ƘUNSHIYA
NAZARI A KAN BAMBANCE-BAMBANCEN DA KE TSAKANIN WAƘOƘIN GARGAJIYA DA NA ZAMANI, BINCIKE NA MUSAMMAN NA WAƘOƘIN SARAUTA NA ALHAJI MUSA ƊANƘWAIRO DA NA GAMA-GARI NA AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA)
NA
ISAH MUHAMMAD KAWU
Lambar Waya: 07047484384
BABI NA DAYA
GABATARWA
1.0 Gabatarwa
Waƙa kowace iri ce; ta
baka da rubutacciya, ta wuce duk inda ake tunanin ta dangane da isar da saƙo ga waɗanda ko inda ake son
isar da saƙon. Shi ne ya sa ma idan har ana so a isar da saƙo cikin sauƙi kuma nan da nan to,
a yi amfani da hanyar isar da saƙo ta waƙa.Wannan ba ya rasa
nasaba da daɗin sauraro da take da
shi wanda da haka ta tsere wa abokan tagwaicinta a adabi wato labaran zube da
da wasan kwaikwayo. Da waƙa a kan faɗakar tare da gargaɗi da nasiha da gyaran
hali da hangen nesa, ko a yi wa al'umma hannunka-mai-sanda dangane da wasu
al'amuran duniya, wato a sa mutum ya fahimci kura-kuransa da kansa domin ya
gyara. Da waƙa a kan yi wa mutane wa'azi cewa su daina wasu ayyukan
ashsha su himmatu wajen aikata halaye na gari waɗanda al'umma mai tasowa za ta koya.
Haka
kuma, da waƙa ake ilmintar da waɗanda basu san wasu wasu abubuwan ba, daga
baya su sami sanin abin, domin ya yi musu amfani a zamantakewarsu ta duniya
wani lokacin ma har da ta Lahira. Akasari a kan yi waƙa ne domin samun abin
masarufi, a zuga dakaru domin gusar da tsoro da fargaba na ƙin ja da baya daga
zukantan mayaƙa. Sannan a kan yi waƙa ne domin haɓaka tsarin sarauta da
duk wasu abubuwan da suka dangance ta tare da haɓaka haɓaka ayyukan jarumai da cusa wa al'umma
son su a cikin zukatansu da bayyana yadda ake gudanar da su.
Daga
ƙarshe,
mawaƙan gargajiy\a da na zamani sukan nuna kwarewa da naƙaltar harshen da suke
yi wa waƙa da shi ta hanyar yin luguden kalmomi da ƙarangiya da siffanta
abubuwa tare da kamanta su, da amfani da baƙin kalmomi da aiwatar
da dabaru da sanabe da ke ƙara wa waƙoƙinsu armashi da zaƙi da sa ƙarsashi mai shiga
jiki.
1.1 Matsalolin Bincike
Kamar
yadda ma'anar kalmar ke nuni ta "matsala" na nufin irin cikas ɗin da na ci karo ko
fuskanta da su a yayin da na fara gudanar da wannan binciken . A duk lokacin da
na samu kaina a cikin irin wannan aikin na binciken, to lallai wajibi ne nasan
zan ci karo da wasu matsaloli da zasu iya kawo min tangarɗa ko tarnaƙi ga wannan aikin
kafin na kai ga nasara wato kafin na kammala shi. A lokacin da zan fara gudanar
da wannan kundi sai da na yi hasashen fuskantar barazanar wasu matsaloli kamar
haka:
Da
farko dai, bincike a kan shaharren mawaƙi, wanda yake baya
raye a duniya a yau wato ya rasu. To da akwai matsaloli da dama wanda duk mai
nazari zai iya fuskanta wajen gudanar da wannan bincike ballantana ma a ce
tauraruwar mawaƙin tana haskawa loko da saƙo a faɗin ƙasar Hausa; kuma ga
shi yanzu baya nan rai ya yi halinsa, abu ne da zai fuskanci matsaloli da yawa
ta ɓangarori mabambanta
waɗanda za su iya hana
ruwa gudu ta ko'ina.
Kasancewar
mawaƙi Alhaji Musa Ɗankwairo ya rasu kuma
yana daga cikin mawaƙan da zasu haska min hanyar da zan gudanar da wannan
aikin na binciken kuma ga shi bani da bansan ko da mutum ɗaya ba a cikin ƴan uwa na kusa da na
nesa ta yadda zan so na zauna da su ko na ƙira su ta wayar hannu
domin na samu ƙarin bayani sosai daga wajensu, faruwar hakan ta kawo min
tasgaro ko tsauko a wannan aikin binciken.
Shi
kuma mawaƙi Aminu Abubakar Ladan idan ƙira shi wayarsa ba
kasafai take shiga ba idan na yi sa'a ta shiga ma ba sosai yake ɗaga baƙuwar lamba ba
ballantana ya ɗaga ya amsa, ni kuma
bani da wani makusancinsa mace ko namiji waɗanda suke da alaƙa ko dangantaka ta
jini da shi wanda zan ziyarce su domin su yin jagoranci wajen na je na samu
Aminu Alan domin na samu bayanai gamsassu a wajensa.
Sannan
bincike a kan shahararrun mawaƙan Hausa na gargajiya da na zamani
musamman Alhaji Musa Ɗankwairo da Aminu Abubakar Ladan, mawaƙa ne da ba za a taɓa mantawa da su ba a ƙasar Hausa. Domin
kuwa kamar shi marigayi Alhaji Musa Ɗankwairo a da da
yanzu duniya ta shaida ya taka muhimmiyar raya wajen raya adabi da al'adu tare
da bunƙasar harshen Hausa musamman a fagen waƙoƙin sarauta da na
jama'a sannan shi kuma mawaƙin zamani Aminu Ala yana taka rawa a
fagen waƙoƙin gama-gari na kowa da kowa gwargwadon iko da
hikimarsa..
Haka
zalika waɗannan mawaƙan su ne mutanen da
zasu yi min jagoranci wajen gudanar da wannan aikin nawa ya tabbata, amma
babbar matsalar da na fara tunkara ita ce; kafin a samu takamaiman littattafan
da suka yi magana a kan tarihinsu an ɗauki lokaci, amma yanzu cikin ikon Allah an
fara samu wasu daga cikinsu.
Daga
ƙarshe
aiwatar da gagarumin aiki irin wannan a kan kari, abu ne da zai ci lokuta masu
tsawo. A lokacin da zan fara gudanar da wannan aikin na fuskanci cewa lokaci ba
zai iya yin halinsa wato rashin samun ishasshen lokaci abu ne da kan iya yawo
wa aikin koma baya sannan aiki a kan mawaƙan gargajiya da na
zamani abu ne da yake buƙatar zurfin aiki kafin a cimma manufa. Don haka karamci
ko rashin zurfafa bincike abu ne da zai ƙawo babban nakasu ga
wannan aikin.
1.2 Dalilin Bincike
Da
akwai dalilai masu tarin yawa, da suka sanya na zaɓi wannan batu a
matsayin wanda zan gudanar da bincike a kansa, ga wasu daga ciki.
i.
Maƙasudin da ya sa zan
yi wannan binciken shi ne domin ya zama min dole saboda a ƙoƙarin da nake wajen
ganin na amshi takardar shaidar kammala karatun digirin farkona a tsangayar
nazarin Hausa a Kwalejin ilmi ta jahar Jigawa da ke Gumel, reshen Jami'ar
Bayero (BUK).
ii.
Domin a gano bambance-bambancen da ke
tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani musamman a waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairo da na Aminu
Abubakar Ladan.
iii.
Domin a bayyana wa ƴan baya musamman ɗalibai da manazarta
wajen share musu fili da ƙarfafa musu gwiwa domin su san yadda zasu san ƴan bambance-bambancen
da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani musammani waɗanda suka shafi
bincikena.
iv.
Domin a jawo hankalan ɗalibai da marubuta da
su ƙara
ƙaimi
wajen nazarin waƙar gargajiya da ta zamani.
1.3 Manufar Bincike
Manufa
kan taimaka wajen fuskantar inda za a dosa a fagen nazari. Manufar wannan
binciken su ne:
i.
Saboda a zai taimaka wa ɗaliban da su ke
nazartar Hausa ta ɓangaren adabi su san
ire-iren bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani musamman na waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairo da na Aminu
Abubakar Ladan.
ii.
Saboda a ɗaga darajar adabi
wajen fito da ire-iren bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani.
iii.
Saboda a bayyana wa ɗalibai da manazarta
da kuma sauran al'umma wajen basu haske kan nazari a kan bambance-bambancen da
ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani.
1.4 Muhimmancin Bincike
Wannan
bincike za a gudanar yana da matuƙar muhimmancin gaske
ga duk wani ɗaliban Hausa da
sauran al'ummar Hausawa gaba ɗaya, manyan muhimman abubuwan da suka sa zan yi wannan
binciken su ne:
i.
Domin a nuna wa ɗalibai da manazarta
da sauran al'umma wata sahihiyar hanya ta bincike wanda za su ji ɓi wajen gudanar da
wasu batutuwa da suka shige musu duhu ko rashin cikekken sani akansa don ƙarfafa musu gwiwa
akan yadda za su na aiwatar da bincikensu.
ii.
Domin a nuna wa ɗalibai wajen gano
bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani musamman na waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairo da na Aminu
Abubakar Ladan.
iii.
Domin a nazarci bambancen-bambancen da
ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na zamani na Alhaji Musa Ɗankwairo da na Aminu
Abubakar Ladan.
Haƙiƙa waƙoƙin gargajiya da na
zamani suna da matuƙar muhimmanci ga rayuwar Hausawa musamman a ƙasar Hausa wajen
inganta rayuwar al'umma. Ina fatan wannan binciken da zan yi zai amfanar da ɗaliban ilmi da
manazarta da sauran al'umma wajen ƙara musu haske a kan
bambance-bambancen da ake samu a tsakanin waƙoƙin.
1.5 Hasashen Bincike
Bayan
kammaluwar wannan bincike, ana sa ran kundin nan zai bayyana irin darajar ɓangaren adabi da ya
ke da shi a idon duniya. Sannan ana hasashen binciken nan zai fito da
bambance-bambancen da ake samu a tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani.Binciken zai bayyana wa ɗaliban ilmin harshen Hausa da maruba waƙoƙi wajen share musu
hanya da ba da su kwarin gwiwa da ƙara ƙaimi da jawo
hankalansu na sanin bambance-bambancen da suke a tsakanin waƙoƙin sarautar gargajiya
da na zamani.
1.6 Tambayoyin Bincike
Waɗannan tambayoyin su
ne za su taimaka wajen gudanar da binciken:
i.
Shin wannan binciken zai gano
bambance-bambancen da ake samu a tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani?
ii.
Shin wannan binciken zai taimaka wajen
fito da ire-iren bambance-bambancen da ake samu a tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani?
iii.
Shin wannan binciken zai bayyana wa ɗalibai da manazarta
da sauran al'umma alaƙar da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani?
1.7 Farfajiyar Bincike
Wannan
binciken kacokan ɗinsa zai duba nazari
ne a kan bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin gargajiya da na
zamani, bincike na musamman akan wasu daga cikin waƙoƙin sarauta na Alhaji
Musa Ɗankwairo da na zamani na gama-jama'a na Aminu Abubakar
Ladan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.