Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari a Kan Bambance-Bambancen Da Ke Tsakanin Wakokin Gargajiya Da Na Zamani, Bincike Na Musamman Na Wakokin Sarauta Na Alhaji Musa Danƙwairo Da Na Gama-Gari Na Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) – 3 Babi Na Biyu

ƘUNSHIYA

1. Shafukan Farko

2. Babi Na Ɗaya

3. Babi Na Biyu

4. Babi Na Uku

5. Babi Na Huɗu

6. Babi Na Biyar

Wannan kundin binciken an samar da shi ne domin samun shaidar takardar karatun digiri na farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Tsangayar Karatun Digiri, Kwalejin Ilmi Da Ke Gumel, Kulawar Jami'ar Bayero, Kano.

NAZARI A KAN BAMBANCE-BAMBANCEN DA KE TSAKANIN WAƘOƘIN GARGAJIYA DA NA ZAMANI, BINCIKE NA MUSAMMAN NA WAƘOƘIN SARAUTA NA ALHAJI MUSA ƊANƘWAIRO DA NA GAMA-GARI NA AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA)

NA

ISAH MUHAMMAD KAWU

Lambar Waya: 07047484384

BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 Gabatarwa

Waiwaye adon tafiya. Masu iya magana suna cewa ‘tuna baya shi ne roƙo. Wannan babi zai yi bayani ne a kan ayyukan da suka gabata. An yi ƙoƙarin duba ayyukan da masu alaƙa da wannan binciken. Domin Hausawa na cewa "idan ka bi wanda ya fi ka kai ma dole a bi ka". Don haka wannan waiwaye zai shafi ayyuka masu alaƙa da wannan binciken kawai, amma wannan alaƙa za ta iya zama ta kusa ko ta nesa. Abu ne mai muhimmanci ƙwarai da gaske a duba wasu ayyuka da suka gabata masu alaƙa ta kurkusa ko da ta nesa. Domin masu hikima sun ce "na gaba idon na baya" Yin hakan zai bada damar samun makamar inda kowane aiki ya sa gaba da kuma matsayinsa a wannan fage na ilimi.

Gaskiyar masu hikima da ke cewa 'abin da babba ya hango daga zaune yaro ko ya hau sama ba zai hango shi ba'. Wannan zance haka yake, duk wani abin da mutum zai gudanar idan har yana buƙatar cin nasara, to akwai buƙatar ya duba tafarkin da masana suka bi dangane da wannan abu. A wajen gudanar da wannan binciken an duba ayyukkan da suka gabata waɗanda suka yi magana a kan waƙa. Za a duba kundayen binciken ɗaliban ilmi na neman digiri na daya da na neman digiri na biyu da kuma na uku, sannan sai aka duba rubutattun littafai na masana musamman waɗanda su ke koyarwa a Jami'o'i daban-daban a faɗin Nijeriya tare duba da muƙalu da mujallu waɗanda masana suka gabatar a tarukan ƙarawa juna sani da kuma yaɗa labarun sashen Hausa.

2.1 Kundayen Bincike

Akwai ayyuka da dama da ɗaliban ilmi suka yi a mabambantan jami'o'i da aka yi masu nasaba da wannan bincike. Daga cikin wadanda suka zo hannu akwai na:

DIGIRI NA FARKO

Abazarri (2008). A kundin binciken neman digiri na ɗaya. Ya bayyana tarihin rayuwar Aminu Ladan Abubakar da waƙoƙinsa da yadda yake tsara waƙoƙinsa da ire-iren waƙoƙinsa da yanayin waƙoƙinsa. Bayan nan kuma ya kwantanta waƙoƙin Ala da na mandiri, har ila yau ya kwatanta waƙoƙinsa da na ƴan fim, ya kuma nuna yadda za a nazarci waƙoƙin.Wannan aikin yana da alaƙa da nawa binciken saboda duka suna magana akan waƙa, sai dai kuma bambancin nasa aikin da nawa shi ne, shi ya karkata ne ga waƙoƙin zamani na Aminu Ladan Abubakar sai ce komai ba a kan waƙar gargajiya. Ni kuma ina yin nazari ne a kan bambance-bambancen da ake samu a tsakanin waƙoƙin gargajiya na sarauta da na zamani.

Buhari (2010). A kundin digiri na ɗaya da ya yi mai taken "Sarkin Zazzau Aminu. A cikin aikin nasa ya bayar da tarihin sarki Zazzau Aminu. Ya kawo wasu daga cikin makaɗan fada irin su: Jankiɗi da Narambaɗa da Alhaji Musa Ɗanƙwairo da sauransu. Wannan bincike nasa yana da rawar da zai taka a nawa nazarin. Sai dai aikin nasa kuma a kan waƙoƙin baka na sarauta ne kawai, ni kuma a kan waƙoƙin sarauta da na gama-gari nake nazarta.

Gatari (2010). A kundinsa na kammala digirin farko wanda ya rubuta mai taken “Jigon yabo a waƙoƙin Mahammadu Shata wannan ɗalibi ya karkasa aikinsa zuwa babi biyar, a babi na ɗaya ya yi gabatarwa ta aikinsa a babi na biyu ya kawo taƙaitaccen tarihin Muhammadu Shata, ya kayan aikinsa da yawace-yawacensa. A babi na uku ya kawo maanar jigo da ire-iren jigo, ya kuma kawo jigon yabo a waƙoƙi na Muhammadu Shata, manazarcin ya kawo yabo da asali, yabo kan addini, sannan da jigon zuga. A babi na huɗu ya kawo ire-iren yabo inda ya kawo yabo da kyauta, yabo da jarunta, da dai sauransu. A babi na biyar kuwa a nan ne ya kammala aikinsa ya zuba manazarta tare da ratayen waƙoƙin da ya yi aiki a kan su.

Wannan kundin yana da alaƙa da nawa aikin saboda dukansu suna magana ne a kan nazarin waƙoƙi ne, sai dai inda na bambanta da na shi aikin shi ne, shi yana kallon yabo a cikin waƙar baka ne na Mamman Shata ni kuma ina nazari ne a kan bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da shi da Aminu Ladan Abubakar.

Sule (2011). Ya yi bayani a cikin kundin digirinsa na ɗaya da ya yi, wanda ya yi batutuwa a kan Alhaji Musa Ɗankwairo da ire-iren waƙoƙinsa; waƙoƙin fada da waƙoƙin noma da na jama'a da waƙoƙin ta'aziya da waƙoƙin siyasa. Bisa la'akari da cewa wannan bincike ya ginu ne a kan waƙa, kuma a cikin binciken nasa ya taɓo waƙoƙin sarauta inda Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya ƙware. Dangane da haka wannan nazari nasa yana da alaƙa da nawa, ta fuskoki da dama saboda ya yi magana ne a kan waƙa kuma ta Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Amma sai dai shi aikin nasa ya karkata ne kawai ga waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo, ni kuma ina yin nazari ne a kan waƙoƙin gargajiya na sarauta da na gama-gari na zamani.

Talatu (2012). Ita ma a kundinta na neman digin farko da ta gabatar mai taken "Waƙoƙin siyasa, a Jamiar Ahmadu Bello Zaria. Ta kawo maanar waƙa da waƙoƙin siyasa na jam'iyyar PDP. Wannan kundin yana da muhimmanci da kuma alaƙa ta kusa da nawa 4binken, saboda duka suna magana ne a kan waƙa, sai dai ni inda na bambanta da nata binciken shi ne, ita gina shi ne kan waƙoƙin siyasa ne kawai, ni kuma ina yin nazari ne a kan bambance-bambancen da su ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani.

Shi ma Muhammad (2012). A kundin neman digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Ya yi aikin binciken nasa mai taken "Salisu Jankiɗi da waƙoƙinsa". Ya ba da tarihin Salisu Jankiɗi da wasu daga cikin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa da jigon waƙoƙinsa.Ya kuma kawo maanar waƙa. Wannan kundi yana da nasaba sosai da nawa binciken saboda dukansu suna magana ne a kan waƙa, amma sai dai shi nasa aikin ya karkata ne a kan mawaƙi Salisu Jankiɗi da waƙoƙinsa, ni kuma a nan zan karkata ne a kan wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Aminu Ladan Abubakar.

DIGIRI NA BIYU

Mashi (1986). A kundin digirinsa na biyu, ya yi bayanin ma’anar waƙa da tarihinta da rabe-rabenta, haka kuma ya kawo maanar siyasa da manufofinta, da kuma tarihin kafuwar siyasa a ƙasar Hausa. Har wa yau kuma a cikin kundin bincike ya yi bayanin sigogi da rabe-raben waƙoƙin siyasa da kuma matsayin makaɗan baka a cikin siyasar jam’iyya. Sannnan kuma ya yi sharhin wasu waƙoƙin jamiyyun NPC da NEPU da kuma PRP. Wannan bincike da nawa suna da alaƙa domin duk suna magana ne a kan waƙoƙin Hausa, amma sai dai bambancin nasa da nawa aikin shi ne, nasa aikin bincike ne a kan waƙoƙin baka na siyasa na janhuriya ta ɗaya da ta biyu. Ni kuma nawa aikin ina yin nazarin bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin sarautar gargajiya da ta zamani na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na Aminu Ladan Abubakar.

Garba (1998). A aikinsa mai taken "Azancin Magana a Waƙoƙin Baka" Kundin digirinsa na biyu a Sashen koyar da Harsunan Nijeriya na Jami'ar Bayero Kano. Wannan aikin yana da alaƙa da nawa saboda dukansu suna yin magana ne a kan waƙa, amma sai dai nasa aikin ya bambanta da nawa shi ne, shi ya karkata ne ga azancin maganganu a cikin waƙoƙin baka, ni kuma nawa aikin na karkata ne ga nazarin bambance-bambancen da ake samu a waƙoƙin gargajiya da na zamani na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Aminu Ladan Abubakar.

Ibrahim (2000). A aikin kammala digirinsa na biyu mai taken " Wasanni da waƙoƙin Yara Mata, a Sashen koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato. Wannan aikin ya dace da nawa aikin saboda dukansu sun ƙunshi waƙa, sai dai bambancin nasa aikin da nawa aikin a nan shi ne, shi ya yi magana ne a kan wasanni da waƙoƙin yara mata kawai, ni kuma a nan ina yin nazari ne a kan wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na Aminu Ladan Abubakar.

Ɗangulbi (2003). A cikin kundin digirinsa na biyu ya yi bayanin tarihin kafuwar siyasa a Nijeriya. Kuma ya yi bayanin wasu jigogin waƙoƙin siyasa na janhurira ta huɗu, kamar jigon faɗakarwa, da jigon yabo da jigon zambo da habaici da sauransu. Haka kuma ya dubi waƙoƙin inda ya fito da siffantawa, da kinaya, da alamtarwa da dabbantarwa da abuntarwa, a cikin wasu waƙoƙin janhuriya ta huɗu. Sannan kuma ya yi sharhin wasu waƙoƙin jamiyyun ANPP da PDP. Wannan aiki nasa yana da alaƙa da nawa aikin, domin duk suna magana ne a kan waƙoƙi. Sai dai bambancin aikinsa da nawa shi ne, shi ya kalli rubutattun waƙoƙin siyasa daban-daban ya yi nazarinsu. Ni kuwa aikina ya keɓanta ne ga waƙoƙin sarautar gargajiya na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da kuma na zamana na Aminu Ladan Abubakar.

Sayinna (2003). Ya kammala kundinsa mai take "Yabo gonar makaɗi" ya bayar da abubuwan da ake yabon mutum da su, da matsayin yabo a adabin Hausa da dangantakar yabo da ƙirari. Kuma ya bada ma'anar Zambo da Habaici da dalilin da ke sa a yi su. Saboda haka, wannan bincike yana da alaƙa sosai da nawa binciken saboda a kan waƙa ne aka gudanar da shi, amma da akwai bambancin da ke tsakanin bincikena da nasa ta inda ya kalli yabo da habaici tare abubuwan da suka ƙunshe su. Ni kuma bincikena ya karkata ne kacokan a kan bambancen waƙar sarautar gargajiya ta Alhaji Musa Ɗanƙwairo da ta gama-gari ta zamani ta Aminu Ladan Abubakar.

Maru (2008). A cikin aikinsa mai taken "Alhaji Ɗankurma Maru da Waƙoƙinsa" wanda ya yi a kundin bincike na digiri na biyu a Sashen koyar da Harsunan Nijeriya a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria. Wannan aikin nasa ya dace da nawa aikin saboda ya ƙunshi waƙa. Ni ma daman a nawa aikin zan yi magana ne a kan waƙa, amma sai dai shi aikin nasa ya karkata ne a kan waƙoƙin Alhaji Abdu Ɗankurma kawai, ni kuma ina yin nazari ne a kan bambance-bambancen a kan waƙoƙin gargajiya da na zamani na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Aminu Ladan Abubakar.

Muhammad (2015). Ya gina kundinsa mai taken "Waƙoƙin Baka na Gargajiya a". Ya bada maanonin waƙar baka da salon waƙar baka da kuma tsarinta. Inda ya yi cikekken sharhi a kan jerin sarƙe a waƙoƙin baka. Babu shakka wannan kundi yana da nasaba da nawa, duk da kasancewarsa a kan waƙokin baka aka yi shi, amma sai shi ya karkata ne a kan waƙoƙin baka na gargajiya ne, ni kuma ina yin bincike ne a kan waƙoƙin sarautar gargajiya da waƙar zamani na gama-gari.

Rabi'u (2018). A kundin bincikensa a Sashen koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato. A cikin aikin da ya yi mai taken "Nazarin Salo a cikin wasu waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo Muradun. Wannan aikin nasa yana da nasaba da nawa saboda dukansu suna magana ne a kan waƙa, sai dai ta inda ya bambanta da nawa aikin shi ne, shi ya yi magana ne a kan nazarin salo a cikin wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun bai ce komai ba a kan waƙoƙin zamani na Aminu Ladan Abubakar ba, ni kuma a nan ina yin nazari ne kacokan a kan bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin sarauta na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na gama-gari na Aminu Ladan Abubakar.

DIGIRI NA UKU

Isma'il (1985). Ya rubuta kundinsa a kan "Waƙoƙin Fada". Inda ya fara da ma'anar fada da kuma abin da waƙoƙin makaɗan fadar suka ƙunsa. Makaɗan sun hada: Buda Ɗantanoma da Ibrahim Narambaɗa da rayuwarsu da ayyukkasu.Da kuma zababbun makaɗan fada na zamani a wancan lokacin waɗanda suka hada Musa Ɗankwairo da Sa'idu faru.Wannan bincike yana da alaƙa da nawa,domin ya yi magana ne akan waƙa, kamar yadda ni ma nake nazari a kan waƙa.Sai dai nasa aikin ya karkata ne a kan waƙar baka da mawaƙa fada kawai,nawa kuma ina yin nazari ne a kan bambance-bambancen da suke tsakanin waƙoƙin sarautar gargajiya da na zamani na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na Aminu Ladan Abubakar.

Bunguɗu (2013). A kundin bincikensa na digiri na uku a Sashen koyar da Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato. A cikinsa mai taken " Waƙoƙi a Matsayin Bara a yankin Zamfara". Wannan aikin yana da dangantaka da nawa saboda dukansu suna magana ne a kan waƙa, amma sai dai shi aikin nasa ya karkata ne ga waƙoƙi a matsayin bara a yankin jahar Zamfara, ni kuma ina bincike ne a kan waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na Aminu Ladan Abubakar.

Abdullahi (2016). A aikin bincikensa mai taken "Waƙoƙin siyasa". Inda da farko ya fara kawo ma’anar waƙa sannan ya yi taƙaiccen bayani kan waƙoƙin siyasa.Wannan bincike nasa yana da alaƙa da nazarin da nake gudanarwa, domin ya yi shi ne a kan waƙa ya kuma taɓo waƙoƙin siyasa.Amma sai dai ta inda nasa binciken ya bambanta da nawa shi ne, shi ya gina bincikensa ne a kan waƙoƙin siyasa. Ni kuma ina yin nazari ne a kan bambance-bambancen da ake samu a waƙoƙin sarautar gargajiya da na zamani.

2.2 Bugaggun Littattafai

Masana da dama sun wallafa littafai masu alaƙa da wannan nazari. Daga cikin littafan da suka zo hannu akwai:

Bunza (2017). Ya yi bayani cikakke wanda zai iya zama jagora ga duk wani mai gudanar da bincike na neman digin farko da na biyu da mai Phd wato digirin digirgir na uku, kai har ma da duk wani mai gudanar da bincike a fagen ilimi. Ya yi bayani a kan bitar ayyukan da suka gabata da sauran fannonin da suka shafi bincike musamman ta fuskar adabi. Wannan littafi ya zama turba ko in ce ya share man fagen binkena tare da zama jigo ko fitila mai haska man hanyar gudanar da wannan nazari. Haƙiƙa Hausawa sun yi gaskiya da suka ce "Tafiya da babba daɗin yaro" wannan littafi ya ba ni gudummuwa sosai wajen gudanar da wannan aiki.

Sipikin (1978). A littafin da ya rubuta mai suna mai taken "Ma'aunin Waƙar Hausa" Studies In Hausa Language, Literature And Culture. Bayero University, Kano. Wannan littafin ya yi daidai da nawa aikin saboda ya ƙunshi waƙa, ni ma kuma zan yi magana ne a kan waƙa, sai dai shi ya karkata ne a kan ma'aunin waƙar Hausa, ni kuma zan yi nazari ne a kan bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Aminu Ladan Abubakar.

Ɗanjuma (1982). A littafin da ya wallafa mai taken "Rabe-raben Waƙoƙin Hausa da Tasirinsu ga Rayuwar Hausawa. Jami'ar Bayero, Kano: bugawar kamfani Triumph Publishing Company. Wannan aikin yana da nasaba da nawa saboda dukansu sun ƙunshi waƙa ne, sai dai shi ya karkata ne ga rabe-raben waƙoƙin Hausa da tasirinsu ga rayuwar Hausawa, ni kuma na karkata ne a nazarin bambance-bambancen waƙoƙin sarauta na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na gama-gari na Aminu Ladan Abubakar.

Gusau (1993). A littafin da ya rubuta mai suna "Jagoran Nazarin Waƙa". Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero da ke Kano. Wanda kamfanin Benchmark Publishers Limited suka buga. Wannan masanin ya karkasa wannan littafi zuwa kashi uku inda babi na ɗaya ya ƙunshi tarihin wanzuwar waƙoƙin baka na Hausa, a babi na biyu kuwa zayyana nau'o'in waƙoƙin Baka na Hausa sannan a babi na uku sai ya yi bayanin hanyoyin nazarin waƙar baka daga kusan ƙarshe sai ya yi jawabin kammalawa sai ya rufe da wasu ratayen waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa a zube.

Wannan littafin yana da nasaba da aikina saboda yana magana a kan waƙa, ni kuma kuma nazartar waƙar na ke yi.

Ɗangambo (1998). A littafinsa da ya wallafa mai suna "Gadon Feɗe Waƙa (Sabon tsari), wanda kamfanin Amana Publishers Limited, Zaria suka buga shi. Wannan littafin yana da alaƙa da bincikena saboda an rubuta shi ne a kan waƙa, sai dai shi masanin ya karkata ne a kan nazarin nau'o'in waƙoƙi ne, ni kuma ina yin nazari ne a kan bambancin da ke samu a tsakanin waƙar gargajiya da ta zamani musamman na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Aminu Ladan Abubakar.

Ibrahim (1983). Ya rubuta littafi mai suna "Waƙoƙin Sarauta". Inda ya yi bayani a kan makaɗan sarauta da jigoginsu da kuma salon sarrafa harshensu sannan ya yi bayani kan makaɗan jama'a a waƙoƙin kasuwanci. Ya kuma yi bayani a kan makaɗan Sana'a da makaɗan maza (Jarumai) da sauransu. Don haka wannan littafi yana da alaƙa da binciken tun da an rubuta shi a kan waƙa. Amma bambancin wannan littafin da bincikena shi ne, an rubuta shi ne a kan waƙoƙin sarauta kawai bai ce komai ba a kan waƙoƙin zamani ba. Inda ni kuma dukansu zan yi nazari a kansu.

Gusau (1996). Ya yi rubuta littafi dangane da tarihin rayuwar makaɗa da mawaƙa guda talatin da uku (33) tun daga haihuwarsu da nasabarsu da asalinsu da ƙurciyarsu da sana'o'insu da yadda suke tsara waƙoƙisu da falsafarsu da sauran ayyukkan da suke yi a rayuwarsu ta yau da kullun.Wannan aiki yana ba da haske dangane da bincikena, don haka zan samu saurin fahimtar wannan littafi tun da yana magana ne a kan makaɗa sannan kuma ya ƙunshi wasu daga cikin waƙoƙinsu, wanda zai zama haske a wannan gina kundin binciken da nake yi.

Gusau (1996). A wani littafinsa mai suna “Makaɗa da Mawaƙan Hausa na ɗaya” a wannan karon masanin ya zuba littafinsa ne a tsarin kashi-kashi kamar haka: Kashi na ɗaya ya kawo makaɗan yaƙi, a kashi na biyu kuma ya kawo makaɗan sarakuna rukuni na I, a kashi na uku kuwa ya kawo makaɗan sarakuna rukuni na II. Kashi na huɗu ya kawo makaɗan jama’a, a kashi na biyar kuma sai ya kawo na makaɗan sana’a, daga nan sai taƙaita ya yi jawabin kammalawa ya rufe daga ƙarshe kuma ya zayyana makaɗan da aka yi shira da su.

Wannan yana da alaƙa da wannan aikin yayin da shi Gusau M.S ya kalli waƙoƙin ya karkasa su kashi-kashi har biyar. Ni kuma na ɗauki wasu waƙoƙin daga ciki sai na nazarce su domin na gano ire-iren bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani.

Shi kuwa Abba da Zulyadaini. (2000). A cikin wani aiki da suka yi mai suna “Nazari A kan Waƙar Baka Ta Hausa waɗannan masana sun gudanar da aikinsu ne a kan tsarin na babi-babi, inda suka kawo tarihin samuwar waƙar baka a ƙasar Hausa da rabe-raben makaɗan baka a ƙasar Hausa, dangane da rukunoninsu da jigogin waƙoƙin baka na Hausa.

Waɗannan masana sun gudanar da aikin su a fannin adabin baka kuma waƙa ni kuma daman aikin da nake da ƙuduri akan adabi ne sai dai yana da bambanci saboda nawa aikin akwai waƙoƙin zamani a ciki. Wannan ya nuna cewa aikin yana da alaƙa da nasu, sai dai su suna kallon dukkannin makaɗa na ƙasar Hausa ne yayin da ni kuma mawaƙan baka kawai nake kallo ba har da na zamani.

Yahaya (2001). A littafin da ya rubuta mai taken "Salo Asirin Waƙa".Babu shakka wannan littafin ya dace da bincikena saboda ya yana magana a kan waƙa, ni kuma daman a kan batun waƙa nake son gina kundina. Sai dai shi marucin ya karkata ne a kan nau'o'in salo a cikin waƙoƙin Hausa, ni kuma ina yin nazari ne a kan bambance-bancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya na sarauta na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na zamani na Aminu Ladan Abubakar.

Dunfawa (2003). Ya rubuta littafi mai suna "Arulin waƙa". Ya fara bayar da ma'anar aruli da ƙafiya, kari wato da Balaraben kari da Bahaushen kari.Haka kuma ya kawo sauti (zahafi) da gwauron sauti da tagwan sauti da sakiyar illa da sakiya mai ragi da kuma sautin rabawa. Sannan ya kawo amsa-amo da amsa-amon gaɓar sauti da babban amsa-amo da ƙaramin amsa-amo da amsa-amon farawa da amsa-amo mai zaman kansa da kuma amsa-amon sauti.

Wannan littafi yana da muhimmanci domin yana nuna mizanin waƙa da masana suka rubuta masu alaƙa da wannan bincike.Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da nawa, domin ya yi cikekken bayani a kan amsa-amon ciki da amsa-amon waje, wato babban amsa-amo da ƙaramin amsa-amo.Wanda duk mai nazarin rubutattun waƙoƙi dole ne ya san su ya kuma fahimce su, domin yana ɗaya daga cikin abin da ya bambanta rubutattun waƙoƙi da na baka.Bugu da ƙari ya kawo maanar waƙa, sai dai bambancin littafinsa da nawa aikin shi ne ya mai da hankali ne a kan arulin waƙa, ni kuma ina yin nazari ne a kan bambancin da ake samu a tsakanin waƙoƙin sarauta na gargajiya da na zamani.

Sarɓi (2007). Ya rubuta littafi mai suna “Nazarin Waƙar Hausa wannan marubuci ya rubuta littafin ne domin masu nazarin waƙoƙin Hausa musamman rubutattu. A cikin wannan littafi nasa ya yi magana a kan jigo, salo zubi da tsari, nau'o'in rubutacciyar waƙa da dai sauransu.

Wannan aiki na Sarɓi yana da alaƙa da nawa aikin saboda ya yi tsokaci a kan waƙar zamani yayin da ni kuma nawa aikin yana magana ne akan waƙoƙin zamanin sai dai kuma inda bambanta da sa aikin shi ne, shi Sarɓi waƙoƙin zamani kawai ya mayar da hankali, bai ce komai ba game da waƙoƙin gargajiya ba. Ni kuma duka biyun nake burin na yi tsokaci akansu.

Haka zalika Gusau (2008). A wani littafinsa mai suna “Waƙoƙin Baka A Kasar Hausa, Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu har wa yau dai masanin ya zuba littafinsa a tsarin babi-babi, inda a babi na ɗaya ya kawo tarihin ƙasar Hausa da yanaye-yanayenta, a babi na biyu kuwa ya kawo kiɗa da kayan yinsa. Sai a babi na uku inda ya kawo makaɗan baka na Hausa. A babi na huɗu kuwa ya kawo halayya da nau’o’in waƙoƙin baka, daga nan dai sai ya shiga babin kammalawa inda ya gudanar da jawabinsa na kammalawa.

Gusau (2008). Ya bayyana tarihin Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi da waƙoƙinsa. Wannan littafi yana da muhimmanci ga wannan bincike.Domin ya bayar da maanar waƙa da kuma yadda ake yin nazarin waƙa, duk cewa shi a kan mawaƙin baka ya gudanar da wannan aiki ni kuma nawa a kan waƙoƙin siyssa na Kabiru kilasik.

Gusau (2008). Ya bayar da tarhin waƙoƙin baka a ƙasar Hausa yanayinsu da sigoginsu da suka haɗa da kiɗa na Hausa da kayan yinsa. Kuma ya binciki makaɗan baka na Hausa da halayyarsu da nau’o'in waƙoƙin baka na Hausa da kuma turke da ire-irensa a wƙoƙin baka na Hausa.

Bunza (2009), ya rubuta wani littafi mai suna “Narambaɗa” wannan littafi da wannan masani Al’dar Hausa ya rubuta, littafi ne wanda ya tsara shi bisa ga tsari na babi-babi har babi goma sha biyu. A babi na ɗaya masanin ya kawo jigogin waƙoƙin Narambaɗa, a karkasa shi wannan babin ya fara da gabatarwa da asalin kalmar jigo da rabe-raben jigo da babban jigo da ƙaramin jigo da yadda ake neman sarauta da yadda sarauta take da naɗin sarauta da makamantan hakan.

A cikin babi na biyu da akwai masarauta a waƙoƙin Narambaɗa, a babi na uku ya kawo sarki a waƙoƙin Narambaɗa, a babin na huɗu ya kawo fada a waƙoƙin Narambaɗa, a babi na biyar kuwa ya kawo ƙananan jigogin waƙoƙin Sarauta. A babi da shidda akwai keɓaɓɓun ƙananan jigogin sarauta, a babi na bakwai nan ne ya kawo salon waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa, a babi na takwas ya ba da falsafar waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa, a babi na tara ya zo da tussan waƙoƙin Narambaɗa, a babi na goma ya yi bayanin fashin baƙin Bakamdamiya, a babi na gaba sai ya rufe da kammalawa.

Wannan littafi da wannan masani ya rubuta ya haskaka da hanya sosai wajen samun dubaru da zan gina nawa aikin don ya ƙayatar. Alaƙarsa da wannan aikin ita ce, shi yana kallon waƙoƙin Narambaɗa da kuma nazarinsu ni kuma zan nazarin waƙoƙi ne gaba ɗaya akansu wato na gargajiya da na zamani. Haka kuma Bunza bai ce komai ba game da bambanci da ke tsakanin waƙar baka da ta zamani ba. Ni kuma dole sai na yi magana akan su saboda su ne jigon bincikena.

Bunza (2009), ya rubuta wani littafi mai suna “Narambaɗa” wannan littafi da wannan masani Al’dar Hausa ya rubuta, littafi ne wanda ya tsara shi bisa ga tsari na babi-babi har babi goma sha biyu. A babi na ɗaya masanin ya kawo jigogin waƙoƙin Narambaɗa, a karkasa shi wannan babin ya fara da gabatarwa da asalin kalmar jigo da rabe-raben jigo da babban jigo da ƙaramin jigo da yadda ake neman sarauta da yadda sarauta take da naɗin sarauta da makamantan hakan.

A cikin babi na biyu da akwai masarauta a waƙoƙin Narambaɗa, a babi na uku ya kawo sarki a waƙoƙin Narambaɗa, a babin na huɗu ya kawo fada a waƙoƙin Narambaɗa, a babi na biyar kuwa ya kawo ƙananan jigogin waƙoƙin Sarauta. A babi da shidda akwai keɓaɓɓun ƙananan jigogin sarauta, a babi na bakwai nan ne ya kawo salon waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa, a babi na takwas ya ba da falsafar waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa, a babi na tara ya zo da tussan waƙoƙin Narambaɗa, a babi na goma ya yi bayanin fashin baƙin Bakamdamiya, a babi na gaba sai ya rufe da kammalawa.

Wannan littafi da wannan masani ya rubuta ya haskaka da hanya sosai wajen samun dubaru da zan gina nawa aikin don ya ƙayatar. Alaƙarsa da wannan aikin ita ce, shi yana kallon waƙoƙin Narambaɗa da kuma nazarinsu ni kuma zan nazarin waƙoƙi ne gaba ɗaya akansu wato na gargajiya da na zamani. Haka kuma Bunza bai ce komai ba game da bambanci da ke tsakanin waƙar baka da ta zamani ba. Ni kuma dole sai na yi magana akan su saboda su ne jigon bincikena.

Bunza (2013). Ya rubuta littafi mai suna "Narambaɗa" inda ya kawo cikakken tarihin Narambaɗa da iyalansa da abokansa da Waƙoƙin sa, da iren-iren waƙarsa da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarsa na yau da kullum.Wannan gagarumin littafi ya haɗa abubuwa da dama masu muhimmancin gaske ga wannan nazari nawa. Gaskiyar masu iya karin magana da ke cewa, "Ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba" Haƙaƙi wannan gagarabadon littafi ya zame mani jagora ga wannan bincike domin ya haska min hanyar inganta wajen kundin binciken. Sai dai inda muka babban da wannan littafin shi ne, masanin bai ce komai ba kan makaɗi Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Aminu Ladan Abubakar ba, kawai dai ya karkata a kan makaɗi Ibrahim Narambaɗa tare da iyalansa, ni kuma zan yi magana ne a kan nazarin da ake samu na waƙoƙin sarautar gargajiya da ta zamani

Gusau (2014). Ya rubuta littati mai suna "Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Sound). Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano. Wannan littafi ya ƙunshi abubuwa kamar haka: Samuwar waƙar baka, masu yin waƙar baka, ire-iren waƙar baka da makaɗa, muhimman sigogi na waƙoƙin baka na makaɗa, matakan nazarin waƙar baka daga ƙarshe sai ya yi jawabin rufewa.

Wannan littafin yana da alaƙa da bincikena domin ya yi magana a kan waƙa hasalima shi ne zai fi yi min jagoranci wajen ɗabbaka wannan kundin binciken.

Gusau (2016). Ya rubuta littafi mai suna" Makaɗa da Mawaƙan Hausa: Littafi na biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano. Wanda kamfanin Century Research and Publishing Limited da ke Kano suke buga. Wannan masanin ya karkasa littafin zuwa matakai goma sha huɗu (14) dangane muhallin nau'o'i ko rukunin kiɗan da suke samarwa ga al'umma. Inda ya zayyano makaɗa guda saba'in (70) sai ya fara gabatarwa sannan ya yi amfani da wasu maganganun bincike kamar haka; Sunan makaɗi ko inkiyarsa, Iyaye, shekarar haihuwa da gari, ilminsa, sana'arsa, fara kiɗa da waƙarsa, abin kiɗansa, ire-iren waƙoƙinsa, ƙungiyarsa ko kaɗaitarsa a kiɗa, Iyali da shuhurar makaɗi, ritaya daga waƙa, adireshin makaɗi da rasuwarsa.

Wannan littafi ya da mutuƙar nasaba da alaƙa da wannan aikin nawa saboda yana magana ne a kan makaɗan gargajiya da na zamani inda nan na karkata a bincikena.

Gusau (2018). Ya rubuta littafi mai suna"Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu'i Na Uku. Matanonin Wasu Waƙoƙin Alh. Dr. Mamman Shata Katsina, a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a jami'ar Bayero da ke Kano: Century Research and Publishing Limited. Masanin ya tsara littafin zuwa kashi biyu, inda kashin farko ya tsara shi a kan Mamman Lawal Shata a waƙar baka sai kashi na biyu a kan rukunoni na matanonin wasu waƙoƙin Mamman Lawan Shata daga ƙarshe kuma ya yi jawabin kammalawa.

Wannan littafin yana ya dace da bincike domin ya yi magana a kan waƙa kuma yana da muhimmanci sosai da zai taimakamin wajen gina wannan kundin.

Gusau (2019). Ya rubuta littafi mai suna "Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓu Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da na Afrika: Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya. Wanda kamfanin Century and Publishing Limited, Kano-Nigeria.

Wannan masanin ya karkasa wannan littafin zuwa kashi biyu, inda kashi na farko ya zayyano waƙoƙin fada sannan a kashi na biyu kuma ya zayyano waƙoƙi na gama-gama tare da ayyukan mawaƙansu. Wannan littafin yana da alaƙa da kundin da nake so na gida saboda duka ta taɓo waƙoƙin sarauta da na gama-gari inda ni a wannan ɓangaren nake bincikena.

2.3 Muƙalu

A ɓangaren Maƙalu ne masana da dama sun yi rubuce-rubuce a kan batutuwa masu alaƙa da wannan nazari. Don haka za a iya cewa sun bayar da gudummuwa wajen gudanar da wannan bincike.

Wannan sashe ne na ɗalibai da masana da kuma sauran al'umma musamman marubuta waƙoƙi waɗanda su ke bayyana ra'ayoyinsu da ba da gudummawa daban-daban da su ke gabatarwa a bainar jama'a musamman a ɗakunan taruka ko a cikin ajjijuwan koyar da darussa a Kwalejojin ilmi da Jami'o'i da kuma waɗanda ake yaɗawa a gidajen Rediyo da na Talabijin da sauran wurare na bayar da ilmi na yau da kullum, akwai masana da dama da suka gabatar da muƙalu a sassan Arewacin Najeriya da sauran ƙasashen nahiya Afrika. Ga kaɗan daga cikin su:

Dumfawa (1995). Wannan masanin ya rubuta wata muƙala mai taken "Zuga a Waƙoƙin Fada". Wannan aikin nasa yana da alaƙa da nawa saboda sun ƙunshi waƙa, amma sai dai shi aikin nasa ya karkata ne a kan zuga a cikin waƙoƙi fada sannan ni kuma nawa aikin yana duban bambancin da ke a samu a waƙoƙin gargajiya da na zamani.

Usman da Faruk. (2019). A cikin wata muƙala da suka gabatar mai taken" Gudummawar Mawaƙan Baka Da Marubuta Waƙoƙin Hausa Ga Yekuwar Gwamnati Kan Shirin Ilmin Zamani. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato. Wanda Mukhtar (2006:130) yace "Waƙar gargajiya wasu saƙonni ne da su ke cikin lafazi da furuci masu inganci wanda ake gudanarwa da su ta hanyoyin daidaitattun kalmomi masu tsari da kuma ƙa'idoji da sauran dabaru masu jawo hankula masu sauraro da karatu. Saboda haka ita waƙar baka maganganu ne na hikima da suke nuna fasahar mawaƙa.

Masanin ya ƙara tofa albarkacin bakinsa dangane da waƙoƙin zamani, inda yace hanyoyi ne na aiwatar da wasu saƙonni da suke cikin ƙayadaddun kalmomi da aka zaɓa waɗanda ake rera su a kan ƙari da ƙafiya a cikin baitoci (Mukhtar, 2006:130). Wannan muƙala ta dace da bincikena saboda ta yi magana a kan mawaƙan baka da marubuta waƙoƙin Hausa, inda ni kuma nan karkata a nazarina.

Yahaya da Dumfawa. (2010). A wata muƙala da su ka yi mai suna "Waƙar motar Siyasa" Saƙon Talakawa zuwa ga ƴan siyasar zamani. A cikin muƙalar Dundaye Journal of Academic Execellence, a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato. Inda suka yi bayani a kan salo da nau'o'insa a waƙa sannan suka kawo wasu daga cikin makaɗan Baka tare da nazarin waƙoƙinsu daga ƙarshe kuma ya yi jawabin kammalawa.

Shi ma wannan aikin ya dace da nawa domin ya yi magana ne a kan waƙa, sai shi ya karkata ne a kan salon waƙoƙi tare da nazarinsu, ni kuma ina nazari ne a kan bambance-bambancen waƙoƙin sarautar gargajiya na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na zamani na Aminu Ladan Abubakar.

Gusau (2011). Ya yi muƙala mai taken "Bitar Littafin Waƙoƙin Baka na Hausa". A cikin takardar da ya gabatar a taron raya al'adun Hausawa da Fulani da ƙaddamar da littafin waƙoƙin Baka na Hausa a Kwalejin Ilmi ta Tarayya, Katsina. Wannan aikin yana da nasaba da nawa aikin saboda dukansu suna magana ne a kan waƙa da alaƙa da nawa nazarin domin a kan waƙa ya gudanar da ita, sai dai wannan muƙalar bambancin ta da nawa aikin shi ne, a kan bitar littafi aka yi. Ni kuma aikina zan kalli ire-iren bambance-bambancen da ake samu a tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani.

Atuwo (2013). Shi ma ya yi muƙala mai taken "Salon Ƙawance a Waƙoƙin Baka". Muƙalar da aka gabatar a taron tattaunawa don ƙara wa juna sani, wanda Sashen koyar da Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato, ya shirya a ranar 23 ga watan Mayu, 2013. Wannan muƙala tana da nasaba da nawa aikin saboda ta yi magana ne a kan waƙa, amma sai dai aikin nasa ya bambanta da nawa, tin da shi a kan salon ƙawance a waƙoƙin baka ya yi. Ni kuma ina bincike ne a kan bambancin da ake samu a waƙoƙin sarautar gargajiya da na zamani.

Gusau (2022). A Taron Ga Fili Ga mai Doki domin gabatar da Littafin Diwanin Waƙoƙi na shida (6) da sauran Littattafan Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau. Wanda Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano ta gudanar a ranar Asabat 15 ga watan Octoban 2022 da misalin ƙarfe 10:30 na safe a cikin babban ɗakin karatu na Jahar Kano da ke kan titin Ahmadu Bello, Kano.

Wannan taron da aka yi ya dace da bincikena saboda an shi ne a kan falsafa da ci gaban da mashurin masanin Adabi na shiryar Afirika ya bayar ga al'umma.

2.4 Naɗewa

Wannan babi an yi bitar ayyukan masana da dama masu alaƙa da kurkusa dangane da wannan binciken, inda aka fara da shafin gabatar da babi wajen amfani da kundayen bincike na ɗaliban mabambanta daga sashinan koyar da Harsunan Nijeriya da sassan Afirika wajen duba kundayen kammala karatunsu na matakan digirin farko da na biyu da kuma na uku wato digirin digirgir (PhD).

Haka zalika binciken ya duba bugaggun littattafan masana da dama da koyarwa a Jami'o'in Nijeriya, suma ayyukansu sun dace da wannan aikin kuma taka gagarumar gudummawa wajen kan inganta gina da wannan kundin. Sannan an duba muƙalun da masanan suka buga kuma gnatar a wajen ƙarawa juna sani a wurare daban-daban a ƙasar Hausa. Ina fatan Allah ya saka kowa da mafificin alkhairi ya ji ƙan magabatansu da sauran waɗanda suka taimaka wajen ba da gudummawarsu ta gina kundaye da bugaggun littatafai da kuma muƙalun, Amin.

Waƙoƙin Hausa

Post a Comment

0 Comments