Taiba
Taiba abinci ne da ake yi da garin kwaki, garin kwaki rogo ne da ake sarrafawa a ƙasashen Kudu. Garin za a tuƙa ya zamo taiba. Yara matasa da ƙananan yara da mata da ‘yan makarantar boko sun fi cin taiba. Saboda abinci ne da nan take ake haɗa shi a ci shi ba da ɗaukar lokaci ba.
i. Garin Kwaki
ii. Ruwa
Da garin kwaki ake taiba. Za a ɗora ruwa cikin tukunya a bar shi har sai ya tafasa. Daga nan, za a kawo garin kwaki a riƙa barbaɗawa
ana juyawa. Bayan an gama sanyawa, za a tuƙa
sosai domin kada ya yi gudaji. Da zarar ya dafu, taiba ya samu kenan. Ana iya
yin amfani da farin gari ko jan gari yayin tuƙa taiba. Sai dai jan gari ya fi kyau.
An fi cin taiba da miyar yauƙi,
musamman guro/kuɓewa.
Kafa
i. Masara
ii. Ruwa
Masara za a surfe a jiƙa
sannan a kai markaɗe bayan ta jiƙu. Bayan an dawo da ita daga markaɗe,
za a tace ta da matata. A gefe guda kuwa, za a ɗora
ruwa bisa tukunya. Bayan ruwan ya tafasa, sai a zuba wannan ƙullu
da aka tace ciki. Za a yi ta tuƙawa
har sai ta haɗe gaba ɗaya
kuma ta yi tauri. Ana kwashewa cikin jarida ko leda ko wani nau’in ganye na
musamman.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.