Soyayyen Dankali
Abubuwan da ake buƙata yayin soya dankali su ne:
i. Dankali
ii. Gishiri
iii. Mai
iv. Ruwa
v. Yaji
Da farko, za a fere dankali a wanke, sai a yanka shi ƙanana kamar yadda ake buƙata. Daga nan za a zuba gishiri a juya (gauraya) shi. A gefe guda kuwa, za a hura wuta a aza tukunya a saka mai a ciki tare da albasa. Cikin wannan mai za a riƙa soyawa. Akan ci wannan soyayyen dankali da yaji ko kuma da miya. Za a iya tafasa shi kafin a soya idan ana da buƙata.
Alkaki
Kayan haɗin alkaki su ne:
i. Alkama
ii. Ruwa
iii. Zuma ko maɗi
iv. Nono mai tsami
Za a samu alkama a fece a gyara ya a tashin farko. Daga nan za a raba ta gida biyu. Rabi za a niƙa, sauran rabin kuwa, ɓarzawa za a yi. Za a haɗa niƙaƙƙen garin da ɓarzajjen garin a kwaɓe su a cikin mazubi guda. Ana yin kwaɓin da tauri, wato ba ruwa-ruwa ba. Bayan kwaɓin ya samu yadda ake buƙata, sai a riƙa ɗebowa ana mulmulawa daidai gwargwadon buƙata. Daga nan za a lanƙwasa mulmulen ya koma a zagaye tamkar naɗaɗɗen kifi.[1] Sai kuma a saka shi cikin man gyaɗa a soya. Bayan ya soyu, za a bar shi ya sha iska, amma ba sosai ba. Za a ɗauko zuma ko maɗi a zuba saman alkakin ko’ina sai ya samu (ya nashe ko’ina a jikinsa). Yayin da ya bushe, zumar ko maɗin zai laƙe a jikinsa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.