Ticker

6/recent/ticker-posts

Waɗansu Daga Cikin Dalilan Da Suka Janyo Kiki-Kaka Tsakanin Gwamnati Da ASUU

Ga dalilai guda tara (9) daga cikin dadlilan da suka janyo kiki-kaka tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU). Zan saka su a sigar mahawara domin saukin fahimta ga mai karantawa. Da fatan wannan gudunmawar za ta taimaka wajen lalubo bakin zaren ta yadda za a magance matsalar.

Waɗansu Daga Cikin Dalilan Da Suka Janyo Kiki-Kaka Tsakanin Gwamnati Da ASUU

DAGA

DR. Saidu Ahmad Dukawa
Shugaban Sashen Nazarin Gudanar da Mulki
Bayero University Kano

Waɗansu Daga Cikin Dalilan Da Suka Janyo Kiki-Kaka Tsakanin Gwamnati Da ASUU

1. GWAMNATI: Ba za mu cire ku daga tsarin IPPIS ba, saboda tun daga ranar da muka fara amfani da shi muke samun rarar kudi daga abinda muke biya na albashi.

ASUU: Ba duka rarar da ku ke gani ce ta samu daga toshe kofar zurarewar kudi ba; IPPIS ta yankewa duk wani ma’aikacin jami’a [babba da karami] albashinsa; misali: Babban Malami (Senior Lecturer) yana rasa naira dubu arba’in (N40,000) duk wata [na yi misali da matakin da nake ne, saboda yakini da nake da shi];

Kun yi mana alkawarin za ku gyara irin wannan kuskuren, idan muka koma daga wancan yajin aikin, amman kimanin shekara biyu da komawarmu, har yau ba ku gyara ba; kuma babu tabbas yanzu ma idan muka amince muka koma idan ba za ku kwata karya alkawari ba.

2. GWAMNATI: To yanzu ku je mun yi muku karin albashi. Daga yanzu duk babban malami yana da karin Naira dubu talatin (N30,000). Amman ku janye yajin aikin. [wannan yana nufin mai rasa 40,000 za a dawo masa da 30,000; rashin ya ragu zuwa 10,000; amman da iyalinsa da duniya za su dauka an yi masa karin albashi].

ASUU: A’A, ku rike karinku. Ku cika mana alkawarin da kuka yi mana a baya, kamar haka:

a) Ku daina yankar mana albashi da sunan IPPIS;

b) Ku dawo mana da kudin da kuka yanka tun daga lokacin da kuka saka mu a IPPIS; sannan

c) Ku yarda mu zauna mu yi yarjajjeniya game da abinda ya kamata a kara mana a tsari na babu cuta, ba cutarwa.

3. GWAMNATI: To ai kudin da kuke nema sun yi yawa, gwamnati ba ta da shi a yanzu.

ASUU: to ai rabi hakki ne na wadanda muke wakilta, kuma ba su ce sun yafe ba. Ku ne kuka yankar musu babu gaira babu dalili. Kuka ki dawo da wanda kuka yanka, kuka cigaba da yanka, har kudin ya taru. Rabi kuma alkawari ne kuka dauka domin gyara jami’o’in da inganta yanayin koyo da koyarwa. Idan kuka hana, jami’o’in za su durkushe.

4. GWAMNATI: To ai idan an bayar da kudin inganta jami’o’in, rashawa ake tafkawa, sai aga kamar ba a bayar ba!

ASUU:  

a) Mu dai a biya wakilanmu hakkokinsu;

b) Ragowar kudi kuma ku baiwa wakilanku (Shugabanni da jagororin jami’o’in); alabarshi

c) Duk wanda kuka kama ya tafka rashawa ku hukunta shi, za mu goyi bayanku.

5. GWAMNATI: To ai yanzu ba ma kwa iya yin wani binciken a zo a gani, ga laifuffuka kala-kala da kuke tafkawa, ga shegen taurin kai!!!

ASUU:

a) Ai yana daga cikin dalilin da ya sa muka yi yarjajjeniya da ku cewa duk shekara biyar za ku rika nada “Visitation Panel” (wani kwamiti mai karfi wanda yake wakiltar Shugaban Kasa a Jami’ar Tarayya, ko Gwamna a Jami’ar Jiha) domin ya ziyarci kowace jami’a, ya aiwatar da binciken kwakwaf, ya baiwa gwamnati shawara akan matakan gyara. Amman sai ku ki nada kwamitin har sai mun yi muku yajin aiki. A yanzu haka kwamitin karshe da kuka nada har yanzu ba ku fitar da shawarwarinsa ba ballanta ku aiwatar.

b) Binciken ilimi kuwa muna yin iya abinda yanayi ya bamu damar yi. Mu ma alfaharinmu ne mu yi fiye da haka, amman yanayin ya yi kunci; shi ya sa muke so ku inganta yanayin ko ma yi fiye da abinda muke yi; amman

c) Taurin kai kuwa, na neman ku fahimcemu ne, ko a gudu tare a tsira tare.

6. GWAMNATI: Duk maganar nan da ake yi don ba kwa son IPPIS ne, saboda ta toshe muku kafar zuwa jami’o’i da yawa kuna koyarwa; ba kwa tara hankalinku wuri guda, kuna cutar da dalibanku.

ASUU: gyara wannan matsalar shi ya fi komai sauki:

a) Ku daina bude jami’o’i barkatai; ku daina baiwa ‘Yankasuwa lasisin bude jami’o’i barkatai; sai a samu saukin zawarcin Malamai daga tsofaffin jami’o’i; kuma masu hadamar cikinmu su rasa kasuwa;

b) Ku inganta mana albashinmu, sai ya rage matsin da yake tura wasu neman wurin da za su je koyarwa; sannan

c) Ku inganta tsofaffin jami’o’in ta hanyoyin da muka baku shawara, sai su kara yawan daliban da su ke dauka. A yanzu tsofaffin jami’o’i ba sa iya daukar fiye da abinda suke dauka saboda kun gagara inganta yanyinsu; wannan ta sa ake samun karancin gurbi ga masu bukatar shiga jami’a; ku kuma sai kuke gwammacewa ku bude sababbin jami’o’i ba tare da la’akari da a ina za a samo Malaman da suka dace ba.

7. GWAMNATI: To, a matsayinku na masu ilimi, ku yi tunanin yadda jami’o’i za su iya rike kansu da kansu mana, a madadin dogaro da gwamnati!

ASUU: Mu ma muna son hakan; amman dole sai gwamnati ta samar da yanayi mai kyau na yin hakan tukunna. Alal-misali, jami’a nawa ce take da “Dam” [matattarar ruwa] a kasar nan, har wacce take ta koyon aikin noma ce? Alhali aikin noma kadai zai iya rike kowace irin jami’a!

8. GWAMNATI: To ba sai dalibai su rika biyan kudi fiye da wanda suke biya a yanzu ba!

ASUU: An zo wurin!!! Watau so ake ace wanda duk ba zai iya biyawa dansa madudan kudi ba ya hakura da tura dansa jami’a, komai basira da hazaka da Allah ya baiwa ‘dan? Watau karatun jami’a ba na ‘dan Talaka ba ne?

To muna yi muku nasiha da cewar wannan halayyar, ta mayar da ilimi kasuwanci, ba za ta haifarwa da Kasar ‘Da mai ido ba.

Kasahen da ake buga misali da su cewar dalibai ne suke ragewa gwamnati nauyin kudin karatu suna da tsari na tallafi da kuma na rance, kuma tsarin ba ya karyewa. Mu kuwa kun karya tsarin bayar da tallafi sannan ba ku samar da tsarin rance ba.

Mu da muke tare da daliban mun san jibin goshin da wasu suke yarfewa kafin su iya biyan kudin da kuke rainawa a yanzu. Muna jan hankalinku cewar idan kuka ce Talaka ya fitar da rai daga muhimmin al’amari irin ilimi, to kuna ginawa Kasar mummunan ramin mugunta!

9. GWAMNATI: To sai ku je da taurin kanku, ku cigaba da yaijin aikin, mu dai ba za mu biya mutum albashi ba matukar yana yajin aiki; domin akwai doka da ta hana biyan mai yin yajin aiki albashi; mu kuma ba za sabawa doka ba, don ku ji da kyau, ehe!!!

ASUU: Mantawa kuka yi, ai an tsara albashin Malamin jami’a bisa sharadin zai rika gudanar da ayyuka kashi uku, kamar haka:

a) Binciken ilimi: wannan ya hada da duk wani karatu da Malami zai yi, tun daga karatun jarida zuwa na mujalla, da na yanar-gizo, har zuwa littattafai, domin inganta koyarwa;

b) Koyarwa: wannan ya hada da dirasa a cikin aji, da tsara jarrabawa, da gudanar da jarrabawa, da duba takardun jarrabawa da kuma fitar da sakamakon jarrabawa; sai

c) Hidima ga al’umma: wannan kuma ya kasu kaso biyu:

i. Hidima a cikin jami’a, wanda ya hadar da daukar nauyin gudanarwa, kamar kasancewa shugaban sashe (HOD), shugaban Tsangaya (Deen), Shugaban Cibiya (Darakta); da kuma

Kasancewa cikin kwamitocin gudanarwa: duk wani al’amari na jami’a yana da kwamitin kula da shi; da abinda ya shafi dalibai, da wanda ya shafi Malamai, da wanda ya shi sauran ma’aikata, da wanda ya shafi kadarorin jami’a, da na tsaro, da na kiwan lafiya, da na binciken ilimi, da komai da kamai;

ii. Hidima ga al’umar gari: wannan ya hadar da amsa gayyatar lacca ga kungiyoyin al’umma, da amsa tambayoyi da fatawouin ‘Yan Jarida, da gudanar da shirye-shirye na musamman a kafafan yada labarai; da rubuce rubuce masu alfanu ga al’umma ko a jaridu, ko mujallu, ko kafafan sada zumunta na zamani, da makamantansu.

To tambayar anan itace: wane bangaren albashin za ku rike? Wace shaida ku ke da ita cewa Malamai sun gudanar da yajin aikin a fannin binciken ilimi da himtawa al’umma?

Yajin aikinmu a fannin koyarwa ne kuma muna sane da cewa hutun jaki da kaya aka ne, saboda sai mun biya duk wani kwantan aiki da ya ke kanmu. Sabanin haka zai bayu ga ba za mu yi aikin da ba a biya mu ba. Don haka duk wani kwantai na aiki sai dai a nemo wasu, su yi shi, a biya su. Kuma wannan yana nufin babu wanda zai fita daga jami’a a yanzu, sannan babu wanda zai gusa daga ajin da yake zuwa aji na gaba!

KAMMALAWA

Tirkashi! Mai karatu, ka ji wannan tirka-tirkar. Kai me ka fahimta daga wannan tsaka-mai-wuyar? Sannan wace shawara za ka bayar domin a fitar da jaki daga duma kuma a fitar da A’I daga rogo?

Allah Ta’ala ya bamu mafita kyakkyawa.

16 – 9 – 2022 

Post a Comment

0 Comments