Ticker

6/recent/ticker-posts

Miya Soyayyiya ko Dafaffiya da Babu Ruwa a Ciki

Za a iya hasashen cewa, soyayyiyar miya ba gadajjiya ba ce ga Bahaushe. A maimakon haka, ya same ta ne a sama sakamakon cuɗanyarsa da baƙin al’ummu. Wannan ne ya sa, ko cikin gari ba a faye samun wannan nau’in miya ba. A ƙauyuka kuwa, sai dai abin da ba a rasawa.

Mahaɗin Miya Soyayyiya ko Dafaffiya da Babu Ruwa a Ciki

Kayan haɗin wannan nau’in miya sun haɗa da:

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Kayan yaji       

iv. Kifi ko Nama (idan akwai)

v. Kori

vi. Magi

vii. Ruwa

viii. Tafarnuwa

ix. Tarugu

x. Tattasai

xi. Thyme

xii. Tumatur

xiii. Zogale ko Alayyafu

Yadda Ake Soyayyiya Ko Dafaffiyar Miyar Da Babu Ruwa A Ciki

Da farko za a iya amfani da zogale ko alayyafu domin samar da wannan miya. Duk wanda ya samu akan wanke shi da gishiri sosai. Idan alayyafu ne sai an yanka shi manya-manya, sannan za a saka shi a cikin tukunya a dafa. Kada a bari ya dafu sosai in alayyafu ne. Idan kuma zogale ne, a zuba zuma da ’yar kanwa a dafa sosai. Daga nan sai a cire ganyen a saka shi cikin kwando a tace sannan a bar shi ya tsane, sai a aje gefe ɗaya. Za a ɗauko kifi ko nama a haɗa da albasa sannan a tafasa.

Daga wannan ya samu, za a yi jajjage sannan a zuba cikin tukunya a haɗa da wannan kifi ko nama tare da mai, kamar yadda ake na sauran miya. Bayan ya soyu, za a sanya kayan ƙamshi da na ɗanɗano. Da zarar sun soyu, za a zuba ganyen, a yi ta juyawa har sai ganyen ya soyu daidai yadda ake buƙata. Akan yi amfani da wannan nau’in miya wajen cin kuskus ko shinkafa ko dambu da dai makamantansu. 

Tsokaci

Irin wannan miya takan daɗe ba tare da ta ɓaci ba. Wannan na faruwa ne sakamakon ba a sanya ruwa cikinta. Wani lokaci ma akan sanya miyar a firijin. A irin wannan lokuta, takan ɗauki kwana da kwanaki ba tare da ta ɓaci ba. 

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments