ƘUNSHIYA
Wannan kundin binciken an samar da shi ne domin samun shaidar takardar karatun digiri na farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Tsangayar Karatun Digiri, Kwalejin Ilmi Da Ke Gumel, Kulawar Jami'ar Bayero, Kano.
NAZARI A KAN
BAMBANCE-BAMBANCEN DA KE TSAKANIN WAƘOƘIN GARGAJIYA DA NA
ZAMANI, BINCIKE NA MUSAMMAN NA WAƘOƘIN SARAUTA NA ALHAJI
MUSA ƊANƘWAIRO DA NA GAMA-GARI
NA AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA)
NA
ISAH MUHAMMAD KAWU
Lambar Waya: 07047484384
BABI
NA UKU
HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
3.0 Gabatarwa
Akwai
hanyoyi da dabaru da dama da ake bi domin gudanar da bincike wanda mai nazari
kan bi su don aiwatar da aikinsa na bincike a cikin sauƙi. Wannan hanyoyin
sun haɗa da dabarun bincike,
tsarin bincike, jama'ar bincike, samfurin bincike, tambayoyin bincike da kuma
hanyoyin tattara bayanai. Waɗannan hanyoyin ko matakan su ne ire-iren abubuwan da
bincikena zan yi tsokaci akansu domin gudanar da bincike yadda ya kamata.
Masu
iya magana na cewa' kowane bakin wuta da irin na sa hayaƙin, hakan na nufin
kowane fagen bincike da akwai al'amuran da suka keɓanta ko jiɓinta da shi. Duk da
haka, cikin kowane fanni na nazari ana iya karkasa bincike zuwa manyan rukuni
guda uku kamar haka: bincike na tarihi, na bayani da na gwaji, to amma Hausawa
na cewa inda baki ya karkata nan yawu ya ke zuba. Wannan bincike zai ta'allaƙa ne akan bincike na
bayani ne kaɗai.
3.1 Dabarun Gudanar da Bincike
Akwai
salo ko dabaru da daban-dabam da ake bin su domin aiwatar da bincike a fagen
ilmi, don haka za a barni a baya ba wajen bi ko amfani da dabaru da basira don
ganin an gudanar da wannan binciken cikin yardar Allah (S.W.A). Bugu da ƙari wannan hanya za
ta taimaka min wajen samun gamsassun bayanai masu inganci dangane da wannan
batu na nazari kan bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani musamman akan waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na Aminu
Ladan Abubakar inda za a zaƙulo wasu daga cikin waƙoƙin sarauta da na
zamani musamman na gama-gari a matsayin tushen bayani a matakin farko sannan za
a ware wasu waƙoƙin domin taƙaita nazari akan su.
Baya
da haka an samu rubuce-rubuce masu tarin yawa waɗanda masana da manazarta suka daidaita
alƙiblar
nazarin, an kuma ɗora su akan ra'ayin
ma'aunin Bahaushe da cewa" So so ne, amma Son kai ya fi".
3.2 Tsarin Bincike
Da
akwai hanyoyin mabanbanta da ake bi wajen amfani da tsarin bincikena zan yi da
hanyoyi guda biyu kamar haka:
3.2.1 Bincike ta Hanyar yi wa Jama'a
Tambayoyin Baka da Baka
A
wannan tsari ne zan yi wa jama'a tambayoyin baka da baka (Interview) domin
samun gaskiyar lamarin abin da nake nema da son yin bincike akansa. Ta wannan
hanya ne zan samu damar yi wa jama'a tambayoyi musamman dattawa ma'abota gani
da son sauraron waƙoƙin gargajiya tare matasa da yara matsakaita masu ra'ayi
jin waƙoƙin zamani sannan garzaya wuraren masana da manazarta da
kuma sauran al'umma Masu sauraron sauraron waƙoƙin Hausa da
karance-karancensu duk saboda ina samu bayanai ingantattu akan wannan binciken.
3.2.2 Raba Tambayoyi A Rubuce
(Questionnaire)
A
wannan hanyar zan rubuta tambayoyi a rubuce sannan a buga su a kwamfuta na kuma
rarraba su ga jama'a masu masaniya akan bincikena don samun sahihan bayanai a
kan abin da na ke son gudanar da bincike akansa. Haka zalika, na rubuta
tambayoyi da dama ta wannan hanyar sannan zan rarraba su ga mutane daga ƙarshe kuma na samu
dukkannin gamsassun bayanai da nake buƙata akan binciken.
3.3 Jama'ar Bincike
A
tsarin kundin bincike, idan aka ce jama'ar bincike su ne nau'o'in mutanen da
mai bincike zai yi amfani da su wajen gudanar bincikensa. Don haka, jama'ar
bincikena su ne ƙabilar Hausa domin binciken zai ta'allaƙa ne kacokan akan
wasu mashahuran mawaƙa a ƙasar Hausa a da da yanzu wato mawaƙin gargajiya da kuma
na zamani waɗanda waƙoƙinsu sun samu karɓuwa da yaɗuwa a ƙasar Hausa har da
wasu sassan nahiyoyin duniya.
Bugu
da ƙari
ƙabilun
Hausa su ne tushe mai ƙarfin gaske, kuma suna da al'adunsu da ɗabi'u da fasahoshinsu
kamar yadda kowacce ƙabilun duniya su ke da su. Wannan ya sa su ma ƙabilun Hausawan su ke
da sarakuna da sauran jagororin al'umma a kowane ɓangare.
3.4 Samfurin Bincike
Kamar
yadda aka sani cewa, samfurin bincike ya ƙunshi ire-iren
hanyoyin da ake bi domin samun tabbatattun bayanai masu inganci daga wajen
masana da manazarta. Kasancewar Alhaji Musa Ɗanƙwairo da shi da Aminu
Ladan Abubakar sun yi waƙoƙi da yawa waɗanda suka shafi fannoni daban-daban na
rayuwar al'umma. Wannan bincike ya taƙaita ne ga waƙoƙin baka na gargajiya
da na zamani, sannan an zaƙulo wasu waƙoƙin da su yi a
matsayin samfurin bincike. Ga su kamar haka;
i.
Waƙoƙin sarauta na Musa Ɗanƙwairo na zambo
ii.
Waƙar nuna tarihi
iii.
Waƙar yabo
iv.
Waƙar Tauhidi
v.
Waƙar raya al'adun
sarauta na tsafi
vi.
Waƙar roƙo
vii.
Waƙar Ta'aziyya
viii.
Waƙoƙin Aminu Ala na yabo
ix.
Waƙar Faɗakarwa
x.
Waƙar akan Magani
xi.
Waƙar Sarauta
3.5 Tambayoyin Bincike
Assalamu
alaikum bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci tare da girmamawa mai tarin
yawa a gare ku. Ni Isah Muhammad Kawu wanda na kasance ɗaya daga cikin ɗaliban shekarar ƙarshe a makarantar
tsangayar karatun digirin farko da ke Kwalejin ilmi ta Gumel, jahar Jigawa,
reshen jami'ar Bayero Kano. Ina fatan tambayoyin nan za su amsu wa daga gare
ku, Allah ya sa.
3.5.1 Tambayar Bincike Ta Baki Da Baki
Na
zaɓi waƙar Alhaji Musa Ɗanƙwairo wanda ya yi wa
mai martaba sarkin Gumel, Alh. (Dr) Ahmad Muhammad Sani ii, domin na yi
tambayoyi ga jama'ar bincikena akan waƙar.
1.
Suna
2.
Shekara
3.
Jinsi
4.
Aiki/muƙami
5. Wurin zama
6.
Lambar waya
7.
Shin ka/kin san wani abu dangane da tarihin Alh. Musa Ɗanƙwairo ?
8.
Me ka/kika sani dangane da mu'amarsa da sauran mawaƙa ?
9.
Yaushe ka/kike tunanin Alh. Musa Ɗanƙwairo ya fara waƙa ?
10.
Shin ko ka/kin san dalilin da ya sa Alh. Musa Ɗanƙwairo ya yi wa Sarkin
Gumel waƙa ?
11.
Shin ko ka/kin taɓa karanta ko sauraron
wannan waƙar ?
12.
Me ka/kika fahimta dangane da wannan waƙar ?
13.
Mene ne salon wannan waƙar ?
14.
Me ka/ki fahimta dangane da sarrafa harshen cikin waƙar ?
15.
Mene ne zubi da tsarin wannan waƙar ?
3.5.2 Tambayoyin Bincike Ta Baki Da
Baki
Na
zaɓi waƙar Aminu Ladan
Abubakar wanda ya yi wa Farfesa Sa'idu Gusau, domin na yi wa jama'ar bincikena
tamboyoyin akan ta.
1.
Suna
2.
Shekara
3.
Jinsi
4.
Aiki/muƙami
5.
Wurin zama
6.
Lambar waya
7.
Shin ko ka/kin san wani abu dangane da tarihin Aminu Ladan Abubakar ?
8.
Me ka/kika sani dangane da mu'amalarsa da sauran mawaƙa ?
9.
Yaushe ka/kike tunanin Aminu Ladan Abubakar ya fara yin waƙa ?
10.
Shin ka/kin san dalilin da ya sa Aminu Ladan Abubakar ya yi wa Farfesa waƙar ?
11.
Shin ko ka/kin taɓa karanta ko sauraron
waƙar
?
12
Wane irin salo Aminu Alan ya yi amfani da shi a cikin waƙar ?
13.
Me ka/kika fahimta dangane da sarrafa harshen da ke cikin waƙar ?
14.
Wane irin zubi da tsari ya yi da shi a waƙar ?
15.
Shin ko ka/ki na da labarin Aminu Ala ya yi yawace-yawace na wurare daban-daban
don yin waƙa ?
Takardar
Baiwa Jama'a Tambayoyi A Rubuce (Questionnaire)
Da
farko dai kamar yadda na bayyana a baya, sunana Isah Muhammad Kawu. Na kasance ɗaya daga cikin ɗaliban shekarar ƙarshe a makarantar
tsangayar karatun digirin farko da ke cikin Kwalejin ilmi ta Gumel, reshen
jami'ar Bayero Kano. Ka/ki ce dukkan wuraren da suka dace da amsarka/ki ta
hanyar yin amfani da wannan alamar da ke cikin akwati.
1.
Suna
2.
Shekara
3.
Jinsi
4.
Aiki/muƙami
5.
Wurin zama
6.
Lambar waya
7.
Mene ne sunan mahaifin Alh. Musa Ɗanƙwairo ?
A.
Usman Ɗan kwanagga B. [ ] Abdu Kurna C. [ ] Ibrahim Narambaɗa
8.
Mene ne sunan mahaifiyar Alh. Musa Ɗanƙwairo
A
Zainabu B. [ ] Ladidi C.[ ] Barmani Coge D. [ ] Ƴarkunu.
9.
A wacce shekarar aka haifi Alh. Musa Ɗanƙwairo
A.
1981. [ ] B. 1950 C. [ ] 1909 [ ] D. 1980 [ ]
10.
Shin a wane garin aka haifin Musa Ɗanƙwairo ?
A.
Ɗankandu
ta Bakura [ ] B. Kano [ ] C. Katsina [ ] D. Sakkwato [ ]
11.
Shin Alh. Musa Ɗanƙwairo ya yi karatun boko da allo ?
A.
Da gaske ne [ ] B. Ba da gaske ba ne [ ]
12.
A wacce shekarar Alh. Musa Ɗanƙwairo ya fara waƙa ?
A.
1920 [ ] B. 1916 [ ] C. 1940. [ ] D. 1930 [ ]
12.
Me ka/kika sani dangane da mu'amalarsa da sauran mawaƙa ?
A.
Bashi da kyakkyawar [ ] B. Yana da kyakkyawar mu'amala [ ]
13.
Me ka/kika sani dangane tarishin sa ?
A.
Na sani [ ] B. Ban sani ba [ ]
14.
Shin ka/kin san dalilan da ya sa Alh. Musa Ɗanƙwairo ya yi wa Sarkin
Gumel waƙa ?
A.
Yabo [ ] B. Faɗakarwa [ ] C. Habaici
[ ] D. Zambo [ ]
15.
Shin ka/kin taɓa karanta ko sauraron
waƙar
da ya yi wa Sarkin Gumel ?
A.
Eh na taɓa ji [ ] B. A'a ban
taɓa ji ba [ ]
16.
Me ka/kika fahimta dangane da wannan waƙar da ya yi ?
A.
Yabo [ ] B. Zambo [ ] C. Soyyaya [ ] D. Nuna tarihi [ ]
17.
Mene ne jigon waƙar ?
A.
Roƙo
[ ] B. Nishaɗi [ ] C. Barkwanci [ ]
D. Yabo [ ]
18.
Wane irin salo aka yi amfani da shi a waƙar ?
A.
Sassauƙan Salo [ ] B. Salo mai armashi [ ] C. Ragon salo [ ] D.
Salo mai aure [ ]
19.
Mene ne zubi da tsarin waƙar ?
A.
Mabuɗinta [ ] B. Marufinta
[ ] C. Yawan baitukanta [ ]D. Yawan layukanta [ ]
20.
Shin Alh. Musa Ɗanƙwairo ya yi yawace-yawace ta dalilin yin waƙa ?
A.
Eh ya yi [ ] B. A'a bai yi ba [ ]
21.
A wacce shekarar Alh. Musa Ɗanƙwairo ya rasu ?
A.
1981 [ ] B. 1991 [ ] C. 2000 [ ] D. 2019 [ ]
1.
Suna
2.
Shekara
3.
Jinsi
4.
Aiki/miƙami
5.
Wurin zama
6.
Lambar waya
7.
Shin mene ne sunan mahaifin Aminu Ladan Abubakar ?
A.
Isah [ ] B. Abubakar [ ] C. Malam Abdu [ ] C. Musa [ ]
8.
Mene sunan mahaifiyarsa ?
A.
Maryam [ ] B. Hussaina [ ] C. Bilkisu [ ] D. Zara'u [ ]
9.
A wane gari aka haifi Aminu Ladan Abubakar ?
A.
Gobir [ ] B. Yakasai [ ] C. Bakura [ ] D. Hadejia [ ]
10.
A wace shekarar aka haifi Aminu Ladan Abubakar ?
A.
1973 [ ] B. 1980 [ ] C. 1990 [ ] D. 1968 [ ]
11.
Shin Aminu Ladan Abubakar ya yi karatun boko da na addini ?
A.
Eh ya yi [ ] B. A'a bai yi ba [ ]
12.
A wace shekarar ya fara yi wa Farfesa Gusau waƙar ?
A.
2004 [ ] B. 2010 [ ] C. 2019 [ ] D. Babu ko ɗaya daga cikinsu [ ]
13.
Me ka/kika sani dangane da tarihin Aminu Ladan Abubakar ?
A.
Eh na sani [ ] B. A'a ban sani ba [ ]
14
Shin wane ne dalilin Aminu Ladan Abubakar ya yi wa Farfesa Gusau waƙa ?
A.
Yabo [ ] B. Habaici [ ] C. Roƙo [ ] D. Nishaɗi [ ]
16.
Shin ka/kin taɓa sauraron waƙar da Aminu Ladan
Abubakar ya yi wa Farfesa Gusau ?
A.
Eh na taɓa ji [ ] B. A'a ban
taɓa ji ba [ ]
17.
Shin me ka/kika fahimta dangane da waƙar ?
A.
Nishaɗi [ ] B. Habaici [ ]
Zambo [ ] D. Yabo [ ]
18.
Shin mene jigon yin waƙar ?
A.
Nuna nasaba [ ] B. Yabo [ ] C. Roƙo [ ] D. Barkwanci [ ]
18.
Aminu Ladan Abubakar wane salo ya bi wajen yin waƙar ?
A.
Miƙeƙƙen salo [ ] B. Salo
mai armashi [ ] C. Salo mai aure [ ] D. Ragon salo [ ]
19.
Mene ne zubi da tsarin yin waƙar ?
A.
Marufinta [ ] B. Mabuɗinta [ ] C. Yawan
baituka [ ] D. Yawan layuka [ ]
20.
Aminu Ladan Abubakar ya yi yawace-yawace ta dalilin yin waƙa ?
A.
Eh ya yi [ ] B. A'a baya yi [ ]
21.
Shin Aminu Ala har yanzu yana yin waƙa ?
A.
Eh yana yi [ ] B. A'a ya dena [ ]
3.6
Hanyoyin Tattara Bayanai
Yayin
gudanar da wannan binciken an bi wasu hanyoyi domin na samu damar sauƙaƙa wannan aikin don
samun bayanan da za su gina wannan kundin saboda ya zama ingantacce wanda dole
ne a kowane bincike na fagen ilmi a yi la'akari da su. Waɗannan hanyoyin da na
bi su ne kamar haka:
i.
Hanyar nazarin bugaggun littattafai
ii.
Hanyar tambayoyin baka da baka
iii.
Hanyar sauraron waƙoƙi
Da
farko a ƙoƙarina na ganin na kammala wannan aikin, na ɗan yi karance-karance
da nazarce-nazarce irin na ƙananan ɗaliban ilmi ta yadda na ziyarci ɗakunan adana bayanan
ilmi (Libraries) inda na samu duba wasu littattafan da muƙaloli, jaridu da
sauran bayanai na wasu daga cikin ayyukan magabata masu alaƙa da bincikena domin
samun kyakkyawan sakamakon abin da nake so na binciko.
Na
biyu, na yi hira da mutane da dama musamman masana da dattijai da matasa tare
da ƴan
mata da dai sauran jama'ar gari waɗanda suke da ra'ayoyin sauraron waƙoƙin Alh. Musa Ɗanƙwairo da na Aminu
Ladan Abubakar inda na yi amfani da su na yi musu tambayoyin baki-da-baki don
samun gamsassun bayanai a wajensu wanda daga bisani hakan ya sa na samu zarafin
buga sakamakon tambayoyin da na yi samu a tatttare da su na buga su a kwamfuta
sannan na rarraba wa ɗaliban ilmi domin su
cike amsoshin da suka dace a wuraren da aka bari.
Na
uku, na yi amfani da wayata ta salula inda na shiga yanar gizo-gizo na binciko
wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Musa Ɗanƙwairo na sarauta da
na Aminu Ladan Abubakar na sauƙe su akan wayata (Download) sannan na
ziyarci wuraren masu tura waƙoƙin gargajiya da na
zamani a nan ma aka tura min wasu waƙoƙin. Daga nan na zo na
saurari wasu daga cikin waƙoƙin domin nazartar
abin da nake buƙata na ganin wannan aikin ya ƙayatar.
Waɗannan hanyoyin da ke
sama su ne hanyoyin da na yi amfani da su wajen gudanar da wannan binciken.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.