𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum mallam dafatan ananan lfy don Allah inada tambaya mace ce budurwa bata
taɓa aure ba, kuma
tana da sha'awa gaskiya mai karfi domin ko sumbata ko kusancin mace da namiji
tagani anayi sai taji hankalinta na tashi haryakai ga tanajin fitar wani ruwa
mai yauki kumburin gaba dakuma sai taji kaman Abu ya tokaremata kofan gaban
nata shin tokarewan alamace ta budurcinta cikakke ne saboda kaman kofan arufe
take kuma shin wannan ruwan zaisa tayi wanka ne a duk lokacinda yafita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu
Da farko
Tsarki kawai za ki yi, Sannan Kuma Zaki nemi Miji kiyi Aure. Domin Wannan
Matsalar Taki Tana da Alaka da Rashin Aure. Shi ne Abin da ya janyo Miki Wannan
Karfin sha'awar. Amma da za ki yi Aure In shà Allahu Baki da Damuwa.
Rashin Aure ga
'ya Mace babu Abin da baya Haddasa Mata Wallahi Har ciwon Hauka Yana Haddasawa
ga Ya Mace ko Namiji, Shiyasa Idan Mukaga Mutum yana Da ciwon Hauka Muke Bayar
da Shawarar a Aurar Dashi ga Mace irinsa ko a Aurar da ita ga Namiji Mai ciwo
irin Nata kuma da ikon Allah, Idan an Kulla wannan Auren Za ka ga Abin Yayi
Sauki. Koda ba Gabaki ɗaya
Bane, Za ka ga Cewar Ba yadda Aka San shi ba.
Sabida haka
Rashin Aure ga Mai Hankali, Mai Lafiyayyan Kwakwalwa Mace ko Namiji. Ba Karamin
Bala'I bane.
A zamanin Sayyadina Umar. Da karfi da yaji Ake
Kama Samari a ɗauki
Dukiyar Baitil Mali A Aurar dasu ga Yan Mata Wadanda Suka Isa Aure. Sabida
Daidaita Zamani. Domin Ba'a yin Aure Lalle Zamani Zai Rikice. Kuma za a Dinga
Samar da 'yayan da Basu da Uba, za a dinga Tsintar Jinjirai a kwalabati ko a
kan tituna ko a Kangon da ba'a gama Gineshi ba.
Tabbas idan
haka tana Faruwa Zamani ya Gurbace.
Ya Allah ka
bamu Mafita Akan Zamanin Mu da Zamanin 'ya'yan Mu da wadanda Zasu Zo bayansu.
Allah ta'ala yasa mudace
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.