Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Wadaran Naka Ya Lalace: Sharhin Turke Da Salon Wakar Guguwar Sauyi Ta Aminu Abubakar Ladan (ALAn Waka)

ALLAH WADARAN NAKA YA LALACE: SHARHIN TURKE DA SALON WAƘAR GUGUWAR SAUYI TA AMINU ABUBAKAR LADAN (ALAN WAƘA)

Daga

Dano Balarabe Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07035141980
Ƙibɗau: danobunza@yahoo.com

Da

Muhammad Abubakar Zabi
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
08136844199
muhammadabubakarzabi@gmail.com

2016

Tsakure

Siyasa dama ce da jama’a ke samu ta walwala. A irin wannan lokaci ne ‘yan ƙasa ke samun sukunin bayyana ra’ayoyinsu dangane da manufofin gwamnati da kuma yadda ake mulkinsu ba tare da jin tsoro ba. Wakokin siyasa sun ginu ne bisa tarihi. Sun faro tun lokacin jihadin mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo inda suke yin amfani da su wajen yin kyamfen. Hausawa mutune ne masu sha’awar waƙa, duk lokacin da wani sabon al’amarin siyasa na jam’iyya ya zo musu, sai su shiga waƙe shi a inda suke bayyana yanaye-yanaye tsari da kuma sigoginsa. Ta wannan hanya ce ake riƙa tallata jam’iyyu da ‘yan takara ta hanyar bayyana manufofinsu da ƙudurorinsu ga jama’a. A cikin wannan takarda za a dubi ma’anar wasu kalmomin da ke cikin takenta yadda masana suka faɗa da kawo tarihin wanda ya yi waƙar wato, Aminu Abubakar Ladan (Alan waƙa), sannan a waiwayi sharhin waƙar ‘Guguwar Sauyi’ kan turakunta da salailan da ke cikinta. A ƙarshe, hanzari da kammalawa za su biyo baya kafin manazartar takardar da za ta biyo baya.

1.0              Gabatarwa

12. Jagora: An zaɓi ruɓa-ruɓa namu da sunan waƙiltar ka,

:A ba su kuɗi su miƙa mu hannu ƙwarya hannu bakka,

:Tunaninsu iyalinsu su tara abin da ba tamka,

:Suna tsoron talaucewa suna tsoron zama talaka,

:Sun zaɓi zama talakkawa a ranar komuwa gunka.

Amshi: Baƙar malfa baƙar jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar karab da gari.

(Waƙar Guguwar Sauyi ta Aminu Ladan Ala).

Al’ummar Nijeriya ta ga salon mulki iri daban-daban kama daga na Turawan mulkin mallaka tun kafin samun ‘yancin kai da na jamhuriyar farko na shekarar 1956 da na soja da kuma na farar hula mai cike da ruɗu, wata rana kuma, sai sojoji su karɓe. Haka aka ci gaba da yi har aka sami wasu sojoji suka fara rikiɗa daga soja domin komawa farar hula saboda irin mulkin da ke gudana a Nijeriya na halin ko-o-ho da wasu shugabanni ke yi domin su ne masu yin hukunci sun fi ƙarfin a hukunta su. Bugu da ƙari akwai dalilin ganin ba mai bakin magana sai shugaba. Idan mutum ya ce uffan ba na goyon bayan gwamnati ba, ba shakka ya san tasa ta ƙare. Wannan ya faru saboda wasu abubuwa da takardar za ta ambata nan gaba kaɗan. Marubucin/mawaƙin ya kai kukansa tare da na ‘yan ƙasa nagari wajen Allah da roƙon ya zaɓa musu shuwagabanni na kirki domin ‘yan ƙasa su sami sauƙi ga matsalolin da suke fuskanta da ba sai an faɗa ba domin, na wata ƙasa ya san su balle ɗan Nijeriya. Takardar za ta kawo sharhin saƙo/saƙonnin waƙar tare da salailan da ke cikinta. Kafin komi za a dubi ma’anar kalmomin da ke cikin taken takardar da ke buƙatar hakan ta yadda masana suka yi bayani. Ga su kamar haka:

2.0 Ma’anar Wasu Kalmomin da ke Cikin Taken Takarda

Kalmomin na da dama da yawansu zai hana mu ba kowace kalma nata kan labara sai dai a haɗe su ta hanyar kawo bayanan dan masana suka faɗa dangane da su. Kalmomin guda bakwai ne aka hango da ke son a ɗan dubi gurbin yadda aka yi amfani da su a cikin waƙar da za a yi sharhi. Akwai kalmar wadaran da lalace da sharhi da turke da salo da guguwa da kuma sauyi.

Kalmar wadaran da wadarai da wadai da waddai duk abu ɗaya suke nufi sai dai kowace da wurin da ake amfani da ita dangane da Karin harshe. An nuna a dubi ɗaya daga cikinsu idan ana neman ma’anar ɗaya. Wadarai a dubi wadai, waddai a dubi wadai, ma’anar wadai it ace, la’ana, ko tsine wa wani (Ƙamusun Hausa 2006:464).

Kalmar lalace kuma, an nuna a dubi kalmar lalata mai nufin ɓata wani abu. Haka ita kuma kalmar lalaci duk ‘yan gida ɗaya ne mai nufin rashin kataɓus ko rashin kuzari (Ƙamusun Hausa 2006:299,300).

An bayyana ma’anar kalmar sharhi da cewa a dubi sharha mai nufin rubutaccen bayani don ƙara fahimtar abu (Ƙamusun Hausa, 2006:409).

Ga abin da aka ce dangane da ma’anar kalmar turke: “Turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi (Gusau, 2008:370)”.

Ita kuma kalmar salo an ce “Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya wadda mawaƙi ya bi domin ya isar da saƙon da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa (Yahya, 2016:30)”.

A wani wuri kuma cewa aka yi, salo na nufin yayi ko sauyi ko launi ko fice (Ƙamusun Hausa, 2006:385). Har yanzu an sami wurin da aka fassara kalmar salo da style[1].

Ita kuma kalmr guguwa na nufin iska mai ƙarfin gaske wadda take miƙewa sama tana juyawa, (Ƙamusun Hausa, 2006:173). Kalmar sauyi kuma na nufin canji ko juyi (Ƙamusun Hausa, 2006:394).

A tamu fahimta kalmar wadaran na nufin yin tir da wani hali ko aiki da aka yi. Lalace na nufin fitar mutumin kirki daga kyawawan ɗabi’unsa da kuma ɗaukar munana ko nakkasar wani abu daga ingancin da aka sani gare shi. Sharhi a wurinmu na nufin ƙarin bayanin kan maganar da wani ya yi ko rubutun da aka yi. Turke da salo kuwa, mun dakata ga ma’anonin da aka bayar zuwa nan gaba. Kalmar guguwa da aka yi amfani da ita a cikin waƙar da za a yi sharhi kanta na nufin wani al’amari mai ban mamaki da bai taɓa faruwa da ake ganin zai faru dangane da zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a Nijeriya ta fuskar mai takara ya doke wanda ke saman kujera.

3.0 Taƙaitaccen Tarihin Aminu Abubakar Ladan (Alan Waƙa)

An haifi Alhaji Aminu ranar 11 ga watan Fabrairu a shekarar 1973, a unguwar Yakasai da ke cikin garin Kano. Aminu ya yi karatun firamare a makarantar Tudun Murtala yayin da ya yi sakandare a unguwar Dakata Kawaji. Alhaji Aminu ya cigaba da karatun gaba da sakandare a makarantar Fasaha da Ƙere-Ƙere da ke Kano wato, School of Technology Matan Fada Kano. Aminu ya sami takardar shedar karatun Diploma a fannin Art and Industrial Design. Har yanzu kuma, yana nan yana ci gaba da neman ilimin don kasancewarsa gishirin rayuwa.

Aminu marubuci ne kafin ya zama mawaƙi don ya rubuta littafai da suka haɗa da ‘Sawaba’ da ‘Baƙar Aniya’ da sauransu. Har yanzu yana da sha'awar rubutu a ransa don nakan tuna wani labari mai ɗaukar hankali da ya fara rubutawa a wani gida mai kama da wanda ya yi wa suna "Ƙuƙumi" wanda a halin yanzu yana nan yana rubuta shi tare da duba yiwuwar buga shi. A fannin sana'arsa ta waƙa a yau, za a iya cewa Aminu ya zarce tsara ƙwarewa da jajircewa da kuma sarrafa harshe tare da adana adabin Hausa. Hakan ya sa yake da kyakkyawar alaƙa da jami'o'i da kwalejojin ilimi, da har suke karrama shi tare da nazarin waƙoƙinsa. Aminu na da halastattun albam guda 27 a kasuwa daga albam na Alhaji Aminu magidanci ne, yana da mãta da 'ya'ya wanda suke zaune cikin farin ciki da walwala. Duk da dai Alan kan ce "Ni mai mata ne da neman ƙari kuma, mai 'ya'ya ne da neman ƙari". Fatarmu Allah ya albarkaci waɗanda yake da ya ƙara masu albarka ya kuma yalwata arzikinsa, ya ba shi ikon kula da su.

4.0 Sharhin Turken Waƙar Guguwar Sauyi ta Aminu Abubakar Ladan Ala (Alan Waƙa)

Waƙar ‘Guguwar Sauyi’ waƙa ce mai ɗauke da turken addu’a sai dai, akan sami wasu tubalan ginin turke da suka taimaka ga ginuwarsa. Babu shakka waƙar siyasa ce mai ɗauke da saƙon addu’a daga mawaƙin tare da bayyana halayen jama’arsa na wulaƙantar da kai da suke yi ga waɗanda ba su ko kai su ba balle su fi su. Haka kuma ya bayyana mafi yawan waɗanda aka zaɓa ba suna zuwa domin jama’arsu ba ne sai don kawunansu. Duk bayanan da za a yi a cikin wannan takarda zai tafi tare da rakiyar ɗa ko ɗiyan waƙar da ake sharhi kanta domin tabbatar da iƙirarin da aka yi.

4.1 Turken Addu’a a Cikin Waƙar Guguwar Sauyi

Kafin a shiga cikin waƙar don kawo hujjojin da ke tabbatar da cewa jigonta shi ne addu’a, sai a duba tun a baitin farko da mawaƙin ya yi a ga abin da ya fara faɗa. Ga abin da ya ce:

1.                  O Allah kaɗa guguwar sauyi Buhari Janar ya karɓi ƙasa,

Ku aje kube sauyi ya zo x2,

Ku aje kibau sauyi ya zo x2,

Masu sanduna sauyi ya zo,

Mai barandami sauyi ya zo,

Bana ƙuri’a fa za ta aje malfa x2

Sai godiya hamdullahi,

Allah alhamdullahi x3

Idan aka lura da abin da mawaƙin ya faɗa a baitin farko za a fahimci roƙon Allah ne ya yi ta hanyar yin addu’a da roƙon Allah kan matsalar da ke ci masa tuwo a ƙwarya. Matsalar da mutum ke fuskanta da buƙatar da yake da ne ke sanya shi yin addu’a, balle matsalar da mawaƙin ke addu’a kanta ba tasa kaɗai ba ce, ta shafi mafi yawan al’ummar Nijeriya. Saboda ɗaukin da yake yi na Allah ya karɓa masa addu’arsa har ya sanya ya biyo da maganar da ke nuna kamar an gaya masa an karɓa masa, inda ya ci gaba da cewa, a aje kube da kibau da sanduna da barandami da faɗar bana ƙuri’a za ta nuna an karɓi addu’arsa. Ba wannan kaɗai ba, ga ladabin addu’a idan buƙata ta biya, godiya ake ga wanda aka yi roƙon gare shi kuma, ya biya buƙatar da aka roƙa. Za a ga haka a inda yake godiya yana cewa, “Sai godiya hamdullahi, Allah alhamdullahi”. A nan, muna da fahimtar yana magana da talakawan ƙasa ne ta duban abubuwan da ya jero da faɗar a aje su ganin kamar an ɗauko su ne an fito zuwa neman ‘yanci domin, ba a haɗa mai mulki da mai hali da waɗannan abubuwa da aka kawo domin ba daidai suke da su ba.

Bayan jagoran waƙa ya faɗi abin da ke ƙona masa zuciya da yin addu’a, ‘yan amshinsa ma ba a bar su a baya ba sai da suka yi addu’a irin ta jagora inda suka ce:

Amshi: Baƙar Malfa baƙar jarfa,

Mai shanye jinin jikin talaka,

Allah kaɗa guguwar sauyi,

Buhari Janar karab da gari.

Ba a nan kaɗai ba, daga amshin farko har zuwa na ƙarshe akwai addu’a a ciki. A idon manazarta duk abin da mawaƙi da ‘yan amshi suka fi faɗa a cikin waƙa dole a sami yana daga cikin saƙon da suke son isarwa ga jama’a. A wani wuri sukan ƙasƙantar da kai tare da nuna cewa abubuwan da suka faru da ke nan suna faruwa babu shakka mu muka janyo wa kanmu. Tare da haka kuma, sai su yi addu’a domin neman Allah ya magance waɗannan matsalolin da ke faruwa. Za a ga irin wannan a baiti na uku inda suka ce:

3.  Jagora:Subbahanaka rabbi mun gode mu jaddada godiya gunka,

Amshi:Baƙar malfa baƙar jarfa

Jagora:Allah Alhamdulillahi gwani sarki kinin bauta ba ma yi maka

Amshi:Shanye jinin jikin talaka

Jagora: Duk yadda ka so da bayinka ba mai tuhuma a mulkinka

Amshi:Baƙar malafa baƙar jarfa

Jagora:Muna tuba da aibunmu ka yafe mana laifuka

Amshi:Shanye jinin jikin talaka

Jagora: Allahu ka dubi bayinka an tashi hana mu bautar ka

Amshi:Baƙar malfa baƙar jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar karab da gari.

A wurin da jagora ke cewa, Allahu ka dubi bayinka an tashi hana mu bautar ka kuka ne yake yi tare da addu’ar neman Allah ya kawo mafita ga matsalolin da suka taso. A farkon baiti na huɗu kuma, addu’a ce yake yi ganin bala’o’in da ke faruwa sun yawaita tare da wuce tunanin mutane kuma, ba abin da ya janyo haka sai rashin adalcin shuwagabanni ga mabiyansu. Ga abin da suka faɗa:

4. Jagora: Masifu sun buwaye mu ka saukar mana jinƙanka

Amshi: Baƙar malfa baƙar jarfa

Jagora :Baƙin mulki na zalunci ake a ƙasarmu ba shakka

Amshi: Shanye jinin jikn talaka

…………………………………

Haka kuma, abin da zai ƙara tabbatar da cewa babban saƙon da waƙar ke ɗauke da shi addu’a ce shi ne baiti na ishirin da biyu da na ishirin da uku kamar haka:

22. Ka yi mana kariya Allah da dangina masoyanka,

Masoya masu bin waƙa bisa lura da sam barka,

Allah ga General namu ka karɓi nufinsa bawanka,

Ka yo sanadi na ceton mu ta hanyar ba shi mulkinka,

Ya share mana kukanmu mu bar ƙangin jinin kaska.

23. Allah ka amsa roƙonmu muna kuka da roƙon ka,

Masifu sun buwaye mu muna kwaɗayi ga tanyonka,

A nan zan sa ɗigon aya a kan nusar da bayinka,

Ka sa waƙar da na tsara ta zan ƙaimi ga bayinka,

Ala mai waƙe al’umma masoyin sahibi naka.

Idan ma aka tsaya ga baitocin da ke sama guda biyu da aka kawo masu lamba ta 22 da 23, za su gamsar kan cewa jigon waƙar guguwar sauyi addu’a ce. A baiti na 22 za a ga cewa layi na 1 da na 3 da na 4 roƙo ne ga Allah kan matsalolin da ake fuskanta cikin ƙasa. A baiti na 23 ma idan aka dubi layin farko za a ga cewa mawaƙin ya faɗa da bakinsa cewa addu’a ce yake yi a inda ya ce, Allah ka amsa roƙonmu muna kuka da roƙon ka. Haka layi na biyu ma addu’a ce tare da faɗin irin matsalolin da ake ciki na damuwar rayuwa. Haka ma layi na huɗu akwai addu’a a ciki inda ya ce, Ka sa waƙar da na tsara ta zan ƙaimi ga bayinka. Da wannan ɗan taƙaitaccen bayani mai karatu na iya fahimtar cewa, saƙon da wa\ɗark e ɗauke da shi babba addu’a ce.

4.2 Ƙananan Jigogin Waƙar Guguwar Sauyi ta Aminu Abubakar Ladan

Bayan babban jigon addu’a da waƙar ke ɗauke da shi akwai ƙananan saƙonnin da ke cikinta da mawaƙin ya kawo. Daga cikin ƙananan saƙonnin da waƙar ke ɗauke da shi akwai:

4.2.1 Labartawa

Labartawa na nufin faɗar wani abu da ya faru ko ke kan faruwa ga wanda ake ganin bai san shi ba ko kuma, ya san da shi da manufar isar masa da wani saƙo. Akwai wuraren da mawaƙin ya kawo, idan aka dubi baiti na goma da na sha ɗaya da na goma sha uku da na goma sha huɗu da kuma na goma sha biyar za a ga cewa labartawa ne yake yi ga mai karatu ko mai sauraro kan halayen waɗanda ake zaɓe domin su waƙilci jama’arsu. Maimakon su yi waƙilci nagari sai suka lalace suka mayar da kansu almajirai ga waɗanda ko bara za a yi su suka fi cancanta da yin bara ba jama’armu ba. Ga baiti na 10-15 a nazarce su a gani ba tare da amshi ba kamar haka:

10-Jagora: Arewar babu mai tari suna tsoron gidan sarƙa

Sun zamto damisar kwali hayagaga a hotonka

Kyanwar Lami cikin ɗaki ba cizo babu bautar ka

Ruɓaɓɓu a ciki namu suna kuma ci da bautarka

Suna inuwa ta addini suna cutar da bayinka.

11.Jagora: Suna miƙa wulayarmu ga mai ƙi a yi bautar ka

Kamar dabba suke jan mu da zalinci muna kuka,

An ƙona wajen karatunmu ana kishin mu ɗaukaka

An ƙone kasuwancinmu a yau baƙi suna shakka

:Ba mai sha’awar ya zo gun da hulɗar kasuwa barka

12.     :An zaɓi ruɓa-ruɓa namu da sunan waƙiltak ka,

:A ba su kuɗi su miƙa mu hannu ƙwarya hannu bakka,

: Tunaninsu iyalansu su tara abin da ba tamka,

: Suna tsoron talaucewa suna shakkar zama talaka,

:Sun zaɓi zama talakkawa a ranar komuwa gunka.

13. Jagora:Sun maishe mu kamar kaji, a ba ka hatsi ka sa bakka,

: Da an buga tambarin zaɓe mutane babu tsoron ka,

:Su sa riga, su sa hula, su ɗau hoto suna ba ka,

:Su ce ma je ka mammanna a ɗau na abinci am ba ka,

:Da sun hau karagar mulki da ƙyar su gane sunanka.

14 -  Jagora: Duw wanda ya hau kujera nan abin ƙin sa a ce sauka

:Ya hau ɗamara ta shiryawa da zango ya yi zai sauka,

:A hau fasali da tsarawa ana son sabuwar doka,

:Ana wai za a sabunta a yo doka da ba kyanka,

:Kundi na gudanuwar mulki su tsarmo sabuwar doka.

15 -  Jagora:Su daidaita da son ransu kawai don kar a ce sauka

:Cikin dimokaraɗiya ake son rai ake hauka

:A mulkin nan na al’umma na zaɓan ra’ayin sonka,

:Mulki daga al’umma aka ce cikin zaɓi na son ranka,

:Ana yi don mutane ne misalin ba ka ‘yancinka,

Ta la’akari da baitocin da ke sama ne ya sanya muka raɗa wa takardar suna “Allah Wadaran Naka Ya Lalace”. Bisa ga ƙa’ida kowa zaɓen sa aka yi don haka, babu dalilin da zai sa mutum ya nakkasa kansa har ya komo baya ga wanda bai dace ya zama Karen farautarsa ba. A farkon baiti na goma cewa mawaƙin ya yi, babu mai yin ko tari a cikin ‘yan arewa saboda tsoron ɗauri. A fahimtarmu ba tsoron ɗauri ba ne, lalacewa ne suka yi suka koma bayan wasu suna fadanci domin tasu buƙata ba ta jama’arsu ba. Idan aka ba su kuɗi domin wata buƙatar masu ba su kuɗin, sai su karbi kuɗin ko da za a cuci al’ummarsu ne domin kansu suke waƙilta a can ba jama’arsu ba. Da jama’arsu suke waƙilta da ba su karbi kuɗin da ake ba su ba, kamar yadda mawaƙin ya nuna. Aikinsu kawai shi ne shiga inuwar addini ana cutar da bayin Allah kamar yadda layin ƙarshe a baiti na goma ya nuna. A farkon baiti na goma sha ɗaya mawaƙin ya faɗi cewa suna ba maƙiyansu goyon baya saboda kwaɗayin abin da suke samu amma, ba su damu da wulaƙancin da ake yi wa jama’arsu ba. Wannan ke tabbatar da samuwar ƙaramin jigon labartawa cikin wannan waƙa.

4.2.2 Sukar Ra’ayi

Suka na ɗaya daga cikin ƙananan saƙonnin da waƙar ‘Guguwar Sauyi’ ke ɗauke da su. A fahimtarmu suka na nufin faɗar illar wani mutum ko wani abu ga jama’a domin su ƙi shi ko su ƙi wannan abu nasa da yake tare da shi, ko kuma domin a guje shi saboda wata manufa da yake da ita mummuna zuwa ga mutane ko kuma domin wata cuta da ya taba yi wa mutane. Mutum ba ya taba suka abin da yake so sai dai ya yaba shi. Haka kuma, an fi samun sukar ra’ayi a siyasa da sauran abubuwan da mutum biyu ke nema bayan an tabbatar da mutum ɗaya ke samun sa. Waƙa ce da aka yi kan siyasa mai cike da abubuwa daban-daban da suka shafi siyasa ga abin da ya bayyana na zahiri a ciki. Al’adar siyasa ce a yabi wani a soki ra’ayin wani, kamar yadda aka gani a cikin kowane amshi a layuka biyu na farko. Ga abin da aka faɗa a cikin layukan biyu:

Baƙar malfa baƙar jarfa

Mai shanye jinij jikin talaka

Kalmar jarfa na nufin (sn, mc) (i) shasshawa ko tsaga da ake yi don ado ko don magani (ii) abin da ake yin shasshawa da shi. A cikin wannan waƙa ma’ana ta biyu ce ta fi dacewa da abin da waƙar ke nufi wato, ƙarfen da ake yin shasshawa da shi ga dabbobi marasa lafiya.

4.2.3 Zambo

Zambo na nufin ƙaga wa mutum Magana wadda za ta muzanta shi ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba; maroƙa sun fi yin haka a cikin waƙa.[2]Bayan wannan akwai wurin da sukar ra’ayin ta rikiɗe ta koma zambo kai tsaye saboda tsananin ƙiyayya. Za a ga wannan a baiti na ishirin inda mawaƙin ke cewa:

20. Matakin kansula har kan president zabi mai son ka

Ku lura da kyau talakkawa kuna zango tsaka-tsaka

Muna dama ta ƙarshe ne gaba ɗaya ba ragen ɗakka

Ƙoyaye kwarkwata tamu a yo zabi a gunshe ka

Da kunne ya ji mun tsira da zalunci na ‘yan iska

Idan aka dubi layi na ƙarshe da aka ture rubutunsa za a ga kalmar ‘yan iska zagi ne kai tsaye ga masu zaluntar jama’a, musamman ta bangaren waƙilcin siyasa.

5.0 Salailan Da Ke Cikin Waƙar ‘Guguwar Sauyi’

Ba sai an ambaci ma’anar salo a nan ba domin bayaninsa ya gabata a shafi na biyu. Akwai salailai masu dama da suka fito cikin waƙar ‘Guguwar Sauyi’ kamar yadda za a gani a cikin sharhin salailan da za a yi. Daga cikin salailan da aka samu a cikin waƙar sun haɗa da waɗannan:

5.1 Salon Buɗewa

Waƙar ‘Guguwar Sauyi’ na da mabuɗin da mawaƙinta ya yi amfani da shi domin buɗe waƙarsa tun a baiti na farko inda yafara da addu’a, yana roƙon Allah ya tare da faɗarburinsa a fili inda ya ce:

1.Jagora: O Allah kaɗa guguwar sauyi Buhari Janar ya karɓi ƙasa.

Ku aje kube sauyi ya zo × 2

Ku aje kibau sauyi ya zo × 2

Masu sanduna sauyi ya zo

Mai barandami sauyi ya zo

  Bana ƙuri’a fa za ta aje malfa ×2

Sai godiya hamdullahi

Allah alhamdulillahi ×3

Bayan wannan buɗewa da mawaƙin ya yi ta fuskar neman Allah ya kaɗa guguwar da za ta zo da sauyin shugabanci a Nijeriya tare da faɗar buƙatarsa dangane da wannan sauyi idan ya zo. Bai wuce ba sai da ya faɗi yadda yake buƙatar sauyin ya kasance kamar yadda ya nuna a baiti na ɗaya. Haka su kuma ‘yan amshi, duk a mabuɗin sun amsa wa jagora da cewa:

Baƙar malfa baƙar jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar ya karbi ƙasa.

5.2 Salon Rufewa a Cikin Waƙar Guguwar Sauyi

Yadda aka sami salon buɗewa a cikin waƙar haka ma akwai salon rufewa wato closing doxology. Akan sami waɗannan salailai a cikin mafi yawan waƙoƙin sha’irai matuƙar ba mantuwa ta same su ba ko yanayin waƙar domin wasu waƙoƙi ba a buɗa su ko rufe su kan ƙa’idar da aka sani ta buɗe waƙa da rufe ta ba. Mawaƙin ya rufe waƙarsa a baiti na ishirin da uku kamar haka:

23:Jagora:Allahu ka amsa roƙonmu muna kuka da roƙonka

:Masifu sun buwaye mu muna ƙwaɗayi da tanyonka

:A nan zan sa ɗigon aya a kan nusar da bayinka,

:Ka sa waƙar da na tsara ta zam ƙa’imi ga bayinka,

: Ala mai waƙe al’umma masoyin sahibi naka,

5.3 Salon Kamance

Salon kamance bangare ne na babban salon siffantawa. Salo ne wanda ke bayyana sifar wani abu ta fuskar kwatanta shi da wani abu daban tare da amfani da kalmomin da za mu ba suna mizani.[3]Waƙar na ɗauke da salailan kamance guda uku da masana suka yi bayani da suka haɗa da kamancen fifiko da kamancen daidaito da kuma kamancen kasawa. Akwai salailan kamance da suka fito cikin waƙar ‘Guguwar Sauyi kamar haka:

5.3.1 Salon Kamancen Fifiko

Kamar yadda sunansa yake nuni kamancen fifiko yakan ɗauki abubuwa biyu: da wanda yake ƙoƙarin ya siffanta da kuma wanda da shi ne yake ƙoƙarin ya siffanta na farkon, sai y ace wannan na farkon ɗin ya fi wannan da ya kawo ma wand aka rig aka sani. Wato dai y ace gwarzona ya fi wancan da ka sani.[4] Akwai kalmomoin mizanin da suka haɗa da : ya fi, ta fi, ya zarce, ta zarce, ya wuce da dai sauran irinsu. Akwai kamancen fifiko a cikin waƘar ‘Guguwar Sauyi’ a baiti na takwas da na goma sha biyu inda za mu ɗauki misalinmu a baiti na takwas kamar haka.

8. Jagora: A sa riga ta Islamu a yo wauta ƙazantarka,

:Sannan fa a jingina kan mu waƙilai babu mai tanka,

:Mu yi burin mutuwa bayi idan mun taka alhakka,

:Tutur ata fau ba za mu yi ba saboda abin da mun shuka,

:Mu bar Allah maƙaginmu mafi girma da ɗaukaka.

Idan aka dubi layin ƙarshe za a ga cewa, mawaƙin ya fifita Allah a kan kowa da komi inda ya yi amfani da kalmar mafi. Babu shakka haka maganar take domin babu mai girma sai wanda Allah y aba shi kuma, Allah ke ɗaukaka kowa a ban ƙasa. Haka kuma duk yadda mutum ya girma ya sami ɗaukaka, bay a kamar Allah.

5.3.2 Kamancen Daidaito

Akwai kamancen daidaito a cikin waƙar ‘Guguwar Sauyi’ da mawaƙin ya yi amfani da shi wajen haɗa abubuwa biyu da suke daidai da juna. Wannan salon a da kalmomin mizani da suka haɗa da awa,kamar, wa, i, ƙoƙa, ya, ce kake da kuma daidai da.[5] Akwai misalign kamancen daidaito a cikin baiti na 9, 10, 11, 13, 15, 16, da 17. Ga baiti na 13 domin ganin misalin da mawaƙin ya kawo na kamancen daidaito kamar haka:

13. Jagora:Sun maishe mu kamar kaji, a ba ka hatsi ka sa bakka,

:………………………………………………………

…………………………………………………….....

5.3.3 Kamancen Kasawa

Kamar sauran kamance-kamancen da aka yi bayani a sama, kamancen kasawa ma na da wasu kalmomin mizani da ake gane shi da su a cikin waƙa ko rubutu baki ɗaya. Kalmomin mizani da ake amfani da su a cikin gane kamancen kasawa sun haɗa da bai kai ba, ya kasa, gara, bai yi kamar, ba ta yi kamar da sauransu. Idan aka dubi wannan waƙa za a sami salon kamancen kasawa a baiti na 16 kamar haka:

16 - Jagora:O amma ko mulukiya ba ta yi kamar haka hauka

………………………………………………….

Idan aka dubi rubutun da aka ture da ke cikin baitin da ke sama za a fahimci salon kamancen kasawa ne mawaƙin ya yi amfani da shi inda ya ce:

O amma ko mulukiya ba ta yi kamar haka hauka.

Wannan na nuna cewa, salon mulkin mulukiya ma bai kai tsananin mulkin da mawaƙin ke magana a kai ba. A fahimtar maaƙin, salon mulkin mulukiya ne ƙoli ga zaluntar jama’a duk da hakanan, salon mulkin da mawaƙin ke zance a kai bai ya zarce na mulukiya da rashin adalci. Ke nan, mulkin mulukiya bai kai tsananin wanda mawaƙin ke magana a kai ba.

5.3.4 Salon Gangara

Akan samu baiti a cikin waƙa wanda kan ƙunshi wani ɗango wanda zaren labarinsa bai cika ba sai a wani ɗango mai bin sa. To irin wannan saƙa ita ce ake kira salon gangara a nazaarin waƙa.[6] Ga binciken da muka yin a wannan waƙa mun tarar da akwai salon gangara a cikin dukkan amshin da ke cikin waƙar kuma, an same shi a cikin baiti na goma sha uku. Ga misalin amshi da baiti na 13:

Amshi  :Baƙar malfa baƙar jarfa

:Mai shanye jinin jikin talaka

:Allah kaɗa guguwar sauyi

:Buhari Janar ya karɓi ƙasa.

Abin da ake nufi da salon gangara shi ne, a sami a cikin baitin waƙa ɗaya mai layi biyu ko uku ko huɗu ko kuma biyar kowane layi bay a tsayi da kansa domin ba da cikakkiyar Magana har sai ya jingina ga wani layi mai bin sa. Idan aka nazarci amshin da ke sama za a tarar da babu layin da ke tsayawa da ƙafarsa domin ba da kammalalliyar ma’ana. Maimakon haka dole sai ya haɗa da ɗan uwansa kafin a sami ma’ana cikakkiya. Misali, inda y ace ‘Baƙar malfa baƙar jarfa’ ma’ana ba ta fito ba amma a layi na biyu da ya ce ‘Mai shanye jinin jikin talaka’ ma’ana ta cika. Haka kuma, cewar da ya yi ‘Allah kaɗa guguwar sauyi’ akwai sauran magana a baya da ake sauraro domin ma’ana ta cika. Layi na biyu kuwa, shi ya taimaka ga cikar maganar da ke a layi na uku. Duk wurin da aka sami irin wannan maganar da ba ta cika a layi na farko sai na biyu ko na uku ko na huɗu ko kuma na biyar, shi ake nufi da salon gangara. Ga wani misali a baiti na goma sha uku inda kowane layi ya dogara ga ɗan uwansa ga ba da cikakkiyar ma’anar maganar da mawaƙin ya yi kamar haka:

13. Jagora:Sun maishe mu kamar kaji, a ba ka hatsi ka sa bakka,

: Da an buga tambarin zabe mutane babu tsoron ka,

:Su sa riga, su sa hula, su ɗau hoto suna ba ka,

:Su ce ma je ka mammanna a ɗau na abinci am ba ka,

:Da sun hau karagar mulki da kyar su gane sunanka.

5.3.5 Salon Aron Kalmomi

A cikin mafi yawan waƙoƙin da marubuta ke rubutawa da waɗanda ke rerawa na Hausa akan sami salon aron kalmomi daga wasu harsuna da suka haɗa da Turanci da Larabci, wani lokaci har da Fulatanci da sauransu. A cikin waƙar da muke sharhin jigo/turke da salailanta mawaƙin ya ari kalmomin Turanci da na Larabci ya yi amfani da su a cikin waƙarsa. Idan aka dubi baiti na 1,2,8,18,20,21 da kuma na 22 duk akwai kalmomin da mawaƙin ya ara daga wasu harsuna ya yi amfani da su a cikin waƙarsa. A baiti na 1 akwai kalmar hamdullahi da alhamdulillahi, a na 2 akwai haɗari da sahibul sabariyya, a na 8 akwai kalmar alhaƙƙa, na 18 akwai kalmar Turanci ta weapon, a na 20 akwai kalmomi biyu na Turanci kansila (councilor) da ta president, a na 21 kuma akwai kalmar janar (General) da kuma kalmar general a baiti na 22.

Kalmomin da ke cikin baitin farko na Larabci ne masu nufin godiya ga Allah da godiya ta tabbata ga Allah. Kalmar haɗari (Khaɗar) na nufin abu mai matsala da ya kamata a shiga saunar sa. Sahibul sabariyya kuwa na nufin ma’abuci haƙuri. Alhaƙƙa na nufin gaskiya a baiti na takwas inda weapon da councilor da president da general duk kalmomin Turanci ne. Weapon na nufin makami. Councilor na nufin wanda aka zaba a mazabar ƙaramar hukuma domin ya waƙilci jama’ar da ta zabe shi. Kalmar president na nufin shugaban ƙasa inda general ke nufin babban muƙami na gidan soja da ake ganin na ƙoli ne ko ba ƙolin-ƙoliyo ba. Duk da bayanin da aka kawo ya dace a kawo ko da baiti ɗaya a matsayin misali. Ga baiti na 20 don ƙara tabbatarwa:

20 - Jagora: Matakin kansila har kan President zaɓi mai son ka,

:…………………………………………………….

……………………………………………………..

5.3.6 Salon Luguden Adabi

A baben adabi da ake lugude a nan su ne irin su Karin Magana da salon Magana da baƙar Magana da tatsuniya da kirari da tashe da makamantansu. Idan aka so a saka su yadda aka san su suka kasa shiga a waƙa sai a kakkarya su a faffalle su a niƙe su a ɗiyan waƙa a bar mai sauraro da dabarar ƙoƙarin gano dawa ce aka niƙe ko masara?[7] Akwai salon luguden adabi a cikin waƙar ‘Guguwar Sauyi’ a baiti na shida da na ishirin inda aka yi amfani da karin Magana. A baiti na shida an yi amfani da Karin maganar nan da Hausawa ke cewa ‘A bugi jaki a bugi taiki’ amma saboda lalurar waƙa ga yadda mawaƙin ya saka Karin maganar:

Jagora: Arewa ƙasarmu ya Allah ta zamma kufai kamar bukka

: Ana ta bugu a kan taiki shi ko jakki yana harka

:…………………………………………………

Karin maganar da ke cikin baiti na ishirin ita ce ‘In kunne ya jiya jiki ya tsira’. Saboda lalurar waƙa sai mawaƙin ya juya ta ta koma ‘Da kunne ya ji mun tsira da zaluncina ‘yan iska’. Ga yadda abin ya zo cikin baitin kamar haka:

:…………………………………………………

:………………………………………………….

Jagora: Da kunne ya ji mun tsira da zalunci na ‘yan iska  

6.0 Hanzari

Hausawa sun ce ‘Wani hanzari ba gudu ba’. Mu kuma a nan muna sheda wa al’umma cewa duk abin da aka gani a cikin wannan aikin sharhi namu, ba ra’ayinmu ba ne mun dai faɗe shi gwargwadon yadda muka fahimce shi daga abin da mawaƙin ya faɗa tare da ‘yan amshinsa. Ba a yi domin cin zarafin kowa ba sai dai, an san cewa mai kaza aljihu baya jimrin as. Idan aka sami kuskuren harshe daga gare mu, muna ba da uzurin kasancewar mu ‘yan tara da ba su kai goma ba. Haka kuma, takardar ta yi ɗan yawan da ba za ta bari a saka ratayen waƙar a ciki ba ta yadda za a ga abin da mawaƙin ya faɗa sai dai, duk bai hana saƙon isa ga waɗanda aka yi abin domin su ba.

7.0 Kammalawa

An raɗa wa wannan takarda suna ‘Allah Wadaran Naka Ya Lalace: Sharhin Turke Da Salailan Da Ke Cikin Waƙar Guguwar Sauyi Ta Aminu Abubakar Ladan (Alan Waƙa) ganin sunan ya ɗan dace da abubuwan da mawaƙin ya bayyana a cikin waƙarsa. Takardar na ɗauke da gabatarwa da bayanin ma’anonin kalmomin da ke cikin takenta. Biye da shi kuma taƙaitaccen tarihin mawaƙin ne aka kawo. Bayan tarihin mawaƙin a taƙaice an biyo da sharhin babban turken waƙar wanda yake shi ne, turken addu’a ko jigon addu’a/roƙon Allah. Bayan babban turken da aka kawo an biyo da ƙananan turakun waƙar da suka haɗa da labartawa da sukan ra’ayi da kuma zambo. Daga nan ne aka cirata zuwa ga sharhin salailan da waƙar ta ƙunsa da suka haɗa da salon buɗewa da na rufewa da salon kamancen fifiko da na daidaito da kuma na kasawa. Bayanin salailan bai tsaya a nan ba sai da aka tabo salon gangara da salon aron kalmomi na wasu harsuna da mawaƙin ya yi amfani da su a cikin waƙarsa da suka haɗa da kalmomin Turanci da na Larabci. Takardar ba ta tsaya a nan kaɗai ba sai da ta kwance zare da abawan salon luguden adabin da ya fito a cikin waƙar. Bayan abubuwan da aka lissafo akwai bayanin hanzarin marubuta takardar da aka kawo da ke biye da rakiyar kammalawa da manazarta a ƙarshe.

Manazarta

Bunza, A. M. (2009) Narambaɗa. Ibrash Islamic Publication Centre ltd. Surulere, Lagos.

Dangambo, A. (1984). Rabe-rabe Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph.

Daura, H. K (2010) “Nazarin kan Waƙar Rayuwa Ta Fati Musa” Himma Journal Of Contemporary Hausa Studies, Vol. 2, Number 4. Department Of Nigeria Languages, Umar Musa Yar’adua University, Katsina State

Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited, Kano.

Gusau, S.M (1995) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Fisbas Media Service, Kaduna

Gusau, S.M (2003) Jagoran Nazarin waƙar Baka.Benchmark publishers ltd.

Kano, B. U. (2006) Ƙamusun Hausa, Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Omar, S. (2013) Fasahar Mazan Jiya: Nazari A Kan Rayuwa Da Waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja. Media Service Ltd, Sokoto

Umar, M. B (1985) Ɗanmaraya Jos da Waƙoƙinsa. Ibadan University Press Limited.

Yahya, A .B (1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna; Fisbas Media Service, Kaduna

Yahya, A. B. (2001) Salo Asirin Waƙa, Fisbas Media Service, Kaduna.

 



[1] Hausa Metalangage shafi na 105

[2] A dubi Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano shafi na 489

[3] A dubi Salo Asirin waka na Abdullahi Bayero Yahya shafi na 67

[4] Daidai da lamba ta 3 shafi na 73

[5] A dubi Salo Asirin Waka na A. B. Yahya shafi na 68

[6] A dubi Salo Asirin Waka shafi na 97

[7] A dubi Narambada shafi na 187-188

 

Post a Comment

0 Comments