Miyar Ugun
Ugun wani ganye ne da ya kasance ɗanyen haki mai kunnuwa manya-manya. Idan aka yanka shi yana da ɗan yauƙi-yauƙi. Yawanci akan shigo da wannan ganye ne daga yankin kudancin ƙasar nan.
Mahaɗin
Miyar Ugun
Akwai abubuwan da za a tanda idan za a
haɗa miyar ugun abubuwan, ga su kamar haka.
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Kayan yaji
v. Kifi
vi. Magi
vii. Mai
viii. Ruwa.
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Tumatur
xii. Ugun
xiii. Wake
Yadda
Ake Miyar Ugun
Idan aka jajjaga kayan miya, sai a daka kayan yaji da daddawa. Za
kuma a hura wuta a saka mai da albasa. Yayin da suka soyu, sai a yi sanwa a
saka kayan ɗanɗano.
Daga nan, za a surfe wake a saka a ciki. Idan suka tafasa, sai a wanke kifi da ruwan zafi a cire ƙayar da ke
jikinsa a zuba a ciki. Bayan tukunya ta tafasa sosai, sai a wanke ugun da gishiri sannan a
yanka a zuba a ciki.
Da zarar miyar
ta gama dahuwa, sai maganar sauƙe tukunya. Kusan akan ci wannan miya da kowane nau’in tuwo.
Tsokaci
Shi ma ugun wani ganye ne daga cikin
ganyaye da mutanen kudancin Nijeriya suke amfani da shi a wajen abincinsu sama
da yadda Hausawa ke ta’ammuli da shi. Ganyen na ugun na da matuƙar amfani ga lafiya kamar yadda
bincike ya nuna.
Miyar Ogobonno
Ogobono wani ganye ne
shi ma kamar sauran ganyaye da ake miya da su. Sai dai shi yana da yauƙi kamar lalo. Idan aka yi miya da shi
har ya fi lalo yauƙi sosai. Wannan
ganye ma akan shigo da shi ne daga yankin kudancin ƙasar nan.
Mahaɗin
Miyar Ogobonno
i. Albasa
ii. Attarugu
iii. Bushasshen kifi
iv. Daddawa
v. Ɗanyar kubewa
vi. Gishiri
vii. Kayan yaji
viii. Magi
ix. Manja
x. Ogobonno
xi. Ruwa
xii. Tattasai
xiii.
Tumatur
xiv. Nama
(idan akwai)
Yadda
Ake Miyar Ogobonno
Yanayin miyar Ogobonno da lalo kusan ɗaya ne. Sai dai ita wannan miyar ba a so ta dahu sosai. Hakan na faruwa
ne a sanadiyyar ganyen ogobonno ba shi da ƙarfi sosai. Akan yi amfani da wannan
miyar wajen cin kusan dukan nau’o’in tuwo tun daga kan tuwon masara da semo da makamantansu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.