Ticker

6/recent/ticker-posts

Sha’awa Tana Takura Min Har Da Fitar Maniyyi A Cikin Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. A cikin Azumi sha’awa tana takura min har da fitar maniyyi, kuma ban san ana wanka domin hakan ba. Shi ne nike tambaya wai yaya zan yi a kan sallolinna da azuminna?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Azumi lokaci ne da musulmi ke yankewa daga bin sha’awoyin ciki da farji da sauran gaɓoɓin jiki. Lokaci ne da yake ƙara kusantar Allaah Ta’aala da kyawawan ayyuka, kuma ya yi nesa da dukkan ayyukan sheɗan na zalunci da cutar kai da cutar sauran jama’a.

Wajibi ne ga mai azumi ya nisanci duk abin da ya san zai motsar masa da sha’awar jima’insa, ta hanyar nisantar kallon fima-fimai ko karatun labarum batsa a cikin litaffan soyayya ko keɓancewa da wanda ko wacce ba muharrama ba, da sauransu.

Wanda ya yi sakaci har ya janyo aukuwan abin da ke ɓata azumin ta irin waɗannan hanyoyin da makamantansu to ya sani cewa azuminsa ya ɓaci, kuma dole sai ya rama shi, tare da tuba ga Allaah da neman gafararsa.

Haka ma wanda ya bar yin sallah a tsawon lokacin da janaba ta same shi, wajibi ne ya rama duk sallolin da ya yi sakaci a kan su kafin zuwan rasuwarsa, tare da tuba da istighfari ga Ubangiji Ta’aala, musamman idan ya yi hakan a sakamakon sakaci ne wurin neman ilimi.

Wajibi ne kowane musulmi ya koyo ilimin abin da addininsa ba ya ingantuwa ko gyaruwa sai da shi, kamar a babin Aqeeda da Tauhidi da Tsarki da Sallah da Azumi da Mu’amalar Aure da Kasuwanci da Maƙwabtaka da sauransu.

Janaba tana samuwa ga mutum ne idan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ya auku

1. Fitar maniyyi daga namiji ko mace ta hanyar babbar sha’awa a barci ko a farke.

2. Fitar maniyyi ta hanyar yin wasa da al’aura daga namiji ko mace.

3. Ɓacewar kan al’auran namiji (hashafa) a cikin farjin mace kamar a lokacin saduwa, ko da kuwa ba su yi maniyyi ba.

Duk lokacin da ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ya auku, to janaba ta samu. Babu abin da ya rage ga mutum a lokacin sai dai ya yi shirin kawar da ita, ta hanyar yin wankan da ake kira Wankan Janaba.

Daga cikin hukunce-hukuncen da suka shafi Janaba da mai Janaba akwai

1. Fitar maniyyi ne yake jawo janaba amma ba fitar maziyyi ba a wurin namiji ko mace.

2. Sai dai wajibi ne ga wanda maziyyin ya same shi ya wanke dukkan al’aurarsa gaba ɗaya, kuma ya sake alwala.

3. Idan kuma maziyyin ya shafi tufa ne to shari’a ta yi sassauci in aka ɗebi ruwa aka jiƙa wurin da ya shafan kawai, ya yi.

4. Yadda mace za ta yi wankan Janaba daidai ne da yadda za ta yi na Haila. Sai dai ba dole ne a janaba ta warware kitson kanta ba.

5. Wanda ya yi mafarkin saduwa kuma da ya farka sai bai ga maniyyi ba, to janaba ba ta same shi ba.

 

6. Wanda ya farka daga barci kuma ya ga maniyyi a jikinsa alhali bai tuna yin wani mafarki ba, duk da haka dai janaba ta same shi, namiji ne shi ko kuwa mace ce, ba bambanci.

7. Wanda maniyyi ya gangaro masa ba da sha’awa ba sai dai saboda rashin lafiya ko sanyi ko dai makamancin haka, yawancin malamai sun ce janaba ba ta same shi ba.

8. Haɗuwa ko shafar al’auran namiji da farjin mace ba tare da shigewa ciki ba wannan bai jawo musu janaba ba. Amma in ɗayansu ya fitar da maniyyi, to shi ne ya yi janaba.

9. Idan namiji ya sadu da mace: Ya shigar da abin da bai kai ‘hashafa’ watau kan al’aurarsa ba, sai dai kuma maniyyinsa ya samu gangarawa cikin farjinta, sannan ita kuma ba ta fitar da maniyyi ba, to a nan mijin ne kaɗai ya yi janaba ban da matar.

10. Idan kuma mace ta ƙare wankan janaba bayan saduwa sai kuma daga baya maniyyin mijin ya gangaro ya fito mata, to a nan ba za ta sake yin wanka ba.

11. Amma ko za ta sake alwala? Malamai sun saɓa wa juna. Mafi kyau dai shi ne: Ba za ta sake ba. Wal Laahu A’lam.

Muhimman mas’alolin da suka wajaba a kula da su sosai a ɓangaren wanka

1. Siffar yadda ake yin wankan janaba daidai yake da wankan Haila ko Nifaasi, sai dai a wurin ɗaura niyya da warware kitson gashin kai kawai.

2. Kar ki yi fitsari a wurin da kike yin wanka, sai fa in shafaffe ko daɓaɓɓe ne kuma sai in kin wanke shi sosai kafin fara yin wankan.

3. Ya halatta ki yi wanka a tsirara matuƙar dai kina cikin rufaffen wurin da ba wani mai iya ganinki ne.

4. Amma ki kula da yin addu’ar Sunnah da ambaton sunan Allaah kafin shiga wurin ko kafin tuɓe tufafin, domin kare kanki daga idanun shaiɗanu.

5. Idan ba ki samu rufaffen wuri ba sai wata ko wani muharraminki kamar miji ya kare ki da labule tun daga farko har ƙarshen wankan.

6. Wadda wankan Janaba da Haila suka hau kanta sai ta yi kowanne a matsayinsa kuma da niyyarsa. In kuma ta haɗa su da niyya guda, waɗansu malaman sun ce: Ya yi.

7. Ya halatta miji ya kewaya dukkan matansa da yin wanka ɗaya. Sai dai ya yi wanka ga kowace ɗaya ya fi.

8. Abin da ya fi shi ne mai janaba ya yi wanka kafin ya yi barci, in kuwa bai samu dama ba sai ya yi alwala ko taimama. In ya farka daga baya ya yi wankan.

9. Haka kuma mai janaba ba zai ci abinci ba har sai bayan ya yi wanka ko kuma alwala.

10. Ya halatta miji da mata su yi wanka tare a wuri ɗaya kuma su riƙa ɗiba daga ƙwatarniya ko bokiti ko baho ɗaya.

11. Ya halatta su kalli al’aurar junansu a kowane lokaci. Da sauransu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments