Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari a Kan Bambance-Bambancen Da Ke Tsakanin Wakokin Gargajiya Da Na Zamani, Bincike Na Musamman Na Wakokin Sarauta Na Alhaji Musa Danƙwairo Da Na Gama-Gari Na Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) – 5 Babi Na Hudu

ƘUNSHIYA

1. Shafukan Farko

2. Babi Na Ɗaya

3. Babi Na Biyu

4. Babi Na Uku

5. Babi Na Huɗu

6. Babi Na Biyar

Wannan kundin binciken an samar da shi ne domin samun shaidar takardar karatun digiri na farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Tsangayar Karatun Digiri, Kwalejin Ilmi Da Ke Gumel, Kulawar Jami'ar Bayero, Kano.

NAZARI A KAN BAMBANCE-BAMBANCEN DA KE TSAKANIN WAƘOƘIN GARGAJIYA DA NA ZAMANI, BINCIKE NA MUSAMMAN NA WAƘOƘIN SARAUTA NA ALHAJI MUSA ƊANƘWAIRO DA NA GAMA-GARI NA AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA)

NA

ISAH MUHAMMAD KAWU
Lambar Waya: 07047484384

BABI NA HUƊU

4.0 Gabatarwa

Waƙa musamman ta baka ta ƙunshi wani babban rukuni na adabin baka wanda ya haɗa da hanyoyin kaɗe-kaɗen Hausa da bushe-bushe da kuma waƙe-waƙen Hausawa. Fage ce wanda ake aiwatar da shi da ka, a isar da saƙonninta da ka, sannan a adana shi da ka. Ɓangaren adabi ne daɗaɗɗe wanda za a iya cewa tun lokacin da aka ga Hausawa aka gan su da abinsu, illa iyaka kawai akan daɗa kyautata shi da bunƙasa shi ta hanyar shuɗewar zamani.

4.1 Ma’anar Waƙa

Wannan aba ta sha gwagarmaya a wajen masana da dama, inda suka ba ta ma'anoni daban-daban gwargwadon fahimtarsu.

Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero ya bayyana waƙa da cewa, "wata tsararriyar magana ce da ake rerawa a kan kari ko rauji", (CNHN, 2006:466). Kodayake, masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar waƙa. A ra'ayin wani masanin, ba kome ba ce waƙa illa maganar fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman(Yahaya, 1988:1). Shi kuwa Yahaya a tasa fahimtar dangane da ma'anar waƙa cewa ya yi:

Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba (Yahaya 1997:4).

A ganin Umar (1980:3), waƙa tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka waɗanda ake ƙira baitoci ko ɗiyoyi kum ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman. Yahya ya ƙara ba da tasa maanar waƙa da cewa:

“Magana ce da ake shisshirya kalmominta cikin azanci, ta yadda wajen furta su ana iya amfani da kayan kiɗa”. Yahya (1997).

Shi kuma Ɗangambo (2007:) cewa ya yi:

“Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa'ida ta baiti, ɗango, rerawa, ƙari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙaidojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.

Idan aka lura da ma'anar da Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero ya bayar, za a ga cewa ya kawo bakandamiya ma'anar waƙa. Domin kuwa maganar fasaha da yake yi a cure. Ta yiwu maganar nan ta baka ce ko rubutacciya. Bayan haka, an nuna a cure za a yi maganar, ke nan idan za a warware ta, ana iya samun wani dogon bayani ke nan. An kuma yi maganar tsari na musamman cikin sha'anin waƙa, wanda ke nufin cewa waƙa ta yi hannun riga da zube domin ita tana da tsari na musamman ba kamar zube ba wanda aka zuba shi kara-zube, ba tare da wata ƙa'ida ba ta musamman ba.

Amma shi Yahaya (1997) a tunaninsa waƙa fa dole ta kasance cikin zaɓaɓɓun kalmomi da aka zaɓa kuma dole sai an auna su don a ga yawan gaɓoɓi ko tsawon ƙafafuwansu yadda za su dace da inda ake son a aza su, kuma a sami damar rerawa. Domin rerawa wani babban ginshiƙi ne a sha'anin waƙa ko wace iri ce.

4.2 Rabe-raben Waƙa

Ta fuskar yanayi, an raba waƙa zuwa gida biyu;

i.Waƙar gargajiya (Waƙar Baka)

ii.Waƙar zamani (Rubutacciyar Waƙa)

4.2.1 Waƙar Gargajiya Ko Ta Baka

A wani aikin kuma, Gusau cewa ya yi: "waƙar baka fage ce wadda ake shirya maganganu na hikima, da ake aiwatarwa a rere cikin rauji tsararre, waɗanda za su zaburar da al’umma tare da kuma hankaltar da su dangane da dabarun tafiyar da rayuwa da za su ba da damar a cim ma ganga mai inganci. Waƙa bisa jimla, takan zama fitila wadda take haskaka rayuwar jamaa kuma take kare rayuwar alumma daga sallacewa Gusau (2011).

Bunguɗu (2014). Kuma ya bayar da ma’anar waƙar baka kamar haka:

“Waƙar baka ta ta ƙunshi wasu jerin hikimomi ne da a kan tsara domin su daɗaɗa zukatan masu saurare, inda a kan yi amfani da wata za’ba’b’biyar murya don rerawa, ana kuma yin amfani da zaɓaɓɓun kalmomi domin fizgar hankalin jama’a ya dawo gare su da zimmar bin diddigin ma’anoni da manufofinsu.

A ɓangare na ma'anar waƙar baka ta fannu, Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya ayyana wasu kalmomi na ƙulla da amsa da ƙara da azanci da kuma shirya waɗanda suke yin nuni dangane da matakai na bayyana waƙar baka ta Hausa. Ɗanƙwairo yace "

Jagora: Duk makaɗan da at Tashe na shahe,

: Hab baki hay ƴan gidan su duka,

Ƴ/Amshi: Babu mai shirya waƙa kamat tawa.

Jagora: Duk makaɗan da at Tashe nai jam'i,

: Hab baƙi hay ƴan gidan su duka,

Ƴ/Amshi: Babu mai shirya waƙa kamat tawa.

Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla wata tai,

Ƴ/Amshi: Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,

: In naƙ ƙulla waƙa a ƙara man,

: Mu haɗu du azanci gare mu,

: Shin a'a mutum guda za ya radde mu.

(Gusau, 2008:104-105).

A lokacin da Muhammad (1979:87) yake bayyana zumunta a tsakanin waƙar baka da rubutacciyar waƙa ya yi ishara dangane da wasu halaye da za su iya yin nuna a kan ma'anar waƙar baka inda ya bayyana, aiwatarwa a wakar gargajiya ta haɗa da rerawa da baki sannan a sadar da ita a gaban jama'a, kuma wadda bisa yawanci ake yi a ƙungiya ta jagora da ƴan amshi, kuma a haɗa ta da ƙida.

Sa'id (1981:235) ya faɗi" waƙar baka ita ce wadda ake rerawa don jin daɗi, a ajiye ta a ka, kuma a yaɗa ta a baka.

Gusau (2003) yana ganin a ma'ana ta ilmin waƙa, waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci wanda yake zuba gaba-gaɓa bisa ƙa'idojin tsari da daidaitawa, a rera cikin sautin murya da amsa-amo na ƙari da ƙida, sau da yawa kuma a tare da amshi.

4.2.2 Samuwar Waƙoƙin Gargajiya

Wak’ar gargajiya dai ita ce waƙar baka. Waƙar baka kuwa abu ce da wadda ta dade a kasar Hausa tun lokaci mai nisa.

Waƙbaka dai ta samu ne tun lokacin da ɗan Adam ya fara neman abinci ta hanyar farauta. Daga nan kuma waƙar baka ta daɗa bunƙasa a sakamakon noma da yaƙe-yaƙe da sanaoi da wasanni da sauran aladun gargajiya.

Akwai saɓanin ra’ayi dangane da samuwar waƙar baka. Wasu daga cikin masana sun ce, Samuwar waƙar baka ta samo asali ne ta hanyar bauta ta gargajiya, ta daɗa bayar da haske wajen kyautata sha’anin waƙa duk daga cikin ra’ayoyin da ke bayarwa dangane da samuwar wakar a kasar Hausa. Wasu kuma suna ganin cewa wakar ta samo asali ne daga wani maroki (Sasana). Da wannan ne ra’ayin wasu ya karkata ga makadan Hausa da cewa, su jikokin Sasana ne wato wancan maroƙi, wanda ya rayu a bangaren Ashiya daga baya wasu daga cikin ƴaƴansa suka yo ƙaura zuwa ƙasar Hausa. A wannan ma’anar kalmar Sasana tana nufin maroƙi da harshen Faransanci. Haka kuma har wa yau wannan ra’ayi yana karfafa cewa, Sasana roƙo ya fara buɗe baki da shi da nufin ya yabi wani mutum ya bashi samu. Sasana shi ne maroki na farko da aka yi tun lokacin jahiliyar duniya.

Ibrahim (1983) Sasana ana nufi dashi wai wani mawaƙin Balaraben wata ƙabila ta Madina mai suna Hassanuɗan Thabitu wanda ya yi rayuwarsa tun lokacin jahiliyar Larabawa har zuwa lokacin bayyanar Annabin Muhammad (SAW). Daga nan ya musulunta ya koma yana yi wa Annabi Muhammad (SAW) wak’a har ya zama babban mawaƙi. Wai jikokinsa ne suka fantsama cikin uwa duniya har suka bayyana a cikin ƙasar Hausa.

Gusau (1983), wannan ra’ayi na Gusau game da waƙar baka ya nuna cewa, Cikin zato Hausawa sun samu waƙa ne daga tsofaffin daulolin Afirka ta Yamma, wato Ghana da Mali da Songhai. Wannan raayi yana gani lokacin daular Mali akwai su da makaɗan fada, kuma suna da alaƙa ta kusa da makaɗan Hausa musamman ma makad’an fada. Da daular Mali ta shud’e sai daular Songhai ta maye gurbinta, sai ta gaje irin wad’annan kaɗe-kaɗe. A lokacin mulkin sarki Askiya Muhammadu ya kwarara da riƙonsa har cikin wasu ƙasashen Hausa. Saboda haka ta nan ne wasu sarakunan Hausawa suka ga tsarin makaɗan su ka koya.

Har ila yau a wannan ƙauli na uku Ibrahim (1983) ya bayyana muna samuwar waƙa da cewa, samuwar waƙar ta samo hasken faruwa ne daga bautar iskoki ko dodanni. Hausawa a lokacin maguzanci suka yi wa iskoki ko dodanni bukin cika shekara, ko kuma idan wani abu ya faru sukan taru wajen abin bautar nan, su yi masa yanke-yanke da shaye-shaye. A wajen abin bautar nan sukan yi bukukuwa da waƙe-waƙe da zuga da kambamawa da hawar da su ta hanyar kirari ko koɗasu (take). Dangane da wannan ra’ayi ana jin ta hasken ƙirari da kaɗa taken waɗannan iskoki ko dodanni aka samu wanzuwar waƙar baka. Kuma ana jin daga nan ne aka samu makadan gargajiya na ‘yan bori.

Amma duk da waɗannan ra’ayoyi da suka gabata ana kyautatazaton cewa, Hausawa sun ƙagi waƙa ne ta hanyar farauta da kirare-kirarenta, daga nan kuma sai ta dada bunkasa ta hanyar noma da yaƙe-yaƙe. Idan muka yi la’akari da wannan za mu ga cewa, waƙar baka ta daɗe da samuwa a ƙasar Hausa. Kuma tana da daɗeɗɗen tarihi wanda ba za a iya cewa ga rana ko lokacin da aka fara ta ba.

4.2.3 Waƙoƙin Gargajiya

A Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006:159) ya bayyana gargajiya da 'ɗabi'a ko wani kaya irin na zamanin da'. Gargajiya a fannin waƙar baka kuwa na nufin asali ko farko wato waƙoƙin baka na asalin Hausawa waɗanda suka fara aiwatarwa da rerawa da kansu. Domin haka, waƙoƙin gargajiya, waƙoƙi ne na kankin kan Hausawa waɗanda suka ƙago su da kansu, suke yin su bisa al'adunsu kuma suke shiryawa da ka, su rera su da ka, sannan su sadar da su da ka, kuma su adana su ta hanyar haddacewa. Zubin kalmomin da jumlolin na waɗannan waƙoƙi duk da ka ake yin su sannan ana ɗora musu amon kiɗa ta amfani kayan kiɗa waɗanda Hausawa suke ƙirƙirar su da kansu gwargwadon yanayi wuri na ƙsar Hausa da suke zaune a cikinsa. Waƙoƙin da ake aiwatarwa da su bisa wannan yanayi kuma suka ɗore a kan haka, su ne ake ƙira waƙoƙin gargajiya na Hausa.

Waƙoƙin Hausa na baka ana iya shirya su ne a ƙungiya ko a kaɗaita kuma suna iya zama waƙoƙi ne na shiri ko ƙire. Haka kuma ana iya yi wa waɗannan waƙoƙin rerawa ɗaya ko biyu ko uku gwargwadon yadda makaɗi ya rage ɗiya da ya zuba wa rerawa ta farko ko kuma ya ƙara su.

4.2.4 Mawaƙan Gargajiya

Kamar dai yadda aka sani ba kowa ne zai iya yin waƙoƙin gargajiya ba sai wanda ya gada ko ya nemi a koya masa ko sha'awar yinta kuma sai har idan yana da zalaƙar yin waƙar. Wasu tuni suka samu zalaƙar yin waƙa kuma suna iya aiwatar da ita a koina ba tare da sun ɗauki wani tsawon lokaci ba. A ƙasar Hausa dai muna da mawaƙan gargajiya da suke yin waƙa iri daban-daban, rabe-raben waƙoƙin ya shafi nau'in jigon waƙoƙin da suke yi da kuma dangantaka da dalilan da suka ake yin waƙoƙin da kaɗe-kaɗen da irin mutanen da ake yi wa waƙoƙin dominsu. Dangane da wannan dalilan, za a iya rarraba waƙoƙin gargajiya kamar haka:

i.Makadan Sarauta/Fada: Kamar yadda sunan ya nuna, waƙoƙi ne da mawaƙa suke yi wa jinin sarauta ko mutanen da suke riƙe da miƙamai na sarauta musamman miƙamin da ya shafi mulkin gargajiya. Misali Sarki, Hakimi, Dagaci, ko manyan fadawa. To, amma yanzu, saboda canjin lokaci, irin waɗannan mawaƙan, su kan yi wa manyan mutane masu kuɗi, ko ma'aikatan gwamnati waƙoƙi. Shararrun kayan kaɗe-kaɗen fada su ne kamar algaita, jauje, kiɗan taushi da sauransu da yawa. A ƙasar Hausa, galibi kowane Sarki da Hakimi yana da mawaƙansa. Irin waɗannan mawaƙa su ne waɗanda kowa kiɗa da waƙa, sai ubangidansu. To, amma wani lokacin sukan mawaƙan sukan nemi uzirin a wajen iyayen gidansu don su je su yi wa wasu Sarakunan waƙa. Kowa mawaƙi da irin waɗandan, yana samun abincinsa, tufafinsa, makwancinsa da sauran abubuwan buƙatun rayuwa daga uban gidansa. A cikin shararrun mawaƙan fada da akwai:Alhaji Musa Ɗanƙwairo, Ibrahin Narambaɗa, Sarkin Taushin Katsina, Alh. Salisu Jankiɗi, Sa'idu Faru, Tauɗo Inugu, Abdulrahman Sarkin kiɗa da sauransu.

ii.Makadan Jama'a (Gama-gari): Su ne waɗanda suke yi wa kowa da kow waƙa, ba sai jinin sarauta ba ko masu riƙe da wani muƙami ba. Su, duk wanda ya ba su kuɗi ko abin duniya ko kuma duk waɗanda suka ga dama, to sai su yi musu waƙa wato su, na kowa da kowane tun daga kan Sarki, talaka, mai kuɗi, mai ilmi, da sauransu. A taƙaice dai, za a yi cewa duk wanda iya ta aura baba ne. Makaɗan jama'a, suna da waƙoƙi da kayan kaɗe-kaɗe iri-iri kamar su: masu kaɗa ganguna, dundufa, kurya, masu busa; sarewa, ƙaho, farai, tiɓallaro, masu izga da tsarkiya; goge, molo, garaya, gurmi, kukuma da sauransu.

A ƙasar Hausa da akwai mawaƙan jama'a da yawa maza da mata daga cikinsu da akwai: Dr. Mamman Shata, Alh. Haruna Uji, Audu Karan Gusau, Alh. Sani Sabulu Kanoma, Garba Sufa, Hassan Wayam, Ɗan Maraya Jos, Musa Gumel, Tsoho Balare, Hajiya Barmani Coge da sauransu da yawa.

iii.Makadan Jarunta (Maza): Mawaƙan maza, su ne masu kiɗa da waƙa ga mutane masu nuna junantarsu ko bajintarsu a fili, misali kamar makaɗa da mawaƙan ƴan dambe, kokawa, tauri (Gangi), yaƙi irin na da, masu wasa da maciji ko kura da sauransu.

Irin waɗannan makaɗan su ne kiɗan yabo ko zuga gwarzayensu saboda karfinsu da jaruntarsu ko rashin tsoronsu. Shahararrun makaɗan maza, su ne irinsu: Muhammadu Bawa Ɗan Anace, Hamisu Ganga, Makaɗan shaɗi da sauransu da yawa.

iv.Makadan Ban-dariya: A nan, abin da ake nufi da ban dariya shi ne, a faɗi wani abu ko a yi shi don yin raha, a yi dariya, a ƙyalƙyale, a yi shewa, a kalli abin a yi murmmushi. Wannan aji na ban-dariya, babban aji ne, domin kuwa ya ƙunshi duk wasu kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe waɗanda suka ƙunshi raha, nishaɗi da ban-dariya. Ire-iren waɗannan mawaƙa ko makaɗan su ne kamar Ƴan kama, Ƴan Gambara, Ƴan Galura, Ƴan Ƙoroso, Ƴan A-Daki-Buzu da sauransu.

v.Makadan Manyan Mata: Waɗannan waƙoƙi da mata suke yin su musamman a lokacin da suke aiwatar da wasu ayyukan cikin gida. Manyan mata suna yin waƙoƙin ne a lokacin da suke yin daka a turmi, ko raino, ko daɓe ko niƙa ko wanke-wanke ko shagulan bukukuwa, ko shantu, ko kiɗan ruwa, ko kiɗan Amada da sauransu da yawa.

vi.Makadan Sana'a: Haka waɗannan mawaƙan ko makaɗan su ne suke waƙoƙinsu kan wata sa'ana ta Hausa wato su ne mawaƙan sana'ar noma ko fawa ko Maƙera, Maharba, Malumai, Mafarauta, Masunta, Ƴan Bori, Ƴan Cacada da sauransu. Su ne yin waɗannan waƙoƙin ne domin zuga manowa a lokacin da suke gudanar da ayyukan na gona musamman ayyukan gayya, su kuma mawaƙan mahauta suna zuga mahautan ne domin su yi bajinta, musamman a lokacin da za su kama Sa da ƙarfin tsiya, su yi masa hawan ƙaho da makamantan haka.

vii.Makadan Sha'awa: Su ne waƙoƙi ne da ake shirya wa abubuwan da suka ba mutum (mawaƙi) sha'awa ko suka ƙayatar da shi. Da wuya a ware mawaƙi ko makaɗi ɗaya daga cikin mawaƙan Hausa a ce waƙoƙin sha'awa kawai yake shiryawa, amma akwai wasu mawaƙan da suke tsarma ire-iren waɗannan waƙoƙi jifa-jifa a cikin waƙoƙinsu kamar su Alh. Haruna Uji, Dr. Mamman Shata Katsina, Ɗan Maraya Jos, Hassan Wayam da Sani Ɗan Indo da sauransu.

A taƙaice dai, waƙoƙin gargajiya na Hausa suna nan jibge kuma sun ratsa dukkan sassan rayuwar Hausawa ta fuskar zamantakewa da siyasar zama ko tattalin arziki ko ta addini ko hanyar al'adu ko wasannai da sauransu.

4.3 Taƙaitaccen Tarihin Musa Ɗanƙwairo Maraɗun

4.3.1 Haihuwarsa

An haifi makaɗi Musa Ɗanƙwairo a shekarar 1909 a ƙauyen Ɗankandu cikin ƙasar Bakura, yankin ƙaramar hukumar Talata Mafara, jahar Sakkwato. Sunan mahaifinsa Usman Ɗankwanada, mahaifiyarsa kuwa ana ƙiranta da suna Ƴarkunu wadda ta fito daga ƙauyen Goron Namaye. Ɗanƙwairo yana da yayu ƴan uwa maza da mata, duk babban yayansu shi ne makaɗi Abdu Kurna. Musa Ɗanƙwairo ya sami laƙabin 'ƊANƘWAIRO' a sanadiyar sunan wani ƙanin mahaifinsa wanda ya yi tafiyarsa yawon duniya da ake ƙira "Ƙwairo" shi dai Ƙwairo yaron Usman ne, kuma yana da zaƙin murya, amma daga baya sai ya bar kiɗa. To, bayan da Musa Ɗanƙwairo ya kai kimanin shekaru bakwai da haihuwa, sai ya fara karɓi tare da mahaifin nasa, saboda yana da zaƙin murya kamar ta Ƙwairo, sai makaɗi Usman ya ce, "Ga Ɗanƙwairo kuma an mayar"2. Shi ke nan sunan Ɗanƙwairo ya bi makaɗi Musa.

4.3.2 Ƙuriciyarsa da Tasowarsa

Rayuwar Ɗanƙwairo ya yi ta ne a birnin Ƙayan Maraɗun, a nan ya tashi ya buɗe ido da sanin abubuwa. Amma an tabbatar da cewa a lokacin ƙuriyarsa, shi yaro ne mai hankali da biyayya da ladabi da kuma ɗa'a da ganin girman manyansa na gaba da shi. Amma makaɗi Musa Ɗanƙwairo bai sami damar shigo makaranta ta Muhammadiya ba wato dai bai yi karatun allo ba, ballantana ma karatun boko. Shi dai Allah ya ba shi ƙwaƙwalwa da fasaha da basirar gane waƙa ne kawai. Kuma yana da da basirar haddace tarihin abubuwa wanda yake ji daga bakunan mutane.

4.3.3 Fara Waƙar Musa Ɗanƙwairo

Musa Ɗanƙwairo ya gaji kiɗa ne gaba ɗaya, kuma buɗa idonsa a cikin kiɗa da waƙar. Ya fara koyon kiɗa a wurin mahaifinsa Usman tun yana ɗan shekara bakwai, watau a wajajen (1916).

Makaɗi Usman yana nan zaune tare da iyalensa a Ɗankadu, ƙauyen Bakura yana kiɗan noma da na sarakai, sai Sarkin Ƙayan Maraɗun Ibrahim (1903-1923) ya aika ya taso ya koma ƙasar Maraɗun da zama makaɗinsa. Ana yi wannan hijira ne lokacin da Ɗanƙwairo yana da shekaru biyar da haihuwa watau a shekarar 1916. A lokacin ya soma da kiɗan kanzagi ne har ya zo ga karɓi, kamar dai yadda ake fara koyon kiɗi.

Bayan da mahaifin nasa ya bar kiɗa sai kai Ɗanƙwairo wajen yayansa watau Abdu Kurna, Ɗanƙwairo a wajen Abdu Kurna ya naƙalci kiɗa sosai, ya dinga bisa zuwa yawon kiɗa wurare daban-dabam. Saboda hazaƙar Ɗanƙwairo, sai Abdu Kurna ya ba shi muƙamin Daudun kiɗi watau Ɗan Galadimansa. Tun yana Ɗan Galadiman kiɗi aka ga alamar zai zama wani hamshaƙin makaɗi, domin yakan taimaka wa Abdu Kurna bayar da waƙa da kuma ƙari gare ta. Shi kuma Musa Ɗanƙwairo duk lokacin da ya sami sauli ba a zuwa wani rangadin kiɗa ko zuwa yammaci, sai ya ɗauki ganguna ya shiga ƙauyuka wajen gayauna, ya dinga waƙoƙin noma tare da yara ƴan uwansa. Amma duk lokacin da ya dawo yawon gayauna yana nuna wa yayansa Abdu Kurna duk abubuwan da ya samo a wannan lokacin. Yana cikin wannan hali, sai makaɗi Abdu Kurna ya ba shi izinin ya fara yi wa ƴaƴan Sarakuna waƙa don ya saba da kiɗan Sarakuna. Waƙar da ya fara yi ta ƴaƴan Sarakuna ita ce wadda ya tafi tare da Uwargidansa Jemo tana yi masa amshi. Ga waƙar:

Gindin waƙa: Ɗan Sarki a gode maka,

Jikan Dodo Ɗan Gwamna.

Ya tafi daji ba shi komowa,

Gyado mai ƙoƙarin gabce.

Mijin Dija jikan Nomau,

Gwarzon Ango karsanin Ali,

Gungaman Iro ɗan Jatau,

Kullum daga duƙe sai duƙe

Gyado mai ƙoƙarin gabce.

4.3.4 Ɗanƙwairo ya Kama Cin Gashin Kansa na Waƙa

A shekarar (1962) Allah ya yi wa makaɗi Abdu Kurna rasuwa. Daga nan Ɗanƙwairo fa ya hau halifar kiɗa da miƙamin Sarkin ko uban kiɗa. Sai ya fara ci gaba da yi wa Ƴandoton Tsahe Alhaji Aliyu ii da kuma Alhaji Amadu Bello Sardaunan Sakkwato waƙoƙi sannan da sarakuna na gado Sarkin Ƙayan Maraɗun Muhammadu (1964-1981).

4.3.5 Ire-iren Waƙoƙin da Musa Ɗanƙwairo ya yi.

Musa Ɗanƙwairo ya yi waƙoƙi da dama ta fannoni iri-iri, ya kuma yi waƙoƙi masu ɗumbin yawa wanda shi kansa a lokacin yana raye bai san adadinsu ba. To, amma a dunƙule dai ga ire-iren waƙoƙin da ya yi:

i. Waƙoƙin Noma

ii. Waƙoƙin Fada na sarauta

iii. Waƙoƙin Ta'aziyya

iv. Waƙoƙin Siyasa

v. Waƙoƙin Gargaɗi

vi. Waƙoƙin Faɗakawa

vii. Waƙoƙin Jama'a.

4.3.6 Yadda Musa Ɗanƙwairo Yake Shirya Waƙoƙi

Makaɗi Musa Ɗanƙwairo yakan tsaya a gida ya kintsa sosai ga waƙa kafin ya fita waje ya je rera ta ga jama'a ko wanda ya shirya wa waƙar. Yawanci makaɗan baka na fada al'adar su ce sai sun shirya waƙoƙinsu kafin su fita zuwa ga rera su. Ɗanƙwairo yakan tara yaransa, su zauna a wuri ɗaya, su yi tunanin yadda za su tsara waƙa ta yi daɗi da kuma armashi.

Da farko za su fara samun launin kiɗa na waƙar, sai kuma a ƙirƙiri kalmomin ɗan gindinta, sannan a je ga sauran ɗiyar waƙar. Amma abin lura a nan shi ne ɗiyan waƙa na daɗa yawa ne dangane da lokacin da ake sake rera ta a wurare daban-dabam. Ɗanƙwairo yakan ba yaransa damar su yi walwala ƙwarai da gaske a cikin waƙoƙinsa, domin haka sukan ƙara ƙulla waƙa da dasa ta. Dangane da shirya waƙa, Musa Ɗanƙwairo yana cewa" In munka tashi yin waƙa wadda muka son ta zama abin tsitsi, watau sai mun yi ta daga gida. Kuma in a daji munka tsara ta, to in munka koma gida, sai mu koma mu bi ta a gidan. Zamu dinga sa wasu ɗiya muna cire wasu, kullum tana ƙaruwa tana daɗuwa.

Musa Ɗanƙwairo ya ce ba su ɗaukan lokaci da yawa wajen shirya waƙa doguwa, misali waƙa mai kai wa kimanin tsawon mintuna ishirin ko ma fiye da hakan, zai ɗauke su kwatankwacin kwana biyu suna tsara ta. Idan waƙar ta yi haske sosai za ta dinga daɗuwa lokaci zuwa lokaci. Kuma lokacin da suka zo fara sabuwar waƙa, abin da su fara yi a nan shi ne samo mata launin kiɗan da zai dace da ita. Bayan samun launin kiɗan za su yi kimanin mintunan ishirin ko rabin sa'a guda, ba abin da su yi, sai kiɗan zallarsa. Daga nan, sai su shiga kawo ɗiyan waƙar, kowa zai dinga zuwa da hikimar da Allah ya ba shi. Sau da yawa sukan hana kansu barci domin tunanin ɗiyan waƙar da za su sawa a cikin waƙoƙinsu.

4.3.7 Mataimakan Musa Ɗanƙwairo Na Waƙa (Ƴan karɓi)

Ƴan karɓin Alhaji Musa Ɗanƙwairo suna daga cikin nau'in ƴan amshi masu cikakkun ƴancin yi wa waƙar ubangidansu ƙari, kamar dai yadda na nuna a baya. Babu bare a cikin duka yaransa daga ƙanne sai ƴaƴa da jikoki, ga su kamar haka:

i. Alhaji Muhammadu (Daudin kiɗi)- ɗansa ne

ii. Alhaji Audu (Wakilin kiɗi)- ɗansa ne

iii. Alhaji Alu- Jikansa ne

iv. Alhaji Sani Zaƙin murya (Marafan kiɗa)-ɗansa ne

v. Alhaji Abubakar (Ciroman kiɗi)

vi. Ibrahim (Sarkin fadan kiɗi)- Jikansa ne

vii. Mamman Jikka- Jikansa ne

viii. Sani (Sanƙira)- Jikansa ne

ix. Ƙanƙahu (Bara)

x. Sada (Sanƙira)

xi. Nabuba (Bara)

xii. Bucaca ƴar kohji

xiii. Amadu Bakura

xvi.Sallah Kwana

xvii. Dauda Ɗangaladima da sauransu

4.3.8 Yawace-Yawacen Musa Ɗanƙwairo a Waƙa

Musa Ɗanƙwairo ya je garuruwa da yawa ta hanyar wannan sana'a ta waƙa, ya je garin Daura da Katsina da Kano da Bidda da da Zariya da Illorin da Kaduna da Kantagora da Lagos da Yamai da Damagaran da sauransu da yawa. Kuma ya zagaya dukkan manyan garuruwan jahar Sakkwato kamar Gusau da Mafara da Maru da Argungun da Yawuri da sauransu.

4.3.9 Waƙoƙin Fadar da Musa Ɗanƙwairo Ya fi Sha'awa

A hirar da aka yi da shi ya yi nuni cewa a cikin waƙoƙin ya fi sha'awar waƙoƙi guda biyu a ransa, su ne kamar haka:

Waƙa ta farko ita ce ta Sarkin Ƙayan Maraɗun Muhammadu (1964-1981)

Gindin waƙa: Ɗan Amadu tsayayye,

: Ko ɗauri ba ya wargi,

: Ya zo da lafiya da girma,

: Ɗan Amadu tsayayye,

: Ko ɗauri ba ya wargi,

: Ci gari Bello ɗan Muhammadu,

: Gagara dako ya niƙace arna.

Waƙa ta biyun ita ma ta Sarkin Ƙayan Maraɗun ce Muhammadu (1964-1981)

Gindin waƙa: Ya ci garin maza ɗan Shehu,

: Gagara ƙarya baƙon dodo,

: Sarki ya tsare ni da kyauta,

: Ni ko na tsare gado.

4.3.10 Dangantakar Musa Ɗanƙwairo da sauran Makaɗa

Makaɗi Musa Ɗanƙwairo ya nuna cewa yana zaune lafiya da sauran makaɗan baka na Hausa, sannan yana ba kowa hakkinsa na girma. Hasalima yana girmama Ibrahim Narambaɗa da Aliyu Ɗandawo, musamman ma su abokanen yayansa ne wato Abdu Kurna ne. Daga cikin makaɗan kotso ƴan uwansa ya fi sha'awar waƙoƙin makaɗi Ibrahim Narambaɗa, a fannin waƙoƙin noma kuwa, waƙoƙin abokinsa makaɗi Kaka Na garin Ƴar kohji ta ƙasar Bakura. Yawanci ma ya haddace wasu daga cikin waƙoƙin waɗannan makaɗan guda biyu, su da yawa yakan rera su shi kaɗai a duk lokacin da yake cikin nishaɗi.

4.3.11. Shaharar Musa Ɗanƙwairo a Waƙa

Makaɗi Musa Ɗanƙwairo babu shakka ya shahara a fagen waƙoƙin sarauta da na jama'a daga bisani, don haka shahararsa tasa tana komawa ga irin waƙoƙin da yake shiryawa daɗaɗa masu ƙayatarwa. Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo sun sami karɓuwa sosai a Nijeriya, musamman a jahohin Arewa irin su Kano da Sakkwato da Kaduna da Katsina da sauran ƙasashen duniya.

4.3.12 Iyalan Musa Ɗanƙwairo

Hausawa kan ce "Iyali suturar mutum, iyali suturar gida". A bisa yanayin zamantakewar bil Adama da aljannu, cikar ɗa namiji da ƴa mace shi ne yadda Allah ya hore musu, ya basu dama, suka assasa zuriya ta karan kansu.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya sami jagoranci na iyaye wajen yin matar farko. A yayin zaman Ɗanƙwairo a doron rayuwar duniya bayan matarsa ta fari, ya auri mata da yawa kimanin mata takwas jumulla sakamakon auri saki da ya yi a lokacin yana raye, sannan wasu daga cikinsu su ne suka haifa masa ƴaƴa har guda goma sha bakwai; maza goma sai mata guda bakwai (Gusau 2021).

4.3.13 Rasuwar Musa Ɗanƙwairo

Dukkan mai rai mamaci ne, Allah ya yi wa Alhaji Musa Ɗanƙwairo rasuwa a ranar Juma'a 13 ga watan Satumba, 1991 a nan gidansa na Kano. Ya rasu ya bar mata da ƴaƴa tare da jikoki da yawa, bayan rasuwar sa zuriyarsa sun ci gaba da hayayyafa, kamar yadda babban ɗansa Alhaji Garba Musa Ɗanƙwairo ya bayyana wa manema labarai. Da fatan Allah ya ji ƙansa ya jaddada rahama a gare shi ya albarkaci bayansa, Amin.

4.3.14 Zuriyar Musa Ɗanƙwairo

Zuriyar marigayi Musa Ɗanƙwairo tana nan zaune tare da dukkan iyalensa a sabon mazuƙunin da aka yi musu na gidan Ɗankano gab da hanyar ɗaukewa zuwa dam na Balakori da sabuwar Maraɗun.

4.4 Gudummawa Da Ci gaban Alhaji Musa Ɗanƙwairo da ya Bayar

A duk lokacin da ake son ganin tarihin wani Bil Adama, ci gabansa tare da ƙalubalen da ya fuskanta ana komawa ne kan adabinsa, ta nan ne ake fuskantar al'adunsa da ɗabi'unsa. Marigayi Alh. Musa Ɗanƙwairo Maradun ya zama wani kundi na adana tarihi da zamantakewa da faɗi-tashi da gwagwarmayar da aka yi a fagen waƙoƙi domin raya adabi da bunƙasar harshen Hausa. Gabanin mawaƙi ya shahara a ji shi a wajen ƙasarsu, dole ya kasance yana fagen da ya fi rinjaya ga waƙoƙinsa. Fagen da waƙoƙin mawaƙi suka fi rinjaye, da yawa da shahara da karɓuwa ga al'ada nan ne fagensa na waƙa ko da mawaƙin ya yarda ko kar ya yarda, abin ya bayyana da shi a hukunce, wanda ya faku ya zarce binciken manazarta sai a bar shi ga masanin gaib.

Alh. Musa Ɗanƙwairo masana adabin waƙa irin su Ɗalhatu (1975) da Ɗangambo (1987) da Gusau (2019) da Zulyadain (2000) da Yahaya (2016) da Dumfawa da Usman (2021) sun ajiye Alh. Musa Ɗanƙwairo a gurbin mawaƙin fada duk da waƙoƙin da ya yi wa shahararrun ƴan kasuwa da ƴan siyasa da sojoji da shugabannin ƙasa, komai daɗinsu da karɓuwarsu ba su fitar da shi a farfajiyar 'mawaƙin fada' ba.

Waƙa tana cikin makarantar farko ta malam Bahaushe wanda a cikinta yake koyon ilmi na rayuwar yau da kullum kuma daɗaɗɗiyar taskar taskace adabi da harshe da tarihi ce. Alh. Musa Ɗanƙwairo na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan fada da suka gwagwarmaya wajen bunƙasa adabi a ƙasar Hausa da kewayenta. Daga cikin jigogin waƙoƙin da ya yi na fada da akwai irin su: zambo, tarihi, zuga, yabo, zamantakewa, al'ada, raya harshe, roko, habaici, kirari, ilmi, soyayya da dai sauransu. Yanzu za a ɗan bayanin wasu daga cikinsu:

i. Waƙar Zambo

Bello (1976:31). Ya ce zambo dai shi ne na faɗin wani mugun abu ga wani mutum a fakaice. Shi ne kishiyar yabo. A kusan dukkan lokuta, waɗanda ake yi wa wannan zambo suna gane da su ake, ko kuma al'umma na iya fahimtar da waɗanda ake, ƙila saboda yadda aka bayyana kamanninsu a cikinsu zambon.

Misali: A cikin waƙar Alh. Musa Ɗanƙwairo wanda ya yi wa Sarkin Dass Alh. Bilyaminu Usman.

Jagora: Wani ɗan sarki mai dogon geme,

Ƴ/Amshi: In yah hece geme,

: Su am man shiya,

G/waƙa: Ba hwaɗa ma ba,

: Sarkin Dass Bilyaminu

: Soma shirin daga.

Ƙarin bayani: gemu an san wata sifa ce, ba halitta ba ce, domin ana samun "shagiri" kuma wasu na aske shi nan take sifar ba ta ɓata.Wanda aka nufa da wannan zambo ya san da shi ake, sauran ƴan uwansa da fadawa da fada su ma sun san kai tsaye da wanda ake.

ii. Waƙar Nuna Tarihi

Tarihi a nan yana nufin ambaton abubuwan da suka gabata a rayuwar yau da gobe kuma sukan shuɗe da suka danganci ainahin rayuwa ta haƙiƙa.

Sanin tarihi abu ne mai muhimmancin gaske domin ta nan ne ake sanin abubuwan da suka gabata don a gyara su da waɗanda za su zo. Kowane abu yana da tarihin yadda ya kafu. A cikin waƙa ana iya sanin kafuwar sarauta ko al'ummarta. A fagen tarihi Alh. Musa Ɗanƙwairo sun yi ta ƙoƙarin fitowa da asalin sarauta ko Basarake da suke yi wa waƙa.

Misali: Alh. Musa Ɗanƙwairo a cikin waƙarsa ta Bai kasa ba, bai gaza ba, wanda ya rerawa marigayi Mai martaba Sarkin Daura Alh. (Dr) Muhammad Bashar yana cewa:

" Nai tambaya a Najeriya ina asalin Hausa Bakwai sun ce Daura,

"A ƙasar Nijar da niyyi tambaya ina asalin Hausa Bakwai, sun ce Birnin Daura,

"A ƙasar Kamaro da niyyi tambaya ina ne asalin Hausa Bakwai, sun ce Birnin Daura,

"Daga Sakkwato har Argungun sun san Birnin Daura, birnin tarihi ne"

Ƙarin bayani: Alh. Musa Ɗanƙwairo ya bayar da tarihin garuruwa da sauran sarakunansu da ma sunayen sarautun da ke tsakanin Sakkwato zuwa Kaduna, tun daga Shuni har zuwa Rigachikun, a cikin waƙar 'mai dubun nasara garnaƙaƙi Sardauna'

"Amadu ya zo Hausa, za shi gida nai rannan,

Ƴan sanda, ƴan doka da matocin Gohe.

Duk jama'a sun taru, suna yi mai bankwana

Suna roƙon Allah"

iii. Waƙar Yabo

Gusau (2002:301), ya bayyana yabo shi ne ambaton sambarka da nufin nuna amincewa da hali ko wani abin da mutum ya yi nagari. Alh. Musa Ɗanƙwairo yana yin amfani da yabo sosai a cikin waƙoƙinsa don ya nuna nagartar wanda ya ke yi wa waƙar.

Misali: A cikin waƙar da ya yi wa Alh. (Dr) Ado Bayero ta 'Bata kura kabarin gaba, wanda ya kwatanta shi da Aljannar duniya saboda tsananin yabo.

Jagora: Aljannar duniya,

: Ɗan Abdulƙadir Sarki Ado

: Na tare da kai ya lilwanta

: Ruwan wankin dauɗa ne"

iv. Waƙar Tauhidi

Tauhidi shi ne kaɗaita Allah (SWA) da bauta masa tare da amincewa da dukkannin abin da ya jingina wa kansa da sunaye da siffofi da ayyuka. Kuma shi ne abu na farko da ke tabbatar da kasancewar mutum musulmi.

Misali: Alh. Musa Ɗanƙwairo a waƙarsa ta Ado Bayero wanda ake yi wa amshi da "Barkak ku da taurin gaba, na yarda da Sarki Ado" a cikin waƙar da akwai tauhidi kamar haka:

"Gaskiya na nan ga wurinta,

Mutane mu yarda da Allah,

Wanda duk yay yarda da Allah,

Ka san wannan bai taɓewa'

Ƙarin bayani: al'amarin yarda da Allah, tauhidi ne da ya game duk kashe-kashen tauhidi. Wannan ɗan waƙa ya game yarda da samuwar Allah, da kaɗaita shi da bauta, da ayyuka da duk wani abin da ya ƙunshi miƙa wuya ga Allah. Haka Ɗanƙwaron ya bayyana sakamakon duk wanda ya tsai da ƙafa ga yarda da Allah a ɗango na ƙarshe na rashin taɓewa koyaushe.

Haka kuma a cikin waƙarsa ta 'Mai dubun nasara garnaƙaƙi Sardauna' nan ma Ɗanƙwairo ya shigo da tauhidi inda yake cewa:

Tun da Allah shi ya hukunci bawa nai,

Shi ka ba shi komai,

Kuma shi ka hana nai,

Ƴan uwa ku riƙa,

Ba ƙarfi nai na ba,

Ƙarfin Allah ne'

Ƙarin bayani: Wannan ɗan waƙa ya ƙunshi tauhidi na kaɗaita Allah da ayyuka. Hukunta kowane lamari ya wanzu, ya tabbata abu ne da ya kaɗaita ga Allah kawai. A nan Ɗanƙwairon ya bayyana Allah (SWA) a matsayin mai hukunta komai ta hanyar bai wa bawansa komai, ko hana shi.

v. Raya Al'adu

Ɗangambo (1984:38) ya bayyana al'ada da cewa "ita ce a bar da aka sa ba yi yau da gobe, akwai al'adu masu kyawu da marasa kyawu.

Misalin Waƙar Tsafi.

Ƙamusun Hausa CNHN (2006:449) ya fassara kalmar tsafi da hanyar ba da gaskiya da wani abu daban da ba Allah ba.

Bunza, (2006:39) ya karkasa rabe-raben tsafi kamar haka:

1. Tsafin bauta.

2. Tsafin buwaya.

3. Tsafi na kare martabar gado.

4. Tsafi na magani

Tsafin Bauta

Tsoron ɗan Adam na cutuwa daga wani abu da bai sani ba, tare da kwaɗayin sakamakon wani aiki da yakan aikata, shi ne ya kawo masa tunanin bauta. A wannan haujin Bahaushe kan yi wa iskoki hidima da nufin neman wasu kariya daga gare su . Bunza, (2006:40) ya tabbatar da cewa: “Yi wa iskoki ɗa’a ga umarnin da sukan sanya mutum na hani da horo, shi ne bautar.” Makaɗa Ɗanƙwairo ya fito da wannan saƙon lokacin da yake wa wani ɗan sarki zambo inda yake cewa:

Jagora: “Ga wani ɗan sarkin Keffi,

: Can nig ganai cikin daji,

: Inda tsamiya, yana ta rawa,

: Yana baya-baya ba ta gani,

Yara : Da ɗan ƙulƙi nai gun Magiro.

Gindi: Muhammadu Cindo bi da maza,

Mamman ɗan Mamman bajimi.

(Waƙar sarkin Keffi, Alhaji Muhammadu Cindo Yamusa).

A wannan waƙa Ɗanƙwairo ya fito da hoton yadda ake wani tsafi na bauta a garin Kwatarkwashi (a can baya, kafin wannan lokaci), domin ya nuna irin yadda wani ɗan sarki ya manta da Allah ne ke bayar da mulki ya koma tsafe-tsafen bauta da nufin neman mulki.

Har wa yau, a lokacin da Ɗanƙwairo ke wa sarkin Gwambe waƙa, ya yi wa wani ɗan sarki zambo, inda ya danganta shi da gudanar da tsafin bauta. Ga yadda yake cewa:

Jagora: Ai ga wani ɗan sarkin Gombe,

: Bai biɗa ga Allah ba,

: Ya sai babbaƙun tumaki,

: Ya sai babbaƙun shanu,

: Sai yak kirayi ‘Yanbori,

: Kullum ana yi mai goge, wawa,

‘Y/Amshi: Bokaye sun canye kuɗinka,

Jagora: Bokaye

‘Y/Amshi: Sun cinye kuɗinka,

Jagora : Ba shi ga Allah ba shi ga Annabi,

Ba shi ga tsuntsu,

‘Y/Amshi: Ba shi ga tarko,

Jagora : Babu kuɗin kuma,

‘Y/Amshi: Babu sarauta.

Gindi : Gagari gaba gwauran giwa,

: Sarkin Gombe Shehu Na Abba.

(Waƙar Sarkin Gwambe, Alhaji Shehu Na Abba).

Tsafin Buwaya

Ga al’adar ɗan Adam bai cika son ƙasƙanci ba, wannan dalilin ne yakan sa ya yi duk abin da ka iya yiwuwa da nufin samar wa abin da zuciyarsa take so (idan ba a yi katari da wanda yake bin addini da gaskiya ba). Wanna ta sanya Makaɗa Ɗanƙwairo ya fito da wannan naui na tsafi a cikin waƙarsa, saboda ya nuna wa masu saurarensa yadda wasu sukan yi wasu ayyuka na kauce hanyar tauhidi da nufin neman ɗaukaka. Misali, lokacin da Makaɗa Ɗanƙwairo yake cewa:

Jagora: Ga wani ɗan sarkin ƙasar Tcahe,

: Yai baƙar tagguwa yai baƙar riga.

Yara: Yai baƙin wando ga baƙin rawani ga kai nai,

: In yai baƙi ƙirin ba ka gane shi,

: Sai nic ce wagga sabga ta tsahi ce.

Gindi: Shirya kayan faɗa mai gida Tsahe,

Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.

(Waƙar Yandoto Tsafe, Aliyu II).

A tsarin Bahaushe, idan ya yi nisa a tsarin bautar iskoki (bori) da camfi yakan riƙi wasu ɗabi’u su zame masa tada a gare shi, da nufin neman ɗaukaka ko kuma wata kariya daga abubuwa masu cutarwa. Irin wannan tunanin Makaɗa yake so ya fito da shi domin ya nuna yadda wani ɗan sarki ya shiga tsafi da nufin neman ɗaukaka.

Tsafi Na Kare Martabar Gado

Bunza, (2006:45) ya nuna idan Bahaushe ya gaji wata sana’a daga gidansu akwai wasu asirrai da babu wanda zai san da su sai ɗangado. A sirran kuwa na ‘yan Tsafe-tsafen da aka saba ne, domin maganin mai son ya wulaƙanta sanaar. Makaɗa Ɗanƙwairo ya bayyana wannan naui na tsafi a lokacin da yake yabon wani mai sanaar noma da wanzanci a waƙoƙonsa na kiɗan noma. Ga bain da yake cewa:

Jagora: Wanzamai tsoronka sukai,

‘Y/Amshi: In dai an ka zana suna,

Kai ɗai aka jira,

Jariri ba shi askuwa sai ka zo.

Gindi: Ya riga su gona,

Mai kalmen wuce maza ɗan Musa.

(Waƙar Giye Ɗanmusa)

A wannan ɗan waƙa Makaɗa ya fito da irin bajintar Giye Ɗanmusa ta mallakar magungunan tsafe-tsafe na kare martabar gadon gidansu. Gaskiya ne, gadon gida alala ga raggo. Kuma kowa ya tsare gadon gidansu bai karambani ba, in ji masu magana.

Waƙa a kan Magani

A tsarin zamantakewa, cututtukan zuciya na neman biyan buƙatar soyayya da farin jini da ɗaukaka waɗanda ake ganin idan ba a biya su ba zuciya ta tawaya. Ibrahim, (2002:366). Irin wannan yanayi, shi ne ya sa Bunza, (2006:47) ya gano cewa: “Tsafin magunguna nau’in tsafi ne da Bahaushe ke yi kawai bisa ga abin da rai ke so yadda yake son abin.” Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya fito da irin wannan naui na tsafi a lokacin da yake ƙulla turken zambo ga wasu ‘ya’yan sarakuna na Birnin Gobir da na Tsafe. Ga abin da yake cewa:

Jagora: Wani ɗan sarkin Sabon Birni,

Bai samu sarauta ba na ganai,

Ƙaura nig gamu da shi,

Ga wuƙa tai a hannu nai.

Amshi: Irin gidan Bawa Jangwarzo,

Na Sanda ya ci garin arna.

Jagora: Ya ce tunda ban yi sarauta ba,

Ba ri yanzu in ta batun tauri.

Gindi: Irin gidan Bawa Jangwarzo,

: Na Sanda ya ci garin arna.

(Waƙar Sarkin Gobir, Alhaji Ibrahim).

Kasancewar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo cikin Bunza, (2006:51) ya nuna tauri tsafi ne, wannan ta sanya makaɗa ya nuna yadda wani ɗan sarki ya koma tsafi saboda bai sami sarauta ba. Ya ci gaba da kawo wannan turke a ɗan waƙarsa, a lokacin da yake yabon sarkin Tsafe Ahaji Aliyu Yandoto II inda yake cewa:

Jagora: Ga wani na jayayya da Ali,

: Har yau bai fasa ba,

: Ya zo gun boka nai,

: Wai a yo mai dibi,

: Da boka yad diba mai,

: Yac ce ba ka sarauta,

: Sai in ka ci tauri,

: A she magana mai sauƙi,

: Ya ci maganin icce,

: Kuma ya ci maganin ƙarhe,

: Bai sami sarautar Tcahe ba,

: Sai tciga tat taso mai,

: A gaida baran ɗan kurjal.

Yara : Ƙi-gama ka bi jiki ka goge.

Gindi: Na Amadu baƙon dole,

: Shi yak kashe wargi Ali,

: ‘Yandoto ana saunarka.

(Waƙar Sarkin Tsafe Alhaji AliyuII).

A wannan ɗan waƙa makaɗa ya fito da yadda wani ɗan sarki ya riƙa cin maganin tauri domin ya zama sarki. A wannan wuri makaɗa ya yi haka ne domin ya fito da turken nau’in tsafin magani da Hausawa suke amfani da shi.

Vi. Waƙar Roƙo

Roƙo ta fuskar addinin musulunci haramun ne, sai in ya zama dole. A al'adance kuwa, roƙo sana'a ce ga wasu mutane waɗanda zuciyarsu ta yi rauni. A ɓangaren mawaƙan bakan Hausa, a gaskiya kowane mawaƙin baka, musamman a idon Bahaushe, to maroƙi ne. Idan kuwa mawaƙi bai roƙo ba a cikin waƙarsa, ga alama babu abin da zai samu ga mutane.

Bunza, A.M. (2009) ya bayyana cewa" roƙo a wajen mawaƙan fada yana da dabaru iri huɗu kamar haka: roƙo na kai tsaye, roƙo na nuni ga abin da ake so, roƙo na zuga, roƙo na godiya ga abin kyauta"

Misali: Ɗanƙwairo a wata mai taken "Babban jigo Na Yari, Uban Shamaki Ture Haushi" wadda ya yi wa Sarkin Daura Muhammadu Bashari. Akwai ɗan waƙar da ke cewa:

"Allah shi ka kawo komi,

Yaƙin Ɗan Bakalori ya ci mu,

Sai in hwaɗa wa Mamman,

Ban da gida yanzu, ban da gona,

Yanzu a cikin damana nake ta shirin,

Ɗan wurin da za ni bacci"

Ƙarin bayani: Wannan roƙo ne muraran a wajen Ɗanƙwairo, amma a fakaice ta hanyar nuni da cewa, yana neman Sarki ya ba shi gida a nan Daura ya kuma ba shi gona.

Vii. Waƙar Ta'aziyyar Ahmadu Bello Sardauna

Ta'aziyya tana nufin juyayi ko aihini game da rayuwar wani masoyi ko wata masoyiya, sannan da tuna wasu abubuwan alheri da ya yi a lokacin da yake ko take raye, daga nan kuma sai a yi kukan rashinsa ko rashinta.

Ta'aziyya ita ce gaisuwar da ake yi wa mutanen da aka yi wa rashi/rasuwa (mutuwa), ana yin ta ne don sanyaya musu zuciyarsu da nuna alhini daga ƙarshe kuma a yi wa mamacin addu'o'in neman rahama ga mahaliccinmu.

Misali: Alh. Musa Ɗanƙwairo ya yi waƙar ta'aziyya ga Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, in da yake cewa:

Gindin waƙa: Ya wuce reni ba a yi mai shi,

Amadu jikan Garba sadauki,

Kungurum ƙashin giwa na Alu ba ka haɗuwa,

Kowah haɗe ka sai ya cake maƙoshi,

Gabas da yamma, Kuda da Arewa,

An san kai ne Sardauna, mai kwana kyauta,

Saboda baiwa......

Amadu saboda hairi aka sakamma,

Firimiyan jihar Arewa Amadu,

Abin da kai ma Nijeriya,

Hak ƙasa ta naɗe, ana tuna ka,

Amadu jikan bawan Allah,

Gamji ɗan ƙwarai X2

Gohe Allah,

Malam Gohe, Allah gafarta ma, Amin.

Sarakunan Da Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi Musu Waƙoƙi:

Makadan fada sune wadanda ke aiwatar da wakokinsu ga wani Basarake guda a matsayin Ubangidansu ba tare da sun hada shi da wani ba, in kuwa sun hada din to sai da izininsa ko wani amininsa kuma da sharadinsa. A duk lokacin da wani Basarake ya riki wani Makadi a matsayin mawakinsa na fada to fa cin wannan makadi da shansa da suturarsa da muhalli da dawainiyarsa duk sun rataya ne kan wannan ubangidan nasa. Da yawa daga cikin wadannan mawakan sun gaji wannan ne daga wajen iyaye da kakanninsu

A wasu lokutan, makadan fada na daina yi wa Basarake kida saboda wani dalili na musaman, ko dai don gaza daukar nauyinsu ko canza ubangida ko rasuwar wanda aka yi wa kidan ko kuma ra'ayi. Misali, Makada Aliyu Dandawo Shuni ya fara da Ardon Shuni Mamman ya kare da Sarkin Yauri Abdullahi Abarshi.

Shi kuma Alhaji Musa Dankwairo ya gaji yi wa Sarkin Kayan Maradun waka daga Babansa; Usman Dankwanaga, anan kuma ya tsaya sai dai ya je Balaguro ya dawo gida Maradun.

Kasancewar Alhaji Musa Ɗan mawaƙi da za a yi sanya shi rukunoni daban-daban na mawaƙa, amma sai a fuskanci a wane ɓangare ya fi ƙarfi wajen ƙaewa da yin waƙoƙi masu tarin yawa. Wannan ta sa a ka tsayarta da shi a rukanan makaɗan fada na sarauta.

Wakokin Makadan Fada

Kafin Hausa, (2002:241) Yace wakokin sarauta wakoki ne da suke cike da hikimomi da fasaha da nuna zalaka irin ta al'ummar Hausawa. Sannan kuma suna dauke da salo iri-iri na Sarrafa harshe kamar su kirari ko Karin Magana da karangiya da dai sauransu da abubuwa masu kara nuna gwanintar harshe. Makaɗan wannan rukunin a baya su ne akan gaba wajen shirya waƙoƙin baka masu ma'ana da nagarta.

SARAKUNAN DA MUSA ƊANƘWAIRO YA YI MUSU WAƘA

i. Sarkin Nasarawa; Alh. Labaran Bajimi Abubakar

ii. Sarkin Muri; Alh. Umaru Abba

iii. Sarkin Daura; Alh (Dr) Muhammad Bashar

iv. Sarkin Dass; Alh. Bilyaminu

v. Sarkin Kano; Alh. Ado Bayero

vi. Sarkin Gwambe; Alh. Shehu Na Abba

vii. Sarkin Gumel; Alh. Ahmad Muhammad Sani II

viii. Sarkin Yawuri; Alh. Yakubu

ix. Sarkin Misau; Muhammad Manga

x. Sarkin Maraɗun; Alh. Ibrahim

Kayan Kiɗan Sarakuna

Mawaƙa da makaɗa a ƙasar Hausa akwai kayan kiɗa da suke amfani wajen yi wa sarakuna waƙoƙi, ga su kamar haka:

Farai, Kakaki, Algaita, Molo, Kotso, Ganga, Tambari, Taushi, Zari, Kuwaru, Banga, Kalangu, Kurya, Ƙirya, Ƙaho, Ɓata, Cali, Gwaini, Kuge, Turu, Jauje, Goge, Ƙwarya, Gantso, Yoho, Ɗungum, Kuma-kumi, Kukuma da sauransu.

Makaɗan Baka na Gargajiya

Makaɗan baka na gargajiya suna da yawan gaske dangane da manufofin kiɗansu da waƙoƙin da suke sadarwa ga al'umma, amma ga wasu daga cikinsu: Alhaji Musa Ɗanƙwairo, Salisu Jan kiɗi, Aliyu Ɗandawo, Alhaji Dr. Mamman Shata, Adamu Ɗan maraya Jos, Ibrahim Na Rambaɗa, Mamman sarkin taushin Katsina, Muhammad Sarki Kakadawa, Abubakar Kassu Zurmi, Alhaji Haruna Uji, Sa'adu Barmani Coge, Abdu Karen Gusau, Abdu wazirin Ɗanduna, Muhammad Bawa Ɗan anace, Sani Sabulu Kanoma, Tsoho Balare, Musa Gumel, Uba Mai kotso, Amadu Doka, Hamza Ibrahim Caji, Adamu Garba Ɗankwamarado, Abdu Mamman Ashana, Babangida Kakadawa, Mari Mai Ƙwarya da sauransu da yawa

4.5 Waƙoƙin Zamani

Masu iya magana, na cewa" zamani riga ce, wanda yaƙi saka ta ya kwana huntu". Asalin wannan kalmar an aro tana daga harshen Larabci wato 'Zaman' sai Bahaushe ya ƙara mata wasalin 'i' a ƙarshenta ta koma zamani. Wanda a harshen Hausa take nufin' Yayi, lokacin da ake ciki, lokaci mai ci yanzu, ko yau, bana ko yanzu. Daga jin wannan kalmar ta 'Zamani' mutum ya san wani abu ne da ya faru ba lokaci mai nisa ba, ko kuma ma a lokacin da ake ciki a yau.

Bahaushe yana amfani da wannan kalma ta fuskar adabinsa, yana cewa"

i.Zamani riga ce wato idan ya zo sai a ɗauka a sanya a jiki, to amma a kula ka da a sanya mummuma ko yageggiya ko mai dauɗa a jikin.

ii.Zamani baya jira, idan ya wuce sai anko.

iii.Zamani gaskiya ne.

iv.Zamani hanjin Jimina; da akwai na ci da akwai na zubarwa

v.Zamani gaskiya ne, abokin tafiya ne.

vi.vi.Idan zamani ya zo gudunsa ƙauyanci ne, rashin karɓarsa wautar kai ne, rashin amfani da shi yana sa a bar al'umma a baya, sannan yaƙi da shi kuma rashin hankali ne.

vii.Allah shi ne zamani.

Ƙamusun Hausa (CNHN 2006:489), ya ba da ma'anar zamani da 'yayi ko lokacin da ake ciki ko mai ci'. Amma ma'anar zamani ta fannu a waƙar baka, tana nufin lokacin da Hausawa suka iya rubutu da karatu na harshen Larabci har suka samar da rubutun Ajami da kuma lokacin da suka iya rubutu da karatun harshen Ingilishi har suka kuma suka samar da rubutun Boko. Ke nan, waƙoƙin zamani waƙoƙi ne waɗanda suka wanzu a sakamakon iya rubutu da karatu na Ajami da na Boko da Hausawa suka yi, sannan bisa yawanci ake shirya su a rubuce, sannan a samar da rauji da kiɗa, a kuma fitar da rerawa a situdiyo. Daga nan ne za a iya sadar da su ta bin ƙaramar murya daga kwamfuta. Ana ajiye waƙoƙin zamani kai tsaye a naɗar da su a CD-CD ko a album-album.

Ana ɗora wa waɗannan waƙoƙi kiɗa ne daga kayan kiɗa na baƙi waɗanda aka tanada a ɗaki na musamman da ake ƙira situdiyo. Daga cikin kayan kiɗan baƙi da ake harhaɗawa a situdiyo akwai fiyano da jita da tashoshi da ganguna na Turawa da bigala da tsintsiya da sauransu.

Yawancin waƙoƙin zamani na Hausa akan yi musu rerawa ɗaya ce a situdiyo, sannan a wajen sadar da su a taruka da bukukuwa da sauran wurare akan maimaita rerawa ne ta bin rerawar farko ta situdiyo. Wannan yanayi ne ya ba makaɗi damar ya iya tsara waƙa, ya fitar da ƙa'idojin shirya ta a situdiyo ta bin kalmomin da ya rubuta, da rauji da kiɗa da kuma rerawa, sannan a naɗe ta a CD, a kuma aika ta wurin da ake buƙata da ita. Ta haka sai a iya sadar da ita ta hanyar na'urar kwamfuta da amsa-kuwa ko ta hanyar DVD da amsa-kuwa da sauransu.

Waƙoƙin da aka aiwatar da su kuma aka rera su, sannan aka sadar da su ta wannan hanya, su ne ake nufi da waƙoƙin baka na zamani.

4.5.1 Samuwar Waƙoƙin Zamani

Waƙoƙin zamani su ne ake kira da rubutattun waƙoƙi, rubutattun waƙoƙi kuwa sun samu ne a ƙasar Hausa bayan da aka samu rubutun Ajami wanda ya samu daga haruffa Larabci. Tarihin samuwar Ajami yana da alaƙa ta ƙud da ƙud da zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Bayan Hausawa sun samu ilimin addinin musulunci ne suka kuma ari adabin Larabawa na waƙa suka riƙa yin kwaikwayo suna gina nasu da shi. A tsarin rubutun waƙar Larabci akwai tsarin tafiyar da kari da kuma wasu ƙafofi da ake gina waƙa da su wato Aruli (ma'aunin waƙa) wanda da sai da shi ake auna waƙa a kuma tsara ta bisa ga wani tsarin da zai ƙara mata armashi.

Hausawa sun ari wannan ne suka kuma daidaita shi da nasu tsarin wanda zai ƙara wa tasu waƙar daɗi, kamar dai ta Larabawa. Sun kasance masu amfani da wannan tsari ta hanyar rubutawa da Ajami.

Abu ne mai wuya a iya cewa ga lokacin da aka fara rubuta waƙa da Hausa, amma kuma ana sa ran an rubuta wasu waƙoƙi da yawa tun kafin jihadin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo. Waɗannan waƙoƙi da ake sa ran a rubuta sun haɗa da waƙar Jiddul-Azizi wadda malam Shiitu Ɗan Abdurrauf ya rubuta, mai magana a kan Fiƙihu da kuma waƙar yaƙin Badar wadda Wali Ɗan Masani ya rubuta.

Amma masana da dama sun bayyana cewa, rubutattun waƙoƙi sun samu bunƙasa da yawa a lokacin jihadin Mujaddadi Shehu Usmanu. Haka kuma a wannan lokaci ne suka samu ingantaccen tsari wato ƙafiya. An bayyana cewa Mujaddadi ya rubuta waƙoƙi da yawa da suka kai kimanin (480), kuma daga ciki ya rubuta guda 25 da kansa 13 ya rubuta su da harsunan Larabci da kuma Fulatanci 12 kuma ya rubuta su da harshen Hausa. Waɗannan ayyuka da Mujaddadi da almajiransa suka yi duk sun yi shi ne cikin ƙarni na sha tara (Ƙ.19).

Bayan wucewar Mujaddadi da almajiransa rubutacciyar waƙa ba ta gushe ba ta kuma ƙara samun gindin zama a cikin ƙasar Hausa musamman a nan gida Nijeriya. a ƙarni na ashirin (Ƙ 20) ne aka samu wasu marubuta waƙoƙin Hausa suka rubuta waƙoƙi da dama dangane da jigogi daban-daban. Jigogin da aka rubuta waƙoƙi a kansu a wannan ƙarni sun haɗa da Jigon addini, siyasar musulunci, soyayya, ilimi da sauransu. Waɗannan marubuta da suka yi gagarumin aiki a wannan ƙarni sun haɗa da: Aƙilu Aliyu, Aliyu Namangi, Mudi Spikin, Muazu Hadejia, Yusuf Kantu, Bawa Shairi Durbawa, Sarkin Gwandu Haruna, Shehu Alkanci da dai sauransu.

Bayan an samu wasu da suka yi rubuce-rubucen waƙoƙi a ƙarni na ashirin (Ƙ 20) sai kuma bayan shuɗewar su aka samu wasu da suka yi rubuce-rubucen waƙoƙi a wannan ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ.21). Wannan ƙarnin ma an samu waƙoƙi da suka isar da wasu saƙonni daidai da ƙudirin marubuta waɗannan waƙoƙi. Kuma sun mayar da hankali ga siyasar rayuwa da ilimi da zamantakewa da soyayya da addini da dai sauransu.

4.5.2 Samuwar Waƙoƙin Baka na Situdiyo

Su kuwa waƙoƙin baka na zamani su ne waƙoƙin da aka sami sauyin rerawa aka sami sauyin kayan kiɗa daga waƙoƙin baka na gargajiya suka sauya zuwa sabuwar hanya ta zamani kamar mandiri da fiyano da kayan kiɗan disko. Irin waɗannan waƙoƙi su ne waɗanda Gusau (2016) ya ambace su da waƙoƙin situdiyo, wato a ciki ne ake haihuwarsu tare da sanya musu tufafi. A yanayin rera waɗannan waƙoƙi da kuma muhallan rerawar akwai bambanci da waƙoƙin baka na gargajiya. Ire-iren waɗannan waƙoƙi sun samu ne ta hanyar tasirin da baƙin alummu suka yi wa Hausawa. Gusau (2014:9) ya ba da ma'anar waƙoƙin baka na zamani da "Waƙoƙi ne da suka wanzu a sakamakon iya rubutu da karatu na ajami da na boko da Hausawa suka yi. sannan bisa yawanci ake shirya su a rubuce, a samar da rauji da kiɗa, a kuma fitar da rerawa a sitidiyo. Daga nan ne za a iya sadar da su ta bin ƙaramar murya daga kwamfuta. Ana ajiye waƙoƙin baka na zamani kai tsaye ta naɗar su a sidi-sidi ko a album-album.

4.6 Taƙaitaccen Tarihin Aminu Ladan Abubakar

4.6.1 Sunansa Na Yanka da Laƙabinsa.

Sunansa shi ne Aminudden ɗan Muhammadu Sani (Ladan) ɗan Mijin yawa ɗan Sarkin Gobir Dambuwa ɗan Sarkin Gobir Gwanki. A wajen mahaifiya kuwa, Aminudden shi ne ɗan Bilkisu ƴar Adamu ɗan Ibrahim ɗan Muhammadu. Bilkisu ita ce ƴar A'ishatu, ƴar Shehu.

Aminudden Ladan Abubakar wani laƙabi ne da aka san shi da shi, kuma shi da kansa ya raɗawa kansa ya sa wa kansa wannan suna, wanda ya haɗo sunayensa guda uku kamar haka: wasalin A yana nufin Aminudden, harafin L yana nufin Ladan hakazalika wasalin A na ƙarshe yana nufin Abubakar.

4.6.2 Asalin Iyayen Aminudden Ladan Abubakar da Nasabarsa

Ta fuskar iyaye maza, Aminu Ladan Abubakar ya fito ne daga gidan sarautar Gobir na Gwamkawa. Aminu Ladan Bagobiri ne bisa nasabar uba. A kuma gidan Gwamkawa Sarki Gwanki ne ya fara yin sarautar Gobir.

Malam Muhammadu kakan Aminu Ladan ne ta ɓangaren uwa Bakatsine ne kuma Bakutumbe. Ya yo ƙaura daga Katsina ya zarce zuwa garin Ɓagwai, ya kafa mazauni a garin Sarkin Ƴa. Muhammadu ya sami ƴaƴa da jikoki a zaman garin Sarkin Ƴa da ya yi.

(Hira da Usman Adamu Jallaba, 5/2/2015).

4.6.3 Shekarar Haihuwar Aminu Ladan Abubakar

An haifi Aminu Ladan Abubakar a ranar 11 ga watan Fabrairu, 1973 a Unguwar Yakasai, cikin birnin Kano, Jahar Kano.

4.6.4 Ilmin Aminu Ladan Abubakar

Aminu Ladan Abubakar ya yi karatun allo na Alƙur'ani mai tsarki, har ya sauƙe Alƙur'ani, ya kama karatun ilmin na sanin hukunce-hukuncen Musulunci. Aminu ya yi karatu a makarantar Malam Zahraddini a Unguwar Tudun Murtala, Kano da Makarantar Allo ta Malam Muhammadu Ɗan Sakkwato. Aminu Ladan kuma ya yi karatun wasu littattafan Musulunci a hannun Malam Umaru Ɗan Sakkwato ɗa a wurin Malam Tijjani Tudun Murtala ɗa a wajen Malam Usaini Ladan da kuma a wajen Malam Albani Zariya da sauransu. Aminu Ladan ya sami rabo mai yawa a cikin ilmin litttatafai na furu'a da hadisi da shari'a da kuma lugga da sauransu.

A ɓangaren karatun boko kuwa, Aminu Ladan ya yi karatun Firamare a Makarantar Firamare ta Tudun Murtala, Kano daga shekarar 1980 zuwa 1986. Ya halarci Makarantar Sakandire ta Dakata, Kano daga shekarar 1986 zuwa 1992.

Aminu ya faɗaɗa ilminsa na boko a Makarantar Kimiyya da Fasaha, Kano daga shekarar 2004 zuwa 2007 inda ya sami Diploma a fannin fasahar zane-zane. Haka kuma Aminu Ladan ya yi ta halartar kwasa-kwasai na ƙara gogewa da ƙwarewa da kuma sanin wasu sirrorin rayuwa.

4.6.5 Sana'a Wajen Aminu Ladan Abubakar

Aminu Ladan ya soma tanadin kansa tun a lokacin ƙuruciya, musamman mahaifinsa, Malam Muhammadu Sani Ladan, ya rasu tun Aminu yana cikin karatun makarantar Sakandare. Alan waƙa ya fara sana'ar ba wa magina ruwan aiki tamkar mai-ga-ruwa, sannan ya faɗa aka dinga aikin leberanci na gini tare mesin-mesin da shi. Tun kafin Aminu ya karanci fasahar zane, yake yin zane-zane ana fanshewa, yana samun abin masarufi da tanadin na kansa.

Bayan da Aminu ya tsunduma cikin fage na waƙa, sai ya zama yana naɗar waƙoƙinsa a cikin robar CD-CD da kuma album-album yana fansarwa masu buƙata, har sai da ya zama mashahurin dillali na ribobin waƙoƙin baka na zamani. Haka kuma Aminu ya buɗe sitidiyo na ɗora kiɗa a muryoyi waƙoƙin baka na zamani, sannan a naɗe su a robobin CD. Wanda wannan wuri ma wata hanya ce wadda Aminu Ladan yake samun kuɗaɗen shiga da yake jujjuyawa a hidimomi na rayuwarsa ta yau da kullum.

4.6.6 Rubutun Aminu Ladan Na Labarun Zube

Kafin Aminu Ladan ya fara waƙoƙi na sitidoyo sai da ya soma rubuta littattafai na ƙagaggun labaran soyayya, littafin da ya fara rubuta wa shi ne Jirgi Ɗaya wanda ya rubuta shi a shekarar 1992, amma sai a shekarar 1999 aka buga shi, ya watsu a hannun jama'a. Littattafan ƙagaggun labaran da Aminu Ladan ya rubuta sun haɗa da: Baƙar Aniya, a shekarar 2000, Cin Zarafi a shekarar 2001, Ƙawazuci da Tarzoma da Sawaba da Jirwaye dukansu a shekarar 2003 sai littafin Jagoraci a shekarar 2004.

4.6.7 Aminu Ladan a Ɓangaren Rubutun Waƙoƙi

Aminu Ladan ya rubuta waƙoƙi a rubuce tun a yayin karatunsa na Islamiyya, musamman a lokacin karatun dare. Kuma ya sha rera irin wannan waƙoƙi a lokutan maulidi waɗanda Malamansa na Islamiyya suke rubutawa, suna ba su, su haddace, sannan su rera a kan dandamali na karatun maulidin. Daga nan ne, Aminu Ladan ya fara rubuta nasa waƙoƙin daga kalmomin. Malam Abdullahi Sani Makarantar Lungu ya taimaka wa Alan waƙa a wajen tsarawa da rubuta waƙoƙin Islamiyya, kuma shi ne ya fara naɗar waƙoƙin rerawar Aminu Ala a rikoda ba tare da kiɗa ko ƴan amshi ba.

Har wa yau kuma Aminu Ladan Abubakar ya sha rubuta waƙoƙi yana karantawa a taruka daban-daban tun ma ba a taro na ƙungiyoyin marubuta ba, kamar ANA.

Aminu Ala yana rubuta waƙoƙin Hausa masu yawan gaske waɗanda wasu daga cikin su ya mayar da su ɓangare na waƙar baka. Alal misali, Aminu Ala ya rubuta waƙa 'Shahara' wadda ya fitar da littafinta a shekarar 2015, sannan kuma ya rera ta a doka ta waƙar baka.

4.6.8 Aminu Ladan a Kiɗa da Waƙa

Aminu Ladan Abubakar ya yi wa fagen waƙar baka haye, bai gaji rera waƙa ba. Jibiliyyar waƙa ne ta ba shi iko da saulin rera waƙar baka. Hikima da nutsuwarsa su ne suka sanya ya zama makiɗin baiwa ko ilhama. Aminu Ala kuma ya zaɓi ya yi waƙa ta hanyar kiɗa na sitidiyo.

4.6.9 Kayan Kiɗan Aminu Ala

Sitidiyo shi ne wuri wanda Aminu Ala yake shiga -/+ ƴan amshi ya buga waƙoƙi waɗanda ake juya su a CD a dinga sadarwa ga jama'a. A ɓangaren rera waƙoƙin Aminu Ala ya fi zaɓar a sa masa kiɗa a waƙa ta hanyar amon waɗannan kayan kiɗa na sitidiyo kamar su Fiyano da Kalangu da Algaita.

Wasu sitidiyo da Aminu Ala yake buga waƙoƙinsa sun haɗa da:

i. Lafazi sitidiyo -Makaɗi Rabi'u Dalle

ii. Castic Media -Makaɗi Ibrahim Cast

iii. Central Hostel sitidiyo -Makaɗi Apolo

iv. Dehood Sitidiyo -Makaɗi Ibrahim Deehod

v. Hikima Multimedia -Makaɗi Khalid Kaciya

vi. Taskar Ala Global -Makaɗi Mubarats da Sayyad Gadon Ƙaya

vii. Taskar Ala Kaduna -Makaɗi Habu Kaduna

viii. Bandirawo Sitidiyo -Makaɗi Ibrahim Jinsi

4.6.10 Fara Waƙar Baka da Bunƙasar Aminu Ala

Aminu Alan waƙa, mawaƙi ne wanda yake rubuta waƙoƙi, sannan ya ɗora musu kiɗa a sitidiyo, ya samar da rauji, a kuma naɗe su a cikin mazubi na robar CD-CD ko album-album.

Tsarin rera waƙoƙin Aminu Ala ya ƙunshi +/- ƙungiya + jagora (+Ƙulli)+/-Ƴan amshi (+/-Ƙari/+/- Rakiya+/Ciko(+G/waƙa).

Wasu waƙoƙin Aminu Ala na farko-farko sun haɗa da waƙar 'Bello Ɗandago Rediyon Kano' da waƙar 'Gagara Gasa' da waƙar 'FM, AM Rediyon Kano (2003)' da waƙar 'Baubawan Burmi (2004)' da waƙar Jami'a Gidan ban Kashi (2004)' da waƙar 'Ƙyalƙyali mai Haskawa (2004)' da sauransu.

Aminu Ala ya yi waƙoƙin sitidiyo waɗanda yake ta ɗorawa a mazuɓin album da suka ƙunshi album na 'Angara' da na Gwadabe da 'Bubuƙuwa' da na 'Fulfulɗe' da na Fuju'a da na 'Kamfa' da na 'Jakadiya' da na 'Zumunci' da na 'Dillaliya' da na 'Lafiya' da na 'Kamaye' da na 'Kawalwainiya' da na 'Duniya Makaranta' da na 'Hantsi' da na 'Zazzau Saraki' da na 'Basasa' da na 'Tauraruwa' da na 'A San Ka a So ka' da na 'Tsinkaya' da na Ta'aziyya' da na 'Raba Gardama' da na 'Shahara' da na 'Alfanda' da na 'Farfeshiya' da sauransu.

4.6.11 Iyali da Ƴaƴan Aminu Ala

Alhaji Aminu Ladan Abubakar yana da iyali da suka haɗa da matansa na aure tare da ƴaƴansa waɗanda ya haifa. Waɗanda jumulla suka kamata mata huɗu tare da ƴaƴa guda goma sha huɗu, daga cikinsu akwai

GUDUMMAWAR AMINU LADAN ABUBAKAR YAKE BAYAR A FAGEN WAƘA

Kusan za a iya cewa, a iskan nan mai kaɗawa, babu wani mawaƙi a yau da za a ce ya shahara, har ya ɗararwa Aminu Ala. Manazarta da maharhanta sun yi ayyuka masu kima da amfani akan waƙoƙin Aminu Ala. Daga cikinsu akwai, Bello (2009 da 2011) da Gusau 2010 da 2011) da Hamza (2011) da Zainab (2013) da Imran (2008). Kaɗan kenan daga cikin irin ayyukan da suka yi akan shi. Wani abin burgewa shi ne, irin yadda ake ta kai kawo da hidima akan waƙoƙinsa, kodaye, Hausawa na cewa "Banza ba ta kai wa zomo kasuwa". Yadda manazarta suka raja'a, suna ta aikace-aikace a kan waƙoƙinsa, wannan ya nuna irin ɗimbin fasaharsa da hikimarsa na shirya waƙa.

Ma’anar Kiɗa da Makaɗi

Da yake aikin ya shafi kiɗa ne, sai na ga ya kamata na bayyana ma’anar kiɗa da kuma makaɗi. Alhassan da wasu (1982:75) sun bayyana kiɗa da cewa “Shi ne buga abubuwan da aka yi musamman don bugawa da busa abubuwan da aka yi don busawa, shi ake kira kiɗa. Kayan kiɗa wato na bugawa da na busawa har ma da na girgizawa suna da yawa a Hausa sai dai a raba su aji-aji”. A wurin

Zarruƙ da wasu (1987:1) kiɗa na nufin “Wanzar da daddaɗan amo daga abubuwan bugawa ko na gogawa ko na busawa ko kuma na girgizawa.”

Shi kuwa Gusau (2014:7) ya bayyana makaɗi a ma'ana ta fannu da cewa "Makaɗi shi ne wanda yake gwama kiɗa da waƙa a lokaci ɗaya, kuma yake shirya kalmomi cikin jumloli ya fitar da matani na waƙa, ya rera shi, ya sadar da shi, sannan ya lizamci yin haka har ya zamani

Ma’anar Yabo

Masu iya magana na cewa" Yabo gonar makaɗi".Yabo na nufin ba da shaida mai kyau game da mutum bayan ya yi wani abin a yaba, na burgewa ko kuma ana so ya aikata abin na burgewa ko na a yaba. Misali:

Jagora: Ka ji waƙa tana fita,

Gurin ɗan Bafillatana,

Abu kamar harsashi,

In na yi hushi harsashin ɗin me?

In dai waƙa ce,

Allah ya yarda. (Gusau, 2009:350).

Anan, za mu fahimci yabo da cewa wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen bayyana zahirin yadda mutum yake, shin waɗannan kalmomin da aka ambata ƙarya ce ko kuma gaskiya ce. Domin akan yabi mutum ta hanyar faɗar abin da yake ba gaskiya ba ne, an dai yi ne kawai domin a faranta masa.

i. Waƙar So da Ƙauna ta Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo

Aminu Ladan Abubakar ya nuna a fili cewa dalilin wannan waƙar tasa, ba wani abu ba ne, ban da so da ƙauna. Wanda yake da tabbacin akwai ta a zukatan al'umma, kamar yadda take a zuciyarsa. Hakan na ɗaya daga cikin dalilin da ke sa mawaƙi, ya yi waƙa. A waƙar an yi amfani da hikima da aka yi karairaya yanayin furta kalma da kuma tsabar sanin ma'anar kalmar yayin furta ta. Domin kowace kalma an aje ta a inda ta dace da zauna a wurin. Babu shakka, Aminu Ala ya nuna gwaninta a wajen shirya wannan waƙa. Ya fara amshin waƙar Farfesa Ɗangambo da cewa:

Garkuwan adabin Hausa sannu Farfesa,

Sannu Ɗangambo na taho in gaishe ka,

Aminu Ala ya yi kyakkyawar basmalla, inda ya ce:

"Karsashi kake yi, ka sanyi Lillahi,

Ɗan mafarin komai fa Bismillahi,

In ka kai aya Alhamdulillahi,

Lamarinka ya yauƙaƙa kai yi albarka".

"Kan na ce uffan, bari in sako Mamman

Ɗaha jagora, gun mu ya zamo liman,

Rabbi ƙara amincinKa gun sa Jarman nan,

Makusanci da ka ƙira ƙaribunKa".

Bayan Aminu Ala ya yi kyakkyawar basmalla, sai ya tsunduma cikin waƙarsa, yana mai rattaɓo martabar da Allah ya yi wa Farfesa, ya ce:

"Za ni hau sarari na yabo da baituka,

In yabonta gwani, turmi masha duka,

Nemi Ɗangambo, ka ji rairayar waƙa,

Rariyar adabi ce, matankaɗar waƙa".

"Maliyar malala, dole sai fa an sha ka,

Ko cikin birni ko a sha a ƙauyuka,

Gani nan girshe, ginshiƙi fa zan waƙa,

Matsirar masana Hausa sai fa labbaika"

"Wani ka koyar da shi cikin aji naka,

Wani ya koya da ganin rubutunka,

Wani an koyar shi a ɗalibai naka,

Wani tsinta yai, a furogiram naka,

"Shi Sa'idu Gusau, na cikin muradinka,

Ni ko Alan waƙa silar rubutunka,

Rabbi na gode, da ya zam ina tsaka,

A zaman jerin ɗaliban da kan………"

Ƙarin bayani: Hausawa na cewa "Yabon gwani ya zama dole". Wannan waƙa ta tattara ne da duk wasu kalmomi na yabo ga shaihun malami, Aminu Ala ya bayyana matsayinsa, da duk ayyukan da yi a harshen Hausa da kuma irin gudummawar da ya bayar wajen ci gabansa.

ii. Yabo Daga Waƙar Aminu Alan Waƙa

Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya yi wa Farfesa Gusau waƙoƙin yabo da dama, amma a wannan takarda an ɗauki waƙa ɗaya mai taken ‘Ga ka Farfesa’ wadda a cikin ta aka zaƙulo yabon da ya yi masa. Ga wasu ɗiya da ya yi yabo a cikin su:

G/Waƙa: Ga ka Farfesa,

Ga ka Farfesa ga ka katibi kan adabi,

Sannu Farfesa Sa’idu ɗan Muhammadu na Gusau.

Jagora: Yau akala na karkata na tunkari Gusau,

Zan yabon masani mutafannunin nan na Gusau,

Wanda yai harsasai kala-kala yam maye sau,

A fagen ilimi yau da gobe ya zamma da sau.

Jagora: Adabin Hausa na yabon ka Farfesa Gusau,

Manazarta ma ka yi tubali sun ɗara sau,

Littafan tarke da dabarbarun Hausa ka sau,

Har da talifin tarke na siya da dama a Gusau.

Jagora: Alan waƙa ke yabon ka don ka ɗara sau,

A fagen waƙa kai rubutuka sun fice sau,

Haka labaran ƙage kai nazar sun fice sau,

Binciken Ala da yawan su taskarka Gusau.

Idan aka lura da waɗannan baituka da suka gabata, za a ga tsantsar yabo ta fuska guda, amma sai aka rarraba shi zuwa wasu rassa amma duk a ɓangaren ilimi. Makaɗin, ya yi ƙoƙarin yabon Farfesa ta fuskar yalwatar iliminsa, inda ya zamana ilimin ba a ɓangare guda ba, wato fanni ne da dama. A kalmar ‘Mutafannun’ wadda ya yi amfani da ita wajen nuna Farfesa Gusau yana da ilimi a ɓangarori biyu ko uku, wato Hausa da Turanci da kuma Larabci. Har wa yau, a wajen yin yabo ga yalwar ilimin nasa, sai ya yabi yadda ya kasance ya yi tarke a ayyukan marubuta littattafan Hausa na ƙagaggun labarai, haka zalika a fagen waƙa ma ya yi irin wannan tarke da rubuce-rubuce da dama.

iii. Waƙar Faɗakarwa

Faɗakarwa tana nufin ƙoƙarin sanar da mutane wasu abubuwa sababbi da suke aukuwa a rayuwar yau da gobe. Duk abin da doso ƙasa wanda jama'a ba su cikekken bayaninsa, sau da yawa, Aminu Ladan Abubakar yakan yi ƙoƙarin fahimtar da jama'a.

Saboda haka, faɗakarwa na daga cikin abubuwan da ake nazarta a cikin waƙoƙin situdiyo, sannan su kansu makaɗan sun shahara wajen aiwatar da waƙoƙin faɗakarwa. Ga wasu misalai nan daga wasu waƙoƙi:

Jagora: Duniya ba madauwamar ɗorewa ba,

: Ba bigire na miƙe sawaye ne ba,

: Mai barci ka wattsake tun ba ta zo ba,

: Mai raba gardama da yayyanke ƙauna.

(Waƙar Ɗamarar ko ta kwana, ɗa na 8, ta Makaɗi Alan Waƙa).

A wannan ɗiya, an ga yadda Makaɗin ya yi faɗakarwa kan mutuwa, inda yake nuni da cewa duniya fa ba gidan zama ba ne, za ta zo kowane irin lokaci ta yi gaba da mutum.

Jagora: Ya ƴanuwa ku tashi mu mata mu kama sanaa,

: Rayuwa in babu sana’a an yi zama na kare a Karofi,

: Rashin sana’a ni na hanga shi ne ke sa aikata laifi,

: ‘Ƴar uwa in ba ki sanaa za ki ɓige da aro na mayafi,

: Haka komai in ya tashi dangi kan ki sa riƙa haufi,

: In ko kina sana’a ba ki aro sai dai ranta.

(Waƙar Mata mu kama sanaa ta Makaɗiya Murja Baba).

A wannan ɗiya, Makaɗiyar ta yi wa mata faɗakarwa ne a kan su tashi su kama sana’a, inda har take ƙoƙarin nuna cewa idan fa mutum ya zama ba shi da wata sanaa to zai kasance cikin ayyukan laifuka, da roƙo.

iv. Waƙa a kan Magani

Magani shi ne dukkanin abin da za a sanya a jiki, ko wani abu da za a karanta, ko a sha, ko a fesa domin waraka daga wata cuta da ta kama ɗan’adam. Amma ga waƙa, maganin kan ɗauki ma’anar wasu ɗiya da za a saurara domin samu waraka ta zuciya ga wanda ya kamu da son jin wata waƙa ko kuma ya shiga wata damuwar da nishaɗin waƙa ce kaɗai zai samar masa da waraka da hucin zuci. Tun lokacin da aka fara shirya finafinai na Hausa, ake kuma tsarma waƙoƙi a ciki, an sami ire-iren waɗannan misalai da dama.

Aminuddeen Ladan Abubakar, ya bayyana haka cikin waƙarsa ta Shahara, inda ya kawo misalan wasu mata da waƙoƙinsa ne kaɗai ke raba su daga cutar da take damunsu. Mai wani ɗa da hakan ya zo a waƙar Shahara ta Makaɗi Aminu Alan Waƙa.

Har wa yau, a wani ɗa ya kawo yadda waƙoƙinsa suka zama sababin zamantakewar aure. Ga abin da ya ce:

Jagora: Ko da tan nutsu ko ta huta,

: Sai ta hau yi mana bayana.

: ‘Yar ɗiyata ce na wanke,

: Sanadin aure na sunna.

: Mun yi mun yi ta zauna,

: Sai ta ce sharaɗin ta zauna.

: Sai an kai matta kaset,

: Wanda nai Ummi Momina.

A nan, mun ga yadda wannan mata ta bayyana ɗiyarta ta kasa zaman aure sakamakon rashin samun waƙar Alan Waƙa, wannan kuwa cuta ce babba.

A wata ɗiya, Makaɗin ya bayyana yadda wata jikar Sarki ta kamu da sonsa, waraka daga wannan cutar shi ne sauraron murya ko waƙar Alan Waƙa. Ga abin da ya ce:

Jagora: Sai labarin Sa’ade,

: Shekarunta bakwai na rana.

: Wata Jikanya ta Sarki,

: Wayonta wuce sanina.

: In ana so tai karatu,

: Sai a sai mata faifayena.

: Waƙa ta hardace su,

: Bitar su dare da rana.

Da waɗannan ɗiyoyi za mu fahimci waƙa magani ce wadda ke kawo waraka daga cutar da ta addabi mutum.

SARAUTA A KASAR HAUSA

Alhassan da wasu, (1980:12) Ya ce Sarauta ita ce shugabantar jama'a don kiyaye addininsu da tafiyar da harkokin siyasarsu, da samun hanyoyin jin dadin rayuwa masu kyau da kyautata hanyoyin tattalin arzikinsu da duk wasu al’amura na yau da kullum, musamman da abin da dan'adam zai bukata na inganta rayuwarsa.

v. Waƙar Alhaji Ado Bayero Bakan Dabo San Kano Ɗan Baiwa

Y/A:Bakan Dabo san Kano dan baiwa,

:Dan Abdallah lafiya takawa.

Jagora:Dan Abdallah san Kano takawa,

:Abin bugun gaban Kano da Kanawa,

:Marmara kashin kasa dan baiwa

:Bango ne majingina gun bawa,

:Matokara ta masu san tasawa,

:Jeji ka fice gaban shingewa,

:Hadari sa gabanka ba a hanawa,

:Madubin sarakuna na arewa,

:Sha kallo da armashin dubawa,

:Mai kallonka ba shi nuna gazawa,

:Dan Bayero fahari ga Kanawa.

Y/A Bakan Dabo San Kano dan baiwa,

:Dan Abdallah lafiya Takawa.

(Aminu Ala, Ado Bayero).

Wasu daga cikin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar

i. Waƙar Yabo ta Farfesa Ɗangambo Abdulƙadir

ii. Waƙar Yabo ta Farfesa Sa'idu Gusau

iii. Waƙar Ta'aziyyar Sarkin Kano Ado Bayero

iv. Waƙar FM, AM Rediyo Kano

v. Waƙar Jamia Gidan ban Kashi

vi. Waƙar Shahara Sanadin Sanina

vii. Waƙar Isah Bello Ja

viii. Waƙar Uwar Iyaye A'isha

ix. Waƙar Sababin Mutuwar Auren Bahaushe

x. Waƙar Mu Nemi Ilmi Fitilar Haskawa

4.7 Mawaƙan Zamani Waɗanda Suke Haɗawa Da Kiɗa

A wannan zamani akwai wasu mawaƙa da ba na gargajiya ba kamar waɗanda muka sani, kuma ba a ƙiransu rubutattun waƙoƙi, saboda galibi kafin a ƙira waƙa rubutacciya sai ta kasance tana ɗauke da wasu sharuɗɗa na zama rubutacciya. Kafin a ƙira waƙa rubutacciya dole ne ya zan ba ta da kiɗa kamar yadda Gusau S.M ya faɗa a wani aiki nasa. Kuma ana ƙiran waƙa rubutacciya idan tana da tsarin aruli a tattare da ita, ko da kuma ba ta da to lallai ta kasance ba mai amshi ba ce, ba mai kiɗa ba, kuma ba wadda ake sakawa a yi ta rawa ba a dandali. Wannan nau’in waƙa ta zamani, ana shirya waƙa a kaita a ɗakin tace waƙa a saka a yi mata kwaskwarima da kiɗa dai-dai da yadda ake buƙata, sai a tace ta dai-dai da yadda ake buƙata a fitar a je a riƙa sakawa a inda ake buƙatarta. Marubuta waƙoƙin siyasa da na aure da na soyayya da sarauta a wannan lokaci su ne suka fi yin wannan.

Akwai nau’ain marubuta waƙoƙi irin waɗannan da suka haɗa da:

Aminu Ladan Abubakar, Auwalu Isah Bunguɗu, Kabir Yahaya Kilasik, Ibrahim Aminu Ɗandago, Abubakar Hikima, Sadi Sidi Shariffai, Adamu Nagudu, Adam A Zango, Nura M. Inuwa, Fati Nijar,Zuwaira Ismail, Dahiru S.K, Dauda kahutu Rarara, Misbahu M Ahamad, Abubakar Sani, Saddiƙ Zazzaɓi, Maryam Saleh Fantimoti, Ma'aruf Shatan Manzo, Murja A. Baba, Nazifi Asnanic, Rabi Mustapha Isah, Shehu Ali Ɗan Maraya Wudil, Bello Ibrahim Billy'O, Abubakar M. Sharif da dai sauransu.

Kayan kiɗan baka na zamani

Sarewa, Ganguna, Tashoshin Turawa, Tsintsiya, Jita, Fiyano da sauransu

Hanyoyin Shirya Waƙoƙin Baka na Hausa

Da akwai hanyoyi guda uku da mutum zai iya bi ta ɗayansu ya shirya waƙa, musamman ma ta baka, har kuma ya zama makaɗi, hanyoyin su ne:

i. Ta hanyar koyo: Masu iya magana na cewa "Da koyo akan iya". Mutum yakan koyi hikima da fasahar shirya kalmomin a matsayin waƙa daga wani mutum wanda ya iya waƙa. Ta wannan hanya mutum zai iya waƙa, ya zama makaɗi, ko mawaƙi.

Misali, makaɗin shiri kan fara ne ta haddace wasu waƙoƙin iyayen gidansu daga nan har su ƙware su dinga shirya nasu waƙoƙin. Idan mutum da tashi a gidan da ake yin kiɗa to babu shakka zai tashi ne da kwaikwayo na me gidansa musamman tsarin riƙon ganga da kiɗan sai ka ji mutane suna cewa "wane yana kama da wane har muryar ta hanyar bin makaɗi ko mawaƙi ta haka ne Hausawa suke cewa" zama da maɗaukin kanwa yakan kawo farin kai". Sau da yawa, makaɗan da suke tsayawa su shirya waƙoƙinsu sukan sami magada har a dinga ƙiran su makaɗan gado. A irin wannan yanayi makaɗi kan fara bin iyayensa, a dinga shiryawa da rera waƙa tare da shi tun yana yaro ƙarami.

Don haka, hanyar koyo ta ƙunshi bin wanda ya iya waƙa, a dinga yi masa hidima kamar ɗaukar kayan kiɗa da yin amshi da ƙida da sauransu. To, idan mutum ya bi makaɗi yakan kasance makaɗi, ya kuma gaje wanda yake yi wa biyayya, walau ɗa ne ko bara.

Makaɗi Musa Ɗanƙwairo yana ƙarfafa wa ƴaƴan jinin sarauta da su dinga yin biyayya domin sai da biyayya ake zama sarki. To, haka ita ma, waƙa take, idan an yi biyayya, a hankali za a zama makaɗi ko mawaƙi. Ga abin da yake cewa:

Jagora : Sai ku yi biyayya ƴan sarki,

Ƴ/Amshi : Da biyayya nan aka samu,

: Kowa naƙ ƙi biya yai ɓarna,

G/Waƙa : Ba takura kaurin gaba,

: Na yarda da Sarki Ado.

ii. Ta hanyar Ɗabi'a (Jibiliyya)

Wannan hanya ta ɗabi'a ita ce ta jibiliyya inda ake haihuwar mutum da wata fasaha ko hikima. Jibiliyyar waƙa wata irin baiwa ce wadda mutum yake tashi da ita inda zai zama mutum mai fasahar iya zance, mai azanci, mai kuma zalaƙa, ta haka ne kawai mutum ya ji yana yin waƙa. A irin wannan hanya mutum yakan zama makaɗi ba tare da ya yi biyayya ga makaɗi ba. Makaɗi da mawaƙa a irin wannan yanayin sukan yi waƙoƙin su ne a matsayin na ƙire wato ba sai an tsaya an tsara kalmomin da za a faɗa a waƙa ba.

Misali, Alhaji Mamman Shata da Aminu Ladan Abubakar suna daga cikin masu matsayin misali babba na wannan hanyar shirya waƙa ta ɗabi'a.

iii. Ta hanyar Lalura ko Buƙata

Tsananin buƙata da matsuwa sukan haddasa waƙa. Alal misali, idan aka wayi gari a gida babu abin da za a karya kumullo da shi, lalle za a shiga cikin damuwa da nuna buƙata. Akwai wani mutum da shi da matarsa waɗanda a sanadiyyar rashin abincin da za su ci su ƙagi wata ga sarkin garinsu. Ga yadda suka shirya waƙar:

Jagora: Sarki ɗan ɗanin-ɗanin, ɗan-ɗan-ɗan,

Sarki ɗan-ɗan-ɗan,

Matarsa: Sarki ɗan zaki,

Sarki ɗan zaki.

Daga wannan waƙa a san babu azanci a cikinta, amma kuma sun kawo wa sarki waƙar ne saboda suna kyautata zato yana da abincin da zai salle su, su sami abin tagaza wa rai.

Misali, Alhaji Sani Sabulu Kanoma da Aliyu Makaho da sauransu da yawa.

HALAYEN MAKAƊAN BAKA NA HAUSA.

Gusau da wasu (2006:116), sun bayyana hali da cewa ɗabi'a ce ta mutum tilo ko al'adarsa, idan an ce halaye ana nufin jam'in ɗabi'u ne ko al'adun da mutane suka aikatawa a rayuwarsu ta yau da kullum. Gusau (2010:13) ya ƙara da cewa halaye ɗabi'u ne waɗanda mutane suke yi a ɗaiɗaikunsu kuma aka fahimci kowane mutum da irin nasa na daban da na wani.

Waɗannan ma'anoni sun nuna cewa hali ɗabi'u ne na ɗaiɗaikun mutane da suke yi waɗanda suka sha bamban da al'adun al'ummar da fito. Misali a ce wane ya cika fushi kamar Soja, ko a ce wane yana da halaye irin na sarauta duk da ba ɗan sarauta ba ne.

1.0 Kyawawan Halayen makaɗa baka na gargajiya da zamani

1.1 Makaɗa mutane ne masu girmama jama'a: Makaɗa musamman na fada da na gama-gari bayan waƙoƙin da suke yi wa sarakuna da sauran rukunan al'umma, suna girmama su ne ta hanyar ladabi da biyayya da ɗa'a kamar yadda sauran fadawa daban-daban musu riƙe da muƙaman sarauta da kuma al'umma masu riƙe matsayi na kasuwanci ko gwamnati ko kasuwanci ta yadda suke yi musu hidima don waƙa tare da ba su kyauta ta musamman. Sai dai su makaɗan sarauta bakasafai su ke zaman fadanci ba inda wasu makaɗan ma sun yi nuni da haka a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsu. Misali ga wani ɗa da Abdu Inka Bakura yace"

Ni dai kiɗi nikai,

Ban tsare sarki mu yi fadanci,

Kai ni dai kiɗi nikai,

Ban tsare sarki mu yi fadanci.

Makaɗa yawancinsu suna da kyawawan ɗabi'un ladabi da biyayya musamman ga makaɗan fada turkakku da sakakku duba da ɗawainiyar da sarakuna su ke ɗauke musu na rayuwa wanda su ke zama tamkar iyayen gidansu wanda lalurar ci da shan su da kyautar muhalli da gonakin da za su je su dinga noma wa duk shekara idan suna da buƙatar hakan ta taso sannan sarakunan suna ba su suturu na alfarma da su da iyalensu tare da kuɗin kashewa. Makaɗa sukan faɗa wa sarakuna mafi yawan buƙatunsu don su taimaka musu ta ganin su warware abubuwan da suka sanya a gaba. A wasu lokutan kuma sarakuna sukan amince wa makaɗansu fiye da sauran fadawansu saboda za su dinga zama tare da su wajen yin hirarraki da zantuka da batutuwa ko yin taɗi har ma da labaran ban dariya na nishaɗi, sarakunan dai sukan sakar wa makaɗansu fuska ainun su zauna cikin aminci na zuciya ɗaya da kuma taimakon juna. Za a iya kafa hujja da abin da makaɗi Ibrahim Gurso ya faɗa a waƙarsa mai gindi ta Gagarau Ɗan Shehu" ta Sarkin musulmi Abubakar a lokacin yana sardaunan mafara a 1938. Yace"

Iro ni na dace,

In sarki yas so ka,

Ka hi gonat taki,

Ka hi hwataucin Gwanja,

Tun da Allah yab ba ka,

Ƙara godiya mukai.

1.2 Mutane ne masu ƙasƙantar da kawunansu: Makaɗa sukan ƙasƙantar da kansu a wajen sarakuna tare da sauran rukunan jama'a waɗanda suke yi wa kiɗa da waƙa a duk lokacin da ya dace a yi musu. Da wahala a samu makaɗa musamman na fada suna guntsarewa sarakuna da butulce musu, ballantana har su yi musu gardama. Makaɗan za suna yawan bin umarni da dokokin sarakunan iyayen gidansu za su ɗora musu yadda ya kamata su bi, kusan sai abubuwan da sarakuna suka ce za su aikata ko su gudanar. Don haka makaɗa suna da wasu ɗabi'u kyawawa na ƙasƙantar da kai ga waɗanda suke yi wa kaɗe-kaɗe ta hanyar bin su sawu da ƙafa tamkar iyaye da ƴaƴa.

1.3 Mutane ne masu faɗar gaskiya

Gaskiya wata ɗabi'a ce mai wuyar yi don ba duka makaɗa ko al'umma za a same su da aikata gaskiya ba, gaskiya tana da wahalar faɗa musamman idan ta faɗo tsakanin iyayen gidan da ake jin kunya ko nauyin su, amma duk da haka ita ce ke nuna cewar mutanen ƙwarai ne waɗanda ba za a yi shakkar yin wasu hulɗoɗi da su ba.

Makaɗan baka su kan faɗi gaskiya a wuraren da suka dace a cikin zamantakewar al'umma kama tun daga kan rayuwar neman aure ga samari da ƴan mata har a kai an yi auren a tsakani inda makaɗa da mawaƙan suke nusar da ma'aurata akan su gina hulɗoɗinsu na auratayya akan gaskiya domin inganta goben su ta yadda hakan zai samar da kawar da damuwa ko abubuwan kaiwa da komowa. Nuna gaskiya zai tabbatar da girmama juna da sauran surukai, amma akasin hakan za a iya samun tangarɗa ko rabuwar kai ko kuma sanadiyar abubuwan da za su janyo mace-macen auratayya a tsakani. Haka zalika a hulɗoɗi na cinikayya da shari'a da ayyukan gwamnati tare da fannoni daban-daban, a wannan fagen ma makaɗa sukan ba da gudummawa ta hanyar waƙe-waƙe wanda idan sun ɗauki saƙwannin da aka isar musu da zasu samu ci gaba a cikin neman su na yau da kullum ko ta wajen samun abokan ciniki to ta irin alherin da za a samu ta wajen riba. Mawaƙa sukan ƙulla batutuwa cikin waƙensu akan ha'inci ko algusu ga ƴan kasuwa ko rasuwar ƙarya ko yaudara ko rashin cika alƙawari ko ɓoya kaya ko samun mummunar riba da sauransu.

Su kuma fannin shari'a da ayyukan gwamnati suna matuƙar buƙatar gaskiya kamar yadda miya take buƙatar gishiri don kuwa suna buƙatar gaskiya fiye da komai waɗanda su ne matakan samun nasara da ci gaban ma'aikatu daga ƙarshe musamman a sha'anin shari'a akan samu mutane guda biyu wanda akan nemi mai gaskiya a cikinsu idan kuma ba a samu ba, ta kan kai har ga yin rantsuwa domin a tantance mai gaskiya a nan sannan kuma a hukunta maras gaskiya. Ita gaskiya kan jawo wa mutane abubuwa kamar haka; mutunci da girma da kyauta da amincewa.

Makaɗi Kassu Zurmi ya yi wa gaskiya take da cewa, “Gaskiya mugunyar magana, ba a sonki sai kin tsufa”. Abin da wannan makaɗi ke nufi bai wuce zancen nan na masu hikima ba da suke cewa, “Gaskiya ɗaci gareta”. Wato ita gaskiya ba ta da daɗi a lokacin da aka ji ta sai bayan an aikata ta sai a ji daɗi. Mustapha, (2003:56-7) ya zayyano ma’anar gaskiya daga bakin masana kamar haka:

Yin abin da ya kamata ba tare da ƙari ko ragi ba, (Gusau 1984). Gaskiya ita ce, aikata wani aiki ko furta wata magana da al’umma suka aminta da kasancewarsa gaskiya.

Haka kuma, wannan aiki ko maganar ya kasance abu ne tabbatacce ga idon Bahaushe a ma’aunin al’adarsa, kuma ya zamo abu ne mai ɗorewa ba mai gushewa ba, domin a daɗe ana yi sai gaskiya, (Bunza 2002).

Gaskiya ita ce faɗin daidai a cikin tunanin ɗan Adam da aikata daidai a cikin harkokinsa, tare da neman gano ko rarrabe abin da ke tsakanin tunanin ɗan Adam da dabba, ko a da lokacin zaman gargajiya, ko a yanzu da addinin Musulunci tare da sauyawar zamani ta zo, (Mu’azu (…..)). Bisa lura da abin da masana suka ambata dangane da gaskiya, za a iya cewa; Gaskiya shi ne faɗin abu yadda yake, ko ba da labari bisa tabbaci da haƙiƙa ba tare da shakka ko kokwanto ba. Yin gaskiya ta kowace hanya abu ne mai kyau da amfani ga mutane a tsarin zamantakewa.

Dangane da haka ne Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya duƙufa wajen ganin ya ɗora

al’umma a kan turbar gaskiya, da faɗinta da kuma aikata ta komai ɗaci da wahalarta a

tsarin rayuwa. Ga misalai a cikin wasu waƙoƙinsa kamar haka:

‘Yan kasuwa a yi ƙoƙari,

A yi gaskiya a yi hanƙuri,

Kwana da wayunwan gari,

Wataran buƙata zai biya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Jama’a a bar yin maguɗi,

A yi gaskiya a yi tarbiya.

Ku ɗalibai in gaya muku,

Ko ko in ƙara tuna muku,

Komai izan ya matsa muku,

Ku faɗi ta hanyar gaskiya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya III)

9. Gyara kayanka domin sanin haƙƙi,

Mai riƙon gaskiya bai shiga kunya.

(Ɗahiru Jahun:Gyara Kayanka Bakandamiya)

Misalan da wannan marubuci ya kawo na koyar da tsayawa tsayin daka ne a kan gaskiya. Wato duk abin da mutum zai yi, to ya yi ƙoƙarin ganin ya yi gaskiya ya kiyayi maguɗi da mugunta a cikinsa domin, mai gaskiya bai shan kunya. Haka kuma duk abin da mutum zai faɗa, to ya yi ƙoƙari a ji gaskiya ce ta fito daga bakinsa.

1.4 Mutane ne masu riƙon amana

Ita dai kalmar amana asalinta daga harshen Larabci take. Hausawa suka aro ta suna amfani da ita kamar yadda take a cikin harshen Larabci. Kalmar tana nufin aminci, wato yarda. Yarda kuwa na iya kasancewa a kan kowace irin hulɗa da ake iya samu a tsakanin mutune. Wannan shi ya sa mutumin da ba ya da riƙon amana wato ba yardadde ba, yake kasancewa abin ƙyama a cikin al’umma.

Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar amana a Hausa, daga cikin waɗannan masana akwai Bargery (1934:27), wanda ya bayyana ma’anar amana a matsayin kyakkyawar fahimta ko yarjewa mutum a kan wani abu. Haka kuma, ya ƙara da cewa amana na iya ɗaukar ma’anar dogara da ban gaskiya a kan abu.

Newman, (1997:289) an bayar da ma’anar amana da amincewa da yarda da mutum. A cikin Ƙamusun Hausa (2006:15) an bayyana amana da ba mutum ajiyar kaya ko wani abu yadda zai adana shi kamar nasa ba tare da wani abu ya salwanta ko wani abu ya same shi ba. A Hausance, Amana na nufin mutum ya kula da wani abu da aka damƙa masa kada ya bari ya lalace ko ya salwanta, (Ibrahim, 2013:186). Idan ya kasance mutum mai amana ne to al’amuransa sukan yi kyau. Idan aka ci amana kuma a sami akasi.

Buƙatuwar gina alumma bisa tarbiyyar riƙon amana tasa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun a cikin waƙoƙinsa ke cewa;

Kuma sai mu gaida ma’aikata,

Wasu na shiga wasu na fita,

Dukkanku ƙwan ku da kwarkwata,

Ku riƙe amanan gaskiya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

58. Gyara kayanka duk wanda ke aiki,

An fi son mai amana da tarbiyya.

(Ɗahiru Jahun: Gyara Kayanka Bakandamiya)

Waɗannan baitoci na Alhaji Ɗahiru na nuna cewa a cikin al’umma ba wanda aka fi so kamar mai riƙon amana, mai gaskiya. Don haka ya ke kiran mutane a kan riƙon amana cikin dukkan ayyukansu da suka sa gaba.

1.5 Mutane ne masu kunya da kawaici

Kunya kamar yadda Yahya da wasu (1992:82) suka bayyana “ta ƙunshi hana harshe yin munanan maganganu da ƙiya wa gaɓɓan jikin mutum aikata miyagun ayyuka. A wata ma’anar kuma, Balbasatu (2009:62) cewa ta yi, “Kunya na nufin jin nauyi da girmamawa ko karamcin da ake yi wa wani na gaba da mutum ko masoyi ko ƴaƴa ko surukai ko baƙo. Kunya na nufin halin ɗa’a da kawaici ko a aikace ko a magance. Kunya ɗabi’a ce kyakkyawa da kan jawo wa mai ita daraja da girmamawa a cikin mutane, (Garba 2010:20).

Kunya tana matuƙar taka rawa wajen nuna zurfin kamala da halayen ƙwarai na mutum domin, siffa ce daga cikin siffofin da ake gane mutum mai tarbiyya. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun a ƙoƙarinsa na tarbiyyantar da al’umma yin kunya, ya kawo baitoci masu nuni da kyawun kunya ga mutum a cikin waƙoƙinsa kamar haka:

Suturar jikinki ta yalwata,

Surar jikinmu ya ɗan ɓata,

Da wuya ace an kunyata,

In an bi hanyar gaskiya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Tsiraici abu ne da ake buƙatar ɓoyewa. Duk mutum mai hankali da kunya ba zai so ya bayyanar da tsiraicinsa ba. Illar bayyanar da tsiraici ga mata ne baitukan Sha’irin ke ƙoƙarin nunawa da cewa, duk mace mai kunya ba za ta bar jikinta a buɗe ba kamar moɗar randar bakin kasuwa. A cikin wani baitin kuwa cewa yake:

49. Ƴan acaɓa ku inganta halinku,

Mai biɗar arziƙi bai rashin kunya.

51. Don waɗansunku kan sa a zarge ku,

Ga rashin hankali ga rashin kunya.

53. Masu tuƙi na mota waɗansun su,

Kan gwada ba mutunci bare kunya.

85. Gyara kaya tuni ne ga matanmu,

Kar a faɗa tafarkin rashin kunya.

(Ɗahiru Jahun: Gyara kayanka: Bakandamiya)

Wato muddin ana son inganta sana’a dole sai an haɗa da kunya domin, rashin kunya na jawo zargi da tsana a wajen jama’a. Har ila yau marubucin ya sake bayyana yadda ake son mutum ya kasance mai kunya a cikin sana’arsa a cikin baitin da ya ke cewa:

Amma gyaran da za ku soma,

Farko ku rage yawan zalama,

Ko buɗe ido da nuna tsama,

Tsiwa da tsuma da nuna tsama,

Da tsageranci cikin mutane.

(Ɗahiru Jahun: Sanaar Acaɓa).

1.6 Mutane ne masu haƙuri

Hausawa na cewa “mai haƙuri yakan dafa dutse har ya sha romonsa”. Haƙuri kamar yadda Adamawa (2007) ya bayyana, shi ne juriya ko shanye wani abu na ɓacin rai ko na rashin daɗi, wato haƙuri da ƙin maida martani don haifar da maslaha. Haƙuri yana yalwata zuciya da janyo soyayyar mutane, kuma yana hana yin nadama. Shi yasa ma Hausawa suka ce “Haƙuri maganin zaman duniya” domin, duk wanda ya laƙanci yin haƙuri to ya sami kyakkyawar shaida a rayuwa. Masu haƙuri su ke tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a gida da gari da kuma al’umma baki ɗaya.

Tarbiyya tana ingantuwa ne da haƙuri, wanda hakan yasa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya ke gwaɓar jama’a don tarbiyyantar da su haƙuri a cikin waƙoƙinsa kamar haka:

To dole sai mu yi yunƙuri,

Mu yi dauriya mu yi ƙoƙari,

Haɗa kanmu ƙauye ko gari,

Da nufin a maido tarbiyya.

To ƴan uwa mu yi ƙoƙari,

Mu yi dauriya mu yi hanƙuri,

A ƙasarmu daji ko gari,

Kowa ya yarda da tarbiyya.

To ƴan uwa mu yi ƙoƙari,

Mu yi dauriya mu yi hanƙuri,

Mu yi maganin mutakabiri,

Daga nesa ba shi da tarbiyya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Haƙuri a kan dukkan wani abu da mutum yasa gaba na rayuwa shi Sha’irin ke ƙoƙarin nunawa a cikin waɗannan baitoci. Sha’irin na nuna komai mutum zai yi to dole sai ya yi haƙuri a cikinsa matuƙar yana son cimma muradi. Haka kuma ya nuna ba a samun nasara a zamantakewa sai da haƙuri.

1.7 Mutane ne Masu Wadatar Zuci

Wadatar zuci shi ne akasin kwaɗayi, rashin ƙwallafa rai kan samu ko mallakar abin da wani ya mallaka na rayuwar duniya. Wato gamsuwa da abin da ka mallaka komai ƙarancinsa, da rashin damuwa da abin da wasu suka mallaka komai yawansa shi ne wadatar zuci. Wadatar zuci wani muhimmin maƙami ne na kyautata tarbiyyar al’umma. A duk lokacin da mutane suka kasance masu wadatar zuci, to sai kishin kai ya shige su, su zama ba su hassadar abin da ke hannun wani. Dukkan mutumin da Allah ya ba wadatar zuci, ya yi dace domin zai zama mai nutsuwa da kwanciyar rai a koyaushe. Haka a duk lokacin da wadatar zuci ya bazu a zukatan jama’a, to lumana da zaman lafiya za su samu a tsakaninsu. Haka lalaci irin na sace-sace da ƙyashi da jiye wa juna za su ragu sosai in har ma ba su gushe ba gaba ɗaya. (Bunza, 2012).

A koyaushe a cikin al’umma a kan samu wasu jama’a da ke yin iya ƙoƙarinsu domin faɗakar da mutane su zama masu wadatar zuci dangane da abin da Allah ya hore musu domin kauce wa faɗawa a wata muguwar hanyar da za ta ɓata tarbiyyarsu, ta fitar da su daga gurbin mutane na gari. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya ƙoƙarta wajen tarbiyyantar da al’umma wadatar zuci a cikin waƙoƙinsa, kamar yadda ya ke cewa:

Najeriyanmu ƙasa ɗaya,

Kuma ga mu al’umma ɗaya,

Jama’a a bar son zuciya,

Ɗa’a ta samu da tarbiyya.

Jama’a a nai mana gargaɗi,

Mu rage azabar son kuɗi,

Wasu na ta haddasa maguɗi,

Sunansu ba su da tarbiya.

Ku saya ku saida halaliya,

Riba kaɗan mu yi godiya,

Duka sun ƙi gwamma haramiya,

Ba sa da ɗa’a tarbiya.

Ba wai ka mallaki naka ba,

Ka fito ka handami namu ba,

Baka san kana kashe kan ka ba,

Don son gwanintan duniya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Son zuciya kan haifar da maguɗi da hassada da handama da son duniya. Duba ga wannan da hanin jama’a kan yin su shi ne sha’irin ya ke kiran jama’a a kansu cikin baitukan da suka gabata. A cikin wata waƙar kuwa ga abin da yake cewa dangane da tallar da iyaye ke ɗorawa yara domin neman abin duniya:

Wasu gun talla ɗa’a takan rushe,

Har su koyo ɗabi’un rashin kunya.

(Ɗahiru Jahun: Gyara kayanka Bakandamiya)

Rashin haƙurin wasu iyaye kan jefa yara cikin miyagun ɗabi’un da ƙarshe za a zo ana da-na-sani wanda da sun sami wadatar zuciya da hakan bai faru da ƴaƴansu ba kamar yadda baitocin waƙar ke nuni. Har wayau marubucin ya sake cewa:

7. shirin gyara kayanka ne ke faɗi,

Musamman a azure na yin gargaɗi,

A taso a barci a bar gyangyaɗi,

A yaƙi dukkan ayyukan maguɗi,

Na masu zalama da yunwar kuɗi,

Misali ta manya da ‘yan burbuɗi,

Na sa yara talla farautar kuɗi,

Ka gansu a lungu cikin turbuɗi,

Da ɗai ba karatu bare tarbiyya.

(Ɗahiru Jahun: Ceton yar talla)

Idan aka dubi waɗannan misalai za a ga cewa babban saƙon da waqar take ƙarfafawa shi ne, mutum ya zama mai wadatar zuci watau ƙana’a. Haƙuri da kaɗan shi ne babbar nasara da nuna godiyar Allah, in kuwa aka ce sai an samu mai yawa to take-yanke za a faɗa cikin haramiya da kuma ɓarnar da ba ta da makari.

1.8 Mutane ne masu zumunci da tafiye-tafiye

Ƙoƙarin kusantar yan uwa da abokan arziƙi, da ziyartarsu a kai a kai, da riƙe dangi ba tare da zaɓunta ko son kai ba, wannan ita ce zumunta. (Zarruƙ da wasu, 1988). Halayen makaɗan baka na ƙasar Hausa tana jaddada ziyarce-ziyarce tsakanin ƴan uwa da abokan arziƙi. Har ma Hausawa suna cewa “Zumunta a ƙafa take. A cikin kowace irin al’umma ana alfahari da mutum mai sa da zumunci. Wannan tasa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun domin ƙarfafar zumunta a waƙarsa ta Tarbiyya II ya ke cewa:

Son ƴan uwa shi ne gaba,

Ka so shi ba zai ƙi ka ba,

Ba ka nuna ka so kanka ba,

Zai sa a zauna lafiya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Wato dai abin da sha’irin yake nuna wa mutane a wannan baiti shi ne, su yi ƙoƙari su riƙe ƴan uwansu domin, shi ne gaba ga komai da ke wanzar da zaman lafiya da son juna. Ya kamata a san shi tare da mutane, ba a ga yana janye jiki yana zama shi kaɗai ba. Da zarar aka samu jituwa a cikin al’amari, to za a tarar da komai na tafiya salin-alin ba kace- nace a cikin al’umma. Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun suna tarbiyyantar da jama’a muhimmancin haɗin kai, kamar yadda wasu misali za su nuna, in da marubucin ke cewa:

Ya ƴan ƙasan nan ƴan uwa,

Mu haɗe mu yarda da ƴan uwa,

Mu zama muna son ƴan uwa,

Mu haɗe mu gyara Najeriya.

Zancen ƙabilanci kuwa,

Mai yinta zai shiga damuwa,

Shi zai ci kansa ya sha ruwa,

Mun gane ba shi da tarbiyya.

Kai mai ƙabilanci bari,

Ko nuna bambancin gari,

Mu dai muna maka shawari,

Ka zama mutum mai tarbiyya.

Muddin ba mu haɗa kanmu ba,

Ba za mu kai burinmu ba,

Ra’ayinmu in ya rarraba,

Zai rarraba mana tarbiyya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Ta lura da lafazin wannan sha’ira, za a ga cewa ba ƙaramin faida ke akwai ba na haɗin kai. Don kuwa zaman lafiya ba zai taɓa wanzuwa ba idan har akwai rashin jituwa tsakanin al’ummar da ke rayuwa a wuri ɗaya, kuma ita kanta ƙasa ba yadda za ayi ta ci gaba, ballantana har jama’ar ƙasar su more amfaninta matuqar babu haɗin kai da zaman lafiya tsakaninsu.

Makaɗan baka suna da yawan tafiye-tafiye duk ta dalilin sadar da waƙoƙi ga jama'a. Misali:

Jagora: Na je ƙasar Kamaru yawo, mutanen Kamaru sun tambaye ni,

: Labarin mu na Nijeriya cikin gwamnonin da an ka yi,

: Ba yi Shehu Kangiwa na ce musu gwamnan Sakkwato sun ji daɗi sun yi murna.

: Na je ƙasar Ghana yawona, mutanen Ghana sun tambaye ni,

: Labarin mu na Nijeriya cikin gwamnonin da an ka yi ba,

: Ba ai yi Shehu Kangiwa, nace musu gwamnan Sakkwato sun ji daɗi su yi murna,

: Kai Alhaji Shehu Kangiwa farin jini wurin jama'a,

: Farin jini a wurin Allah,

: Nijeriyan ga an sonka,

Ƴ/Amshi: Har ma ƙasashen waje an son ka.

(Ɗanƙwairo waƙar Gwamnan Sakkwato: Shehu Kangiwa)

Bayan ga waɗannan ɗiyoyin waƙar ta Alh. Musa Ɗanƙwairo ya zagaya wurare daban a ƙasar Nijeriya kamar su Zariya, Kano, Bidda, Gusau, Talata Mafara, Maru, Argungun, Yawuri, Damagaran, Daura, Yamai, Ilorin, Kaduna, Kantagora da sauran garuruwa manya da ƙanana da ke cikin Nijeriya.

Alhaji Mamman Shata na cewa"

Farau-farau farar tabarma,

Baƙin cikin mai baƙunta.

1.9. Mutane ne Masu Kare Mutuncin Kansu

‘Tsira da mutunci ya fi tsira da kaya’ inji masu hikimar zance. Sanin darajar kai da tsare kai da kuma tsare mutuncin sauran mutane yana daga cikin mutunci, musamman idan aka darajantasu saboda shekarunsu ko ilminsu ko kuma saboda kasancewar su mutane na ƙwarai. Mutunci shi ne mutum ya ji kunyar aikata duk wani abin da zai zubar masa da darajarsa. Mutunci shi ne mutum ya saba wa kansa da kiyaye halaye mafiya kyau da cika. Wato kada ka aikata wulaƙantaccen abu. Kada ka nuna halin ƙasƙanci wanda zai rage darajarka ka zama ba ka da girma wurin ƴan uwa (Abubakar 1966:21).

Mutunci abu ne mai kyau da kusan kowane mutum yake maraba da shi domin, yana taimaka wa zaman lafiya ya tabbata, tare da ɗaukaka darajar al’umma kamar yadda tufafi kan suturta mutum, abinci kan kyautata lafiyar jiki a sami kuzari. Mutunci yakan ƙarfafi darajar mutum da kuma al’umma baki ɗaya. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun yana faɗakar da al’umma dangane da kare mutuncin kai da sanin daraja da ƙima a cikin waƙoƙinsa.

Misali

Dama mutunci ne mutun,

In ba mutunci ba mutun,

Mai hankali ka riƙe batun,

Ladabi da ɗa’a tarbiyya.

Bari nuna kai ɗan wane ne,

Ko don ace kai wane ne,

Kowannenmu ai ɗan wane ne,

Don kar ka ja mana tankiya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Har wayau, a wani wuri Marubucin a cikin

waƙar Gyara Kayanka yana cewa;

12. Gyara kayanka domin gudun sharri,

Duniya lahira kar a sha kunya.

22. Gyara kayanka kan malam ilmu,

Kar a koya wa yara rashin kunya.

23. lakcaran Jami’a ko mu ce tica,

Mun yi fatan a inganta tarbiyya.

24. Don sifofi ɗabi’un waɗansun ku,

Kan gwada ba su daidai da tarbiyya.

25. Tun da yara sukan ɗau sifar malam,

Bar fitowa da siffar rashin kunya.

(Ɗahiru Jahun: Gyara kayanka Bakandamiya)

Da jin waɗannan kalamai na cikin baitocin wannan waƙa za a fahimci cewa kashedi ne ake yi wa mutum ko hannunka mai sanda game da irin yadda ake so duk abin da zai yi, to ya yi ƙoƙarin kare mutuncinsa. Kar ya aikata abin da za a zarge shi domin, mutunci Hausawa sun ce “madara ne”. an kuwa yi amanna cewa madara idan ta zube ƙasa to ba kasuwa take yi ba.

1.10 Mutane ne Masu Haɗin Kai da Son Zaman Tare

Hausawa sukan ce, “Mutum na mutane ne”. wato mutum in dai mai lafiya ne, to ya kamata a san shi tare da mutane, ba a ga yana janye jiki yana zama shi kaɗai ba. Da zarar aka samu jituwa a cikin al’amari, to za a tarar da komai na tafiya salin-alin ba kace- nace a cikin al’umma. Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun suna tarbiyyantar da jama’a muhimmancin haɗin kai, kamar yadda wasu misali za su nuna, in da marubucin ke cewa:

Ya ‘yan ƙasan nan ƴan uwa,

Mu haɗe mu yarda da ƴan uwa,

Mu zama muna son ƴan uwa,

Mu haɗe mu gyara Najeriya.

Zancen ƙabilanci kuwa,

Mai yinta zai shiga damuwa,

Shi zai ci kansa ya sha ruwa,

Mun gane ba shi da tarbiya.

Kai mai ƙabilanci bari,

Ko nuna bambancin gari,

Mu dai muna maka shawari,

Ka zama mutum mai tarbiyya.

Muddin ba mu haɗa kanmu ba,

Ba za mu kai burinmu ba,

Ra’ayinmu in ya rarraba,

Zai rarraba mana tarbiyya.

(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)

Ta lura da lafazin wannan sha’ira, za a ga cewa ba ƙaramin faida ke akwai ba na haɗin kai. Don kuwa zaman lafiya ba zai taɓa wanzuwa ba idan har akwai rashin jituwa tsakanin al’ummar da ke rayuwa a wuri ɗaya, kuma ita kanta ƙasa ba yadda za ayi ta ci gaba, ballantana har jama’ar qasar su more amfaninta matuƙar babu haɗin kai da zaman lafiya tsakaninsu. Makaɗa da mawaƙan baka mutane ne masu haɗin kai da son junansu wanda a waɗansu lokutan ma suke yi wa junan su ko ambatar junan su a cikin waƙa. Misali:

Waƙar Son Juna

Jagora: Ja bari kora ganga ji biri kora X2

Wannan kiɗan, kiɗa ne,

Wannan kiɗan Shata ne,

Uban mawaƙa,

Mai tumbura na Balkin Sambo

(Waƙar Sani Sabulu Kanoma ta Dr. Mamman Shata)

Haka ma makaɗi Musa Ɗanƙwairo ya yi wata inda yace"

Jagora: Mijin Asabe ya wuce raini,

Na Garba waƙa rena ma,

(Waƙar Musa Ɗanƙwairo ta Alh. Dr. Mamman Shata)

1.11 Mutane ne Masu Son Tsafta

Cikakkiyar kula ga jiki, da tufafi, da wurin zama, da duk wani abin mu’amala mai alaƙa da mutum, ta hanyar gyara shi, da inganta shi da tsaftace shi zuwa ga mafi dacewar kama ko yanayin da ya fi ƙayatarwa da jan hankali, shi ne tsafta. Ban da kasancewar tsafta cikon addini, takan jawo farin jini da ƙauna ga jamaa. Mutane kan yi na’am da maraba da mai tsafta, sannan takan sa masa farin jini da duk wani abu da ya dangance shi. Hakan yasa masana da manazarta suka duƙufa wajen tsawatarwa game da tarbiyyar tsafta. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun na sahun gaba wajen ba da gudummuwarsa ta fuskar waƙa don kula da tsafta, kamar yadda misalan wasu daga cikin baitocin waƙoƙinsa ke nunawa kamar haka:

73. Tsaftace zuciya tsaftace aiki,

Gyara kayanka inganta tarbiyya.

75. Gyara kayanka tsafta cikin Ofis,

Har gidaje da gona da kan hanya.

(Ɗahiru Jahun: Gyara kayanka Bakandamiya)

Da farko ya nusar da mutane ne dangane da tsaftace niyya a cikin kowane irin aiki da mutum zai yi. Ma-da-mar ba a samu kyakkyawar niyya a cikin kowane irin aiki ba, to lallai za a iya fuskantar gajiyawa. Sannan kuma sai kiyaye ko kula da tsaftar jiki, da abinci da muhalli.

6. Ƴan karkara ƙauye ko birane,

Samun rashin tsafta kuskure ne,

To gyara kayanka kar ka manta.

10. To gyara kayanka sai a lura,

Tsaftar jiki ɗaki ko ta shara,

Sai masu Imani ke kula ta.

12. To gyara kayanka don kulawa,

Kan wanda ke tsafta sai daɗawa,

Domin rashin tsafta ba a son ta.

13. Tsaftar jiki ita kam zahirun ne,

Farkon shirin tsafta ya mutane,

Kowa ya ɗau tsafta can zukata.

39. Kowa da sunansa ya mutane,

To ko cikin ƙauye ko birane,

Sunan marar tsafta mai ƙazanta.

(Ɗahiru Jahun: Tsaftar Muhalli da Kewaye)

Wannan sha’iri ya taɓo wasu muhimman sassa da tsaftar ɗan Adam ya kamata ta taka rawa a cikinsu, wanda ya haɗa da jiki, da muhalli ko mazauni. Abin da sha’irin ke ƙoƙarin nunawa shi ne, matuƙar ana son lafiya ta wanzu a cikin al’umma a daina cututtuka, to wajibi ne sai an kula da tsaftar jiki da kuma ta muhalli domin, tsafta ita ke samar da lafiya a jikin mutane.

Makaɗan baka musamman na sarauta mutane masu matuƙar tsafta da kula jikinsu domin a wasu lokutan idan aka gan su sai a yi tunanin wasu mutane ne masu riƙe muƙamun sarautar gargajiya kamar bulamai ko dagatai ko kuma hakimai ne don irin shigar alfarmar da suke yi na raya al'adunsu.

1.12.0. Suna inganta rayuwar al'umma ta hanyar yabo da ta'aziyya da faɗakarwa da gargaɗi, soyayya da siyasa da wayar da kai, hanka mai sanda, ilmantarwa, nishaɗantarwa da sauransu:

1.12.1 Nuna Yabo

Turken yabo shi ne turken da makaɗan baka suka fi yin waƙa a kansa. Gusau (2008, sh. 376) ya bayyana ma’anar yabo da cewa:

Mafi yawan waƙoƙin baka manufofinsu sukan zamanto yabon waɗanda ake yi wa su rukunan al'umma ne na daban. Yabo shi ne ambaton kalmomin sambarka da nufin nuna amince wa da hali ko wasu abubuwan da mutane su yi nagari. Ko kuma a iya cewa yabo wani lafazi ne da ake yi ga wasu mutane domin a nuna halayensu da siffofinsu kyawawa da cewa abin so ne kuma abin ƙauna ne. “Yabo a cikinsa makaɗa sukan yabi ubangidansu da ambaton darajar kakanninsa, da jarumtaka da kuma alheri” (Ibrahim, 1983, sh. 9).

Bello (1976) da Yahya (1997) sun bayyana cewa akan yabi mutum ta ambaton addini ko asali da zuriya ko jarumta ko iya mulki ko kyauta ko kyan hali. Wannan bincike ya tsinto wasu waƙoƙi da makaɗan baka da dama sun yi waƙoƙin su akan wannan jigon ta amfani da turken yabon alheri, kamar haka:

Misali:

Jagora: Ran assabar sai nij je gidan Sarki,

: Ɗanƙwairo ya ba ka tu tauzan,

: Daudin kiɗi da shi da Marafa,

: Kowane ga babbar rigatai,

: Mu biyu sai yab ba mu tu tauzan,

: Yaran Ɗanƙwairo goma sha uku,

: Kowa riga da tu hondiren naira,

: Kuɗin Ƙwairo da na yara,

: Sun zama fayif tauzan da siks hondiren naira.

(Waƙar Alh. Musa Ɗanƙwairo ta Zaki ba ja da gaba ba,

: Sarkin Murin Uban Galadima.

Alhaji Amadu Doka Mai kukuma Kaduna a cikin waƙarsa ta "Komai Zaka Yi Rinƙa Yin Tunani, cewa ya yi:

Jagora: Ashe kyauta na ƙure mai waƙa,

: Waƙa na ƙure kyauta,

: Na ce riga an haɗo da jamfarta,

: Na biɗi wando har agogo an ba ni,

: To ka ga kyautarka ta ƙure ni,

: Har ban san abin da zan faɗi ba.

(Waƙar Alh. Amadu Doka Mai Kukuma ta Komai za ka yi rinƙa yin tunani).

Shi kuma Alh. Mamman Shata ya bi sahunsu a inda ya ce"

Jagora: Liman yake mai kwana kyauta,

: Ko'ina ya ganan yay yi min kyauta,

: Suka ce mini-Alhaji mai shata,

: Haka nan yake bai son rowa ba.

(Waƙar Alh. Mamman Shata ta gaisheka ta ƴan Liman)

Ita ma waƙar Hajiya Mariya Sunusi Ɗantata, wadda Alhaji Sirajo Mai’asharalle ya yi:

Jagora: Alhaji ya Mariya Sunusi,

‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi,

Jagora: Najeriya ka game ta kwata,

: Ba mata masu kallabi ba,

: Had da mazan duk na haɗesu su duka,

: Ban ga ɗiya mai kama da ke ba.

‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

Jagora: Malaman cikin Kano gaba ɗai,

: Suna faɗar Mariya Sunusi,

: Inda Kano Allah ya bamu ukku,

: Kuma ukkun mai irin halinta,

: Da talakawa ba su ƙ ara kuka.

‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

Jagora: Dattawan cikin Kano gaba ɗ ai,

: Suna faɗar Mariya Sunusi,

: Yaushe rabon da ai irin halinta,

: Tun zamanin nan na Annabawa.

‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

(Sirajo Mai’asharalle: Waƙar Hajiya Mariya Sunusi Ɗantata).

A waɗannan ɗiyan waƙa da suka gabata, makaɗin ya yi ƙoƙarin nuna kyawawan halayen Hajiya Mariya Sunusi Ɗantata, a ɗa na farko inda yake yabonta da cewa duk Nijeriya maza da mata babu mai irin halinta. Kamar yadda masana suka bayyana ambaton kyauta tubali ne na gina turken yabo. A ɗa na biyu da na uku da aka kawo ya bayyana cewa tana da kyauta, wanda ya ce malaman Kano da dattawan Kano duk sun yabi halinta na kyauta da cewa da akwai masu kyauta irin ta guda uku da talakawa sun daina kukan talauci a Kano.

A cikin waƙar dai ya yi amfani da ambaton zuriya wanda shi ma wani tubali ne da ake gina turken yabo da shi, kamar haka:

Jagora: Uwar Wafa’ilu uwar su Abba,

: Uwar su Sani uwar Aliyu,

: Uwar su Fatima uwar Hadiza,

: A Inna uwa mai hana mu kuka.

‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

(Sirajo Mai’asharalle: Waƙar Mariya Sunusi Ɗantata ).

Haka ya mamaye waƙar da kalmomin yabo tun daga farkonta har ƙarshenta. A wani misalin kuma, Amadu Sheme ya yi amfani da turken yabo a waƙoƙinsa. Misali:

Waƙar Sarkin Birnin Gwari wadda ya yi wa Alhaji Zubairu Sarkin Birnin Gwari.

G/Waƙa: Sarkin Birnin Gwari,

: Zubairu Sarki bawan Allah,

Jagora: Sarki Zubairu shi ya biya mani Makka,

`: Alhaji ya ƙara mani Makka ya ba ni gona,

: Sarki ya ban gida kuma ya ban mota Sarki.

‘Y/Amshi: Sarkin Birnin Gwari,

: Zubairu Sarki bawan Allah.

Jagora: Na yarda shugabanci yai ma kyawu,

: Baba sarauta tai ma kyawu,

: Ga ka da ilimi,

: Ga son Allah,

: Ga sadaka kuma ga alheri,

: Da taimako ga dubun al’umma Sarki.

‘Y/Amshi: Sarkin Birnin Gwari,

: Zubairu Sarki bawan Allah.

Jagora: Kai ba ni ke faɗi ba,

: Amadu me mai waƙa,

: Malamanmu na Birnin Gwari,

: Suna ji sun canja mai suna,

: Mai ƙurani jeri-jeri,

: Ga su a mota,

: Ga su a ɗakin kwantawar Sarki.

‘Y/Amshi: Sarkin Birnin Gwari,

: Zubairu Sarki bawan Allah.

(Amadu Sheme: Waƙar Sarkin Birnin Gwari Zubairu)

A waɗannan ɗiyoyin da suka gabata ya yabi Sarki da kyawawan halaye irin na kyauta da ilimi da son Allah (addini) da sadaka da taimako da riƙo da addini, wanda har ya hakaito cewa malaman Birnin Gwari sun canja masa suna zuwa Mai ƙurani jeri-jeri. Haka ya ci gaba da ambaton kyawawan halaye da zuriya da nasaba da addini da kyauta da addu’a da ambaton abokan arziki, waɗannan tubala su suka mamaye waƙar tun daga farko har ƙarshe. Don haka sun tabbatar da turken waƙar yabo ne.

1.12.2 Saƙon Taaziyya

Ta’aziyya na nufin “gaisuwa da ake yi wa mutanen da aka yi wa mutuwa don sanyaya musu zuciya” (CNHN, 2006, sh.416). Wannan kalma ta ta’aziya tana nuna juyayim ko alhini game da rasuwar wani masoyi, sannan da tuna wasu abubuwan alheri da ya yi a lokacin da yake raye, daga nan kuma sai a yi kukan rashinsa.Ta’aziyya takan ƙunshi yi wa mutanen mamacin gaisuwa da taya su juyayi da ba su haƙuri saannan da roƙar wa mamacin gafara da sauransu (Gusau, 2008, sh. 379).

Duba da waɗannan bayanai za a fahimci cewa ana gina turken ta’aziyya ta hanyar nuna tausayi da nadama tare da yin addu’a ko nuna alhini ko baƙin cikin rabuwa da mamaci ko yabon kyan halin mamaci. A wannan bincike an fito da wasu waƙoƙi da makaɗi ɗan asharalle na Jihar Katsina suka yi masu ɗauke da turken ta’aziyya. Kamar haka:

Misali:

Waƙar Taaziyyar Marigayi Sarkin Katsina

Kabir Usman” wadda Usamatu Iliyasu Wada

Uban Maryama ya yi:

G/Waƙa: Ya Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Ya Zuljalali Allah Ubangiji,

: Ka amshi duk roƙona da nike.

‘Y/Amshi: Ya Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Ya Zuljalali Sarki mai kyauta,

: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

‘Y/Amshi: Ya Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Yau Najeriya faɗinta kakaf,

: Duk mun yi tagumi mun rasa rashi.

‘Y/Amshi: Ya Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Ya Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Kamar in yi kuka mai kiɗa,

: Lokacin Sarki Katsina,

: Garinmu duk kaf ba a hwaɗa,

: Talakawa duk sun yaba shiri.

‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Fulani mu da manoma,

: Inyamurai da ƴaƴan Hausawa,

: Gaba ɗayanmu Alhaji ba a hwaɗa.

‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Yarabawa har da kare-kare da Fulani,

: Yau duk ba mu hwaɗa.

‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Ya samu mun riƙe addini,

: Ya samu mui zumunci kullum,

: Kullum yana ƙira mu koma shiri.

‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Ku mui ta addu’a talakawa,

: Mata da maza mui ta addu’a.

‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

Jagora: Allah ya yahe ma laihin da ku kai x 2.

‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙan Sarkin Katsina.

A waɗannan ɗiyoyin makaɗin ya yi amfani da salo na addu’a da juyayi da tuna halayensa na kirki da iya mulki da son addini, kamar yadda masana suka bayyana cewa a yayin ta’aziyya ana nuna juyayi ko alhini game da rasuwar wani masoyi da kuma tuna ayyukansa na ƙwarai.Wanda tun a gindin waƙar ya fara da addua haka ya ci gaba da juyayi da alhini na rashin Sarkin har zuwa ƙarshen waƙar.

Haka ma, Alhaji Amadu Sheme ya yi waƙar ta’aziyya wadda ya yi wa tsohon shugaban ƙasa na farar hula Umaru Musa Yaraduwa, kamar haka:

G/Waƙa: Shugaban ƙasa Allah jiƙan,

: Ummaru Musa Ƴaraduwa.

Jagora: Ummaru angon Baturiya,

: Mai ban sha’awa,

: Ƙani ga Shehu Musa Ƴaraduwa,

‘Y/Amshi: Ƴaraduwa,

: Shugaban ƙasa Allah ji ƙan,

: Ummaru Musa Ƴaraduwa.

Jagora: Mu Umar,

: Ka riƙe mu tamkar ɗa da iyaye.

‘Y/Amshi: Shugaban ƙasa Allah ji ƙan,

: Ummaru Musa Ƴaraduwa.

Jagora: Mu Umar ya riƙe mu,

: Tamkar ƴaƴa da iyaye.

‘Y/Amshi: Shugaban ƙasa Allah ji ƙan,

: Ummaru Musa Ƴaraduwa.

(Sheme: Waƙar Taaziyyar marigayi shugaban ƙasa Ummaru Musa Yaraduwa).

A waɗannan ɗiyan waƙar da suka gabata makaɗin ya yi amfani da salon tuna abubuwan da ya yi na kyautata wa al’umma da yabo haɗe da yabon kyawawan halayen shugaban ƙasa wajen yin taaziyya, inda a wajen yabon yake danganta shi da matarsa da ɗan’uwansa. A wajen yabon kyawun hali kuwa ya bayyana yadda Ummaru Musa Ƴaraduwa ya riƙe al’ummar Nijeriya kamar riƙon ɗa da iyaye. Ya sake kawo irin wannan salo na ambaton kyawun hali a wani ɗan waƙar kamar haka:

Jagora: Kai jama’a ga shi babu rai nai

‘Yar’aduwa,

: An rikirkita mu ƙasar nan,

: Mu ƴan arewa mun rasa inda akai,

‘Y/Amshi: Mun rasa inda akai,

: Shugaban ƙasa Allah ji ƙan,

: Ummaru Musa ’Yar’aduwa.

(Sheme : Waƙar Taaziyyar Marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa).

A wannan ɗan da ya gabata, yana yabon mamacin ne da cewa lokacin da yana da rai ana zaune lafiya, amma bayan ransa an rasa zaman lafiya a ƙasa musamman a Arewa. Haka ya ci gaba da kawo kyawawan halaye na mamaci da kuma yabo, wanda waɗannan su ne suka ƙarfafi turken har ya kai ga isar da saƙon.

1.12.3 Siyasa

A luggace siyasa na nufin “tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su (CNHN, 2006; sh. 397). Ma’anar kalmar siyasa ta fannu kuwa tana nufin: “Hanya ko dabara wadda ake amfani da ita a cim ma wani mataki na shugabancin al’umma. A tsarin siyasa akwai siyasar addini da siyasar kishin kai da siyasar kishin ƙasa da siyasar jam’iyya” (Gusau, 2002; sh. 34).

Gusau ya ƙara da cewa: Turken siyasa ya ƙunshi waƙoƙi waɗanda ake gina su a kan manyan saƙonni na siyasa da suka haɗa da bayyana manufofin jam’iyya ko yi wa jam’iyya kamfen na yaƙin neman cin zaɓe ko wayar da kai kan zaɓe ko yabon ƴan siyasa da sauransu. (Gusau, 2002; sh. 34).

Ta la’akari da waɗannan bayanai da suka gabata, za a iya kasa waƙoƙin siyasa zuwa gida uku kamar haka:

a. Waƙoƙin Siyasar kishin kai.

b. Waƙoƙin Siyasar kishin ƙasa.

c. Waƙoƙin Siyasar jamiyya.

Daga cikin wa ƙoƙi masu turken siyasa akwai waɗanda aka yi su a kan kishin ƙasa da kishin kai da kuma kishin addini. Alhaji Amadu Sheme ya yi waƙa ta neman jiha a yankinsu wadda za mu iya ɗora ta a kan kishin ƙasa. Misali:

G/Waƙa: Ƴanuwa kowa ya yi addua,

: Allah ya ba mu jiha ta Karaɗuwa.

Jagora: Yara in muka samu jiha a ƙara haɗuwa,

: Hedikwata.

‘Y/Amshi: Na birnin Funtuwa.

Jagora: Ai ko hedikwata.

‘Y/Amshi: Na birnin Funtuwa.

Jagora: In ko hedikwata aka yi ta a Funtuwa,

: Sai in biya.

‘Y/Amshi: In karɓa in wuce.

Jagora: Da na zo sai in biya.

‘Y/Amshi: In karɓa in wuce,

: Ƴanuwa kowa ya yi addua,

: Allah ya ba mu jiha ta Karaɗuwa.

A wannan ɗan waƙa da ya gabata Amadu Sheme ya nuna inda suke buƙata da ya zama babban birnin Jiha, idan har sun sami Jihar da suke nema wadda suka kira da Karaɗuwa. Sannan ya ci gaba da bayyana arziƙin da ke yankinsu a matsayin dalilansu da suka sa suke ganin yankin nasu ya cancanci zama Jiha, kamar haka:

Jagora: In ma’adanai ke sawa ai Jiha,

: Ma’adanai da yawa a Karaɗuwa,

: Farar ƙasa,

: Na birnin Ƙanƙara,

: Idan kana so.

‘Y/Amshi: Zo a gwada maka.

Jagora: Dutsen kuɗi,

: Akwai kwaranda,

: Birnin Sheme.

‘Y/Amshi: Idan kana so zo a gwada maka.

Jagora: Sannan muna da zinarenmu,

: A Sabuwa.

‘Y/Amshi: Idan kana so zo a gwada maka.

Jagora: Malam muna da alherinmu a Sheme,

: Muna da sinadarin da ake haɗa kwano.

‘Y/Amshi: Idan kana so zo a gwada maka,

: ’Yan’uwa kowa ya yi addu’a,

: Allah ya ba mu jiha a Kara ɗ uwa.

(Amadu Sheme : Waƙar Neman Jihar Karaɗuwa).

A wannan ɗa kuma ya nuna irin arzikin da ke ƙananan hukomimin da suke ƙarƙashin Jihar da suke nema. Wanda idan har ma’adanai ko arzikin ƙasa ke sawa a yi Jiha to akwai su a yankin da suke neman Jihar. Haka kuma ya bayyana ƙananan hukomomin da za su zama cikin sabuwar Jihar kamar haka:

Jagora: A kan wannan neman Jiha,

: In muka samu Karaɗuwa,

: Musawa Lokal Gwammet,

: Suna cikin kwamitin.

‘Y/Amshi: Neman Jiha .

Jagora: Musawa Lokal Gwammet ,

: Sun hwaɗi.

‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

: Neman Jiha.

Jagora: Matazu Lokal Gwammet ,

: Sun hwaɗi.

‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

: Neman Jiha.

Jagora: Ƙanƙara Lokal Gwammet,

: Sun hwaɗi.

‘Y/Amshi: Suna cikin kwamititin,

: Neman Jiha.

Jagora: Malunfashi Lokal Gwammet,

: Sun hwaɗi.

‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

: Neman Jiha.

Jagora: Bakori Lokal Gwammet,

: Sun ka hwaɗi.

‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

: Neman Jiha.

Jagora: Ƙafur Lokal Gwammet,

: Sun hwaɗi.

‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

: Neman Jiha,

: ’Yan’uwa kowa ya yi addu’a,

: Allah ya ba mu Jiha a Karaɗuwa.

(Amadu Sheme : Waƙar Neman Jihar Karaɗuwa).

Shi ma makaɗi Abdu Karen Gusau ya yi wata waƙa ta siyasa inda yake cewa:

G/waƙa: Ciyaman Malam Magaji Garun Danga

(Waƙar Abdu Karen Gusau ta Ciyaman Malam Magaji Garun Danga)

1.12.4 Nuna Soyayya

Kalmar soyayya a ma’ana ta harshe na nufin “nuna ƙauna daga ɓangarori biyu na masu ƙaunar juna, musamman mace da namiji” (CNHN, 2006; sh. 398). “ Soyayya kuwa tana nufin so da yake aukuwa a tsakanain masoya guda biyu inda za su dinga ƙaunar juna, suna masu begen juna” (Gusau, 2008; sh. 393).

Makaɗa da mawaƙan baka sukan gina waƙoƙinsu a kan turken soyayya ta ɓangarori kamar haka: ko dai su yi waƙa a kan soyayyar da suke yi da wata budurwa ko ƴan mata, ko kuma su yi waƙa a kan soyayyar da ke tsakanin wasu ba su ba, ko kuma su yi waƙa a kan soyayyar kanta. Dangane da turken soyayya a wajen makaɗi Ɗan asharalle na jihar Katisna an same su ne a wajen makaɗi Audu Boda. Daga cikin waƙoƙin da ya yi na soyayya akwai wadda ya yi wa soyayyar ita kanta kamar haka:

G/Waƙa: Soyayya da ɗi ta fi zuma daɗi.

Jagora: In na yi tunani,

: Audu na san soyayya,

: In nai nazarina,

: Audu na san soyayya,

: Don na taɓa soyayya,

: Ni na san soyayya,

: Na san da dinta,

: Na san haɗarinta,

: Yara in so cuta ne,

: Haƙuri magani ne,

: Wadda yac ci amana,

: Amana kau za ta ci shi,

: Mai haƙuri mawadaci,

: Wata ran zai dafa dutse.

‘Y/Amshi: Soyayya da daɗi ta fi zuma daɗi.

(Audu, Boda: Waƙar Soyayya).

A wannan ɗa da ya gabata Audu Boda ya yi bayani ne a kan soyayya na da daɗi kuma tana da haɗari, don haka yake ba wa matasa shawara da su yi takatsantsan idan so cuta ne to haƙuri magani ne. Maana, idan mutum ya kamu da soyayyar wani ya ga zai gamu da wata wahala to ya yi haƙuri. A wani ɗan kuma ya bayyana haɗarin soyayya da cewa: Shi ne ranar rabuwa, kamar haka:

Jagora: Kun ji akwai wata rana,

: Wadda nake tsoranta,

: To du akwai wata rana,

: Wadda nake tsoranta,

: To da ɗa sai wata rana,

: Wadda nake tsoranta,

: In na yi tunani,

: dole nake tsoranta,

: Ni in nai nazarina,

: Sai na riƙa tsoranta,

: Don rabuwa da masoya,

: Dole yai mamu ciwo.

‘Y/Amshi: Soyayya da ɗi ina soyayya.

(Audu Boda: Waƙar Soyayya)

Makaɗi Amadu Garba Ɗankwamarado ya yi wata waƙar soyayya inda yace:

Jagora: Wata yarinya Ladiyo,

: Ku zo ku ji waƙar Ladiyo,

: Ita Ladiyo bata yin faɗa,

: Kuma bata son mai yin faɗa.

(Waƙar Ɗankwamarado ta Soyayya)

Mawaƙi Billy O shi ma ya yi waƙar soyayya kamar haka:

Jagora: Yaushe za ki dawo,

: Umaima yaushe za ki dawo,

: Da safe ko da rana.

(Waƙar Billy O ta Gobe za ki dawo).

1.13 Suna da ganin kimar kansu kuma suna da yawan riƙe al'adu tare da adabinsu: A yau kusan makaɗan baka na Hausa baga ɗayansu kaf duka shiga ne ta sutura irin na Bahaushe usil, sai dai ɗan kama yakan saɓa da sauran makaɗa domin shi yana shiga ta sutura irin ta mahaukata. Wasu makaɗan kuma idan suka yi shiga sai a ga kamar wasu sarakai ne ko jinin sarauta, misali makaɗa Salihu Jankiɗi wanda har ma doki su ke hawa su ɗaura rawani da shiga ta alfarma irin ta sarakai da kuma shiga irin ta Aminu Ladan Abubakar, Alan waƙa.

A ɓangaren adabi kuma Hausawa suna kallon makaɗa a matsayin wata fasahohi ko hanyoyi na adana adabin su sannan suna kallon makaɗan a matsayin wata makaranta ce wanda take gina al'umma wato wani wuri ne na musamman na ilmintar da jama'a saboda waƙoƙin da su ke yi har ma su ke yin tasiri a cikin al'ummu daban-daban. Don haka al'ummun su ke ganin kima da daraja tare da girmama su da ba su matsayi. Misali Makaɗa irin su Alh. Sani Sabulu Kanoma da Dr. Adamu Ɗanmaraya Jos da Aminu Ladan Abubakar, Alan waƙa da sauransu da yawa.

Waɗannan makaɗan da wasun su wanda ba a ambata ba, mutane suna ganin matsayin su sosai saboda waƙoƙin da su ke yi masu amfanarwa ne ga jama'a ne bisa rayuwarsu sannan kuma sukan yi la'akari da hankalinsu idan makaɗan sun kasance suna yin waƙoƙin fasahohi da na hikimomi ta yin amfani da sarrafa harsuna da zalaƙa da basira da maganganun azanci tare da shirya kalmomi da jumloli masu karsashi da ma'anoni. To ta haka ne makaɗan suke samun matsayi a wuraren al'ummu daban-daban. Matsayin da su ke samu sukan kasance kamar haka; ƙauna da ƙiyayya da hantara da kuma kyauta.

Don haka sanya suturu da adabi a fagen waƙoƙin baka na Hausa tamkar hoto ne ko madubi ga rayuwar al'umma wanda da zarar a gani suturun da su ke sanya a jikinsu tun daga nesa za a fahimci waɗancan mutanen Hausawa ne na asali kuma da zarar an ji maganganun da suke shiryawa na waƙa za a ga Hausawa ne. Ke nan suturu ko al'ada da adabin Hausawa suna koyar da harshe da naƙaltarsa da ilmintarwa ga al'umma da adana hikimomi da al'adun Hausawa da taya su hira ko taɗi da sanya nishaɗi da nuna martaba da cusa alfahari da girmama abubuwan da aka gada daga iyaye da kakanni da koyar da dabarun zaman duniya da inganta rayuwa kamar faɗakarwa, gargaɗi, ilmintarwa, gyaren hali da sauransu da bunƙasa ilmi da ƙishin ƙasa da sauransu da yawa.

Misali Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a cikin wakarsa ta tunatarwa ga al'ummar Hausa da kada su manta da al'adunsu na gargajiya yana cewa:

Amshi: Mu bi al’adunmu na gargajiya,

Kar mu sake mu mance su.

Jagora: An ce a bari anki bari.

Amshi: Ka ji bata aiki.

Jagora: An ce a yi an ce ba a yi

Amshi: Ka ji bata aiki.

Jagora: Tsaron gaskiya ya fi tsaron karya.

Amshi: Shi af farika.

Jagora: Al’adu Ba karya ne ba.

Ku duba tun ga manoma,

Gona sukan shigewa,

Suna ta bidan abinci,

Amshi: Mu bi al’adun mu na gargajiya,

Kar mu sake mu mance.

Jagora: Ku duba tun ga mamaka.

Kullum muna ta waka,

Muna ta bidar abinci,

Domin haka munka iske.

Amshi: Mu bi al’adunmu na gargajiya,

Kar mu sake mu mance.

Jagora: Kyawun ɗan Arewa babbar riga,

Ga rawani da taggo,

Ko ran salla ko ran suna,

Ko ran Juma’a ya dauka.

Amshi: Mu bi al’adunmu na gargajiya,

Kar mu sake mu mance.

Jagora: Ku ko matan Arewa,

Ƙwairo na gargaɗinku,

Ibada munka gada,

Ku sa sutura isassa,

Ku bar sa siket da yak kanti

Kuna biyar rariya – rariya,

Abin gay a ba da kunya.

Amshi: Mu bi al’adunmu na gargajiya,

Kar mu sake mu mance.

Jagora: Ƴan Arewa da an nan,

Wadanda ad diyan Musulmi,

Ƙwairo na gargadinku,

Ku zan azumi da sallah,

Ku zan kono da zakka,

Ku zan azumi da sallah.

Amshi: Mu bi aladunmu na gargajiya,

Kar mu sake mu mance.

Jagora: Masu gari ina horonku,

Ko da kana da mota,

Ka sai dokinka ka daure,

Wurin mota daban ne,

Kuma wurin doki daban ne

In ka tashi hawan doki,

Ka hau ka je kilisa,

Ka dawa gida ka daure.

In ka tashi hawan mota,

Ka hau motarka ka sheka.

Amshi: Mu bi al’adunmu na gargajiya,

Kar mu sake mu mance.

(Waƙar Musa Ɗanƙwairo ta bi al'adunmu na gargajiya)

2.0 Munanan Halayen Makaɗa:

Waɗannan wasu ɗabi'u ne da makaɗan baka na Hausa su ke aikata su wanda al'umma su ke gyamar su. Ga wasu daga cikin su:

2.1 Fanɗare wa Koyarwar Musulunci ta Hanyar Zambo:

Makaɗan baka musamman na saurauta sun shahara wajen yin zambo, domin ƙawata waƙoƙinsu. Masana da dama sun bayyana ma’anar zambo gwargwadon fahimtarsu. Gusau, (1984 p. 37) ya tafi kan cewa “Akan yi zambo don adanta waƙa da muzanta wanda ke hamayya da wanda ake yi wa waƙa. Abba da Zulyadaini, (2000 p. 63) sun bayyana zambo da cewa: “... nau’i ne na muzanta mutum ta hanyar ƙasƙantar da shi, ko wulaƙanta shi, domin a baƙanta masa tare da dusashe masa kwarjini a idon jama’a. Mawaƙan sun fi shahara da zambo don su aibanta duk wani ɗan sarki da ke ja da ubangidansu. Muhammad, (2005) kuwa na da ra’ayin cewa zambo zagi ne kai tsaye,... saboda akan ba da hoton wanda ake yi wa tare da bayyana cikakkiyar sifarsa ta hanyar ambaton duk wani abu da ya dace da shi. A lokacin da aka yi ma wani zambo akan fito da hotonsa ne zahiri, ta yadda duk wanda ya san shi zai gane cewa da shi ake. Muhammad, (2005 p.28).

A taƙaice ke nan, zambo yana ƙunshe da ma’anar ƙaga wa mutun magana wadda za ta muzanta shi ta ɓata masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba. A dubi misalign zambon da Alhaji Musa Ɗankwairo ya yi wa wani ɗan sarautar Tsafe:

Kun san zamanin ga ya canza,

Ga wani ɗan sarki da kandaye,

Ya shaho hoda kamar Delu.

(Ɗankwairo: Waƙar Sarkin Tsahe).

Wannan zambon da Ɗankwairo ya yi wa ɗan sarki ya kai matuƙa wajen aibanta ɗan sarkin ta hanyar kamanta shi da ɗan daudu. Hakan ba ƙaramin muzantawa da dushe masa kima ya yi a idon al’umma ba. Tabbas kuwa hakan ya saɓa wa dokokin addinin Musulunci. An umurci Musulmi da ya tsare (kame) harshensa da yin furucin abin da bai halatta ba, kamar keta mutuncin ɗan uwansa Musulmi ba tare da wani abu mai wajabtawa ba na shari’a. Allah na cewa:

Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa, da ba wa ma’abocin zumunta kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana yi muku gargaɗi ko da kuna tunawa. (Surar Nahli: 16:90).

Idan aka dubi wannan ayar za a tarar ta yi hani ga yi wa wani mugun baki (mugun fata), sannan ta yi hadi ga alfasha. Ya kuma yi umurni da tausayawa tare da yin abu bisa gaskiya. Daga ƙarshe ta yi hani a kan haintar wani ta kowane ɓangare. Wannan na iya kasancewa ta hanyar lafazi ko a aikace. Ta la’akari da wannan ɗiyar waƙar, za a tarar mawaƙin ya kauce wa dokar da Allah ya ɗora masa.

Annabi (S.A.W) ya ce:

Haƙiƙa, mafi sharrin mutane a matsayi wurin Allah a ranar alƙiyama shi ne wanda mutane suka ƙyale shi don ƙiyayyar alfasharsa. (Muslim ya ruwaito).

Wanda duk wani mawaƙi ya yi wa zambo, to zai guje shi tare da yin kaffa-kaffa da al’amarinsa. Sau da yawa akan ba su kyauta ne bisa tilas don gudun zambonsu. A irin wannan yanayin idan aka nazarci hadisin, za a ga a nan ma sun kauce wa koyarwar Annabi (S.A.W).

A wani Hadisin kuwa Annabi (S.A.W) cewa ya yi: “Mumini bai kasancewa mai yawan suka ba ko yawan la’anta ko yawan alfasha, ko mai sakin harshe” (Tirmizi ne ya ruwaito shi).

Wannan hadisin ya fito ƙarara ya bayyana mana cewa, duk mawaƙin da ya ba da gaskiya ga Allah da ranar lahira da manzancin Annabi S.A.W., zai kasance mai bin dokokin Musulunci kamar yadda suke. Hakan kuwa zai sanya ya guji yi wa Musulmi zambo. Akwai misalan wuraren da makaɗan jama’a suka yi wa abokan hamayyarsu zambo ta hanyar zagi kai tsaye. A irin wannan lamari ne mawaƙin jamaa kan fito da halayen mutun a fili, sannan ya zage shi. Misali, a waƙar Gagara Badau, Alhaji Mamman Shata cewa ya yi:

Shata: Allah ya tsine ma tsohon mazinaci,

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

Shata: Allah ya tsine ma da kai da iyalinka.

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

Shata: Yanzu babban ɗan bai gani,

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

Shata: Babban jikanshi kuma yana kama agwaginmu,

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

Shata: Gida ya lalace.

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

Dubi yadda Shata yake zagin wani basarake tare da nuna ɗansa ya makance, ya kuma kira jikansa ɓarawon agwagi. Wannan ba ƙaramar fanɗarewa ba ce, domin a shara’ar Musulunci an umurci Musulmi da ya kiyaye da yin zance da bai halatta ba, kamar ƙarya, da zage-zage da keta mutunci Musulmi.

Allah na cewa: “... Kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana muku gargaɗi ko da kuna tunatuwa.” (Alƙurani, Suratul Nahl, 16:90).

2.2 Fanɗare wa Koyarwar Musulunci ta Hanyar Habaici

Habaici ko gugar zana salo ne ko azancin yi da wani a kaikaice ta yadda sai wanda ya san shi kuma ya san abin da ake magana game da shi ne kaɗai zai iya ganewa. Habaici wata hanya ce da makaɗan baka suke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin ƙara musu armashi, ta hanyar ƙasƙantar da wani mutun ko kuma muzanta shi ko su zage shi ko kuma su soka masa wata magana a kaikaice. Misali,

A cikin waƙar Mai Dubun Nasara Sardauna, Alhaji Musa Ɗankwairo yana cewa:

Jagora: Ga kare ga kura kowane ya hangi wani,

Ga aura ya koma,

Wagga nan hanya ba mu ga wurin wali ba.

(Alhaji Musa Ɗankwairo, Waƙar Mai Dubun Nasara, ta Sardauna).

Yayin da aka dubi ɗiyar wannan waƙar za a ga yadda Ɗankwairo ya siffanta Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da kura. Ya yi hakan ne domin bayyana irin ƙarfinsa kamar yadda kura ke da shi. Wannan kuwa ya shafi yadda take iya tauna ƙashi da kuma kwarjini da waibuwarta na sanya rashin kuzari ga halittar da ta tunkare ta. A gefe guda kuwa, sai ya ƙira wanda yake yi wa habaici da kare, saboda ba sa zama inuwa ɗaya da kura. Hasali ma kare ba ya hangen nesa sosai, kuma mai gidansa yakan yi amfani da shi ne wajen farauta. Ƙiran mutum kare ba ƙaramin ƙasƙantarwa ba ne a aladance. Wannan ne ya sa makaɗan baka sukan siffanta waɗanda suke son wulaƙantawa da kare saboda halayyarsa da ɗabi’unsa.

Musulunci ya hana keta mutuncin Musulmi ko wulaƙanta shi ko zagin sa ko laƙa masa munanan sunaye, ba tare da haƙƙin sharaa ba.

Allah na cewa: “… kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye” (Alƙurani, 49:11).

Idan muka dubi wannan ayar, za mu ga cewa ta hana a ƙira Musulmi da sunan da zai kasance tamkar zagi ne gare shi. Yin haka kuma fanɗare wa umurnin Ubangiji ne.

Annabi S.A.W. ya ce: “Zagin Musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙar sa kafirci ne” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

Idan aka dubi wannan hadisin cikinsa da wajensa, aka kuma nazarci ɗiyar waƙar da ta gabata, za a tarar cewa, makaɗin ya kauce wa faɗar Annabin S.A.W., ya yi gaban kansa. Yin haka fanɗarewa ne ga dokokin addinin Musulunci. Bin dokoki da ƙaidojin Musulunci kuwa dole ne, inda har Allah ke cewa: “Kuma abin da Manzo ya zo muku da shi, to ku riƙe shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu” (Surah Al-hashr, 59:9).

2.2 Suna Goyon Bayan Yin Izgilanci Ga Addini

Izgilanci ga abubuwan da addini ya zo da su na nuni ga halin ko-oho ga lamarin addinin. Musulunci kansa ya tsawatar da riƙo da dokokin da ke ƙunshe cikinsa ba tare da wargi (wasa) ba. Duk da haka, akan samu wuraren da mawaƙa suka yi izgilanci ga lamarin addini. Alhaji Muhammadu Bawa Ɗan’anace a waƙar da yi wa Shago yana cewa:

Jagora: In da lahira ana kasa dambe...

‘Y/Amsohi: Da Walakiri ya ji ƙwal ga gaba nai.

Jagora: Duk wanda bai yi kallon Shago ba,

Aradu yana da sauran kallo,

Ya zaka duniya kamar bai zo ba,

Kamar zuwan kare ga aboki,

Tamkar mutum ya mari budurwa,

Ko ya mutu ba a gafarta mai.

In aka dubi wannan ɗan waƙar, za a tarar cewa, wannan makaɗin ba ƙaramar kasada ya yi ba. Ya nuna rashin jin tsoron aukawar wani haɗari (hatsari) ko shiga cikin abin da bai san sakamakonsa ba. Allah na cewa: “Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi a kansa.” (Surar Isra’i, 17:36). Idan muka nazarci wannan ayar, za a ga yadda Mahaliccin sammai da ƙassai ya faɗakar da masu imani da su yi kaffa-kaffa ga dukkan lamarin da ba su san haƙiƙanin yadda yake ba. Ko bayan batu kan abin da mutum bai sani ba, batutuwan da ke ƙunshe cikin ɗiyar waƙar na tattare da izgilanci ga abin da ya shafi imani da mala’iku da ranar ƙiyama.

2.3 Suna Goyon Bayan Yin Kisan Kai

Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa: “Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwami a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya tanadi azaba mai girma a gare shi” (Alƙur'ani, 4:93).

An jiyo Makaɗi Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago yana cewa:

Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,

Ba kukan tuwo ba,

Ba na hura ba...

‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi,

Suna kirarin banza.

Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin

‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake....

A wani wuri yana cewa:

Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma.

Ɗan Abdu...

‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.

(Muhammadu Bawa Ɗananace:

Bakandamiyar Shago)

Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi la’akari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:

i. Kusheyi

ii. Lahira a kai miki gawa

iii. Lahira tana yin baƙo

iv. Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu.

Makaɗi Gambo Fagada ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:

Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,

Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,

In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,

Don wagga ba sata ta ba Gambo.

(Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

2.4 Suna Yin Hani ga Bautar Ubangiji.

Ko bayan kira zuwa ga aikata ɓarna da fasadi, akwai misalan ɗiyan waƙoƙi kuma da ke kira ga barin bautar Ubangiji. Na biyu a cikin shika-shikan Musulunci ita ce salla. Tana da matuƙar muhimmancin da har ya kasance kadarko tsakanin mutum da kuma shirka da kafirci. Duk da haka, sai ga ɗiyan waƙa da ke hani ga yin salla:

Bayarwa: Ɗan Abdu ban da sallas swahe,

‘Y/Amshi: Domin yawan sallan nan yana rage maka ƙarhi.

(Muhammadu Bawa Ɗananace:

Bakandamiyar Shago).

2.5 Suna Goyon Bayan Yin Karuwanci.

Kalmar karuwa, suna ne na mace. Jam’i kuwa shi ne karuwai. Karuwa na nufin mace mai zaman kanta wadda mazan banza ke neman ta su ba ta kuɗi domin saduwa (zina) da ita. Zina kuwa tana nufin saduwa (jima’i) da matar da ba ta halatta ga mutum ba ta hanyar aure, wato wadda ba matarsa ba. Tun kafin bayyanar Musulunci a farfajiyar ƙasar Hausa, Bahaushe ya ƙyamanci zina.

Don haka karuwanci bai samu wurin zama ba, balle a yi zina. Duk da kasancewar akwai al’adar tsarance, a inda saurayi kan gayyaci budurwarsa ta je ɗakinsa har ma ta kwana. Sakamakon irin wannan al’adar ce, ya Sanya su amfani da al’adun tsafi domin tabbatar da amarya ba ta taɓa sanin wani ɗa namiji ba (zina) kafin a yi mata aure. A irin wannan al’adar ce, idan yarinya ta san maza kafin a yi mata aure, za ta kunyata a cikin jama’a. Idan kuma ta ɓoye ba ta faɗa ba, ta mutu, kamar yadda Ibrahim, (1985 p. 5) ya nuna. Yayin da addinin Musulunci ya bayyana, sai ya haramta zina. Hasali ma ya sanya ta cikin manyan laifuka, bayan kafirci, wato haɗa Allah da wani da kashe ɗan Adam. Allah yana cewa: “Kuma kada ku kusanci zina, lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Alƙurani; Suratul Israi, 17:32). Haka kuma Musulunci ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da za ta iya zama sanadin aikata zina ta hanyar wajabta wa mata Sanya hijabi. Sanya hukuncin jefe mazinaci da mazinaciya har su mutu a bainar jama’a, idan sun yi aure, ko a yi musu bulala idan ba su taɓa yin aure ba, na nuni da girman zunubin.

Duk da wannan umarni na Ubangijin talikai da kuma uƙubar da aka tanadar wa mazinata, sai aka sami wani mawaƙi da ake ƙira Habibu Sakarci ya yi wa wata karuwa waƙa. A cikin ɗiyan waƙar yana cewa:

Jagora: Shehuwar mata Safiya Kano,

Ta gidan ‘Yajja Safiya Kano.

Jagora: ‘Yan birni roƙo suke,

Allah ba mu jaka bakwai,

Mu gano ɗakin Safiya Kano.

Jagora: Direbobi ma roƙo suke,

Allah ba mu jaka bakwai,

Mu gano ɗakin Safiya Kano.

Jagora: Mutan birni yanga suke,

Domin darajar Safiya Kano.

Yayin da aka nazarci ɗiyan waƙar, za a ga cewa Habibu Sakarci yana tallar wannan karuwa ta hanyar bayyana ta a matsayin ƙasaitacciyar karuwa. Har ma ya nuna ‘yan birni da dirobobi na burin Allah ya ba su kuɗi masu yawa, don su tafi ɗakinta. Hasali ma ya bayyana ta fi sauran karuwan birnin kyau. Wannan ba ƙaramar fanɗara ba ce da keta dokokin Allah. Shi ma Alhaji Mamman Shata ya yi makamanciyar wannan waƙar, a inda ya yi wa wata mata da ake ƙira Karo Oma:

Jagora: Duk ɗan birnin da ya riƙa,

Ni kar ya yi mini yanga,

In yana so ya isa,

In gan shi gidan Kara Oma.

(Alhaji Dakta Mamman Shata: Waƙar Kara Oma).

A nan Mamman Shata ya fito ƙarara ya tura yan birni su tafi gidan wannan karuwa idan har sun isa. A ɗaya ɓangaren kuwa cicciɓa ta ya yi da cewa, sai manyan mutane wayayyu ne kawai suka isa su yi hulɗa da ita. Wannan waƙar ba abin da ya raba ta da fanɗare wa dokokin Allah da ya shata wa Musulmi. A shara’ar Musulunci, an san Musulmi da kunya. Hasali ma kunya tana cikin halayensa, kuma tana daga cikin Imani. Imani kuwa shi ne aƙida da rayuwar Musulmi. Manzon Allah yana cewa: “Kunya da imani suna zozozo da juna. Idan babu ɗayansu, ɗayan ma ba za a same shi ba” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

2.6 Suna Goyon Bayan Yin Sata

Abubakar (2015, p. 431) ya bayyana cewa, sata “tana nufin ɗaukar abin wani ba da saninsa ko izinin ba.” Sata na nufin ɗaukar wani abu da hukuncin shari’a ko hankalin tuwo bai mallaka wa wanda ya ɗauka ba, tare da amfani da shi ko musanyensa da wani abu mai daraja kwatankwacin na kuɗi ko kuma mai amfanarwa, ba tare da izinin wanda ko waɗanda ke da mallakin abun ba. Sata ta kasu zuwa nau’uka daban-daban. Sun fi danganta da salon yadda aka gudanar da satan. Fitattu daga cikinsu sun haɗa da:

i. Cuta

ii. Damfara

iii. Fashi

iv. Fizge/Wabce/Fauce

v. Ƙwace

vi. Sane

Sata babbar abar ƙyama ce a farfajiyar Hausa da Hausawa, tun ma kafin bayyanar addinin Musulunci. Sauyawan al’amurra da cuɗanyar Hausawa da baƙin alummu sun wanzar da taɓarɓarewar tarbiyyar al'umma da ƙoƙarin neman tara abin duniya ido rufe. Ta kai ga fanɗararru marasa kishin kansu cikin al’umma sun tsunduma a fagen wannan ta’addanci.

Yayin da addinin Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa, sai ya ƙara ƙarfafa wa Hausawa ƙyamar wannan muguwar sana’a. Musulunci ya zo da dokoki domin kawar da duk nau’o’in sata. Allah na cewa: Ɓarawo kuma da ɓarauniya sai ku yanke hannayensu ya zama sakamako ne na abin da suka aikata, (wannan horo ne) daga Allah. Allah kuwa mabuwayi ne Gwani . (Alƙurani,

5:38). A addinin Musulunci ta kowace fuska ana ƙoƙarin kare dukkanin alumma ta yadda za a zauna cikin aminci game da dukiyoyi da rayukan al’umma. Ita kuwa sata, mugun hali ce da ke haifar da rashin kwanciyar hankali da salwantar rayuwa a tsakanin al’umma.

Don haka ne shari’a ta tanadar da hukuncin yanke hannun ɓarawo wanda zai hanawatsuwar irin wannan muguwar ta’asa a tsakanin al’umma. Allah na cewa: “Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar cuta” (Alƙurani, 2: 188).

Ayar tana tabbatar wa masu imani cewa, cuta haram ce. Ba ya halatta ga Musulmi ya yi zalunci ta hanyar zaƙin baki ko dabara. Haka kuma, bai halatta ya yi jagora don a cuci wani ba. Duk da irin waɗannan dokokin da Allah Maɗaukakin Sarki ya shimfiɗa domin samar da kyakkyawan zamantakewa da aminci a doron ƙasa, an samu gungun mawaƙa da ke jayayya da dokokin cikin lafuzzan waƙoƙinsu.

Bunza, (2014) ya kawo baituka da dama daga bakin Alhaji Muhammadu Gambo Fagada. Gambo ya bayyana ƙarara cewa:

Jagora: Don waɗanda ka sata nay yi ganga,

Ba do wani sarki mai naɗi ba.

(Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Tsoho Tudu).

A cikin waƙarsa ta Nazaƙi kuwa, an ga yadda hirarsu ta gudana da Nazaƙi bayan ya tuba

daga sata. Sannu a hankali har Gambo ya sake zuga shi yadda har sai da ya dawo satan. Gambon da kansa ya bayyana cewa:

Ɓarawo in ina kusa ba tuba yakai ba,

Ko ya aje gemu, ko ya yi saje,

Ko ya fidda farin gashi ga kaina,

In Gambo na kusa ba tuba yakai ba,

Ba ko batun shegantaka ba.

(Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Nazaƙi).

A wannan ɗiyan waƙa, sai da ya jaddada cewa, batunsa ba “batun shegantaka” ba ce kawai. Wato dai haƙiƙanin gaskiya yake faɗa cewa idan yana kusa ɓarawo ba ya tuba domin kuwa zai ziga shi ya hana shi tuban. Wasu makaɗan sukan yi waƙoƙin yabo ne ga ɓarayin. Misali Alhaji Mamman Shata ya yi wa wani ɓarawo mai suna Mamman Ɗan’yarbayye waƙa, a inda yake cewa:

Jagora: Mai hannun taɓa ƙofa in an bacci,

Masu samame baƙon Ɗanmani.

Na faɗa maka Mamman.

In dai ka ɗauko sa’a,

Har ka buɗe ƙofa,

Ka tarar an bacci,

To zari akwati tsakiyar shi ya fi kaya.

Na saman hoto ne,

Na ƙasan maganin ƙwari ne.

Tafi zari akwatin tsakiyar shi ya fi kaya.

Na Abdu ƙyale dangi sai an bacci,

Iyalin Mamman, waɗanda ba su so a yi haske,

Su sun fi so a tabka duhu da ruwa yaf-yaf-yaf.

Wani don ya taka kara bai mai ƙara ba,

Sannan ganyen ganji duk ya bi ƙasa.

(Alhaji Dakta Mamman Shata: Mamman Ɗan’yarbayye).

A waɗannan ɗiyan waƙar, mawaƙin ya yabi ɓarawon tare da ba shi shawarar yadda zi gudanar da sana’arsa ta sata. Wannan ya haɗa da yi masa ishara ga irin lokuta da yanayi da dabarun da zai bi wajen yin satar, da kuma nau’in abin da zai sata da ya fi saura daraja. Hakan kuwa karan-tsaye ne ga dokokin addini. Hadisin Manzo (S.A.W.) ya bayyana cewa: Ɓarawo ba ya sata a lokacin da yake da imani” (Buhari ne ya ruwaito hadisin).

Allah Maɗaukakin Sarki ya kawo nau’in hukuncin da ya dace a zartar wa masu fashi da makami, a inda yake cewa:

Ba wani abu ne sakamakon waɗanda suka yi wa (Musulmi masu bin) Allah da manzonsa fashi ba, kuma suke tafiya a bayan ƙasa da ɓarna ba, sai kawai a kashe su ko kuma a tsire su ko a yanke hannayensu da ƙafafuwansu a tarnaƙe, ko kuma a kore su daga ƙasa. (Yin) wancan ƙasƙanci ne a gare su a duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma. (Alƙurani, 5:33).

Allah ya bayyana mana cewa masu yin fashi da makami suna ƙoƙarin ɓata tsarin Allah da Manzonsa ne, saboda aiwatar da fashi ya kauce wa hanyar gaskiya da adalci, waɗanda Musulunci ke ƙoƙarin tabbatar da su a doron ƙasa.

2.7. Suna da Roƙo ga Jama'a

Roƙo shi ne neman taimako daga wani mutum na musamman kamar Basarake, Jami'in gwamnati, attajiri da sauran su don samun biyan wata buƙata. Kusan ana samun wannan jigo a cikin kowace waƙa ta baka domin roƙo ne tushen dalilin rera waƙar. Mabaraci na ambaton abin da yake roƙo a cikin waƙar da yake rerawa, wani lokaci ya ambaci abin da yake roƙo wani lokaci ya tsaya ga wani abin na daban. Mawaƙan baka na roƙon iyayen gidajensu domin su basu abinci ko sutura ko muhalli ko kuɗi ko doki ko neman wata biyan buƙata ta daban.

Har wa yau makaɗan baka na fada a jiya suna rokon iyayen gidajensu ko a fakaice, ko a bayyane wato kai tsaye domin su biya musu buƙatun su dake damun su. Misali, Sa'idu Faru a cikin waƙar Sarkin gabas na Mafara, Alhaji Shehu (Koma shirin daga na Mu'azu) yana cewa:

Jagora: Daudu kullum mafalki ni kai Sabo,

: Shehu ya ba ni doki da kayanai,

: Danda hwari biyat wanda an nan haka,

: Inda Liman Kabi zai Massallaci”.

(Waƙar Sa'idu Faru ta Sarkin Gabas na Mafara Alhaji Shehu)

Shi kuwa Marigayi Salihu Jankiɗi Rawayya yana cewa a cikin waƙar Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello (Sardauna zaki hana ay wargi).

Jagora: Shantali Maganar dokina nai,

: Har na kahwa turke gida na”

Alh. Dankwairo Maradun a cikin takensa na ɗan Amadu Tsayayye da ya rera wa Sarkin ƙayan Maradun, Marigayi Alh. Muhd Tambari yana cewa:

Jagora: Muhammadu sarki ka kai ni Makkah Amma hwa da kuɗɗinka ba da namu ba”.

Makaɗin Damalgo Na Ayi shi ma ya yi roƙon baka makamacin haka, inda yake cewa"

Jagora: Ban sabi da Manzon Allah,

Kyautar mu sai biya ai,

Bar guduna mu ɗan halak mu ke yi wa roƙo,

Ba ma yi wa matsiyaci...,

Mai tagwayen yara,

Ai kowa ka gani da biro ilminsa ne ya ba shi,

Wani kuma dan ado yake soka wa.

Ƴ/Amshi: Alaseni yallaɓai ustaz,

Jagora: Akaramulla ustaz dubi gemunsa,

Ka roƙi ɗan halak ka ji daɗi,

Wanda ya roƙi kafiri ya wahala.

(Na Ayi mai kiɗan Damalgo)

Sannan waɗanda ke wa sarakuna waƙa suna amfani da kalmomin roƙo ga sarakunan da suke yi wa waƙa kamar yadda mawaƙan fada suke yi a jiya. Misali, Naziru M. Ahmad a waƙarsa da ya yi wa sarkin Kano Muhammad Sunusi na II yana cewa:

Jagora: Da na ji gangunan sun tashi,

: Sai na ƙira Yarima Ingawa,

: Da na ji duniya ta dauke,

: Sai in kira yarima Ingawa,

: Ruwan dala yana min dai-dai,

: Wannan sagin ya nai don dan Lamido

(Waƙar Naziru M Ahmed ta sarkin Kano Sunusi ii)

2.8 Suna da Ƙwaɗayi ga Al'umma:

Makaɗan baka sukan yi wannan ɗabi'a ne a dai-dai lokacin da su ke buƙatar wani abu na musamman kamar abinci ko gona ko muhalli ko kuɗi ko mota ko doki ko wasu abubuwa makamantan haka na son abin duniya. A wannan yanayin sukan shirya waƙoƙinsu ne domin a biya su buƙatun da su ke neman a wajen iyayen gidansu. Misalan waƙoƙin da aka yi a wannan halin na kwaɗayi:

Jagora: Ɗanbayero mai raba kaya,

Ado sarkin yaƙi,

Allah ya bar mana sarki Ado,

Kullum mu fatanmu.

(Abdurrahman Sarkin kotso, waƙar Sarki Ado Bayero)

Jagora: Na Sanda ikon Allah,

Wayyo na Sanda ikon Allah,

Muna da canji um ba na ƴar bakwai ba,

Yana da kyauta sai dai bata da abki.

(Na Ayi mai kiɗan Damalgo)

Jagora: Don samu mu ke waƙa ko can,

In zo yaz zan babu samu,

Sai mu bari, mu huta, mu dakanta,

Tun da kyau ba salati ba ne,

Balle mu dage, mu zan yin shi don gobe.

(Ɗanƙwairo waƙar shirye kayan faɗa mai gidan Tsahe: Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba)

Jagora: In dai ana yi min kyauta,

: Fasali yanzu ba ya ƙarewa.

(Ɗanƙwairo waƙar mai kashe haƙi Ɗan Indo)

Jagora: Kwaɗayi mabuɗin wahala,

: Kwaɗayi majanyin magana,

Kwaɗayi wajen ba da ƙafa, an sha maɗaci a zuma a farga ba ƙuda ya wahala,

Ƴ/Amshi: Maimaici.

Jagora: Wajen zuwa sai ka daɗe ba ko zo ba in ka sha kaya,

Mai shana'a sai ya shige da abin sa kai kana baya,

Su dai kuɗi za a yi ne a barka in kana ɓuya.

Ƴ/Amshi: Ina iyaye a wula kwaɗayi da son ƙarya.

Jagora: In riƙa ɗan ɗaga ƙafa da duniya ana baya,

Shi Rabbana in yai ya ƙagi abin sa ko ana niyya,

Ko ba a so yadda ya so haka zai yi don a je aya,

Haka za mu yi ta son abu,

Sai mu so mu mutu kan abu, amma abin ba alkhairi tun da ba sanin gaibu,

Haka za mu yi ta ƙin abu, mu tsana mu ƙara ƙin abu ne alkhairi garemumu,

Ta godewa, amma rashin sani bai Malam,

Kwaɗayi irin hakan bai ba, rashin haƙuri na ƙaddara bai ba...

(Naziru waƙar Kwaɗayi).

2.9.1 Suna da Yawan Shaye-Shaye da Goyon Bayan Shan Giya

Shaye-shaye dai na nufin amfani da wani abun sha ko sheƙa ko shanshana ko haɗiya da sauran wasu nau'o'i daban-daban waɗanda suke gusar wa mutum da hankali ko ya saka maye ta hanyar sha ko shinshinawa ko ci ko busawa ko kuma allura. A zamanin baya, sai dai mu ji labarin irin wannan dabi'ar a ƙasashen ƙetaren ƙasar Hausa, wasa-wasa wannan mummunar ɗabi'ar har ta shigo cikin ƙasarmu da alummarmu ta Hausawa. Da yawa daga cikin mutane ba su san mene ke jawo wannan dabi'ar ta shaye-shaye ba, ko kuma suna kan hanyar faɗawa shaye-shayen ba tare da sun sani ba.

Dubi wasu ɗiyan waƙa wanda mawaƙin ƴan shaye-shaye ya shirya ta inda yake cewa:

Jagora: Wannan kiɗa, kiɗa na mashaya,

Ai kowane gida akwai ɗan iska sai gidan da babu mutane,

Shaye-shaye ba shi da gori, um ba ka sha ba ɗanka na tsotsawa,

Ko ɗan uwanka na tsotsawa,

Wani ƙanin uban shi ke tsotsowa,

Wani ma uban shi ke tsotsawa,

Ka ga tsoho cikin kwata yai kwance,

Wallahi idan ruwa ya yi ruwa ai babu tangaɗi sai kwance,

Wallahi ɗan giya sarki ne, amma garin da ba ƴan sanda,

Shaye-shaye kala-kala ne Malam ni ba uban da ban gane ba,

Kasan waɗansu ƴan asbin ne,

Kasan waɗansu ƴan landon ne,

Kasan waɗansu ƴan bensin ne,

Wasu rosiman su ke kunnawa,

Kasan waɗansu ƴan madara ne,

Kasan waɗansu ƴan linda ne,

Waɗansu kokwan su ke tsotsawa,

Kasan waɗansu tiramol su ke tsotsawa,

Waɗansu diyaza su ke tsotsawa,

Waɗansu kodin su ke tsotsawa,

Waɗansu wiwi su ke tsotsawa,

Waɗansu kaftin-bilam su ke molawa,

Waɗansu kwata su ke shaƙawa, ni ba uban da ban gane ba.

(Haro mai kiɗan mashaya)

2.9.2 Suna Goyon Bayan Shan Giya

Giya, kalmar suna ce da ke cikin jerin sunaye jinsin mata. Ita kuma nau’i ce da ake yi da hatsi ko alkama ko inibi wadda ake sha a yi maye. Ana kuma kiranta barasa., kamar yadda ƙamusan CNHN (2006 p. 168) ya nuna. Shan giya a tsakanin al’ummar Larabawa kafin bayyanar Musulunci abu ne sananne. Shi ne ƙashin bayan doron ginin tattalin arzikinsu, kuma giya na daga cikin kayan fataucinsu. Har matansu sun kasance shahararru wajen haɗa ta. Hasali ma kowane gida akan same ta. Wannan ya sa har suna yabon giya a cikin waƙoƙinsu.

Su ma al’ummar Hausawa ba a bar su a baya ba, domin sun mayar da shan giya musamman a lokuttan bukukuwan aure da na haihuwa tamkar ƙawa. Yayin da suka samu rabauta na karɓar addinin Musulunci, saisuka guje ta a sakamakon hanin da addinin ya yi gare su. Kasancewar Musulunci addini ne mai sauƙi da ke ƙunshe da dabarun magance abubuwan da ke haifar da fitsara da ta’addanci a tsakanin al’umma, sai ya fara bayyana wa muminai rashin kyanta. Daga nan kuma ya hana kusantar wurin ibada yayin da aka sha ta. Daga ƙarshe ne kuma ya sauƙar da hani kai tsaye game da shan giya inda aka ce:

“Ya ku waɗanda kuka yi imani, ku sani cewa, giya da caca da gumaka da ƙyaurayen duba ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nisance su don ku rabauta (Alƙurani; 5:90).

A wannan ayar an bayyana wa masu Imani munanan ayyuka da ake buƙatar mumini ya nisance su. Kuma duk al’ummar da ta rungume su za ta faɗa cikin masifa da rashin kwanciyar hankali. Ayar ce kuma ta zo da haramcin shan giya kai tsaye. Akwai hadisai da dama da suka tabbatar da haramcin shan giya da kuma abin da ake kira da giya. Annabi (S.A.W) yana cewa: “Duk abin da ke bugarwa giya ce, kuma kowace irin giya haramun ce” (Muslim ne ya ruwaito shi).

A wani hadisin kuwa cewa ya yi: “Allah ya tsine wa giya, da masu shan ta, da waɗanda suka zuba ta, da waɗanda suka sai da ita, da waɗanda suka saye ta, da waɗanda suka tatso ta, da waɗanda suka ɗauki kayan da ake tatsarta, da waɗanda suke ɗauke ta, da waɗanda aka kai wa ita, da waɗanda suka samu kuɗi a gare ta” (Abu Dawuda, da Al-Hakem a isnadi ingantacce, suka kawo shi) Yayin da aka dubi waɗannan nassoshi, za a tarar cewa, ƙin bin su sau-da-ƙafa keta shara’ar Musulunci ne, wato fanɗarewa faɗar Allah da annabinsa ne. Duk da haka, an ci karo da waƙoƙin da suka yi kira da a sha gida. Alhaji Mamman Shata Katsina ya waƙe giya. Har ma cewa ya yi:

Jagora: Ka ji karatun masu bugun ruwa, Waɗanda

‘Y/Amshi: Ke zikiri a Kuloniya.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

Jagora: A nan muke sallarmu ta Juma'a,

Mu tattara kayanmu mu kai Neja,

Ku sha ruwan nan...

‘Y/Amshi: Ba laihi ba ne.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

Jagora: Ruwa na kwalba ba laihi ba ne, Ai kun ga...

‘Y/Amshi: Alhaji Shata sha yake.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

Jagora: Yara mu koma wasa Kuloniya,

Mu tashi kana mu koma Neja,

‘Y/Amshi: Nan ne muke zikirinmu na Juma'a.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

Jagora: Malam ka sha ai ba laihi ba ne,

Ga taka ga tau...

‘Y/Amshi: Kowa ya aje.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

Idan muka nazarci waɗannan ɗiyan waƙar za a ga yadda mawaƙin ya yi fito-na-fito da dokokin Allah da Manzonsa. Allah ya haramta, shi kuma ya halatta. Dubi yadda mawaƙin ya ce a sha giya ba laifi ba ne, bayan Annabi (S.A.W) ya ce kada a sha, a inda yake cewa: “Kada ku haɗa fulawa da dabino gaba ɗaya, kuma kada ku haɗa busasshen tafarnuwa da dabino sam-sam, ku bar su idan an niƙa su.

Yayin da aka niƙa su, nan take suna bugar da wanda ya sha su. Don haka ne Annabi ya umarci masu imani da kada su sha a haɗe yayin da suke niƙe, kamar yadda Munhajul Muslimu Jadawali na uku: Abinci da Abinsha ya nuna. Hasali ma mawaƙin ya bayyana cewa shi ma yana shan giyar tare da yaransa. Akwai hadisai da dama da suka nuna haɗarin Musulmi ya mutu yana shan giya, ko da bai halatta ta ba. To ina ga wanda ya halatta shan ta? Daga cikin ire-iren waɗannan hadisai akwai wanda Ibni Abbas ya ce:

Manzon Allah S.A.W. ya ce: Duk wanda ya mutu yana cikin ɗabi’ar shan giya bai tuba ba, zai tarar da Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki tamkar wanda ya bauta wa gumaka (Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin).

A wata waƙar ta mawaƙin da ake kira Horo/ Horu, an ga baitukan da suka nuna ba laifi ba ne shan giya da ma cin mushe. Mawaƙin na cewa:

Jagora: Arnaaa ku sha giya ku ci mushe,

Aljanna mai rabo zai sama.

A wani wuri kuwa, har ya nuna ma kashi ne

ga mutum ya sha giya ‘yar kaɗan kuma ta

wahalshe shi. Yana cewa:

Jagora: Kowa ya sha giya yai yi amai,

Ba ɗan halas ba ne, shege ne!

Jagora: Su wane ‘yan giyan ƙarya ne,

Shegu, kwalba guda take ka da su (faɗuwa).

2.10 Suna da Yawan Faɗar Baƙaƙen Maganganu ga Jama'a

Zambo da habaici da baƙar magana da shaguɓe da ba’a da arashi da gatse da gugar zana da dungu, kai hatta ma da tumasanci, suna daga cikin maganganun hikima ko azancin magana da wasu Hausawa suke shiryawa ta furucin baki. Hausawa sukan ƙirƙiri maganganun hikima a hulɗoɗin rayuwa a zamantakewa ta dare da ta rana domin hannunka-mai-sanda da yin gargaɗi da jan hankali da tunasarwa da faɗakarwa da neman a yi taka-tsantsan da sauransu (Gusau, S. M. (2011) sh: 14-15).

Kamar yadda bincike ya tsinkayo, zambo da habaici da baƙar magana da baa da barkwanci, azance-azance ne na hikima da sukan tusgo ko kutso ko ratso zubi na wasu matanoni na waƙoƙin baka na Hausa domin hannunka-mai-sanda ko nuni cikin waƙa ko faɗakar da al’umma ko jan kunne ko madangantan waɗannan halaye.

Alal-Misali, Budan Zakka, Makaɗa Buda Ɗantanoma, Argungu ya furta wani ɗa na waƙa inda ya faɗi:

Jagora: Sama ba yaro ba,

: Ba aboki nai ba,

Y/Amshi: Ba sake faɗin an yi,

Jagora: Mamman mai wada yas so,

Y/Amshi: Sarkin ɗibah haushi,

: Gagara Ƙarya Sadauki,

: Jangwarzon Alƙali.

(Waƙar Buda Ɗantanoma ta Sarkin Kabin Argungu Muhammadun Sama (Gusau, S.M. 2008, Sh;234).

A wannan ɗa na waƙa, Buda Ɗantanoma, ya baza himma wajen ayyana wasu fitattun halaye na ƙima da daraja da ƙwato wa jama’a haƙƙoƙinsu da tsayuwa kan gaskiya wofintu daga yin ƙarya na Ubangidansa, Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama. Ƙari a haka kuma, akwai wasu makaɗan baka da sukan kare ko daɗa bunƙasa mutunci da muruwa na Ubangida ta fuskar shirya wa wasu zambo ko habaici domin nuni cikin waƙa.

Dubi wata magana ta hikima cikin ishara da makaɗi Ibrahim Narambaɗa Isa yake gaya wa Sarkin Gobir na Isa, Alhaji Amadu Bawa a wani zance da wasu suka yi maras tushe. Ga kalmomin da ya yi masa nuni da su cikin waƙa:

Jagora: Baban Maiwurno bar su can su yi zancen banza,

Y/Amshi: Mai ga-noma bai yi ƙwazon mai gona ba.

Jagora: Ka ji wai mai roƙo hura ya sha ya shige danga ta,

Y/Amshi: Sai ka ji ya raina mai dame arba don ƙarya,

: Ka san tabbatar tsiya ga matsaci an nan,

: Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa,

: Baban Doda ba a tam ma da batun banza.

(Waƙar Gwarzon Shamaki ta Ibrahim Narambaɗa wadda ya yi wa Sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa (Gusau, S. M. 2008, Sh; 255-256)

A yayin zaman tare, a wasu lokuta, akan sami gilmayya da faruwa na wasu abubuwa kamar damuwa da nuna ƙiyayya ko wata jayayya ko cin dudduge ko wasu ayyuka na wuce gona da iri da ire-irensu. A aukuwar ire-iren waɗannan halaye, makaɗan baka sukan shirya kalmomi a cikin ƙananan saƙonni domin su kiyaye mutunci da baiwoyi na Ubangida ko su yi masa garkuwa ta katangar dutsi ko ta kalmomin ƙarfe irin na kandiri ko kwangiri. Ga wani misali daga wani ɗan waƙa ta ‘Gagara Ƙarya, ta Buda Ɗantanoma Argungu shi ne:

Jagora: Kanta Ubanzagi, Jibo as Sarki,

Y/Amshi: Ba Sarkin ƙaƙe ba,

: Gagara ƙarya sadauki,

: Jangwarzon Alƙali.

A wannan ɗa Buda Ɗantanoma yana yi wa wasu habaici ne masu yawo da wata ƙaramar magana suna nuna Ubangidansa, Muhammadun Sama Argungu, wai ba jarumin Sarki ne ba. A wani ɗan waƙa kuma makaɗa Buda Ɗantanoma Argungu yana kare kansa da kansa inda yake faɗin:

Jagora: Mai nuƙura da Buda Sarkin Turu,

Y/Amshi: Bai san Allah na ba,

: Gagara Ƙarya Sadauki,

: Jangwarzon Alƙali.

(Gusau, S. M. 2008, Sh; 243-247).

Makaɗi Sa’idu Faru ya mutunta wasu tsuntsaye, suda da burtu, ya mayar da su mutane ko makaɗa, kuma suna ta rera wa Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo wani ɗan waƙa na kwarzanta shi da bayyana darajojinsa. Hatta Larabawa ma sun shiga yi wa Sarkin Kudu Macciɗo (Sarkin Musulmi) waƙoƙi masu mutunta shi da fito da darajojin da Allahu ya yi masa. Ga kalmomi na wannan dogon ɗa na waƙa kamar haka:

Jagora (Ɗani) : Nic ce suda waƙa akai,

: Tac ce lallai waƙa nikai,

: Waƙam Muhamman Sarkin Kudu,

: Waƙan nan da Ɗanumma yai mashi,

: Baicin uwat tsuntsaye nike,

: In da kamam Mulki na nikai,

: Da nai mai wasiƙa yai min kiɗi,

: Dannan ni ko sai niw wuce,

: Can nat taɓa yat tafiya kaɗan,

: Sai ni ishe burtu na kiwo,

: Shina ta waƙar Sarkin Kudu,

: Ala Sabbinani ɗan Amadu,

: Allah shi ƙara mai nasara,

: Nic ce burtu waƙa akai,

: Yac ce lallai waƙa nikai,

: Waƙam Muhamman Sarkin Kudu,

: In na yi ta za ni wurin kiwo,

: In na zo abinci sai na rage,

: Sai ni ko sai niw wuce,

: Can na taɓa yat tafiya kaɗan,

: Nik kai bakin bahar Maliya,

: Sai ni ishe Larabawa wurin,

: Suna ta waƙas Sarkin Kudu,

: Rainai ya daɗe Sarkin Kudu,

: Ala Sabbinani ɗan Amadu,

: Allah shi ƙara ma nasara,

: Ɗan mai daraja Sarkin Kudu,

: Jikan mai daraja ɗan Amadu,

: Sannan mai daraja shi yay yi shi,

: Shina gida zanne a Sakkwato,

: In ya yi salla yai tazbaha,

‘Y/Amshi: Hasken nashi han nan kallo mukai,

: Kana shirye Baban ‘Yan’ruwa,

: Na Bello Jikan Ɗanfodiyo.

(Waƙar Saidu Faru ta Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo (Sarkin Kudun Sakkwato a da) Gusau, S. M. (2009) Sh: 155-156).

Kamancin Waƙoƙin Gargajiya Da Na Zamanni

Waƙoƙin gargajiya da na zamani suna da kamanci da juna kamar dai yadda za a gani a nan, kamancin kuwa su ne:

i. Dukkansu suna isar da saƙo.

Isar da saƙo wasu dabaru ne da mawaƙan baka na gargajiya da na zamani su ke amfani da su wajen yaɗa manufofinsu a waƙe ko a rubuce a takan takarda. Ana isar da waƙoƙin ne ta hanyar rerawa mutane a wurare da lokuta ko yanayi daban-daban. Bayan an sadar da waƙoƙin ana kuma ajiye ko adana su ta juya su a na'urori mabanbanta ko a ɗabba'a su. Wasu waƙoƙin saƙon ilmintarwa ke magana wasu kuwa faɗakarwa ko gargaɗi ko yabo ko siyasa ko soyayya da sauransu. Don haka mawaƙan baka na gargajiya da na zamani sun bayar da gudunmuwa sosai wajen taya gwamnati yin yekuwa ga al’umma a kan a rungumi ilimin zamani wato ilimin boko ganin yadda mutanen Arewacin Nijeriya suka yi masa riƙon sakainar kashi, ba kamar yadda mutanen Kudancin Nijeriya suka ɗauke shi ba. A haka ne Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi wata waƙa a kan ilimin zamani mai suna, “Waƙar Ilimi. Tun daga gindin waƙar Ɗanƙwairo ya fara fito da muhimmancin ilimi:

Gindin Waƙa: Farin cikinmu mu sami ilimi,

: ‘Yan makaranta mui ta niyya. (Gusau, 2019)

Wannan gindin Waƙar Ilimi da Ɗanƙwairo ya kawo, yana kira ga yan makaranta da su himmatu su ɗauri niyyar neman ilimin addini da na zamani, saboda ba wani farin cikin da ya wuce samun ilimin addini da na boko a duniya. Ɗanƙwairo ya nuna cewa, da neman ilimin da samunsa duk farin ciki ne ga ɗalibi. Daga nan sai ya ci gaba da kawo ɗiyan waƙa masu jawo hankalin yan makaranta dangane da muhimmancin ilimi. Dubi ɗiyoyin:

Jagora : Kowa ya sami ɗa shi kai makaranta,

Y/Amshi : Don ilimi tushen arziƙi ne.

Jagora : Kowa yah haihi ɗa shi kai makaranta.

Y/ Amshi : Don ilimi tushen arziƙi ne.

: Farin cikinmu mu sami ilimi,

: ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Tun daga duniya hal Lahira,

: Ilimi babban gwaddabe ne,

Y/Amshi : Kwab bi shi ba ya kunya,

Jagora : Ta tabbata kwab bi shi ba ya kunya.

Y/Amshi : Farin cikinmu mu sami ilimi,

: ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Ba a sarauta sai da ilimi,

: Ba a sana’a sai da ilimi,

Y/ Amshi : In ga ilimi ya fi kyawo,

Jagora : Ta tabbata in ga ilimi ya fi kyawo,

Y/Amshi : Farin cikinmu mu sami ilimi,

: ‘Yan makaranta mui ta niyya. (Gusau, 2019.)

Idan aka lura da waɗannan ɗiyoyin waƙa uku, za a ga cewa suna kawo muhimmancin ilimi ga rayuwar ɗan’adam. A ɗan farko, Ɗanƙwaro ya yi kira ga iyayen yara cewa, duk wanda ɗansa ya isa sa wa makaranta, to ya daure ya kai shi makaranta, saboda muhimmancin ilimi na kasancewa tushen arziƙi, wato duk wani arziƙi na duniya da Lahira yana samuwa ne daga ilimi. Idan a duniya ne, bayan ka yi ilimin boko ka kai wani mataki, sai ka sami managarcin aikin gwamnati mai albashi mai tsoka, to duk abin da ka samu na arziƙi, tushensa daga ilimin nan ne. Ko kuma a ce ka yi ilimin aiwatar da wani kasuwanci, wato ka sami fasahar ƙera wani abu, ko dabarun tafiyar da wani kasuwanci, ka sami arziƙi sosai, to idan ka natsu, za ka ga dai asali daga ilimin da ka yi ne.

Dangane da ilimin addini kuma, bayan mutum ya yi shi, zai san yadda zai bauta wa Mahaliccinsa yadda Ya tsara. Idan ya je Lahira Allah zai saka masa da gidan aljanna. Babu mai arziƙi kamar wanda aka gama hisabi ranar Lahira ya sami gidan Aljanna. Kuma shiga aljannar nan da mai ilimi ya yi, tushensa daga ilimin da ya yi ne, shi ne kuma ya ba shi wannan damar. Bugu da ƙari, a ɗan waƙar nan na uku, Ɗanƙwairo ya sake kawo muhimmancin ilimi, inda ya nuna cewa shi ilimi babbar hanya ce da ya kamata bayin Allah su bi domin samun tsira daga wahalhalun duniya da Lahira. Kuma duk wanda ya yi ilimi ba zai ji kunya ba duniya da Lahira. Manufar wannan ɗan waƙa shi ne, babu hanyar rayuwa da ta kamata kowane Ɗanadam ya bi domin gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum kamar ilimi. Ilimi ne kawai zai koya wa Ɗanadam gudanar da rayuwa yadda zai mori zamansa na duniya ya kuma sami rufin asiri daga Mahaliccinsa. Duk wanda talauci ya yi masa kanta a yau duniyar nan, to asirinsa ya tonu. Kuma mai ilimi da wuya ya yi talauci saboda hanyoyin yaƙi da fatara da talaucin da ke tattare da ilimi.

A ɗan waƙar nan na uku da ke sama, yana nuni da cewa sarauta, wato shugabancin mutane a gargajiyance da kuma sana’a duk ba sa yiwuwa sai da ilimi. Da ilimi ne ake sanin matakin jagorancin jama’a har a aza su bisa turba madaidaiciya. Sai shugaba ya san makamar mulki, sannan zai samu biyayya daga mabiyansa, a kuma sami ɗorewar zaman lafiya da yalwar arziƙi. Haka kuma, babu wata sana’ar da za a iya gudanarwa, ba tare da an san yadda za a yi ta ba, kuma a inganta ta. Inji Ɗanƙwairo, ko da za a iya yin sarautar ko sana’ar, sam! Ba za su yi ma wani armashi ba, sai da ilimi. Wato dai mulkin mai ilimi ko sana’arsa sun fi inganci fiye da na jahili. Bayan muhimmancin ilimi, sai kuma Ɗanƙwairo ya kawo koma baya da naƙasu ko illar jahilci wato rashin ilimi. Saurari waɗannan ɗiyoyi:

Jagora : Wanda bai ilimin Ƙurani,

: Sannan ba ilimin boko,

Y/Amshi : Wayo nai bai kammale ba,

: Farin cikinmu mu sami ilimi,

: ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Marar Ilimi ba wayo garai ba,

: Idan ɗan yaro yay yi ilimi,

: Sai ka gane shi cikin dattiɓai,

Y/ Amshi : Dattiɓai na ba shi shawara,

: Don sun san mai hankali ne,

: Farin cikinmu mu sami ilimi

: ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Mai jahilci ba shi gwamna,

: Mai jahilci ba shi Di’o,

: Mai jahilci ba shi Rasdan,

: Mai jahilci bai Uban Ƙasa,

‘Y/Amshi : Balle har ya zamo Kwamanda,

: Farin cikinmu mu sami ilimi,

: ‘Yan makaranta mui ta niyya. (Ɗanƙwairo: Waƙar Ilimi)

Dangane da illar jahilci a waɗannan ɗiyoyi da Ɗanƙwairo ya kawo, za a ga cewa a ɗan farko, mawaƙin na nuna wa alumma illar rashin yin ilimi. Idan mutum bai yi ilimi ba, al’umma tana yi masa kallon maras wayo, ko yana da shi dai kaɗan ne. A ɗa na biyu, ya ƙara jaddada illar rashin ilimi da takan haifar da rashin wayo. Sai kuma ya ƙara da cewa duk jahili bai isa ya zauna tare da manyan mutane ba, balle har su ba shi shawara ta gari wadda za ta ƙare shi a rayuwa. Duk wanda bai yi ilimi ba, dattijai da manyan mutane ba su yarda ya matso kusa da inda suke ba, saboda ba su ɗauke shi mai cikakken hankali ba. Amma wanda ya yi ilimi, sai ya shiga cikin manyansa babu wata matsala, ko da kuwa yana da ƙarancin shekaru saboda ilimin ya ƙara masa girma, daraja da martaba a idanunsu.

A ɗa na uku kuma, mawaƙin ya nuna illar jahilci na yadda yake hana mai shi ya kai ga wasu manyan muƙaman gwamnati na jan ragamar al’umma, kuma muƙaman kowa na so ya kai gare su. Daga cikin waɗannan muƙamai akwai Gwamna da Rasdan da Dio da Uban Ƙasa. Babu yadda za a yi jahili ya riƙe waɗannan muƙamai na gwamnati, sai ya fita daga cikin duhun jahilci.

Bayan haka, Ɗanƙwairo ya kwatanta aikin mai ilimi da jahili, inda ya kawo labarin wasu matafiya, ɗaya yana da ilimin inda za su je, wato ya san wurin. Yayin da ɗayan bai sani ba, wato ya jahilci inda za su je. Ga Ɗanƙwairo da jamaarsa:

Jagora : Sanin hanya ko can ya ɗaram ma sauko,

: Ga wanin nan yai sabkonai na banza,

: Sannan yaɓ ɓace cikin daji,

: Shi ko wanda yas san hanya,

: Sai da safe yaf fita gari,

: Hay ya riga shi inda za su,

: Ya sha ruwa, ya sha hura,

Y/Amshi : Hay ya huta bai taho ba,

: Hay ya huta bai taho ba,

: Ka ga sani yai nashi aiki,

: Farin cikinmu mu sami ilimi,

: ‘Yan makaranta mui ta niyya.

A cikin wannan ɗan waƙa na sama, mawaƙin ya kwatanta tafiyar wanda ya san hanya da wanda bai sani ba. Shi wanda ya san hanyar zuwa wani wuri, idan ya tashi tafiya ba sai ya tsaya tambaye-tambaye ba, saboda haka zai isa da wuri ba tare da ya ɓata lokaci ba. Amma wanda bai san hanya ba, sai ya tambaya idan bai yi hankali ba yana iya ɓacewa a daji kamar yadda wannan mutum da Ɗanƙwairo ya ba da labarinsa a ɗan waƙarsa ya ɓace. To haka ayyukan mai ilimi da jahili suke. Kodayaushe mai ilimi ba ya shan wahalar aiwatar da lamurransa na rayuwa, sai ya yi su cikin nasara da kyau, su yi haske har al’umma ta amfana da su. Amma shi jahili kodayaushe cikin duhu yake, yakan daɗe bai gane yadda lamurran rayuwa suke tafiya ba.

ii. Ana Amfani da su Wajen Nishaɗantarwa

Makaɗan baka na gargajiya da na zamani sukan nishaɗantar da jama'a ta hanyar waƙe don su ji daɗi tare da yi wa rai yayyafi ta bayar da dariya. Yawancin su suna yin waƙoƙinsu ne na ganin dama ko da kyauta ko babu, idan suka nishaɗu sai kawai su fara yin waƙa a lokacin da suka ga dama.

Misalan makaɗan wannan rukunin su ne kamar haka: Dr. Adamu Ɗanmaraya Jos da Alh. Haruna Uji da Mai kuɗi Ɗanduma da Ali Makaho. A wasu lokutan kuma har da ƴan kama da ƴan gambara da ƴan galura da sauransu.

iii. Sukan Zo da Tarihi

Mawakan baka na Hausa da suke yi wa sarakuna waƙoƙi a yau suna amfani da tubalin tarihi wajen gina waƙoƙin sarauta .Misali Amin Ladan Abubukar Alan waka a wakarsa ta Sarkin lafiya, Alhaji Isa Mustafa Agwai yana cewa:

Jagora: Na waigo da tarihin Elkanemi Barno ‘yamfaya,

: Asalin mutan Yamen can Madina na Makiyya,

:Ga asalin Babebari tun daga Yamen har ga Lafiya,

:Jinin Sultan Sa'f Aty sarki na Sana'a a tun jiya,

:Mamman Ali Madu Ahmad jini Isa Agwai mazan jiya,

:Mamman Ali Madu Ahmad jinni Isa Agwai mazan jiya,

:Tun karni na sha bakwai zan bitar talifin mazan jiya,

:Kawo har ishirin da daya zangin Isa Maliya,

Allah kara lafia Isa Mustapha Agwai,

:Mai nasabar gida Ali toron giwa ko na ce giye, :Allah kara lafiya, Allah ƙara lafiya.

(Waƙar Aminu Ala ta Sarkin Lafiya Isah Mutapha Agwai)

iv. Dukkansu Suna da Hawa da Saukar Murya

Hawa shi ne furucin jagora wato kaɗaita. A matsayin 'hawa' jagora zai iya rera saɗara ɗaya ko biyu ko fiye da haka a ɗan waƙa ɗaya, gwargwadon dai yadda yake buƙata.

Sauƙa kuma ita ce furucin ƴan amshi. Sauƙa ta ƙunshi layi ko layukan da ƴan amshi suka rera a ɗan waƙa, amma ban da gindin waƙa da sukan maimaita rera shi.

v. Akan Samu Yabo a Cikinsu

Marigayi Ibrahim Narambada, a cikin wakar Sarkin Gobir na Isa, Amadu na daya mai taken "Amadun Bubakar gwarzon yari dodo na alkali" yana cewa:

"Dokin nan da kabbani

Ko da uban mutum assarki

Iri nai yakan Hausai".

Makadi Maidaji Sabon birni, yana cewa a cikin wakar Sarkin Gobir Umaru na Sabon birni, gwarzon Galadima, ya ci fansa, uban yari babban barga Na bango".

“Zamaninka dan Inna mun yi saibi

mun sha hurar Nono, mun ci kalwa

mun hau dawakayye mun yi zama”.

Makadan fada a yau sukan yabi Basaraken da za su yi wa waka da kalamai na yabawa da jinjina da kuzantawa.Misali Naziru M Ahmad a wakarsa ta "jikan Dabo" yana cewa:-

Jagora: Ka ga maza ka shiga gurbin nema,

:Ka zama kogi da ruwa ai wanka,

:Rai nai ya dade rai ya dade Ado

Bayero :Dan sarki da ruwan alfarma,

:Ka ga kudi masu tukwicin nema,

:Kai da ka taso baka san tsoro ba,

:Karriki mai shi ba a ma wayo ba,

:Kazzama Mahdi masshahurin sarki.

Jagora:Mun ga ado mun ga ado Ado Bayaro,

:Kai dawisu gidan mai dama,

:Ka ga gida ka fa kudi mai dama.

vi. Suna Ilimantarwa

Akwai ilimantarwa a cikin kiɗa da waƙa. Ta hanyar kiɗa da waƙa akan koyi azanci maganganu, Karin magana , iya sarrafa harshe, a wasu lokutan ma da sanin tarihi . Misali, idan aka ɗauki waƙar Alh. Musa Dankwairo Maradun yana bayar da tarihingaruruwa da sunan Sarakunansu da ma sunayen Sarautar garuruwan da ke tsakanin Sakkwato zuwa Kaduna, tun daga Shuni har zuwa Rigachikun, a cikin wakar mai dubun Nasara garnakaki Sardauna.

“Amadu ya zo Hausa, za shi gida nai rannan, Yansanda,

Yandoka da Ministocin Gohe.

Haka in aka lura

da waƙar Aminu Ladan Abubakar ta Duniya

Budurwar wawa yadda yake ilimantar

da mai sauraro game da duniya.

Misali:

Jagora: Ranar da ba tsumi ba dubara,

Ranar da za ni kwanta kushewa.

Duniya budurwar wawa,

Matar mahaukaci ko wawa.

Gidan maras gida mai ƙawa,

Gidan maras rabo ran tsaiwa.

Wa ke biɗar ganin ruɗewa,

Yana ga mai sahun miƙewa.

Mai tara dukiya don ƙawa,

Zato yake ana ɗorewa.

Ruɗi na dukiyar tarawa,

Ta sa shi ya zamanto bawa.

Bawan ciki da bai ƙosawa,

Kullum a ba shi bai turewa.

Kainuwa dashen mai kowa,

Saman ruwa take tohowa.

Gamji sassaƙa da sarewa,

Ba ta hana ka kai tohowa.

Rashin jini rashin tsagawa,

A na zuwa a ke iskewa.

Sarrari wuyar a ƙurewa,

Mai sa mataffiya sarewa.

A kwan a tashi mai gillewa,

A kwana wattaran ba kowa.

Ayau da ni ake damawa,

Ina ta jan zaren saƙawa.

A kwan a tashi na zama gawa,

Koko zaren ya zam tsinkewa.

Duniya fa ba ɗorewa,

Babu wanda zai ɗorewa.

Aminu ɗan Kano ta Kanawa,

Saƙo na zo nake idawa.

Talla nake fa ba hargowa,

Mai hankali kaɗai ka tayawa.

Ga magani a gonar kowa,

Mai izgile ka yi hargowa.

Allah wadan ido gululu,

Idon da babu tsinkayowa.

Da kunnuwan da ke jin sowa,

Fage na gargaɗi ɗoɗewa.

Da sau da ke zuwa ga fasadi,

Ba sa zuwa ga amfanarwa.

Da sautuka da kan furtawa,

Ba furrucin da zai shiryarwa.

Da baituka da kan tsarawa,

Bisa hululu don sheƙewa.

Fiɓe sencery organs dubawa,

Gani da ji da saurarawa.

Shaƙa da ɗanɗanon ganewa,

Da ji na zahirin ganewa.

Dukkansu mai halittar kowa,

Ya yi su don mu zam ganewa.

Mu zam rabe kaloli tsanwa,

Mu bautace shi ba ƙosawa.

Abin bugun gaba gun bawa,

Tsoron Mamallaki mai kowa.

Dukkan abin da yai farawa,

Tabbas gare shi kwai ƙarewa.

Da ka ji alhudusu ta zuwwa,

Sai ka ji alfana'u ƙirewa.

Wannan kaɗai fa ya ishi bawa,

Taku da waiwayen dubawa.

Mai izgili shira shiryawa,

Ba ya zuwa gaba dubawa.

Ina uba a gun duk wawa,

Abu Lahabi ya ƙarewa.

Uban maƙaryata mai kwarwa,

Abdu Salulu ya sheƙewa.

Uba ga jahilai mai tsiwa,

Abu Jahala ya taɓewa.

Ga mutakabbirin Misrawa,

Fir'auna ya yi ya kwantawa.

Ƙaryar Ubangiji mai kowa,

Komai gudu tana iskewa.

Gata kake da shi koko wa?

Nabiyu mursalai ba kowa.

Tun daga Adamu na Hauwa,

Uba na talikai har kowa.

Cikamakon nabi ɗan baiwa,

Wannan da kansa an ƙarewa.

Malla nabiyu ba'adahu kowa,

Mai izzini na ceton kowa.

Wa yar rage abin dubawa,

Wa ke da mattsayi zartarwa.

Allah ka sa mu zam dacewa,

Mu yo gamon katar ran tsaiwa.

vii. Dukkansu Ana Rera Su

Rerawa tana nufin 'kakkarya murya da tausasa ta wajen yin waƙa' (CNHN, 2006: 370). Rerawa a fannin waƙar baka ita ce dabara ta daidaita rauji da kiɗa a furta kalmoni na waƙa. Ana rera waƙoƙin baka na Hausa a cikin ƙungiya inda za a sami jagora da ƴan amshi ko kuma a kaɗaita inda jagora ne kawai zai dinga rera waƙa ba tare da ƴan amshi ba. Ke nan, wasu daga cikin matakai na rera waƙar baka ta ƙungiya su ne ake yi ta hanyar +Ƙungiya+Jagora+Ƴ/Amshi=+Ƙulli+Ƙari+/-Ɗani+/-Zagi+/-Takidi+/-Rakiya/Karɓeɓɓeniya-/+Bayayyeniya+Gindin waƙa+Kiɗa (Gusau, 2008:453).

Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya ƙara bayyana tsarin rerawa a waƙoƙin baka na Hausa na rukuninsa wato rukunin (i) kamar haka:

Ƙulli: Duk makaɗan da at Tsahe na sahe,

: Hab baƙi ha ƴan gidan su duk

Ƙari : Babu mai shirya waƙa kamar tawa.

Takidu:Ƙulli: Duk makaɗan da at Tsahe nai jam'i,

: Hab baƙi na ƴan gidansu duka,

Ƙari: Babu mai ƙulla waƙa kamar tawa,

: Ga makaɗi ya ƙulla waƙatai,

: Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,

: In nak ƙulla waƙa a ƙara man,

Tarbe:Ƙari: Mu haɗu duk azanci gare mu,

: Shin a'a mutum guda za ya radde mu,

: Shirya kayan faɗa Mai gida Tsahe,

: Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.

(Waƙar Ɗanƙwairo ta Ƴandoton Tsahe Aliyu).

Aminu Ladan Abubakar ya yi waƙarsa mai suna Baubawan Burmi, inda ya bi tsarin rerawa ya aiwatar da ita kamar haka:

Gindin waƙa: Baubawan Burmi, X3

: Iye-iye, X3

: Kasassaɓarmu ce kan zaɓan jagora,

: Iye-iye.

Jagora: Allah malikin mulki,

: tutal mulki man tasha'u a kan mulki

Ƴ/Amshi: Iye-iye.

Ita kuma rerawa ta kaɗaita ta ƙunshi+kaɗaita+Jagora-Ƴ/Amshi-Gindin waƙa+Kiɗa=+Ƙulli-Ƙari-Tarbe-Ɗani-Rakiya+/-Takidi-Gindin waƙa+Kiɗa (Gusau, 2008:454).

viii. Dukkansu ana Ƙiransu Waƙa

Masana sun karkasa waƙoƙin Hausa zuwa gida biyu kamar haka:

i. Waƙar baka: Ita ce wadda ake rerata da ka, kuma ake adana ta da ka.

ii. Rubutcciyar waƙa: Waƙa ce da ake rubutata bisa wani tsari na musmaman, sanan a rereta. Yahaya (1997) ya bayyana ma’anar waƙa da cewa “Waƙa maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani sako da ke kunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu”

Mukhtar (2005) ya ce “Rubutacciyar waƙa wata hanya ce ta gabatar da wani saƙo a cikin ƙayyadaddun kalmomi da aka zaɓa waɗanda ake rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin baitoci”.

Sa’id (2002) ya bayyana cewa “Waƙar baka ita ce wadda ake rerawa don jin daɗi, a ajiye ta a ka a kuma yaɗa ta da baka. Rubutacciyar waƙa kuma ita ce wadda aka tsara aka rubuta ta a takarda don karantawa”.

Dangambo (2007) ya na cewa “Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararryar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙaidoji da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogi da ba lallai ne hakan su ke a maganar baka ba”. Sarɓi (2007) ya ce “rubutacciyar waƙa hanya ce ta isarwa ko gabatar da wani saƙo cikin ƙayyadaddun kuma daidaitattun kalmomi da akan rubuta kuma a rera lokacin buƙata.

ix. Dukkansu Ana Tsara Su Bisa ga Tsarin da ya Dace da Su

Waƙoƙin baka na gargajiya da na zamani ana tsara su bisa bin wasu matakai ko yin amfani da kalmomi muhimmai da a iya fito da ma'anar ta. Ga su kamar haka: rerawa da hawa da sauƙar murya da daidaita sautin murya cikin amsa-amon ƙari da rauji da azanci da naƙaltar harshe da hikima da fasaha da kiɗa da karɓi ko amshi da gaɗa da tafi da zabiyanci da saƙo.

Dukkan waɗannan tubala ne na ginin waƙoƙin baka waɗanda idan aka rasa su, to sai dai wani abu, amma ba waƙar baka ba. Sannan kuma rashin wasu daga cikinsu kan raunana waƙoƙin baka su zama lami ba armashi tamkar miya babu gishiri a cikinta.

X. Dukkansu Suna da Sauƙin Isar da Saƙo

Muhammadu Bello Gwaranyo a waƙarsa ta, Jahilci Rigar Ƙaya, ya nuna tun a cikin gindin waƙarsa cewa jahilci tamkar rigar ƙaya yake. Gudun kada rigar ta sa mutum kafin shi ya sa ta, sai Gwaranyo ya ce:

Gindin Waƙa : Jahilci rigar ƙaya ne

:Yara mu je makaranta.

(Muhammadu Bello Gwaranyo: Waƙar Jahilci Rigar Ƙaya)

A cikin wannan gindin waƙa da ke sama, Gwaranyo ya kawo muhimmancin zuwa makaranta ga ɗalibai, wato don su tsira daga saka rigar ƙaya, wadda babu mai son ya saka ta a rayuwa. Haka kuma, makarantar da Gwaranyo yake kira a je, makarantar boko ce da kuma ta Muhammadiya. A wani ɗan waƙa kuma sai ya soki jahilci wato ya kawo irin illolin da jahilci yake kawowa.

Jagora : Wanda bai san nun-‘ara ba,

: Ebisidi bai iya ba,

: Ka tabbata jakin duniya ne.

(Muhammadu Bello Gwaranyo: Waƙar Jahilci RigarƘaya)

Rashin ilimi ko jahilci yana rage ƙima da darjar mutum ya zuwa dabba. Dubi yadda Gwaranyo ya bayyana cewa wanda bai yi ilimi ba, da shi da jakin duniya darajarsu guda. Dangane da illolin jahilci kuma, sai Bello ya siffanta jahilci da rigar ƙaya, rigar da take mai matuƙar ƙunci wajen sakawa (Rambo da Haliru, 2018:449).

xi. Ana Iya Samun Salo da Sarrafa Harshe a Kowace Daga Cikinsu

Sarrafa harshe na nufin dabara ko hanya da ake bi a yi wa harshe ado ko kwalliya domin a isar da saƙo ko manufa. In mawaƙi bai yi amfani da dabarun zaɓo kalmomi ba waɗanda zai gina ko tsara waƙarsa ta kasance mai jawo hankali ba, to akan ce ya yi amfani da lamin salo wato salo mara karsashi. Mawaƙan baka gwanaye ne wajen yin amfani da salon sarrafa harshe ko adon harshe a cikin waƙoƙinsu. Yayin da kuma akan sami wasu jefi-jefi suna yin amfani da lamin salo wajen isar da saƙonsu ga jamaa. Daga cikin dabarun da ake amfani da su don yi wa waƙoƙi na baka ado akwai, kinaya da kamance da jinsarwa da alamtarwa da zayyana da salon hira ko labari da Ƙarangiya da dai sauransu. Waɗannan nau’o’in salon da aka ambata, su za a yi bayani tare da misalai daga cikin waƙoƙin da aka yi. Ga bayanin guda ɗaya nan tare da misalai.

1. Kinaya

Salon kinaya dabara ce ta sakaya ko lulluɓe magana ta zauna a madadin wata maganar wato in an yi kinaya akan nashi ma’anar asali zuwa ga sabuwar ma’ana mai kama da ta asalin don dai a isar da wata manufa. Don ƙarin bayani, duba Yahya, (2001 :59-67) da Gusau, (2003:60).

Mawaƙan baka, gwanaye ne a fagen amfani da salon kinaya cikin waƙoƙinsu. Ga wasu daga cikin misalan kinaya kamar haka:

A. Ya gade gidan Bello,

Riƙa wandara sai Madi,

Manyan maza maƙara magana toron giwa.

B. Ɓauna masha dahi Garba,

Ya ba maƙiya haushi.

C. Rijiyar tsakar daji,

Mai ila ka faɗa,

Turbar bisa sai tsuntsu.

(Salihu Jankiɗi: Abubakar III Ya Gade Gidan Bello)

D. Mai lihiddan faɗa, gimshiƙin shamaki,

Baba shimgin ƙaya,

Mai wuyur ratce.

E. Toron giwa kake mai Garewa Alu,

Ba a hwaɗa ka,

Tilas a kauce ma.

(Musa Ɗanƙwairo: Yandoto Aliyu Shirya Kayan Faɗa)

Rubutacciyar Waƙa (R/W)

F. Kai ne Mu’azu haƙiƙa ka zama Ummaru,

Ka gadi Abdu mu bi ka ɗan Hassani,

Himma riƙa Ɗibgau salamun Makaye,

Shimgi na Gatau kamdaren Usmani,

(Alƙali Haliru Wurno: Yabon Sarkin Musulmi Abubakar III)

Rawar salo a wajen sosa zuciya tana da yawa. Domin haka ba za mu iya fayyace dukkan salailan da rawar ta shafa ba. Sosa zuciya kuwa iri-iri ce kamar yadda aka san cewa haliyya tana da nau’o’i. Saboda haka ba kuskure ne ba idan aka ce salo shi ne musabbabin waƙa ta sosa zuciya. Ga wasu ƙarin misalan

·                     Damo maƙi gudu,

Ba banza ba ɗan Soba

(Wari Mai Zari, Waƙar Sarkin Gobir Yakubu)

·                     Kowa ya gasganta tsohuwatai,

Guguwa ta kashe ƙwarya,

Na ga gyartai ana ta tuma.

(Kurna, Waƙar Bi da Arna na Jekada)

·                     Kwarankwatsa tahi da mai ƙaramin kwana,

·                     A ci ki a kwan rirriƙam mutum za shi garin kewa,

Ya zamni gabas da yamma kai az zakara,

Zamfara ba wani mai ja ma.

(Sa'idu Faru, Waƙar Gwarzon Giwa na Shamaki)

xii. Dukkaninsu Suna Iya Tarayya a Jigogi Ɗaya

Jigon waƙa, masana da dama kamar Yahya (1997), ya bayyana ma'anar jigo a matsayin wani abu wanda ke nufin saƙo ko manufa ko bayani ko ruhin da waƙa ƙunsa, wanda kuma shi ne abin da waƙar ke son isarwa ga mai sauraro ko rubutu ko nazari. Ɗangmbo (2007), cewa ya yi 'abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo, manufa, ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da waƙar take magana a kai. Ɗangambo na ganin za a fi fahimtar da jigo ne ta hanyoyi guda uku (3) wato ta hanyar furucin gundarin jigo/ƙwayar jigo ko jawabin jigo da jigo a gajarce da kuma warwarar jigo da shimfiɗarsa.

Shi kuwa Gusau (1993), ya bayyana jigo ne a matsayin abin da waƙa take magana a kansa tun daga farkonta har zuwa ƙarshe. Wato dai ainahin manufar waƙa, ko kuma zaren tunanin makaɗi ko mawaƙi. Misalan jigon waƙoƙin ta'aziyya.

Jagora (Ƙulli): A zamanin rashin Murtala,

: Nijeriyan tamu,

: Har tai kwana bakwai,

: Har ma ƙasashen waje,

: Ai su ma sun sauƙe tuta,

: Tuta tasu kwana ukku,

: A ƙasa, martabar Janar Murtala,

Ƴ/Amshi: Allah jiƙan Janar Murtala.

(Waƙar Abdu Karen Gusau ta ta'aziyyar Murtala).

Shi kuwa Alh. Mamman Shata Katsina ya yi wa Habibu Fari waƙar ta'aziyya inda yace"

Jagora: Allah ya jiƙan Habibu Fari

Allah ya gafarta wa Habibu Fari X2

Allan da ya kawo Habibu Fari,

Ya ɗauki abinsa kai ku ji wai.

(Waƙar Shata ta ta'aziyyar Habibu Fari).

Garba Gasuwa wanda ya rubuta waƙar ta'aziyya ga abin da yace"

Jagora: Allah ya jiƙan maza na jiya,

Sun bar mu cikin ɗakin duniya,

Su sunka tafi da tarbiyya,

Kan hanya kuma babu kaya,

Ba su yarda mu keta tsidau ba.

(Garba Gasuwa, waƙar APP, bt na 61).

Shi ma Aminu Ladan Abubakar ya yi wa Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero waƙar ta'aziyya inda yake cewa:

Jagora: Sa'i ne ya yi, rabuwa da masoyi Ado Bayero,

Za mu kai shi kushewa,

Mai tagwayen masu Ado Bayero hamshaɗin Sarki,

Lamarin mutuwarka ya da ɗa duka yo mulkin banza ba,

Bankwana da masoyi Ado Bayero sa'i nai ya yi,

Rabuwa da masoyi Ado Bayero za mu kai shi kushewa,

(Ala, waƙar ta'aziyyar Sarki Ado Bayero)

Waƙoƙin Yabo:

Jagora: Ka ga masu umarni da hani bisa sha'anin Allah X2

Ɗan Datti dattijo Abdulƙadir Furofesa,

Yau gida na malumta na taho zana yi wa ƙa'ida,

Yau jinin Sarakai zan waƙe a rubuce na shida,

Bahari na taso na yi wa rabo masanin al'ada,

Bahari na fannonin adabi na gama da al'ada,

Ɗan Abdulƙadir, Abdulƙadir ku min shaida.

(Aminu Ala, waƙar yabon Furofesa Ɗandatti Abdulƙadir)

Aminu Ladan Abubakar ya sake yi wa Furofesa Sa'idu Muhammad Gusau inda yake cewa"

Jagora: Ga ka Furofesa, ga ka katibi kan adabi,

Sannu Furofesa Sa'idu ɗan Muhammadu na Gusau,

Ƴ/Amshi: Maimaitawa,

Jagora: Maimaitawa,

Jagora: Rabbi na gode da dubin basira da ka ban,

Kuma na gode da tulin basira da ka zuban,

Falalar Allah da ka bani a watan Sha'aban,

Ka riƙe mini ita ka yo zan ta zam nai rusau,

(Alan waƙa, waƙar yabon Furofesa Sa'idu Muhammad Gusau).

Bambancin Waƙoƙin Gargajiya Da Na Zamani

Duk da cewa waƙoƙin gargajiya da na zamani suna da kamanci, haka kuma akwai inda suka bambanta kamar dai yadda za a gani a nan:

i. Waƙar gargajiya tana da kiɗa, amma ita rubutacciya ba ta da kiɗa.

Zarruƙ, Kafin Hausa da Al-Hassan (1987), sun wassafa kiɗa a matsayin: “Wanzar da daddaɗan amo daga abubuwan bugawa, ko na gogawa ko na busawa ko kuma na girgizawa.” Ita kuma waƙar baka rubutacciya, kamar yadda Ɗangambo (1981) ya bayyana ta da cewa " wani saƙo ne da aka gina kan tsararriyar ƙa'ida ta baiti, dango, rairawa, kari (bahari) amsa amsa amo (ƙafiya) da sauran ƙa'idojin da suka shafi daidaita kalmomomi, zubinsu da amafani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a magana ba"

ii. Waƙar gargajiya tana da ƴan amshi, yayin da rubutacciya ba ta buƙatar ƴan amshi.

iii. Waƙar gargajiya ana iya gadonta, amma ita rubutacciya sai wanda yake da ilimin yinta.

iv. Waƙar gargajiya tana tafiya da sauti, rubutacciya kuma ƙafiya ne take tafiya da shi.

v. Waƙar gargajiya ɗiya gareta, amma ita rubutacciya baiti ne take da shi.

vi. Waƙar gargajiya tana da yawan maimaici don amfanin abin da aka fada, yayin da a rubutacciya ba a maimaita abin da aka fada komai faidarsa.

vii. Waƙar gargajiya ana amfani da ita don a samu kuɗi, yayin da rubutacciya saƙo ne kawai aka fi mayar da hankali a kansa.

viii. Waƙar gargajiya ana yinta a dandali, amma ita rubutacciya ba a yinta a dandali.

ix. Zubi da tsarin waƙoƙin yana bambanta da juna.

Waɗannan su ne wasu daga cikin bambance-bambancen da ke samu a tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani.

Amfani Da Muhimmancin Waƙa

Masu iya magana kan ce “Ko kare yana da ranarsa” to in haka ne ballantana wannan al’amari da muka saka a gaba wato fagen ilimi. Idan muka dubi irin rawar da waƙa take takawa a fagen yaɗa addinin musulunci tanan ma zamu mu fahimci cewa waƙa tana da gagarumin amfani ga alummar Hausawa musamman ta wajen adanawa da bunƙasa rumbunsu na kalmomi da aladunsu. Misali manyan mashahuran malamai irin su Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da ƙannensa Abdullahin Gwandu da ɗansa Muhammadu Bello da ‘Yarsa Nana Asma’u da almajiransa dukansu sun yi amfani da waƙa wajen yaɗa addinin Musulunci. Ko bayan su kuma muna ittifaƙin cewa, kaɗan daga cikin muhimmancin waƙa sun haɗa da:

i. Sauƙin jawo hankali: wato ta hanyar waƙa ne akan samu sauƙin jawo hankalin masu sauraro ko mai son su koyi wani abu na daban.

ii. Nishaɗantarwa: Ta hanyar waƙa mutum ko mutane sukan samu walwala su ji nishaɗi kuma su ji an kawar masu da damuwa a zukatansu da farantawa wanda aka yi waƙar ya ji daɗi, ya kuma bayar da kyauta ko wani abin duniya nan take. Farfesa Ɗangambo A. (1984) ya ce" wannan aji na ban-dariya, babban aji ne, domin kuwa ya ƙunshi duk wasu kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe waɗanda suka ƙunshi raha da nishaɗi da kuma bayar da dariya.

iii. Samun Sauƙin shiga kai: Idan mutum yana bukatar sakonsa ya yi saurin karbuwa ga jamaa yakan yi amfani da waka saboda ta fi saurin shiga kai. Misali dubi yara yan makaranta za ka ga sun fi rike duk wani abu da aka koya masu da waka.

iv. Waƙa tana ɗebekewa: Waƙa kan taimaka ainun wajen cire kewar wani abu, musamman na ɓacin rai. Da zarar mutum ya nishaɗantu da jin waƙa sai ɓacin ran da yake fama da shi ya gushe a jikinsa.

v. Ƙarfafa Gwiwa: Daga cikin amfanin waƙa da akwai ƙarfafa gwiwa. Misali idan muka ɗauƙi rukunin makaɗan maza, sukan yi kiɗansu da waƙarsu ne domin zaburar da gwarzon da suke yi wa waƙa, su zuga shi ya ƙara dagewa wajen fafatawa da abokan wasa musamman a wasan dambe ko kokawa. Dubi yadda makaɗi Muhammad Bawa Ɗan Anace yake zuga Duna inda yake cewa" Ba a wa mutum takakka Wandara kai kaɗai ke wa mutum takakka, in ka so ka ko buge shi ka dawo".

vi. Ilmintarwa: Da akwai ilmantarwa sosai a cikin waƙa. Ta haka ne a kan yi koyi azancin maganganu, karin magana, iya sarrafa harshe, a wasu lokutan ma da adana tarihi. Misali idan aka dubi waƙar Musa Ɗanƙwairo ta Sarkin Daura Alhaji (Dr) Muhammad Bashari. Wacce a cikinta ya bayyana asalin Hausa bakwai a tarihince.

Haka zalika Makaɗi Adamu Ɗan Maraya Jos a cikin wata waƙarsa da ya yi ta" Daura Buduruwar Wawa yake ilmantar da masu sauraro game da Duniya.

vii. Samar da aikin yi: Waƙa sana'a ce, saboda haka tana samar da ayyukan yi ga masu yin ta domin samun na masarufi don biyan buƙatun yau da kullum.

viii. Waƙa babbar hajace ga ƴan kasuwa da masu sana'o'i daban-daban.

ix. Waƙa hanya ce ta jawo ra'ayin al'umma a lokutan siyasa domin zaɓen wasu ƴan takara. Mawaƙan baka na da babban gurbi wurin tallata ƴan takara ta hanyar kurara su da fito da ayyukansu na alkhairi da halayensu nagari tare da kushe abokan takararsu a waƙe.

x. Waƙa hanya take inganta rayuwar al'umma ta fannin ilmantar da su, wa'azantarwa, faɗakarwa, gargaɗi da wayar da kan jama'a da hannunka mai sanda da sauransu.

xi. Babbar hanya ce da al'umma za su iya bayyana kukansu ga gwamnati ko wata majiya a matsayin ƙungiya ko ɗaiɗaikun jama'a.

4.8 Taƙaitawa

Wannan binciken ya shafi makaɗin baka da na zamani wato Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Aminu Ladan Abubakar, babu shakka wannan aikin bincike ne mai matuƙar faɗin gaske, amma an bi wasu hanyoyi mabanbanta wajen gudanar da shi sannan bincike ne da yake da matuƙar wahala domin kuwa, ɗaya daga cikin waɗanda aka binciko bayanan akansa ya rasu, amma duk da haka an yi iya bakin ƙoƙarin aiwatar da wannan aikin gina kundin ta hanyoyi da yawa waɗanda suka taimaka wajen aiwatar da wannan gina kundin kamar ziyartar ɗakunan karatun na makarantun gaba da na Sikandire da sauraron wasu daga cikin waƙoƙin baka na gargajiya da na zamani musamman na sarauta na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na gama-gari na Aminu Ladan Abubakar, an zaƙulo wasu bayanan a shafin yanar zigo masu alaƙa da wannan binciken daga ƙarshe kuma an yi tambayoyin baka da baka ga dattijai da matasa da ɗalibai masu sha'awar sauraron waƙoƙin baka na Hausa.

4.9 Sakamakon Bincike

Biyo bayan zurfafa binciken da aka yi, an samo ma'anar ire-iren waƙoƙin baka na Hausa da tarihin samuwar su a ƙasar Hausa sannan aka bi diddigin samo wa bayanan tarihin rayuwar Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maraɗun da ta Aminu Ladan Abubakar, Alan waƙa tare da gudummawa da kuma ci gaban da su ka bayar a fuskar adabi don inganta rayuwar Malam Bahaushe. An leƙa ciki kuma an zayyano kamanci da bambanci da suke tsakanin waƙoƙin baka na gargajiya da na zamani tare da bayanansu. Ta la’akari da nassoshin Alƙurani da Hadisan Annabi (S.A.W) da kuma ƙumshiyar halayen wasu waƙoƙin makaɗan baka kyawawa wanda ake so da munana wanda ake ƙi na makaɗan baka na Hausa, za a a iya cewa, mawaƙa na wuce gona da iri a waɗansu lokuta. Yawanci hakan na faruwa ne yayin da suka yi ƙoƙarin adanta waƙoƙin nasu domin burge wanda aka yi wa waƙar da kuma sauran masu sauraro. A haka ake samu ɗiyan waƙoƙin sun yi wa dokokin Musulunci karan-tsaye.

A wannan nazarin an fahimci cewa duk wani aikin da ɗan’adam ya aikata wanda Allah da manzonsa suka yi hani da shi, yin haka nau’i ne na fanɗare wa dokokin Allah. Ya zama tilas kowane Musulmi ya nemi ilimin duk wani lamarin da ya shafi rayuwarsa, (kamar yadda mai Ahalari ya bayyana) don gudun auka wa fushin Ubangiji. An kuma fahimci cewa, a Musulunci kowane irin al’amari an ɗora shi a kan mataki-mataki. Wannan ne ya wajabta wa kowane Musulmi ya yi umurni da aikata alheri da kuma hani ga mummunan aiki gwargwadon ƙarfin ikon mutun.

Waƙoƙin Hausa

Post a Comment

0 Comments