Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Rage Tsananin Sha'awa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam menene maganin rage sha'awa? Ina da yawan sha'awa abu kadan yeke tada mun sha'awa. Malam ko akwai wata magani da zan sha don daina sha'awa ko rageta, wallahi ina da matsaninciyar sha'awa wanda ko da yaushe inna cikinta shi ne nake tsoron faɗawa halaka, don Allah a taimaka ni budurwa ce.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ita sha'awa sinadari ce ta musamman wacce Allah ya gineta ajikin Ɗan Adam kamar irin su barci, yunwa, kishirwa, etc. Don haka bata da abin da ke danneta sai dai idan mutum ya tarbiyyantar da zuciyarsa akan guje ma hakan.

Kuma ita sha'awa tana daga cikin amanonin da Allah Maɗaukakin Sarki ya ajiye ajikin bayinsa, Kuma yayi iyakance halastattun wuraren da ake ajiye wannan amanar. Kuma yayi bayanin cewa waɗanda suka kasa kiyaye wannan amanar, sakamakonsu ita ce Wuta in har basu tuba ba.

Allah Maɗaukakin Sarki ya gaya ma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam wata nasiha wacce ya umurceshi ya gaya ma muminai. Yace

قُلْ لِّـلْمُؤْمِنِيْنَ يَغُـضُّوْا مِنْ اَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوْا فُرُوْجَهُمْۗ ذٰلِكَ اَزْكٰى لَهُمْۗ اِنَّ اللّٰهَ خَبِيْرٌ بِۢمَا يَصْنَـعُوْنَ

"ka gaya ma muminai maza su runtse idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, wannan shi yafi tsarkaka garesu.. domin Allah masani ne game da abin da suke aikatawa". (Surah: An-Noor, Ayat: 30)

وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ ...

"ka gaya ma muminai mata su runtse daga idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu". (Surah: An-Noor, Ayat: 31)

Wannan umurni ne daga Allah (SWT) zuwa ga Matayen Muminai, bayan kuma ya gargadi Mazaje Muminai.

Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya bama dukkan Samari da 'Yan mata shawara. Yace "YAKU TARON SAMARI!! WANDA YAKE DA IKON ƊAUKAR NAUYIN IYALI TO YAYI AURE. DOMIN SHI (AURE) YAFI SANYA RINTSEWAR IDANU DA KUMA KIYAYE AL'AURA. WANDA BASHI DA IKO KUMA TO YAYI AZUMI DOMIN SHI (AZUMI) TAKUMKUMI NE".

To kinga dole sai kin kiyaye idanunki daga kalle-kallen haramun, ki kiyaye zuciyarki daga tunanin saɓa ma Allah, Kuma ki shagaltar da jikinki da zuciyarki wajen yawaita azumi da sauran ayyukan bin Allah.

Idan kuma kina da dama da iko to kije kiyi aure kibi sunnar Anmabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) shi yafi.

lallai ki kamewa daka gane-gane domin kallace-kallacen wasu abubuwa da hotunan tsiraici masu motsa sha'awa yana kai mutum zuwa haram. Idan kina chating da samari mai motsa sha'awa kiji tsoron Allah ki daina. Ki yawaita yin azumi Ki daina hirar batsa da maza ko mata yan'uwanki.

Ba zai yiwu kina kalle-kallen abin da Allah ya haramta miki ba, sannan ki rika zargin kanki wai kina da Qarfin Sha'awa ba. Kowa da kike gani yana da ita ajikinsa. Amma tsoron Allah ne ke sanya kowa ya kiyaye.

Daga cikin magungunan Musulunci waɗanda ake amfani dasu wajen dakile sha'awa akwai

1. SHAJARATU MARYAM: Bishiya ce wacce ake amfani da ita don magance matsalolin Mata. Kuma Idan namiji yasha, tana cire masa sha'awa sosai daga jikinsa da zuciyarsa.

2. Ki Yawaita shan Lemon tsami (Idan baki da Olsa). Ko kuma Jar kanwa ('Yar Qalilan).

3. Ki samo kuzbara busassa wanda akayi garinta kwatankwacin karamin cokali sai azuba aruwan mai sanyi da yamma har zuwa asuba sai asanya sukari asha, In shã allah yana saukaka tsananin sha'awa ga namiji ko mace.

4. Ki samo wani haki da'ake cemasa ARRAJLA sai arika tafasawa anashan sa shima yana saukaka tsananin sha'awa ga maza ko mata, zaki iya samun sa amma sai dai a Kano.

5. Ki samo Zait Kafuur sai ki rika diga ɗan kaɗan acikin kofin shayi, idan ana shan wannan yana kashe tsananin wutar sha'awa.

6. Ki samo YANSUN da KAKO sai ki rika tafasawa kina sha, shima yana saukaka tsananin sha'awa.

7. Ki samo kwayoyin SALAK Irin wanda masu lambu suke shukawa yafito sannan su dasa shi yagirma yazama SALAK, to wannan kwayoyin da'ake yafawa su zaki samo sai kirika tafasawa kinasha, wannan hanya yana yanke tsananin sha'awa gaba ɗaya, sannan wanda yake fama da yawan mafalakai koda yaushe amma da wannan hanyar za'a iya samun waraka.

Ubangiji Allah yabamu dacewa, masu yawan yimana tambaya akan yadda zasu rage tsananin sha'awa ga hanya. Lallai ga wanda yake da tsananin sha'awa ko bashida da mata. ko bata da miji, kuma babu halin yin Aure to amaimakon yin Istiminai (musterbution) to kwara bin ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin domin asami sauki!!!

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments