Ɓula
Ɓula abinci ne da ya daɗe da ake amfani da shi a cikin abincin gargajiyar Bahaushe. Gero ne da masara za a surfe a jiƙa ko markaɗen ƙullu. Ƙullun ruwa-ruwa da za a yi amfani da shi a tuƙa ya zamo a matsayin ɓula. Ɓula ba zai yiwu ba sai an niƙa ƙullun, sannan ɓula zai iya zama tuwon ƙullu don kamar su ɗaya a wajen yin sa. Mata da maza suka fi yawan cin ɓula. A kowane ɓangare na ƙasar Hausa da wuya ka samu garin da ba a cin ɓula, kusan har yanzu ana cin sa.
Mahaɗin
Ɓula
i. Gero da Dawa koMasara da Maiwa
ii. Ruwa
Za a jiƙa gero da farko, wani lokaci kuma ana haɗawa
da masara da dawa. Bayan ya kwana za a kai markaɗen ƙullu.
Za a tace wannan markaɗe idan an dawo da shi. A gefe guda
kuwa, za a tafasa ruwa. Sannan a zuba wannan ƙullu ciki. Yayin da aka zuba ƙullu cikin tukunya, za a yi ta juyawa har sai ya yi
kauri. Wannan shi ake kira kafa. Sai
a lura sosai domin ba a so ya yi gudaji.
Za a sake ɗora wani ruwa bisa murhu daban a gefe a bar shi har sai
ya tafasa. Sai a riƙa ɗibar wannan kafa ta hanyar amfani da mara, za ana
mulmulawa sannan a nasa (sanya) cikin wannan ruwan zafi. A gefe kuwa, za a tanadi ruwan sanyi a wani babban
mazubi. Yayin da ɓulan ya nuna, zai taso saman ruwa. Sai a riƙa ɗauka
ana sanyawa cikin wannan ruwan sanyi da aka tanada. Yayin da aka cire waɗanda suka nuna, za a sake zuba ruwan sanyi a saman
tukunyar. Wannan ne zai sa ba zai ɓuɓɓule ba.
Tsokaci
Ɓula abin marmari ce sosai. Sannan abinci ne da yake daɗewa bai ɓaci ba. Bayan an dafa ɓula, ana iya ajiye shi na tsawon kwanaki. Yayin da za a
ajiye ɓula, cikin ruwan sanyi ake sakawa a
rufe. Abin da ake buƙata kawai shi
ne a riƙa sauya wannan ruwa. Ana cin ɓula
da miya ko a yi ɗatu da yajin ƙuli wani lokacin har da kayan lambu.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.