanki.
A waɗannan baitukan Bello Sa’id ya yi amfani da salon siffantawa inda ya
bayyana irin halin ɗimauta da kaɗuwa da ya samu kansa saboda masoyiyarsa, har
ya nuna cewa sai da ya yi shekara cur ba hankali a tattare da shi, kullam
zuciyarsa cikin ƙunci take saboda rashin masoyiyarsa kusa da shi, shi yasa ma
duk baccin da zai yi sai ya fara ganinta a cikin baccin. Kai ƙarshe ma ya
bayyan cewa shi saboda rashinta ibada ma na neman susuce masa domin ko sallah
yake to zuciyarsa na wajenta. Ko shakka babu wannan salon yana taka rawa sosai
a waƙoƙin gazal musamman da ya kasance dama waƙoƙin ne da suke cike da
siffantawa da kamance da kuma kwatanci na masoya ta fuskoki da dama.
Waɗannan salalai su ne misalan wasu daga cikin salalan da ake samu a cikin
waƙoƙin gazal in an lura za a ga cewa dukkaninsu salalaine na kwatance da kuma
siffantawa sai kamantawa, wanda kuma dama waƙoƙin gazal a nan suka fuskanta. Za
a iya samun sauran wasu salon, a waƙoƙin gazal na Larabawa da Hausawa, sai dai
waɗannan sun fi shahara.
6.0 Sakamakon Bincike
Babu ko shakka duk wani bincike
da aka gudanar to daga ƙarshe akwai buƙatar a ga wane irin sakamako wannan
bincike ya samar, musamman ga al’ummar da aka yi binciken domin su.
Maƙalar ta gano cewa tsakanin
nau’o’in waƙoƙin Gazal na Larabawa da na Hausa akwai kamanci sosai tsakaninsu
musamman yadda mawaƙan ke gina waƙoƙin.
Maƙalar ta gano cewa akwai
bambanci tsakanin nau’o’in rubutattun
waƙoƙin Gazal na Larabci da na Hausa ta fuskar adadin ɗango da kuma waƙar Gazal
da ake shiryawa domin yiwa shugaba ko uban gida, wanda a Hausa ne ake samun
wannan fasali, sannan a Hausa ne ake samun adadin ɗango ya wuce biyu.
Ta fuskar Salo maƙalar ta gano
cewa kusan duk wasu salalai da ake amfani da su a Larabci to a Hausa ma dai
sune, domin tushen waƙoƙin Gazal na Hausa dagha Larabcin aka samo su.
Maƙalar ta gano cewa Al’ummar
Hausawa da Larabawa tamkar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai kan abin da ya shafi ayyukan
adabi na waƙa, domin kwatanta waƙoƙin Gazal na Larabawa da na Hausa ya taimaka
ƙwarai wajen sanin yanayin yadda Larabawa ke gudanar da rayuwarsu da kuma
abubuwan da suke da alaƙa tsakanin Larabawan da Hausawa.
Maƙalar ta gano cewa babu wani
nau’in waƙa da ya kai na Gazal sanya hikima da kuma nuna gwanitar harshe da
naƙaltarsa, kasantuwar mafi yawan waƙoƙin Gazal sai an yi fashin baƙinsu sannan
ake fahimtar su, saboda yadda ake sanya salo da adon harshe da fasaha da
naƙaltar harshe a cikinsu.
7.0 Naɗewa
Wannan
maƙala ta bibiyi Nau’oi da salon rubutattun waƙoƙin Gazal tsakanin Larabci da
Hausa. An yi bayani ne inda aka duba
nau’o’in waƙokin da suka yi kamanci aka
yi fashin baƙinsu da misalai, sannan aka dubi bambancin da ke tsakanin nau’o’in
rubutattun waƙoƙin Gazal na Larabci da na Hausa tare da kawo misalai a
tsakaninsu. An kuma yi nazarin ire-iren salon da masu rubuta waƙar ke amfani da
shi domin yin kwatanci tsakanin na Larabwa da na Hausa. Sai kuma aka kawo
sakamon binciken, ma’ana abinda aka gano bayan da aka kammala binciken.
Manazarta
Abdullahi, Y. (2016). Al-Muzanatu baina ƙasidatal
ash-shai’raini, amirul-mumina
Muhammu
Bello wa Muhammadul-Bukhari firasat’ ammihima Al-Ustazu Abdullahi Bn Fodiyo. A
Dissertation Submitted to the Posgraduate School Usman Danfodiyo Unversity.
Ainu, H.A. (2005). Rubutattun waƙƙoƙin addu’a na Hausa: Nazarin jigonsu da
salailansu.
[Kundin Digiri na Uku] Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami’a Usmanu Danfodiyo.
Al-Harthi, M.J.
(2010). I
have never touched her: The
body in al-ghazal al-‘udhri.
[Unpulished
PhD, Thesis]
University of Edingburgh College of Humanities and Social Science School of
Litereatures, Languages and Cultures Department of Islamic and Middle Estern
Studies.
Al-askandariya da Wasu (BS) Taikhul Adab. Naqada Printing and Publishing
Company,.
Al-alamiyya, J.D (2001).
Al-adab Wannusu Wal Balaga wan
Nakad. Jami’atul Da’awatul
Islamiyya.
Adamu, M. (2019). Kawatanci tsakanin
rubutattun waƙoƙin
siyasar jumhuriya ta uku da na jumhuriya ta huɗu a Nijeriya [Kundin Digiri na Uku]
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.
Babangida, A.Y (2011). A comparative literary study of
the hamziyya panegyric poetry of
the
prophet ( p.b.u.h) by Ahmad Shawqiy and Aliyu Jarim.
[Unplished Masters Degree] Department of Arabic. Bayero University.
Baffa, S.A (2021). Sabon zubin waƙoƙin
Hausa a ƙarni
na ashirin da ɗaya.
[Unpublished
Ph.D Dissertation] Usman Danfodiyo
Unversity.
Funtua, A.I (2002). Waƙoƙin Siyasa na Hausa a Jamhuriya
ta Uku: Jigoginsu da Sigoginsu”.
Takardar da aka gabatar
a taron ƙara wa Juna Ilimi, Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Ibrahim, A. (2004). Nazarin jawo hankali cikin
rubutattun waƙoƙin soyayya na
Abdullahi
Bayaro Yahaya. [Kundin Digiri na Ɗaya]
Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.
Ibn Khutaiba (BS). Kitab
Al-shi’r Wa-al-shua’ara. Dar-Alma’arifa.
Isah, H (2021). Salon tsakuren nassi cikin waƙoƙin
Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu.
[Unpublished
Dissertation of Masters of Arts]
Department of Nigerian Languages. Usman Danfodio University.
Jalajel, D (2007). “A short history of Ghazal” Ghazalpage
Jangebe, M.M (1991). Nazari kan rubutattun waƙoƙin
yabo na garin Sakkwato [Kundin
Digiri Na Biyu] Sashen Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Nuhu, A (2012). Sauye-sauye a tsarin waƙoƙin
zamani: Nazari a kan waƙoƙin
finafinan
Hausa [Kundin Digiri Na Biyu] Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ojolowo, S.A (2013). A comparative study of erotic poetry of Imru’ul
Qais and Umar bn abi
Rabi’ah. [Unpublished
Dissertation Masters Degree] Submitted to the Department of
Arabic Bayero University.
Ramlatu, M.A. (2015). Fannu al-rasa’ilada al-sha’ir al-shaikh Usmanu
Naliman: Dirasah
adabiyyah tahaliliyyah [Unpublished
Dissertation of Masters of
Arts] Department of Arabic. Usman
Danfodio University.
Sa’id, B (1982). Dausayin
Soyayya. Northen Nigerian Publishing Company.
Satatima, I.G (2009). Waƙoƙin baka na ɗarsashin
zuciya: Yanaye-yanayensu da sigoginsu.
[Kundin Digiri na Uku] Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Kano: Jami’ar Bayero.
Yahaya, A.B (2014). Gudale WaƘar Soyayya: Misalin Ghazal
a cikin rubutattun waƙoƙin
Hausa. Cikin Feschcript na Farfesa Abdulqadir Ɗangambo.
Zaiti. A (2007). Tarikhul Adbil Arabi. Dar-al-ma’arifa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.