A sama an yi bayanin yadda karas yake. A ɓangare guda kuwa, ƙoda ɓangare ne na kayan cikin dabba. Yayin samar da wannan miyar, karas da ƙoda suke kasancewa mafi rinjaye cikin kayan haɗin da ake sanyawa.
Mahaɗin
Miyar Ƙoda
da Karas
Akwai
abubuwan da ake buƙata yayin samar da wannan miya. Abubuwan sun haɗa
da:
i. Albasa
ii. Karas
iii. Koren wake
iv. Ƙoda
v.
Ruwa
vi.
Tarugu
vii.
Tattasai
viii.
Tumatur
Yadda Ake Miyar Ƙoda
da Karas
Za a sami ƙoda a yanka ta sai a wanke a saka gishiri da magi da kayan ƙamshi sannan a soya. Idan ta kusa
soyuwa, za a yanka albasa a samanta a lokacin ne
kuma za a barbaɗa fulawa kaɗan a zuba ruwa, shi ma ɗan kaɗan. Daga nan kuma za a jajjaga kayan
miya a zuba a ci gaba da juyawa har sai ruwan ya
kusa ƙonewa sannan a zuba karas da koren
wake da magi a rufe. Yayin da aka kai wannan gaɓa, akan sanya wuta ne kaɗan-kaɗan
domin kada ta ƙone. Za a iya
cin ta da shinkafa ko sakwara ko tuwon samo da makamantan waɗannan.
Tsokaci
An fi samun wannan nau’in miya a birane, saɓanin ƙauyuka. Ko cikin biranen ma, ba kasafai ake wannan miyar ba. Akan yi ta ne lokaci zuwa lokaci. Za a iya cewa, miya ce ta ƙwalama.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.