Citation: Maimota, A. S (2021). Kallo Ya Koma Sama: Makomar Ƙagaggun Labaran Hausa a Yau. Harsunan Nijeriya Volume XXIX. Center for Research in Nigerian Languages, Translation & Folkore, Bayero University, Kano. Pg 38-53
KALLO YA KOMA SAMA: MAKOMAR ƘAGAGGUN LABARAN HAUSA A
YAU
Daga
Aishatu Shehu Maimota
Tsakure
Wannan takarda ta bibiyi makomar rubutattun ƙagaggun labaran Hausa a yau. An fara da kawo yadda masana suka
bayyana ma’anar rubutaccen ƙagaggen labari sannan aka
bibiyi tarihin wanzuwarsa kamar yadda masana irin su Yahaya (1988) da Furniss
(2000) da Mukhtar (2004) suka bayyana. Duba da bayan sai takardar ta binciki
yadda aikin ƙagaggun labarai ya ci gaba
musamman a ƙarni na 21. Daga bayanan
masana sai aka fahimci akalar rubutattun ƙagaggun labaran Hausa tana juyawa a lokuta daban-daban, sannan ana
samun sauye-sauyen zamani a harkar rubutun ƙagaggun labarai. Domin haka maƙalar ta bibiyi yadda aikin rubuta labari da wallafarsa tare da
cinikinsa ya juya daga takarda zuwa shafukan intanet. An gudanar da wannan
bincike ne ta hanyar tattaunawa da marubuta labaran Hausa daban-daban, an gana
da wasu makaranta da masu bugu da sayar da littattafai, da jami’an gwamnati
masu ruwa da tsaki wajen tace ayyukan adabin Hausa. Wannan bincike ya gano an
sami koma baya ƙwarai a harkar rubutu da
bugu da sayar da littattafan Hausa. Haka kuma an gano wannan koma baya ta samu
ne sakamakon ɓullowar ƙagaggun labaran Hausa a
shafukan sada zumunta daga wurin sababbin marubuta na intanet. Haka zalika
binciken ya gano waɗannan labarai na intanet suna da tasiri ƙwarai a zukatan masu karanta su waɗanda yawanci matasa ne. an
kuma gano yadda mrubuta shafukan intanet suke cinikin waɗannan labarai a intanet.
Daga ƙarshe takardar ta hasko makomar ƙagaggun labaran Hausa tare da bayar da shawarwari na yadda za a
magance matsalar.
Kalmomin bincike: ƙagaggen
labari, intanet, shafin sada zumunta.
1.0 Gabatarwa:
Rubutaccen ƙagaggen labari na Hausa wallafa ce da ake baza kolin hikimomi a
zube, ba a tsari na waƙa ba, ba wasan kwaikwayo
ba, ba kuma a siga ta alƙaluman lissafi ba, sai dai
yakan zo a zube cikin shafuka, da zummar sadar da wata manufa da mawallafi
ya ƙirƙira. An fahimci cewa an rubuta ire-iren waɗannan labarai a mabambanta
lokuta, hakan ya sa ake kallon su bisa rukuni-rukuni. Wato akwai waɗanda aka yi zamanin Turawan
Mulki, da waɗanda suka
samu sakamakon gasa ta 1933 da waɗanda aka wallafa bayan samun ‘yancin Nijeriya, akwai kuma waɗanda aka kira adabin
kasuwar Kano, da kuma waɗanda suka samu a ƙarni na 21 waɗanda ake wallafawa a
shafukan sada zumunta na intanet.
Wannan takarda ta bibiyi yadda makomar ƙagaggun labaran Hausa
take a yanzu ta yadda karance karance ya koma intanet. An fara da bibiyar
ma’ana da tarihin wanzuwar ƙagaggun labaran Hausa
kamar yadda magabata suka samar. Takardar ta kawo bayani kan yadda harkar
wallafar littattafan ƙagaggun labarai da cinikinsu ta koma a yau, sannan aka
bibiyi wanzuwar ƙagaggun labaran Hausa a shafukan sada zumunta na
intanet da yanayinsu da kuma irin tasirin da suke da shi a wajen masu karanta
su tare da irin karɓuwar da suka samu a
wajen al’umma.
1.1
Hanyoyin
Gudanar da Bincike
An gudanar da wannan bincike ta hanyar tattaunawa da
marubuta ƙagaggun labaran Hausa na littattafai da na intanet,
haka kuma an tattauna da masu harkar bugu da sayar da littattafai. Haka kuma an
tattauna da makaranta ƙagaggun labaran Hausa musamman masu bibiyar na
shafukan sada zumunta. An kuma gana da jami’an gwamnati da ke da alhakin kula
da tace ayyukan adabin Hausa. An kuma bibiyi ayyukan da masana suka gudanar kan
abin da ya shafi ƙagaggun labarai na Hausa.
1.2
Bitar
Ma’anar Ƙagaggen Labari na Hausa a Taƙaice
Masana da
malamai irin Yahaya da Ɗangambo (1986) da Mukhtar
(1993) da Ɗangambo (2008) da Mukhtar (2004) da Malumfashi (2006) da Asiya
(2012) da Adamu (2013) da Abu Sabe (2016) sun yi bayani dangane da ƙagaggun labaran Hausa. Duba da waɗannan bayanai na masana, za a iya bayyana rubutaccen ƙagaggen labari da duk wani rubutu da aka yi a shimfiɗe ta sigar shafuka, wanda
ya ƙunshi labarin da ba lalle ne ya auku ba amma kuma akasari ana
tsara shi a kan rayuwa ta zahiri, da nufin isar da wani saƙo ga al’umma.
1.3
Taƙaitaccen Tarihin
Wanzuwar Ƙagaggun Labarai na Hausa
Dangane da tarihin wanzuwar ƙagaggun labaran Hausa
masana kamar Yahaya (1988) da Mukhtar (2004) sun tabbatar da rubutaccen ƙagaggen labari ya fara
ne daga rubuce-rubucen Turawan mulkin mallaka a ƙoƙarinsu na samar da kayan
karatu ga ɗalibai masu koyon Hausar
book, hakan ya sa su wallafa gajerun ƙagaggun labarai daga
tatsuniyoyin Hausawa. Masanan sun tabbatar da cewa gasar da aka yi ta samar
da ƙaggun labarai da Hukumar Talifi ta saka ya dasa
harsashin samar da ƙagaggun labarai daga Hausawa ‘yan ƙasa, inda aka buga
labarai guda biyar da suka kai ga nasara, su ne; Ruwan Bagaja da Shaihu
Umar da Ganɗoki da Idon Matambayi da kuma Jiki
Magayi. Tun daga wannan lokaci aka ci gaba samun wallafe-wallafe
na ƙagaggun labarai daga Hausawa, musamman maza da suka
sami ilimin book.
Furniss (2000) ya tabbar da cewa daga farkon shekarun
1990 mata sun yi ruwa da tsaki a harkar rubutun ƙagaggun labarai na
Hausa, sakamakon ilimin bai ɗaya na kyauta daga gwamnatin ƙasa, hakan ya sa an buɗe makarantun boko da
dama, haɗe da na yaƙi da jahilci, domin haka
mata da dama sun sami wannan ilimi. Mukhtar (2004) ya tabbatar da samuwar wani
sabon nau’in adabi da aka kira ‘Adabin kasuwar Kano’, wanda ya fara samuwa
daga ƙarshen shekarar 1980 ya yawaita daga shekarar 1990 har
zuwa 2000.
Maimota (2021) ta bayyana samuwar wani nau’in
adabi ɓangaren ƙagaggun labarai, wato
yadda aka sami sababbin mawallafa ƙagaggun labaran Hausa a
shafukan sada zumunta na intanet. Wannan adabi ya samu a shekarar 2013.
2.0 Ƙagaggun Labaran Hausa a
Yau
Idan aka yi duba da yadda tarihin ƙagaggun labaran Hausa
yake, za a fahimci koda yaushe yanayi rubutun yana sassauyawa ne, ta yadda yake
tafiya da zamanin da ake ciki. Domin haka aka kalli littattafan ƙagaggun labaran Hausa
yadda suka zama a yanz da kuma yadda sababbin labaran Hausa na kafar intanet
suke.
2.1 Littattafan Ƙagaggun Labaran Hausa a
Yau
A
tattaunawa da aka yi da wasu fitattun marubuta littattafan ƙagaggun labaran Hausa da masu bugawa da sayar da littattafan, sun
tabbatar da cewa, daga shekarar dubu biyu (2000) har zuwa shekarar 2010 an
cigaba da samun littattafan ƙagaggun labaran Hausa
sosai, musamman na ‘Adabin Kasuwar Kano’. Amma an tabbatar harkar ta ja da baya
daga shekarar 2013. Amma duk da ja da baya da aka samu a wannan harka an sani
wata marubuciya da ba ta fasa harkar buga littafi ba duk da ita ma ta bayyana
cewa kishin abin ne ya sa take buga wa ba wai don tana samun ciniki ba. Wannan
marubuciya ita ce Sumayya Abdulƙadur wadda aka fi sani da
Takori, domin daga shekarar 2010 har kawo yau tana samar da littattafan ƙagaggun labarai. Daga cikin littattafan da ta rubuta daga shekarar
2010 zuwa yau akwai:
- Alƙawari Bayan Rai (2010) Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Yakanah (2011) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Amanita (2012) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Zuciyar Mutum (2013) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Babban Goro (2014) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Rayuwar Rayhana (2015) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Zumuntar Kenan (2016) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Kwana Sittin (2017) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Sanadin Kenan (2018) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Auren Kwangila (2019) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Aalimah (2020) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
- Kulsum (2021) na
Sumayya Abdulƙadir (Takori)
Bayan
Sumayyya akwai wasu marubutan da suka wallafa ɗaiɗaikun littattafai, daga
cikinsu akwai:
- Garkuwar
Iraƙi (2010) na Ibrahim Ahmad
Daurawa
- Alƙawarin So (2011) na Fatima Uba
Adamu
- Baƙin Bunu Ɓata Baibaya (2012) na Biklisu Yusuf Ali
-Tuwon
Tulu (2013) na Sadiya Garba Yakasai
- Ummulkhair (2014)
na Sadiya Garba Yakasai
- Babban
Kuskure (2016) na Ruƙayya Adamu Mu’az
-Ba
Hujja Ba Ce (2017) na Jamila Halliru G/Dutse
- ‘Yar
Gado (2018) na Haj. FurairaHabibu Dubanni
- Baƙon Al’amari (2019) na
Khadija Adamu Shitu.
2.1.1 Yadda Aikin Rubuta
Littafi da Cinikinsa ya Koma a Yau
A tattaunawa da aka yi da
wasu marubuta littattafan ƙagaggun labaran Hausa da
masu bugawa da sayar da littattafan, sun tabbatar da cewa, daga shekarar 2000
har zuwa shekarar 2010 an cigaba da samun littattafan ƙagaggun labaran Hausa musamman daga marubuta ‘Adabin Kasuwar
Kano’. Amma kuma harkar wallafa da cinikin littattafai ta fara ja da baya tun
wajajen shekarar 2011.
Marubutan
sun ƙara tabbatar da cewa yanzu ba sa sana’ar rubutu domin babu riba
sai faɗuwa,
hasali ma wasunsu sun watsar da rubutun, sun kama wasu sanao’i. Daga 2013 sai
aka samu cewa harkar rubuta littattafan ƙagaggun
labarai ta taɓarɓare sosai, an ƙara tabbatar da haka a
lokacin da aka bi shaguna sayar da littattafai, domin an tarar da yawa daga
cikinsu ma an rufe, kuma masu sayar da su musamman a Kano da take cibiyar
rubutawa da cinikin waɗannan littattafai, sun ce babu kasuwar littafi kwata-kwata domin
harkar gaba ɗayanta ta shiga ƙaƙa-na- ka- yi. Alhaji Kabiru Yusuf Anka da Alh. Mahrazu mai
littattafai da Adamu Yusif Indabo sun tabbatar da haka. Maharazu mai
littattafai wanda ya fi shekara 15 yana harkar bugawa da sayar da littattafan,
ya ƙara da cewa a da marubuta irin su Maryam Kabir Mashi da Hadiza
Salisu Sharif da sauransu sukan buga littattafai kwafi 5000 su ƙare a ƙasa da wata biyu, amma
yanzu duk wadda da buga kwafi 1000 sai ya ɗau shekaru bai ƙare ba.
Su kuwa
wasu manya a harkar rubuta littattafan labaran, sun ce su ba su karaya ba duk
kuwa da koma-baya da aka samu a harkar, musamman abin da ya shafi tattalin
arziki, amma suna ci gaba da rubuta littatafai saboda kishi da suke da shi na
son ci gaba da bunƙasar adabin Hausa.
Za
a ƙara tabbatar da taɓarɓarear harkar bugu da sayar da littattafan ƙagaggun labaran Hausa ta taɓarɓare idan aka yi duba da yadda aka sami rushewar da yawa daga
cikin ƙungiyoyi marubuta da kuma rufewar wasu shagunan da kamfanonin da
ake cinikin littattafan ƙagaggun labaran Hausa.
A da musamman lokacin da ‘Adabin Kasuwar
Kano’ ke tashe marubuta littattafan ƙagaggun labaran Hausa suna da ƙungiyoyi masu ɗauke da mambobi da yawa. Kawo yanzu
wasu ƙungiyoyin sun rushe, amma duk da haka akwai waɗanda suke da ƙarfi, kuma suke cigaba da
gudanar da ayyukansu, don har yanzu wasunsu na gudanar da mitin na wata-wata
wasu kuma suna taruka na shekara wasu kuma suna gudanar da ayyukan ƙungiya kama daga tattaunawa
da zumunci ta kungiyoyi da suke buɗewa a kafar sada zumunta ta
Waz’Af. Misali ƙungiyar marubuta ta ƙasa wadda aka fi sani
da ANA tana gudanar da taronta na shekara-shekara a garuruwa
da take da reshe. Daga cikin ƙungiyoyin da suka rage kuma suke gudanar da hulɗa akwai; Association of Nigerian
Authors (ANA) da Ƙungiyar Mace Mutum da Kallabi Writers da Hausa
Authors Forum (HAF) da Tsintsiya Writers da Kainuwa
Writers da Potaskum Writers da HAWAN da
sauransu
Duba da yanayin da wallafa da cinikin
littattafan ƙagaggun labaran Hausa ya shiga a wannan lokaci an zazzaga
kamfanoni da shagunan sayar da littattafan domin a tantance ya abin yake. A
Kano da ta zama cibiya ta ɗab’i da cinikin waɗannan littattafai an tarar da wasu kamfanoni
da shagunan suna buɗe, duk kuwa da suna kukan
babu kasuwa, amma duk da haka an tarar da wasu suna aikin, ma’ana suna harkar
bugawa da sayarwa wasu kuma suna sayarwa. Wasu kuma an tarar suna sayar da
littattafan amma sun haɗa da kayayyaki na sayarwa
kamar yadidduka da Shaddoji. Daga cikin waɗanda aka tarar a buɗe akwai:
i. Kamfanin Gidan Dabino da ke Sabon Titin
Mandawari layin Gidan Ƙanƙara, Kano.
ii. Shagon Mahrazu Bookshop, da ke Shahuci
kantinan gidan Umma Bayero, Kano.
iii. Al-Amin Bookshop da ke kasuwar Sabongari,
Kano.
iv. Salami Bookshop da ke kasuwar Sabongari,
Kano.
v. Mace Mutum Bookshop da ke kasuwar Sabogari,
Kano.
vi. Gimbiya Publishers/Anka Graghics/ AGF
Multimedia Nigeri Limited, da ke kasuwar Sabon gari, Kano.
Akwai kuma kamfanoni da shagunan da aka tarar
an rufe, babu ma alamar an taɓa bugawa ko cinikin
littattafai. Daga ciki akwai:
i. Arziki Bookshop da ke Shahuci, kantunan gidan
Umma Bayero, Kano.
ii. M.Ali Bookshop da ke Shahuci, kantinan gidan
Umma Bayero, Kano.
iii. Maman Ummi Bookshop da ke ‘Yankura, Kano.
iv. Al-Amin Bookshop Sabon Titin Mandawari, Kano.
v. Harafi Bookshop da ke kasuwar Sabongari, Kano
vi. Mashi Bookshop da ke Sabon Titin Mandawari,
Kano.
vii. Sadi Bookshop da ke sabon Titin mandawari,
kusa da makarantar Ɗandago, Kano.
viii. Zahraddeen Bookshop da ke Shahuci kantinan
gidan Umma Bayero, Kano.
2.2 Kallo
ya Koma Sama: Ƙagaggun Labaran Hausa a
Kafafen Intanet
Duba da
yadda rubutu da cinikin litattafan labaran Hausa ya ja da baya sosai, sai aka
fahimci ‘Kallo Ya Koma Sama’, ma’ana tun daga shekarar 2000 da aka sami wayoyin
hannu, sai ya zamana kullum wayoyin nan yawa suke ƙara yi a samfura daban-daban, har Allah Ya kawo lokacin da kusan
kowa na iya mallakar wayar hannu. Samuwar waɗannan wayoyi ƙirarSmart phones waɗanda suke ɗauke da samfuri na na’ura
mai ƙwaƙwalwa, ya sa kusan dukkannin wasu al’amura na rayuwar duniya da
ake gabatarwa a rubuce cikin takarda sun koma waɗannan na’urori na kwamfuta. Kusan kashi tamanin (80) na matasa
suna riƙe da irin waɗannan wayoyi waɗanda suke saka wasu muhimman bayanansu na rayuwa a ciki.
A ɓangare ɗaya wannan sabuwar fasahar
ta zamani ta yi tasiri ƙwarai a dukkan al’amuran
rayuwa, ciki kuwa har da ɓangaren rubutattun ƙaggagun labarai. A binciken
da aka yi an fahimci matasa sun fi karance-karance ta wayoyin hannu fiye da
littattafai. Za a iya cewa karance-karance ta kafar intanet ya karaɗe duniya baki ɗaya. Wannan na daga cikin
dalilan da suka sa aka sami koma-baya ƙwarai a
harkar rubutu da karatun littattafan ƙagaggun labaran Hausa. Kuma
da ma matasa sun fi karance-karancen labaran, su kuma hankulansu na kan waɗannan wayoyi.
2.2.1 Ƙagaggun Labaran Hausa a
Shafukan Sada Zumunta na Intanet
Shafin
sada zumunta wanda da Turanci ake kira Social Media, fasahar
sadarwa ce ta zamani da jama’a ke sada zumunci tsakaninsu daga sassan duniya
daban-daban, ta hanyar amfani da cibiyar sadarwa ta zamani da aka fi kira da
netiwak wanda yake aiki da intanet. Jama’a daga sassan duniya suna samun damar
sada zumunci ta hanyar tattaunawa wato, ta hanyar yin magana ko kiran bidiyo (Ɓideo Call) ko kuma tattaunawa
ta hanyar musayar saƙo (chats).
Ƙagaggun
labaran Hausa na shafukan sada zumunta, waɗanda da Turanci ake kira Online Hausa Noɓels, ƙagaggun labarai ne da ake rubutawa a shafukan sada zumunta na
zamani. Ana rubuta su yawanci a wayoyin hannu wadda ake kira smart
phones, tare da amfani da Cibiyar Sadarwa wadda take amfani da
Intanet. Bayan an rubuta, marubutan na watsawa a ƙananan shafukansu ko su tura a ƙungiyoyi
na Fezbuk da Waz’Afda sauransu. A wasu lokuta kuma masoyansu ke buɗe ire-iren waɗannan ƙungiyoyi su tura labaran. Kamar yadda aka bayyana a sama, su dai
waɗannan
labarai ba a littafi ake rubuta su ba, ana rubutawa ne kwamfutoci da wayoyin
hannu ƙirar iPhones da Samsung da sauran Androids. Za
a iya kiran waɗannan labarai da “Adabi A Tafin Hannu”, musamman idan aka yi duba
da yadda waya take koyaushe a hannun jama’a yanzu. Waɗannan labarai an same su ne
a ƙarni na ashirin da ɗaya. Haka kuma marubuta waɗannan shafuka suna buɗe ƙananan shafuka ne na kansu da ake kira blogs da wattpad da
sauransu.
2.2.2 Samuwa da Yanayin Ƙagaggun
Labaran Hausa na Shafukan Sada Zumunta na Intanet.
Dangane
da tarihin samuwar ƙagaggun labaran shafukan
sada zumunta na zamani, an samo bayanai daga bakin wasu marubutan waɗannan shafuka da wasu masu
karanta labaran, da cewa an fara rubuta su a shekarar 2013. Tun daga wannan
lokaci ake samun yawaitarsu. Kawo yanzu, waɗannan littattafai ƙara bunƙasa suke ta hanyar yawaita, tare da samun ƙaruwar marubutan da makarantan. Idan muka yi duba da tarihin
samuwar wannan sabon nau'in adabi, sai a ga bai daɗe ba, domin kwata-kwata bai
fi shekaru takwas ba amma ya sami karɓuwa ƙwarai musamman a wurin
matasa da mata.
Ana samun
waɗannan
labarai ne ta kafar intanet, wato bayan sun saka shi a ƙananan shafukansu da suka haɗa da bulog (blog) da Watfad (wattpad) da wodfires (wordpress)
da sauransu sai a watsu ta Fezbuk ko a karanta kai tsaye ta intanet, wato ta
Ofera da Gogul da Kurom da sauransu. Daga baya kuma wasu masoyansu sai su watsa
a Waz’Af musamman a shafukan ƙungiyoyi, wato groups.
A wasu lokutan kuma su marubutan ne suke buɗe ire-iren waɗannan shafuka.
A
tattaunawa da aka yi da wasu marubuta waɗannan labarai, sun tabbatar da cewa kusan dukkan marubuta labaran
ba su taɓa rubuta
littafin ƙagaggen labari ba sai da aka fara rubutu a shafukan sada zumunta
na zamani. Haka zalika masu yin wannan rubutu suna rubuto shi daga sassan
duniya daban-daban su watso shi ta kafar intanet yadda duk mai sha’awa zai iya
karantawa nan take.
Dangane
da yanayin yadda ake rubuta labaran shafukan sada zumunta na intanet kuwa kusan
duka marubutan suna rubuta su ne zango-zango (Episode), ma’ana suna
dakatawa idan an zo wata gaɓa, sai kuma su ɗora a wani lokaci da suka shirya. Wasu sukan fitar da zango ɗaya kullum wasu bayan kwana
biyu ko uku, wasu bayan mako ko makwanni, ya danganta da da lokacin da marubuci
ya tsara.
2.2.3Wasu Marubuta Labaran Shafukan Sada Zumunta da Labaransu da
Shafukansu
Wannan
bincike ya tabbatar da akwai marubuta ƙagaggun
labaran Hausa sama da ɗari maza da mata duk kuwa da mata sun rinjayi mazan da sama da
kaso tamanin (80) cikin ɗari. Ga wasu daga cikin waɗannan marubuta da labaransu:
i. Benaɗir Omar,
mawallafiyar Ke ce Gudalliya (2013) da wasu.
ii.
Khaleesat Hydar, mawallafiyar Inteesar (2015) da wasu.
iii.
Maryam Alƙali wadda aka fi sani da Mamu, mawallafiyar Wa Zan
Aura? (2014) da wasu
iɓ. Hassana Sulaiman
Isma'il wadda a shafin sada zumunta aka fi sani da Sanah Matazu,
mawallafiyar Yanar Gizo (2014) da wasu
ɓ. Zainab Idris Makawa, mawallafiyar Takari (2017)
da wasu.
vii. Fatima
Bello Salim wadda a shafin sada zumunta aka fi sani da Batul Mamman,
mawallafiyar Al’adun Wasu (2017) da wasu.
ɓii. Safiyya Jibril wadda aka fi sani a shafin sada zumunta da
Ummu Abdul, mawallafiyar Kururuwan Shaiɗan (2016) da wasu.
ɓiii. Rufaida Umar mawallafiyar Mahaifiya da
wasu,
ɗ. Ayusher Muhammad mawallafiyar Kainuwa… (2017/18)
da wasu.s
2.2.4 Ƙungiyoyin Marubuta da na Masu Karanta Labaran Shafukan Sada Zumuta
A
tattaunawa da aka yi da wasu marubutan shafukan sada zumunta, sun tabbatar da
suna da ƙungiyoyi waɗanda suke ɗauke da mambobi da dama. Marubuciyar shafukan sada zumunta Maryam
Alƙali cewa ta yi waɗannan ƙungiyoyi suna ɗauke da marubuta masu yawa,
misali kamar ƙungiyarsu mai suna Nagarta tana da a ƙalla mambobi hamsin (50). Haka kuma ire-iren waɗannan ƙungiyoyi suna tattaunawa a tsakaninsu domin magance matsaloli da
suka shafe su, kasancewar ba a raba ire-iren waɗannan ƙungiyoyi da matsaloli.
Hassana Sulaiman Isma'il ta Ƙungiyar Fikra ta ƙara tabbatar da haka, sannan kuma ta ƙara da cewa a cikin su akwai waɗanda suke yi musu taciya (editing) kafin a saki labari, gudun kar
a fitar a sami kurakurai. Lubna Sufyan ita ma mamba a ƙungiyar Fikra ta ƙara da cewa ƙungiyarsu na ɗauke da mambobi ashirin, amma da suna cikin ƙungiyar Nagarta ne wadda take ɗauke da maza da mata, daga baya suka buɗe ta Fikra mai ɗauke da mata zalla. Daga
cikin ƙungiyoyin marubuta kawai akwai: Nagarta Writers da Fikra
Writers da Haske Writers da Kainuwa
Writers da Manazarta Writers da Tauraruwa
Writers da Pure Moment of Life da Eɗclusiɓe Writers da Talent Writers da Eleƙuent Writers da Online
Hausa Writers da Ƙueen Writers da Fantastic Writers da NWAN da Tauraruwa da
sauransu.
Waɗannan ƙungiyoyi na sama na marubuta ne zalla, kuma suna buɗe su ne ta kafar sada
zumunta (online), ta nan suke tattaunawa da hirarraki. Bayan
waɗannan ƙungiyoyi, akwai kuma waɗanda suke buɗewa na haɗaka tare da masu karanta labaran. A irin waɗannan ƙungiyoyi na haɗaka masu karatun na samun damar yin sharki ko ƙorafi kan wani labari da ake turowa a wannan ƙungiya. Ire-iren waɗannan ƙungiyoyin wasu na
wucin-gadi ne, wato ana buɗe su ne don wani labari, musamman na kuɗi, saboda haka da an ƙare labarin sun gama aiki. Wasu kuwa ana barinsu ne dindindin ana
tura labarai daga marubuta daban-daban. Kusan duka waɗannan ƙungiyoyi mata ne zalla. Daga ciki akwai; Hausa Noɓels da The Sparklle da Zaki Paid Group da KDM da KDM
Comment Section da Makawa Sarutar Mata da Taskar
Fikra da Zauren BieBie Isa da sauransu.
Waɗannan ƙungiyoyi na sama ana buɗe su ne ta kafar Waz’af. Akwai kuma ƙungiyoyi waɗanda ake buɗe su ta kafar Fezbuk, kuma wanda duk ya hau kafar Fezbuk din, ya
rubuta sunan ƙungiyar zai ga ire-iren labaran da ake turawa. Misalan irinsu
akwai; Billyn Abdul Hausa Noɓel da Hausa Noɓels Only da Hausa Noɓels and Gyaran Jiki da Gidan
Nishaɗi and
Hausa Noɓel da Gidan Uncle
Hausa Noɓel da Dandalin
Aisha Hausa Noɓels da Ƙueen Mermue Noɓels Fan’s da Prince and
Princess Hausa Noɓels da Seemaluɓ Hausa Noɓels da M K Hausa Noɓels Group da Assadiya
Hausa Noɓels da Duniyar
Hausa Noɓels da Hausa
Books Noɓels da Mijin
Kwaila Hausa Noɓels.
Ƙungiyoyin
Fezbuk haɗaka ne na
maza da mata, kuma wasu maza ke buɗe su wasu kuma mata. Akan sami jagora da ake kira Admin idan
mutum ya bukaci shiga ƙungiyar zai danna inda aka
rubuta join an yi alama da shuɗin inki, idan jagora ko jagorori sun amince sai su karɓi mutum. Wasu ƙungiyoyin na Fezbuk suna tantance mutum kafin su karɓe shi, suna tantancewa ne
ta hanyar yin tambayoyi (interɓiew).
Ƙungiyoyin
Fezbuk na ɗaukar mambobi da yawa. Misali, ƙungiyar Seemaluɓ Hausa Noɓels an buɗe ta ranar 31 ga watan
Disamba, 2016, tana ɗauke da Mambobi sama da dubu goma sha takwas (18,000). Akwai
kuma ƙungiya mai suna Assadiya Hausa Noɓels, wadda aka buɗe aranar 22 ga watan Disamba, 2016, tana da mambobi dubu biyar
da ɗari shida
(5600). Sannan akwai ƙungiya mai suna Hausa Noɓels, an buɗe ta ranar 30 ga watan Yuni, 2019, tana da mambobi dubu ashirin
da ɗaya
(21000). Sai kuma Duniyar Hausa Noɓels wadda aka buɗe ranar 6 ga watan Oktoba, 2020, ita kuma tana ɗauke da mambobi dubu goma
sha ɗaya
(11,000). Akwai ƙungiyar Mijin Ƙwaila Hausa Noɓels wadda aka buɗe ranar 5 ga watan Nuwamba
shekarar 2020, tana ɗauke da mambobi dubu ashrin da shida da ɗari huɗu da talatin da ɗaya (26,431). Ƙungiyar Gidan Uncle Hausa Noɓel an buɗe ta ranar 15 ga watan Nuwamba, tana ɗauke da mambobi sama da
dubu goma sha uku (13000). Akwai kuma Gidan Nishaɗi Hausa Noɓels da aka buɗe ranar 24 ga watan Janairu, 2021, tana ɗauke da mambobi sama da
dubu 6500.
Haka kuma
akwai wata Manhaja mai suna Bakandamiya, wadda wani mutum mai
suna Alhaji Lawan Ɗalha mazaunin ƙasar Saudiyya ya ƙirƙira, kamar yadda Mukhtar Ƙarami
hadimi na wannan manhaja ya bayyana. Shi dai Alhaji Lawan Ɗalha ɗan Nijeriya ne ɗan asalin jihar Taraba, wanda ya zama mai so da kishin harshen
Hausa. A wannan manhaja ana gudanar da abubuwa daban-daban kama daga abubuwan
da suka shafi ilmi da lafiya da girke-girke da adabi da duk wani abu da zai yaɗa Hausa da Hausawa a
duniya. Daga shirye-shirye da ake gudanarwa akwai fili da ake kira filin baƙonmu na mako, inda ake tattaunawa da marubuta shafukan sada
zumunta na intanet. Masu karatu na bibiyar wannan hira har su yi wa marubutan
tambayoyi kan labaran da suke rubutawa. Ana iya sauke wannan manhaja daga
babban rumbun sauke manhajoji wadda aka fi sani da Play Store. Ƙarƙashin wannan manhaja ta Bakandamiya, ana tattaunawa ne da marubuta
sauran marubuta da masu karatu na bi tare da yin sharhi kan hirar da ake. Ana
fara tallata ranar da za a yi wannan tattaunawa haɗe da hoton marubuciyar da
za a yi hira, tare da sanar da rana da lokaci na yin wannan hirar. Ana kuma
tura ƙagaggun labarai na marubuta daban-daban ƙarƙashin manhajar.
2.2.5 Rawar da Marubuta Labaran Hausa na Shafukan Intanet ke
Takawa a Duniyar Adabin Hausa
A
binciken da aka gudanar an tabbatar da cewa waɗannan marubuta da labaransu suna taka rawa a duniyar adabi, domin
ta kai har suna shiga gasa da ake shiryawa ta ƙagaggun labarai. Misali a shekarar (2018, 2019 da 2020) kusan
marubuta shafukan sada zumunta ne suka lashe gasar rubutun gajerun labarai ta
mata ta BBC Hausa, wato Hikayata. Waɗanda suka kai ga nasara su
ne; a shekarar 2018 akwai, Safiyya Jibril Abubakar (Ummou Abdul) da
labarinta ‘Ya Mace ita ce ta farko, sai Sakina Lawal da ta zo
ta biyu da labarinta mai suna Sunanmu Ɗaya sai kuma Bilkisu Abubakar
da ta zo ta uku da labarinta mai suna Zina a shekarar 2019
kuma akwai Maraici’ na Safiya Nuhu Ahmed ya zo na ɗaya, sai Ba a yi
Komai ba na Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo. Akwai kuma labari mai
suna A Juri Zuwa Rafi na Jamila Babayo wanda ya zo na uku.
Haka zalika a shekarar 2020 marubuta shafukan sada zumunta ne suka lashe, domin
gwaraza ukun duka marubuta ne na shafin sada zumunta. An sami labarai kusan 500
da suka shiga gasar amma guda uku ne suka lashe matsayin gwarazan shekara, su
ne: Maryam Umar (Mermu) wadda ta fito daga jihar Sokoto, ita ta zo ta ɗaya da labarinta mai
suna Rai da Cuta. Sai Surayya Zakari wadda ta fito daga jihar
Kano ta zo ta biyu da labarinta mai suna Numfashin Siyasata. Rufaida
Umar wadda ita ma ta fito daga Kano ta zo ta uku da labarinta mai suna Farar Ƙafa.
Wani abin
lura gasar ‘Hikayata’ ta BBC Hausa, tana da ƙa’idoji
sosai kafin a kai ga nasara. Daga cikin aikin akwai amfani da daidaitacciyar
Hausa da bin ƙa’idoojin rubutu. Sannan wasu masana ko malamai na adabi ɓangaren ƙagaggun labarai na daga cikin alƙalan
wannan gasa.
Haka kuma
akwai gasa da wata ƙungiya mai suna ‘Tsangayar
Marubutan Hausa’ ta saka, aka fitar da zakarun da suka yi nasara ranar
30/12/2018, su ne: Kamal Muhammad Lawan da ya zo na ɗaya da labarinsa mai suna “Nakasar
Zuci” da Hassana Sulaiman Isma’il (Sanah) da ta zo ta biyu da
labarinta mai suna “Kuskurena”. Sai kuma Isah Muhammad Machina da
ya zo na uku da labarinsa mai taken “Kukan Zamfara”.
Akwai
gasar Gajerun labarun Hausa ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ta shekarar 2020. Cikin
waɗanda suka
shiga gasar suka yi nasara akwai marubuta ƙagaggun
shafukan sada zumunta na Intanet. An zaɓi guda goma 13 da suka yi nasara aka buga su cikin littafi mai
suna MUHALLI, SUTURA Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun
Labarai A kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa. A wannan gasa akwai
marubuta littattafai da dama, amma cikin waɗanda suka yi nasara har da marubuta shafin sada zumunta. Akwai
labari na uku a jerin labaran da aka buga mai suna Laifin Wa? na
Bilkisu Muhammad Garkuwa, mawallafiyar wannan labari ta tabbatar min ba ta taɓa rubuta littafi ba, sai
a online, wato tana nufin sai na shafin Intanet.
Akwai
wata gasa ta hanyar kaɗa ƙuri’a ta shafin intanet, wata mata ce (makaranciya) ta saka a
shafin sada zumunta a watan Disambar shekarar 2020 wadda ta kira Choice
for Your Choice: Most Brilliant Writer. Ta kasa kashi uku kowanne
kashi akwai labarai huɗu da suka yi tashe na marubuta daban-daban, za a yi zaɓe ta tsarin wata da’ira(chart)da
suka tsara a haka ake cire gwarzon labari ɗaya. Misali a kashi na uku akwai labarai kamar haka; Ku
Dube Mu na Fatima Bello Salim (Batul Mamman), da Rayuwar
Najwa na Hassana Isma’il (Sanah Matazu), da Tana Ƙasa Tana Dabo na
Safiyya Galadanci, sai kuma Ƙarshen Makirci na Rahma Kabeer. A kasha na ukun Batul Mamman da labarinta Ku
Dube Mu ta yi snasara da ƙuri’u 1547 da kaso 72.73
cikin 100.
2.2.6 Yadda ake Cinikin Ƙagaggun
Labaran Shafukan Intanet
Dangane da yadda marubuta
labaran shafukan sada zumunta na intanet ke cinikin labaransu, bincike ya gano
cewa tun da aka fara rubutu a shafukan sada zumunta waɗannan marubuta suna rubuta
labaran ne kyauta ba tare da an biya ko sisi ba. Amma a ƙarshen shekarar 2018 wasu daga cikin marubutan Fikra su bakwai (7)
suka buɗe wani
shafi na kuɗi, ta
kafar Waz’Af (WhatsApp), wanda duk mai so zai tura kuɗi ta asusun banki da suka
bayar da lamba, bayan an tura wannan kuɗi sai a tura hoton shaidar an biya ga ɗaya daga wakilan shafin (admins)
ita kuma sai ta saka mutum a ƙungiyar. Sunan wannan ƙungiya ‘Taskar Fikra (original) , marubuciya Lubna Sufyan ce ta buɗe ta ranar 25/11/2018 kuma
wannan ƙungiya ta kasance da marubuta da makaranta (duka mata) su ɗari da casa’in da shida
(196), cikin mambobi har da ni. An fara tura labarai a ƙungiyar ranar 01/12/2018 ana bayar da labarai guda bakwai
i. Gumin
Halak, na Batul Mamman (Fatima Bello Salim)
ii. Dr.
Sheerah, na Jeedderh Lawals
iii. Alƙalamin ƙaddara, na Lubna Sufyan
iɓ. A Dalilin Ɗa Namiji, na
Fareeda Abdallah
ɓ. TANI Yar Amana, na
Rufaida Omar da Fulani Bingel
ɓi. Gidan Bunu, na Sanah Shahada (Hassana Zakariyya Maidaru)
ɓii.Dan Makaho, na Biebee Isa (Zainab Isa)
Batul
Mamman ta buɗe
kwatankwacin wannan ƙungiya ranar 04-02-2019,
inda take tura labarinta mai suna Ku Dube Mu a kan naira 300.
Haka ita ma Zainab Idris Makawa ta buɗe irin wannan ƙungiya ranar 07-03-2019
inda take tura labarinta mai suna Sarautar Mata a farashin
naira 300. Ana tura wannan kuɗi ta lambar asusun banki da suke turawa. Wasu marubutan na bayar
da dama a tura musu kuɗi ko katin wayar tafi-da-gidanka.
Kawo
yanzu wasu marubuta na yin labaran kyauta wasu kuma musamman waɗanda aka san labaransu suna
ci gaba da sayarwa. Akwai dabara da sukan yi don su tallata labaran, wato sukan
fara fitar da wasu shafuka na labara kyauta a matsayin ɗanɗano, idan sun kai wata gaɓa sai su dakata su ce sai
an biya kuɗi ko
katin waya za a saka mutum a ƙungiya, sannan sai a ci
gaba. Hakan na sa wa su yi ciniki sosai, domin sukan sami kasuwa sosai a ƙalla ba a samun ƙasa da dubu 60.
Marubutan Hausa na shafukan
intanet da yawa suna ɗora labaransu su sayar a kan manhajar Okada. Ana
sauke manhajar Okada daga rumbun Play Store, bayan
an sauke wannan manhaja a kan waya, mutum zai iya bincika wannan manhaja ya ga
tarin labaran da suke kai da haka sai ya zaɓa. Da ma an riga an saka farashin kuɗin kowanne a jikinsa. Kuma mutum yana iya biya a tura kuɗin zuwa asusun bankin Okada
ko a tura katin waya. Kuma dama da mutum ya sauke manhajar akwai asusu da ake
ba shi, wanda zai ringa zuba kuɗi daga asusun bankinsa. Daga wannan asusu da Okada suka
ba wa mutum za a ringa saka kudin littafin ko a saka katin waya.s
3.0
Makomar Ƙagaggun Labaran Hausa a Yau
Duba da
bayanan da aka samu a wannan bincike za a iya cewa harkar rubuta littattafai da
cinikinsa ta mutu. Haka kuma duniyar gaba ɗaya ta koma tafin hannu, domin zamani ya kawo fasahar sadarwa ta
zamani wadda ta haifar da karance-karance ta shafukan intanet. Wannan fasaha ta
intanet ita ta nakasa harkar rubuta littattafai da sayar da su. Fasahar intanet
ta haifar da samuwar marubuta ƙagaggun labaran Hausa a waɗannan hafuka, samuwar waɗannan labarai sai ta tafi
da hankalin jama’a musamman matasa waɗanda su suka fi karanta labarai kuma su suka fi ta’ammali da
wayoyi ƙirar smart phone waɗanda tanan ake samu labaran.
4.0
Kammalawa
Wannan
bncike ya gano cewa ‘kallo ya koma sama’ duba da yadda harkar rubutu da karatu
da ciniki na ƙagaggun labaran Hausa ya koma shafukan intanet, wanda hakan ya
kawo koma baya wajen wallafa littattafai na ƙagaggun
labarai da sayar da su. domin haka a ƙarshe wannan bincike yake
bayar da shawarwari kamar haka;
Kasancewar
adabin al’umma yana bunƙasa ne a duk lokacin da
al’umma take mu’amala da wasu al’ummomi, sannan kuma idan al’ummar tana karɓar duk wani sauyi da tai
karo da su, na zamani, domin haka ya kamata masana da masu nazarin adabin Hausa
su yi ƙoƙarin shiga a dama da su kan duk wani abu sabo da ya samu, domin
hakan zai sa a ƙaru da wani ilimi. Abin da nake nufi yana da kyau masanan da masu
nazari su ringa bibiyar shafuka da ake da su na sabuwar fasahar sadarwa na
zamani, domin kar a bar Hausawa a baya.
Kasancewar
duka al’amuran rayuwa yanzu an fi aiwatar da su da wayoyin hannu masu amfani da
intanet, hakan ne ya haifar da shafukan sada zumunta da dama, wanda kuma suka
yi sanadiyyar samuwar ƙagaggun labaran Hausa.
Domin haka ya kamata masana da malamai da masu nazari su ringa ziyartar waɗannan shafukan domin hakan
zai ba su damar bayar da gudunmawa da za ta bunƙasa
adabin Hausa da ake fitarwa a waɗannan shafukan. Haka kuma a yi ƙoƙarin ɗora tsoafaffin littattafai da ake da su a shafukan ciniki na
intanet irin su Okada saboda a adana tarihi. A kuma ba wa
marubuta shawara kan su ringa samar da littattafai kan labaransu bayan sun
fitar ta intanet.
Haka kuma
ina ba masana da malamai shawarar su ringa gudatanar da nazari a kan irin waɗannan labarai, a kuma
ba ɗalibai
dammar nazarinsu domin hakan zai sa a raya adabin baya tare da rainon sabon da
ya shigo.
Manazarta
Abu Sabe, B. (2016) “Ƙagaggun Labaran Zamani Na
Hausa Da Na Masar: (Nazarin Kwatance).” Kundin Digiri na Uku. Egypt: Jami’ar
Cairo.
Abu Sabe, B. (2017) “Fasalin Jigo a Ƙagaggun Labaran Zamani na Hausa da na Masar.” Takarda da aka
Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani ‘Hausa
Language, Literature and Culture in the 21st Century: Current
Trends and Perspectiɓess’ a Jami’ar Jihar Kaduna. 18-20- Mayu.
Abu Sabe, B. da Wasu (2020) MUHALLI, SUTURA Labaran Da
Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai A kan Muhalli Ta Arc Ahmed Musa
Dangiwa. Katsina: Darma Digital Prints.
Adamu, Y. M. (2014). "Modern Hausa Prose-Fiction in the 21st Century"
Paper PresentedAt the International Conference on African Languages and
Literature in the 21st Century.6-8 August. Nairobi:
Kenyatta Uniɓersity.
na Hausa.” Kundin Bincike na Digiri na Biyu. Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Zariya:
amana.
Furniss, G. (2000) “Documenting Hausa Popular Literature.” Maƙalar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa
Juna Ilimi. Jamus
Maimota, A. S. (2021) “Kwatanta Wasu LittaLittattafan Ƙagaggun Labaran Hausa da Wasu Ƙagaggun
Labaran Hausa na Shafukan Sada Zumunta na Intanet.” Kundin Digiri na Uku,
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero, Kano.
Makawa, Z.I. (2017/19) Takari (Labarin Shafin
Sada Zumunta na Zamani)
Malumfashi, I. (2002) “Adabi da Bidiyon Kasuwar Kasuwar Kano a
Bisa Faifai: Taƙaitaccen Tsokaci.” Maƙala da aka Gabatar a
Cibiyar Hausa, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Malumfashi, I. (2006). "Ginuwar Ƙagaggun Labaran Hausa: Ƙarin Haske."Takarda
Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies. Ɓol. 1 No. 4.
Muhammad, A. (2018) Kainuwa (Labarin Shafin Sada
Zumunta)
Mukhtar, I. (1993) “Yanayin Ƙagaggun
Labarai Na Hausa.” Takarda da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani na uku kan Harshe da Adabi da Al’adun Hausa.
Kano: Jami’ar Bayero.
Mukhtar, I. (2004) Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai (Tsari na biyu) Kano:UsmanAl-Amin Publishers.
Mukhtar, I. (2018) "Stylistic Theories and the Linguistics of
Hausa Prose Teɗt:The Systematic Functional Linguistics (SFL) Approach."
Professorial Inaugural Lecture. Kano: Bayero Uniɓersity.
Nafi’u, A. M. (2012) “Magana Jari Ce (1-3): Nazarin
Salo da Sarrafa Harshe” Kano: Jami’ar Bayero Kano.
Yahaya, I. Y. da Ɗangambo, A. (1986) Jagoran
Nazarin Hausa. Zaria: NNPC.
Yahaya, I. Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce
Cikin Hausa.Zaria: NNPC.
https://en.m.wikipedia.org.socialmedia
https://www.duniyarcomputer.com
m.dw.com/ha/ko-wa-ya-ƙirƙiro.whatsapp
https://muhdabbagana.blogspot.com
www.hausanewsblog.wordpress,com
https://www.sanahsulaiman.wattpad.com/story
https://www,batulmamman.blogspot.com
thoughtcatalog.com
|
1 |
Yusuf M. Adamu |
53 |
Farfesa/Mawallafin Littafin Ƙ/Labarai |
Jami’ar Bayero, Kano |
14/2/2018 |
|
|
2 |
Isma’il Muhammad Na’Abba (Afakalla) |
50 |
Shugaban Hukumar Tace Finafinai
da Ɗab’i |
Ofishinsa dake ARTƁ, Kano. |
02/3/2021 |
|
|
3 |
Ado Ahmad G/Dabino |
57 |
Marubucin Littafi da Ɗab’i |
Kamfanin Gidan Dabino. Kano |
16/2/2021 |
|
|
4 |
Bilkisu Yusuf Ali |
45 |
Malama/marubuciyar Littafi |
Jami’ar Alƙalam, Katsina |
17/2/2019 |
|
|
5 |
Balaraba Ramat Yakub |
63 |
Marubuciyar Littafi da Ɗab’i |
Kamfanin Ramat, Kano |
5/5/2019 |
|
|
6 |
Kabiru Yusuf Anka |
|
Marubucin Littafi da Ɗab’I da sayar da Litttafi |
Kano |
15/2/2021 |
|
|
7 |
Adamu Yusuf Indabo |
38 |
Sayar da Littattafai |
Kano |
15/2/2021 |
|
|
8 |
Maharazu Suleiman |
41 |
Sayar da littattafai/ Bugawa |
Kano |
24/2/2021 |
|
|
|
||||||
|
9 |
Sumayya Abdulƙadir |
33 |
Marubuciyar Littafi |
Kano |
5/10/2019 |
|
|
|
||||||
|
10 |
Hasana S. Isma’il |
27 |
Marubuciyar Intanet |
Kano |
6/8//2018 |
|
|
11 |
Zainab Idris Makawa |
25 |
Marubuciyar Intanet |
Birnin Kebbi |
8/3/2018 |
|
|
12 |
Ayusher Muhammad |
28 |
Marubucciyar Intanet |
Kano |
7/5/2018 |
|
|
13 |
Fatima Bello Salim (Batul Mamman) |
|
Marubuciyar Intanet |
Kano |
5/2/2019 |
|
|
14 |
Maryam Alƙali |
30 |
Marubuciyar Intanet |
Sokoto |
7/1/2019 |
|
|
15 |
Rufaida Umar |
26 |
Marubuciyar Intanet |
Kano |
9/2/2021 |
|
|
16 |
Shafa’atu Aminu |
32 |
Makaranciyar labaran Intanet |
Kano |
8/7/2018 |
|
|
17 |
Zainab Muhd |
35 |
Makaranciyar Labaran Intanet |
Dutse/ Jigawa |
5/6/2019 |
|
|
18 |
Aisha Umar |
40 |
Makranciyar Labarin Intanet |
Kano |
9/11/2019 |
|
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.