Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Auren Kisan Wuta a Musulunci

TAMBAYA TA 153

Assalamu alaikum

Mene ne hukuncin Auren Dibar wuta a Musulunci?

Shin hukuncin Yana da bambanci idan Macce ce ta shirya Auren Dibar wutar ba tare da sanin tsohon Mijinta ba?

Mene ne hukuncin idan matar da Mijin suka shirya Auren Dibar wutar?

Sannan hukuncin

yana da bambanci idan sabon mijin da Aka Aura yana da Masaniya akan Auren Dibar wuta ne za a yi da shi?

 (daga Barrister Isma'il)

AMSA

Wa alaikumus salam wa rahmatulLah.

Wannan tambayar mun riga mun amsa irinta achan baya. Amma saboda muhimmancin Mas'alar, da kuma yawan faruwarka a cikin al'ummah, sai na ga cewa ya zama wajibi mu sake amsa wannan dinma.

Imamuz-Zahabiy (rah) ya fada a cikin shahararren littafinsa mai suna "KITABUL-KABA'IR" akan shafi na 141, Laifi na 53, yana cewa:

Hadisi ya inganta daga Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (ra) yana cewa: "MANZON ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) YA TSINEWA MAI AUREN KISAN WUTA, DA KUMA WANDA AKA YI AUREN KISAN WUTAN DOMINSA".

Imam Tirmidhy (rah) ya ce:

Aiki a bisa wannan fahimtar (rashin halarcin auren kisan wuta ta kowacce fuska) ya tabbata agun ma'abota ilimi. Daga cikinsu akwai

Umar bn Khattab,

Uthman bn Affan

Abdullahi bn Umar (Allah shi Ƙara yarda dasu).

kuma wannan shi ne fahimtar FUƘAHA'U daga tabi'ai.

Imamu Ahmad bn Hanbal da Imamun Nisa'iy su ma sun ruwaito irin wannan hadisin Da isnadai masu inganci.

Wani mutum ya tambayi Abdullahi bn Umar (ra) cewar:

"YAYA KAKE GANI? Shin ya halatta in auri matar da wani mutum ya saki domin in halatta ta a gareshi??

Sai ya amsa masa da cewar:

A'a bai halatta ba. sai dai in za ka aureta, to ka aureta domin kwadayin zama da ita, idan kaga ta yi maka shikenan ka zauna da ita. Idan kuma ba ta yi maka ba ka sake ta. (Amma auren kisan wuta haramun ne). Ya ci gaba da cewa: MUN KASANCE MUNA ƘIRGA SHI (irin wannan auren) AMATSAYIN KWARTANCI AZAMANIN MANZON ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam).

Imamul-Athram da Ibnul-Munzir sun daga Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) yana cewa:

"BA'A TAƁA ZUWA MIN DA MASU AUREN KISAN WUTA BA, FACHE SAI NA JEFESU (RAJAMUWATO JIFA IRIN NA HADDI).

Wani Mutum ya saki matarsa (Saki uku) dama kuma 'Yar baffansa ce, Sai daga baya ya dawo yana nadama, sai wani mutum kuma ya zo yake tambayar Sayyiduna Abdullahi bn Umar (radhiyalLahu anhu) cewa: Shin ya halatta inje in aureta, (daga baya in sake ta) domin in halasta masa ita??"

Sai ya ce masa "Zaman Zina sukeyi ko da sun kai shekara 20 suna tare. In dai an daura auren da wannan niyyar.

Imam Ibrahim An-Nakha'iy ya ce IN DAI DAYAN CIKIN MUTUM UKUN NAN (wato mijin farko, ko miji na biyu, ko kuma ita matar) in dai WANI DAGA CIKINSU ya yi NUFIN AUREN KISAN WUTA, TO AUREN NA BIYUN DANA FARKON DUK SUN LALACE. (Dama bai halatta ba). KUMA DUK DA HAKA MATAR BA TA HALATTU GA WANCAN MIJINTA NA FARI BA (Koda ta dawo hannunsa).

Imam Hasanul-Basary ma ya ce: In dai dayan cikin mutum ukun nan ya yi niyyar auren kisan wutan, to auren ya 'baci.

Daga Cikin wadanda suke kan wannan fahimtar akwai:

IMAMU MALIK

SUFYANUTH THAURY

IMAMU AHMAD BN HANBAL

IMAM LAYTHU BN SA'AD.

Irin wannan auren bai halatta ma tun farko adaura shi ba (Mutukar Malamai da waliyyan auren sun fahimci niyyar masu auren) Kuma ya kamata hukuma ta rika ladabtar da dukkan wadanda aka samesu da hannu a ciki.

WALLAHU A'ALAM.,

DAGA ZAUREN FIƘHU JUNE 15 2013 (ANYI RUBUTUN NAN TUN SHEKARU 12 DA SUKA GABATA). YA ALLAH KA SANYA IKHLASI CIKIN DUKKAN AYYUKANMU AMEEN.

EMAIL ADDRESS: zaurenfiƙhu@gmail.com

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments