Yadda Za Ku Yi Amfani Da Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Da Ke Aiki A Kan Kowace Kwamfuta

    Manazarta: Sani, A-U. (2022). Yadda za ku yi amfani da baƙaƙen Hausa masu ƙugiya da ke aiki a kan kowace kwamfuta. An cirato daga: https://www.amsoshi.com/2022/09/yadda-za-ku-yi-amfani-da-baaen-hausa.html.

    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya

    Yadda Za Ku Yi Amfani Da "Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya" Masu Aiki A Kan Kowace Kwamfuta Ko Waya

    Abu-Ubaida Sani

    Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Nigeria Email:  abuubaidasani5@gmail.com  or  abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng WhatsApp:  +2348133529736

    Matashiya

    Rubutun Hausa na amfani da waɗansu baƙaƙe na musamman da ake kira "Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya." Manyan baƙaƙe masu ƙugiya su ne "Ƙ", "Ɗ", da "Ɓ". Su kuma ƙananan sun kasance kamar haka: "ƙ", "ɗ", da "ɓ". Kasancewar keyboard ɗin kwamfuta bai zo da waɗannan baƙaƙe ba, a bisa dole ake bin matakan samar da su. Waɗansu daga cikin yunƙuri da aka yi na samar da hanyoyin rubuta baƙaƙe masu ƙugiya a na'urori sun yi nasara sannan sun samu karɓuwa.

    Tsarin rubutun Rabi'at da Abdallah su ne suka fi fice a matsayin hanyoyin rubuta Hausa tare da baƙaƙe masu ƙugiya. A dukkannin hanyoyin biyu, akan girke (installing) tsarin rubutun (fonts) a kan na'ura a matsayin Tsarin Rubutu (fonts style). Idan aka girke tsarin rubutun Rabi'at a kwamfuta sannan aka zaɓe shi yayin yin rubutu, kai tsaye za a riƙa yin amfani da waɗannan baƙaƙe:

    i. "X" zai ba da "Ɗ"
    ii. "Q" zai ba da "Ƙ"
    iii. "V" zai ba da "Ɓ"
    (Haka ma abin yake ga ƙananan baƙaƙe).

    Ga tsarin rubutun Abdalla kuwa:

    i. "SHIFT + {" zai ba da "Ƙ"
    ii. "SHIFT + }" zai ba da "ƙ"

    iii. "SHIFT + [" zai ba da "Ɗ"
    iv. "SHIFT + ]" zai ba da "ɗ"

    v. "SHIFT + |" zai ba da "Ɓ"
    vi. "SHIFT + ~" zai ba da "ɓ"

    Naƙasu

    i. Kwamfuta ba za ta iya gane waɗaɗannan baƙaƙe ba har sai idan an girke mata tsarin rubutun a kanta.
    ii. Idan aka ɗora rubutun a wata kwamfutar da ba ta da wannan tsari, to rubutun zai ɓaci.
    iii. Idan aka ɗora wannan rubutu a intanet, to zai ɓaci.
    iv. Dole ne mai rubutu ya riƙa sauyawa tsakanin tsarin rubutu daban-daban idan abin da yake rubutawa ya ƙunshi Hausa da Ingilishi da kuma alamomin rubutu na musamman.

    Cigaba Da Ka Samu

    Abin farin ciki shi ne, kamfanin Microsoft sun zo da mafita mai sauƙi ga wannan matsala. Akan kira tsarin baƙaƙe masu ƙugiya da suka kawo da suna "Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari" (ma'ana dai waɗanda za a iya amfani da su a kan kowace na'ura).

    Domin amfani da wannan cigaba da aka samu a kwamfutarku, ku bi matakan da aka zayyana a ƙasa:

    i. Je zuwa "Control Panel"
    ii. Buɗe "Language Region" (Ku yi amfani da wurin searching domin nemo shi). Duba hoto a ƙasa:
    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari
    iii. A cikin language region ɗin ku dubo jerin sunayen harsuna
    iv. Daga cikin jerin sunayen harsunan, ku zaɓi "Hausa (Latin-Nigeria)"

    LURA: Nau'ukan Hausa da ke wurin sun haɗa da "Hausa "Latin-Nigeria", "Hausa (Latin-Niger)", da "Hausa (Latin-Ghana)"

    v. Ku danna "Save".

    Shi ke nan!

    Aiki Da Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari A Kan Kwamfuta

    i. Idan kuka buɗe fayil ɗin Microsoft domin fara rubutu, to ku nemo inda aka rubuta "ENG" a "taskbar" na kwamfutar (ko dai a sama ko a ƙasa ko a gefe, ya danganta da inta "taskbar" ɗin kwamfutarku yake).
    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari
    ii. Ku danna kan "ENG" ɗin inda za ku ga wannan:
    HAU Hausa (Latin)
    Hausa Keyboard
    iii. Ku danna kansa
    iv. Yanzu wurin da da aka rubuta "ENG" za ku ga ya koma "HAU"
    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari
    Aiki ya yi!

    Yayin rubuta baƙaƙe masu ƙugiya, ku yi amfani da:

    i. "ALT GR + K" zai ba da "Ƙ"
    ii. "ALT GR + X" zai ba da "Ɗ"
    iii. "ALT GR + V" zai ba da "Ɓ"

    Haka ma ga ƙananan baƙaƙe:

    i. "alt gr + k" zai ba da "ƙ"
    ii. "alt gr + x" zai ba da "ɗ"
    iii. "alt gr + v" zai ba da "ɓ"

    You may also like:

    Idan kuna da tambaya ku rubuta a wurin "Comment" da ke ƙasa.

    7 comments:

    1. Mun gode.

      Wani ya faɗa mini cewa wai amfani da insert symbols ya fi sauƙi. Shi ne na ce masa:

      Please, ka shawarci mai wancan rubutu idan ka san shi da cewa ya yi updating, domin an wuce wannan babi tun tuni. Amfani da *Insert Symbols* tsohuwar hanya ce mai tattare da matsaloli da suka haɗa da:

      1. A iya kan Microsoft yake amfani. Yanzu idan zan yi rubutu a kan Facebook ko wani website da kwamfutata, sai in yi yaya ke nan? Ka ga zancen insert symbols bai ma taso ba.

      2. Akwai manhajoji da dama da idan ka ɗora baƙaƙe masu ƙugiya da aka ɗuko daga wurin, to za su jirkice ne abin da ake ce wa *Bogus Rendition*.

      3. Babu typist ɗin da zai ce zai maka amfani da insert symbol sai dai idan sabon koyo ne. Kafin ka yi typing ɗin 1,000 words da insert symbol, mai amfani da universal hooked-letters zai iya typing ɗin 1,500 words.

      4. Yanzu ba ma kowane Office pakage ke zuwa da waɗannan symbols ba. Yawancin sababbin pakkages ba sa zuwa da su saboda already an saka su a tsarin da aka yi bayani cikin rubutun, wato zaɓen Hausa Latin.

      ReplyDelete
    2. Watau wani babban abin ƙayatarwa a nan shi ne, duk na'urar da aka ɗora wannan rubutu, to haƙiƙa zai bayyana da lanƙwasarsa ba tare da an sake lalubo wata hanya ko dabarar sake rubuta su. Ko da kuwa an aika da rubutun ta kafar intanet ne. Muna godiya da wannan tsari da ya kasance gagarumin cigaba a fagen fasaha sadarwa.
      An gaida Amsoshi!

      ReplyDelete
    3. Na wayoyi akwai apps ɗinsu.

      Shi dai na kwamfuta ko da an tura rubutun cikin waya ba zai jirkice ba.

      Sannan idan da kwamfuta mutum ke Whatsapp, Facebook ko waɗansu chats na daban, to zaibiya amfani da su lafiya ƙalau.

      ReplyDelete
    4. Tambaya ta a Nan ita ce, ta Yaya za a yi amfani da bakaken Hausa a wayar hannu?

      ReplyDelete
    5. A yi downloading ɗin Swift keyboard daga Play Store.

      ReplyDelete

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.