Miyar Albasa
Albasa na ɗaya daga cikin ganyayen Bahaushe wanda yake nomawa. Tana matuƙar kama da gadali. A saman albasa akwai lawashi (ganye). A ƙasa kuwa, akwai asalin ƙwallon albasar wanda ke ruɓanye, wani saman wani. Shi ya sa ma Bahaushe ke da kacici-kacicin da ke cewa: “Cikin ma da cikin cikin, cikin ma da cikin, “wato albasa.
Mahaɗin
Miyar Albasa
Akwai abubuwan da za a tanada idan za
a haɗa miyar albasa. Abubuwan sun haɗa
da:
i. Albasa
ii. Attarugu
iii. Gishiri
iv. Kayan yaji
v. Kori
vi. Magi
vii. Mai
viii. Ruwa
ix. Nama ko kifi (idan da hali)
Yaddda
Ake Miyar Albasa
Ana ɗora tukunya ne sannan a
zuba albasa a soya a jajjaga albasa mai yawa tare da tarugu. Sannan sai a yanka nama ƙannan a soya su tare. Idan an yanka
naman za a zuba a cikin
tukunya ya soyu sosai. Za a saka magi da gishiri da kori da kayan yaji. Ruwan
da ake sanyawa yayin sanwa kaɗan ne. Bayan sanwa ta tafasa, za a
zuba albasa mai yawa da aka yayyanka kuma aka wanke. Akan ci wannan miya da shinkafa ko kuskus ko tuwon semo da sauransu.
Tsokaci
Kusan birni da ƙauye ana miyar albasa, duk da cewa an fi samunta a birane.
Babu garin da ba a samun albasa a cikin garuruwan ƙasar Hausa. Duk da haka, ba kowa ke shan miyar
albasa ba, a dalilin warinta da wasu mutane ke ji musamman maza.
Miyar Karas
Karas na ɗaya daga cikin kayan marmarin Bahaushe. Akan ci shi haka nan ko da ba a haɗa shi da komai ba. Kamar dai yadda aka gani a sama (cikin
bayanan wasu nau’o’in abinci), karas na iya kasancewa mahaɗin wasu nau’o’in abinci na daban. Amma a wannan gaɓa, za a yi maganar karas ne a matsayin
babban mahaɗin miya.
Mahaɗin
Miyar Karas
Akwai wasu kayan haɗin da ake buƙata
yayin samar da miyar karas. Abubuwan sun
haɗa da:
i. Albasa
ii. Albasa
iii. Gishiri
iv. Karas
v. Kayan yaji
vi. Magi
vii. Mai
viii. Nama (idan da
hali)
ix. Ruwa
x. Tafarnuwa
xi. Tarugu
xii. Tattasai
Yadda
Ake Miyar Karas
Akan samar da miyar
karas ne kamar
yadda ake samar da
ta kabeji. Wurin da suka bambanta shi ne, a maimakon a sanya kabeji, a nan akan
zuba karas ne. Akan wanke karas sosai sannan a yayyanka shi sala-sala
kafin a zuba. A yayin sanwarta, ba a zuba ruwa sosai. Akan ci wannan miyar da shinkafa ko kuskus ko tuwon shinkafa ko sakwara da dai makamantansu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.